Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 69 p. 164-p. 165 par. 2
  • Mala’ika Jibra’ilu Ya Ziyarci Maryamu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mala’ika Jibra’ilu Ya Ziyarci Maryamu
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Mala’ika Ya Ziyarci Maryamu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 69 p. 164-p. 165 par. 2
Mala’ika Jibra’ilu Ya bayyana wa Maryamu

DARASI NA 69

Mala’ika Jibra’ilu Ya Ziyarci Maryamu

Wani mala’ika ya bayyana wa Yusufu a cikin mafarki

Alisabatu tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu da ke zama a Galili a birnin Nazarat. Maryamu ce Yusufu yake so ya aura kuma shi kafinta ne. Sa’ad da cikin Alisabatu ya kai wata shida, sai mala’ika Jibra’ilu ya zo wurin Maryamu. Ya ce: ‘Barka da war haka Maryamu. Jehobah ya albarkace ki sosai.’ Amma ba ta gane abin da Jibra’ilu ya ce ba. Sai ya ce mata: ‘Za ki yi juna biyu kuma za ki haifi ɗa, kuma za ki kira shi Yesu. Zai zama sarki. Zai yi sarauta har abada.’

Sai Maryamu ta ce: ‘Ta yaya zan iya haifan ɗa tun da yake ban san namiji ba?’ Jibra’ilu ya ce: ‘Ba abin da Allah ba zai iya yi ba. Ruhu mai tsarki zai sauko miki kuma za ki haifi ɗa. ’Yar’uwarki Alisabatu ita ma tana da juna biyu.’ Sai Maryamu ta ce: ‘Ni baiwar Jehobah ce. Kamar yadda ka ce, bari ya kasance haka.’

Yusufu ya yarda ya dauki Maryamu wanda take da juna biyu a matsayin matarsa

Maryamu ta je wurin Alisabatu. Da Maryamu ta gaishe ta, sai yaron da ke cikin Alisabatu ya yi motsi. Cike da ruhu mai tsarki, sai ta ce: ‘Jehobah ya albarkace ki Maryamu. Ina farin cikin marabtar mahaifiyar Almasihu zuwa gidana.’ Sai Maryamu ta ce: ‘Ina yabon Jehobah da dukan zuciyata.’ Maryamu ta yi wata uku a gidan Alisabatu, bayan haka, sai ta koma Nazarat.

Yusufu ya so ya saki Maryamu sa’ad da ya ji cewa tana da juna biyu domin ya yi zato cewa wani ne ya yi mata ciki. Amma wani mala’ika ya bayyana masa a mafarki kuma ya ce masa: ‘Kada ka ƙi auran ta. Ba ta yi wani laifi ba.’ Sai Yusufu ya auri Maryamu.

“Ko mene ne da Ubangiji ya ga dama, hakanan ya yi, cikin sama da ƙasa.”​—Zabura 135:6

Tambayoyi: Mene ne Jibra’ilu ya gaya wa Maryamu game da ɗanta? Yaya Alisabatu da Maryamu suka ji game da abin da ya faru da su?

Matta 1:​18-25; Luka 1:​26-56; Ishaya 7:14; 9:7; Daniyel 2:44; Galatiyawa 4:4

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba