WAƘA TA 3
Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
Hoto
	(Misalai 14:26)
- 1. Ya Jehobah, ka ba mu bege, - bege mai tamani. - Mun gode don wannan begen, - muna yin shelar sa. - Amma matsalolin rayuwa - na iya sa mu gaji, - Kuma mu daina yin ƙwazo - a yin hidimarka. - (AMSHI) - Ƙarfinmu, begenmu, - makiyayinmu, - Kana biyan bukatunmu. - Muna yin wa’azi - da gaba gaɗi - don muna dogara da kai. 
- 2. Ya Jehobah ka taimake mu, - mu riƙa tunawa - da dukan alkawuranka - lokacin wahala. - Kuma dukan alkawuranka - za su sa mu yi ƙwazo, - Domin za su ƙarfafa mu - mu yi shela sosai. - (AMSHI) - Ƙarfinmu, begenmu, - makiyayinmu, - Kana biyan bukatunmu. - Muna yin wa’azi - da gaba gaɗi - don muna dogara da kai. 
(Ka kuma duba Zab. 72:13, 14; Mis. 3:5, 6, 26; Irm. 17:7.)