WAƘA TA 18
Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu
Hoto
	- 1. Allah Jehobah yau, - muna a gabanka, - Don ka nuna mana ƙaunar - da ba kamarta. - Ka aiko da Ɗanka Yesu - don mu rayu. - Babu wata sadaukarwar - da ta kai wannan. - (AMSHI) - Ya ba da ransa dominmu. - Ya yi hakan da jininsa. - Har abada - za mu riƙa yi maka godiya. 
- 2. Yesu ya yi sadaukarwar - da son ransa. - Ya ba da ransa domin - yana ƙauna sosai. - Yanzu muna da bege don - ya cece mu. - Muna da begen yin rayuwa - har abada. - (AMSHI) - Ya ba da ransa dominmu. - Ya yi hakan da jininsa. - Har abada - za mu riƙa yi maka godiya. 
(Ka kuma duba Ibran. 9:13, 14; 1 Bit. 1:18, 19.)