Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 90 p. 210
  • Yesu Ya Mutu a Golgota

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Ya Mutu a Golgota
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • An Kashe Yesu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Ya Sa Za Mu Kaunaci Yesu
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Menene Mulkin Allah? Yadda Za Mu Nuna Muna Son Shi
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 90 p. 210
Sa’ad da aka rataye Yesu a kan gungume, wani sojan Roma da wasu mabiyan Yesu, har da Maryamu da Yohanna sun tsaya kusa

DARASI NA 90

Yesu Ya Mutu a Golgota

Manyan firistoci sun kai Yesu wurin gwamna mai suna Bilatus. Sai Bilatus ya tambaye su: ‘Mene ne kuke zargin sa da shi?’ Suka ce: ‘Ya ce shi Sarki ne!’ Bilatus ya tambayi Yesu: “Kai Sarkin Yahudawa ne?” Yesu ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.”

Sa’an nan Bilatus ya tura shi wurin Hiridus wanda shi ne mai mulkin Galili don ya bincike shi ko yana da laifi. Hiridus bai same shi da laifi ba, sai ya sake tura shi wurin Bilatus. Sai Bilatus ya ce wa mutanen: ‘Ni da Hiridus ba mu sami mutumin nan da laifi ba. Don haka, zan sake shi.’ Mutanen suka yi ihu suna cewa: ‘A kashe shi! A kashe shi!’ Sojojin suka yi wa Yesu bulala, suka tofa masa yau kuma suka buge shi. Sun saka masa rawanin kaya kuma suna cewa: ‘Barka dai Sarkin Yahudawa.’ Bilatus ya sake ce wa mutanen: ‘Ban sami mutumin nan da laifi ba.’ Suka yi ihu suna cewa: ‘A rataye shi a kan gungume!’ Sai Bilatus ya ba da shi don a kashe shi.

Sojojin sun kai Yesu wani wuri da ake kira Golgota, suka kafa masa ƙusa a kan gungume, sai suka ɗaga gungumen sama. Yesu ya yi addu’a ya ce: ‘Ya Uba, ka gafarce su don ba su san abin da suke yi ba.’ Mutanen sun yi ma Yesu dariya, suna cewa: ‘Idan kai Ɗan Allah ne, ka sauko daga kan gungumen! Ka ceci kanka.’

Ɗaya daga cikin ɓarayin da ke gefensa ya ce: “Ka tuna da ni lokacin da ka soma Mulkinka.” Yesu ya yi masa alkawari cewa: ‘Za ka kasance tare da ni cikin Aljanna.’ Da rana, sai gari ya yi duhu har sa’o’i uku. Wasu daga cikin mabiyan Yesu sun tsaya kusa da gungumen, har da Maryamu mahaifiyar Yesu. Yesu ya ce wa Yohanna ya kula da Maryamu kamar yadda yake kula da mamarsa.

Sai Yesu ya ce: “Ya cika!” Ya sunkuyar da kansa kuma ya ja numfashi na ƙarshe. Nan take, sai aka yi girgizar ƙasa. A cikin haikali kuma babban labule da ya raba wuri mai tsarki da mafi tsarki ya tsage. Wani soja ya ce: ‘Hakika, wannan Ɗan Allah ne.’

“Gama ta wurinsa ne Allah ya cika dukan alkawuran da ya yi.”​—2 Korintiyawa 1:​20, Juyi Mai Fitar da Ma’ana

Tambayoyi: Me ya sa Bilatus ya ƙyale a kashe Yesu? Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya fi damuwa da mutane fiye da kansa?

Matta 27:​11-14, 22-31, 38-56; Markus 15:​2-5, 12-18, 25, 29-33, 37-39; Luka 23:​1-25, 32-49; Yohanna 18:28–19:30

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba