Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 42 p. 102-p. 103 par. 3
  • Jonathan Mai Karfin Hali da Aminci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jonathan Mai Karfin Hali da Aminci
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Sun Kulla Abota ta Kwarai
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Jonathan​—“Babu Abin da Zai Iya Hana” Jehobah
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Ka Kasance da Aminci ga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Ci Gaba da Nuna Kauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 42 p. 102-p. 103 par. 3
Jonathan da kuma mai rike masa kayan yaki

DARASI NA 42

Jonathan Mai Ƙarfin Hali da Aminci

Jonathan ne babba cikin yaran Sarki Saul kuma shi soja ne mai ƙarfin hali sosai. Dauda ya ce Jonathan ya fi gaggafa sauri kuma ya fi zaki ƙarfi. Wata rana, Jonathan ya ga wasu Filistiyawa a kan wani tudu. Sai ya gaya wa mai riƙe masa kayan yaƙi cewa: ‘Sai Jehobah ya nuna alama kafin za mu kai musu hari. Idan Filistiyawan sun ce mu zo, sai mu kai musu hari.’ Filistiyawan suka yi ihu suka ce: ‘Ku zo mu yi faɗa!’ Sai mazan biyu suka hau kan tudun kuma suka kashe sojoji guda 20.

Jonathan ya ba wa Dauda wasu abubuwansa

Tun da Jonathan ne babba a cikin yaran Saul, shi ne ya kamata ya zama sarki bayan babansa. Amma Jonathan ya san cewa Jehobah ya zaɓi Dauda ya zama sarkin Isra’ila kuma bai yi kishin Dauda ba. Jonathan da Dauda sun zama abokai. Sun yi alkawari cewa za su taimaka wa juna. Har ma Jonathan ya ba Dauda rigarsa da doguwar wuƙarsa da bakansa da kuma ɗamararsa don ya nuna irin abokantakar da ke tsakaninsu.

Sa’ad da Dauda ya gudu don Saul yana nema ya kashe shi, Jonathan ya je wurinsa kuma ya ce masa: ‘Ka kasance da ƙarfin zuciya. Jehobah ya riga ya zaɓe ka ka zama sarki. Kuma babana ma ya san da hakan.’ Shin za ka so ka sami aboki kamar Jonathan?

Sau da yawa, Jonathan ya sadaukar da ransa don ya ceci abokinsa. Ya san cewa Sarki Saul yana so ya kashe Dauda. Don haka, ya gaya wa mahaifinsa cewa: ‘Za ka yi zunubi idan ka kashe Dauda domin bai yi wani laifi ba.’ Saul ya yi fushi da Jonathan sosai. Bayan wasu shekaru, sai aka kashe Saul da kuma Jonathan a yaƙi.

Bayan Jonathan ya mutu, sai Dauda ya nemi ɗan Jonathan mai suna Mephibosheth. Da Dauda ya same shi, sai ya ce wa Mephibosheth: ‘Mahaifinka abokina ne sosai. Don haka, zan kula da kai har ƙarshen ranka. Za ka zauna a fādata kuma ka ci abincin da nake ci.’ Hakika, Dauda bai taɓa manta da abokinsa Jonathan ba.

“Ku yi ƙaunar juna, kamar yadda ni na ƙaunace ku. Ba wanda yake da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, wato mutum ya ba da ransa domin abokansa.”​—Yohanna 15:​12, 13

Tambayoyi: Ta yaya Jonathan ya nuna cewa shi mai ƙarfin hali ne? Ta yaya Jonathan ya nuna cewa shi mai aminci ne?

1 Sama’ila 14:​1-23; 18:​1-4; 19:​1-6; 20:​32-42; 23:​16-18; 31:​1-7; 2 Sama’ila 1:23; 9:​1-13

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba