Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • CO-pgm20 pp. 7-8
  • Bayani ga Wadanda Suka Halarci Taron

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bayani ga Wadanda Suka Halarci Taron
  • Tsarin Ayyuka na Taron Yanki na 2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TARO NA MUSAMMAN
  • Bayani ga Wadanda Suka Halarci Taron
    Tsarin Ayyuka Taron Yanki na 2024
  • Bayani ga Waɗanda suka Halarci Taron
    Tsarin Ayyuka na Taron Yanki na 2019
  • Bayani ga Wadanda Suka Halarci Taron
    Tsarin Ayyuka Taron Yanki na 2025
  • Bayani ga Waɗanda Suka Halarci Taron
    Tsarin Ayyuka na Taron Yanki na 2018
Dubi Ƙari
Tsarin Ayyuka na Taron Yanki na 2020
CO-pgm20 pp. 7-8

Bayani ga Waɗanda Suka Halarci Taron

BAFTISMA Za a keɓe wurin zama kusa da dakalin magana don waɗanda za su yi baftisma, idan ba a shirya wani wuri dabam ba. Waɗanda za su yi baftisma su zauna a wurin kafin a soma jawabin baftisma a ranar Asabar da safe. Kowa ya zo da tawul nasa da kuma rigar da ta dace don yin baftisma.

GUDUMMAWA An kashe kuɗi sosai don shirya wurin taron nan, da sauti, da na’urorin nuna bidiyo, da wasu abubuwa da suke sa mu ji daɗin taron yankinmu kuma mu daɗa kusantar Jehobah. Gudummawarku za ta taimaka wajen biyan waɗannan bukatun, kuma za ta taimaka wa wa’azin da ake yi a dukan duniya. An saka akwatunan gudummawa a wurare dabam-dabam a majami’ar nan don ya yi muku sauƙi ku ba da gudummawarku. Ƙari ga haka, za ku iya ba da gudummawarku ta intane a dandalin donate.jw.org/⁠ha. Muna matuƙar godiya don gudummawar da kuke bayarwa. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana alfahari da yadda kuke ba da gudummawa saboda hidimar Mulkin Allah ta sami ci gaba.

HIDIMAR BA DA KAI Idan kana so ka taimaka da wasu ayyukan da ake yi a wannan taron, ka je Sashen Samun Bayanai da Ayyuka.

JINYAR GAGGAWA Don Allah ka tuna cewa wannan wurin jinyar gaggawa ce kawai.

MATATTARIN TSINTUWA A kai dukan kayayyaki da aka tsinta Sashen Matattarin Tsintuwa. Idan ka ɓatar da wani abu, ka je wannan sashen ka neme shi. A kai yaran da suka ɓace zuwa wannan sashen. Amma muna roƙonku ku riƙa kula da ’ya’yanku, kuma ku tabbata cewa suna tare da ku, don kada su ɓata.

TSARIN ZAMA Don Allah ku tuna cewa waɗanda za ku iya kama musu wurin zama su ne, iyalinku, da waɗanda kuke tafiya tare a cikin mota, da waɗanda kuke zama a gida ɗaya, da kuma waɗanda kuke nazari da su. Kada ku ajiye abubuwa a kan kujerun da ba ku kama ba don wasu su sami wurin zama.

’YAN ATENDA Aikin da aka sa ’yan atenda shi ne, su taimaka muku. Don haka, muna roƙonku ku bi umurnin da suka ba ku game da faka motoci, da shiga da fita daga wurin taro, da kama kujera da dai makamantansu.

TARO NA MUSAMMAN

Wata Mashaidiya tana ma wata mata wa’azi.

Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki Majagaban da ke tsakanin shekaru 23 da 65 da suke so su faɗaɗa hidimarsu, su halarci taron da za a yi don Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki a ranar Lahadi da rana. Za a sanar da ainihin lokaci da kuma wurin da za a yi wannan taron.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce ta shirya wannan taron

© 2020 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba