WAƘA TA 92
Wurin da Muka Gina Don Sunanka
Hoto
	(1 Labarbaru 29:16)
- 1. Gata ne babba, ya Jehobah, - Mu gina maka gidan nan! - Muna miƙa maka shi duka - Domin a yabe ka sosai. - Dukan abin da muka ba ka, - Ai naka ne tun asali. - Kuzarinmu da dukiyarmu, - Mun miƙa su, Ya Jehobah. - (AMSHI) - Yanzu bari mu miƙa ma, - Gidan nan don ibada. - Mun keɓe maka gidan nan, - Ya Uba ka karɓe shi. 
- 2. Bari mu ɗaukaka Jehobah, - Don ikonsa da ƙaunarsa. - Muna roƙo ka ji addu’ar - Masu so su san Kalmarka. - Kai muka gina wa gidan nan, - Duk za mu kula da gidan. - Mun san cewa zai ba da Shaida - Ga sunanka, Ya Jehobah. - (AMSHI) - Yanzu bari mu miƙa ma, - Gidan nan don ibada. - Mun keɓe maka gidan nan, - Ya Uba ka karɓe shi. 
(Ka kuma duba 1 Sar. 8:18, 27; 1 Laba. 29:11-14; A. M. 20:24.)