WAƘA TA 116
Muhimmancin Yin Alheri
Hoto
(Afisawa 4:32)
1. Jehobah muna yabon ka sosai
Da dukan zucinmu,
Domin kirkinka da alherinka,
Duk da kai Maɗaukaki ne.
2. Ubangijinmu yana tausaya
Wa duk gajiyayyu.
Ƙaunarsa da kuma alherinsa
Suna sanyaya zuciya.
3. Jehobah Allah da Yesu Kristi
Suna yin alheri.
Yin koyi da su zai sa mu zama
Masu alheri da jinƙai!
(Ka kuma duba Mik. 6:8; Mat. 11:28-30; Kol. 3:12; 1 Bit. 2:3.)