Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 17 p. 46-p. 47 par. 2
  • Musa Ya Bauta wa Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Musa Ya Bauta wa Jehobah
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Aka Ceci Musa Yana Jariri
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Mugun Sarki Yana Sarauta A Masar
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Dalilin Da Ya Sa Musa Ya Gudu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Allah Ya Ceci ’Ya’yan Isra’ila
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 17 p. 46-p. 47 par. 2
’Yar Fir’auna ta sami jariri, Maryamu kuma ta buya a wani wuri tana kallon abin da yake faruwa

DARASI NA 17

Musa Ya Bauta wa Jehobah

Sa’ad da Yakubu da iyalinsa suke ƙasar Masar, an soma kiransu Isra’ilawa. Bayan da Yakubu da Yusufu suka mutu, wani Fir’auna ya soma sarauta. Ya ji tsoro cewa Isra’ilawa za su fi mutanen ƙasar Masar yawa. Sai wannan Fir’aunan ya sa Isra’ilawa suka zama bayi. Ya sa su dole su riƙa yin bulo da kuma aiki a gonakinsu. Amma cin zalin da mutanen ƙasar Masar suka yi musu bai hana su yin yawa ba. Da yake Fir’auna ba ya son su yi yawa, sai ya ce a riƙa kashe yara maza da aka haifa. Isra’ilawa sun ji tsoro sosai, ko ba haka ba?

Wata ’yar Isra’ila mai suna Jochebed ta haifi wani jariri mai kyaun gaske. Don kada a kashe shi, sai ta saka shi cikin kwando kuma ta ɓoye shi a ciyayin da ke bakin Kogin Nilu. Sai ’yar’uwar jaririn mai suna Maryamu ta tsaya a wurin don ta ga abin da zai faru da shi.

Da ’yar Fir’auna ta zo wanka a kogin, sai ta ga kwandon. Ta ga jariri a ciki yana kuka kuma ta ji tausayinsa. Sai Maryamu ta ce: ‘In nemo miki matar da za ta kula da shi?’ Sa’ad da ’yar Fir’auna ta yarda, sai Maryamu ta je ta kawo mahaifiyar jaririn, wato Jochebed. Sai ’yar Fir’auna ta ce: ‘Ki ɗauki wannan yaron, ki yi mini renonsa, zan ba ki kuɗi.’

Musa ya gudu

Da yaron ya girma, Jochebed ta kai shi wurin ’yar Fir’auna. Sai ’yar Fir’auna ta saka masa suna Musa kuma ya zama ɗanta. Musa ya zama yarima kuma zai iya samun duk abin da yake so. Amma bai manta da Jehobah ba. Ya san cewa asali shi ɗan ƙasar Isra’ila ne ba Masar ba. Saboda haka, ya yanke shawarar bauta wa Jehobah.

A lokacin da Musa ya kai shekara 40, sai ya ce yana son ya taimaka wa mutanensa. Da ya ga wani ɗan Masar yana wahalar da wani ɗan Isra’ila, sai ya kashe ɗan Masar ɗin. A lokacin da Fir’auna ya ji labarin, sai ya so ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu zuwa ƙasar Midiya. Kuma Jehobah ya kula da shi a wurin.

‘Ta wurin bangaskiya Musa . . . ya ƙi yarda a ce da shi ɗan ’yar Fir’auna; ya fi so a wulaƙanta shi tare da mutanen Allah.’​—Ibraniyawa 11:​24, 25

Tambayoyi: Mene ne mutanen ƙasar Masar suka yi wa Isra’ilawa? Me ya sa Musa ya gudu ya bar ƙasar Masar?

Farawa 49:33; Fitowa 1:​1-14, 22; 2:​1-15; Ayyukan Manzanni 7:​17-29; Ibraniyawa 11:​23-27

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba