WAƘA TA 145
Allah Ya Yi Mana Alkawarin Aljanna
Hoto
(Ru’ya ta Yohanna 21:4)
1. Allah zai dawo da aljanna
Ta sarautar Yesu Kristi.
Zai kawar da dukan zunubi
Da mutuwa da azaba.
(AMSHI)
Yin rayuwa a Aljanna,
A duniya zai yi daɗi.
Allah zai sa Ɗansa Yesu,
Ya cika alkawuran nan.
2. A aljanna Jehobah zai sa
Ɗansa ya ta da matattu.
Yesu ya ce: ‘Za ka kasance
Tare da ni a Aljanna.’
(AMSHI)
Yin rayuwa a Aljanna,
A duniya zai yi daɗi.
Allah zai sa Ɗansa Yesu,
Ya cika alkawuran nan.
3. Yesu Kristi ne Sarkin Mulkin,
Shi ne Sarkin da ya dace.
Muna murna don albarkun nan,
Muna yabon Jehobah fa.
(AMSHI)
Yin rayuwa a Aljanna,
A duniya zai yi daɗi.
Allah zai sa Ɗansa Yesu,
Ya cika alkawuran nan.
(Ka kuma duba Mat. 5:5; 6:10; Yoh. 5:28, 29.)