Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 29
  • Me Ke Faruwa Sa’ad da Muka Mutu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ke Faruwa Sa’ad da Muka Mutu?
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Ina Matattu Suke?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Wane Bege Ne Matattu Suke da Shi?
    Albishiri Daga Allah!
  • Me Ke Faruwa da Mutum Sa’ad da Ya Mutu?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Me Ke Faruwa Bayan Mutuwa?
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 29
Darasi na 29. Mata da miji suna addu’a a gaban wani dutse a makabarta.

DARASI NA 29

Me Ke Faruwa Sa’ad da Muka Mutu?

Hoto
Hoto
Hoto

Wani naka ya taɓa rasuwa? A lokacin, za ka iya yin tunani cewa: ‘Me yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu? Za mu sake ganin waɗanda suka rasu kuwa?’ A wannan darasin da kuma na gaba, za mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da batun nan.

1. Me ke faruwa sa’ad da muka mutu?

Yesu ya ce mutuwa tana kama da barci mai zurfi. Mutumin da yake barci mai zurfi bai san abin da ke faruwa kusa da shi ba. Ta yaya mutuwa take kama da barci? Idan mutum ya mutu, ba ya jin zafin kome. Ko da yana ƙaunar abokansa da iyalinsa kafin ya rasu, ba ya fama da kaɗaici. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Matattu ba su san kome ba.”​—Karanta Mai-Wa’azi 9:5.

2. Ta yaya sanin gaskiya game da mutuwa take taimaka mana?

Mutane da yawa suna jin tsoron mutuwa da kuma matattu! Amma abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da mutuwa zai ƙarfafa ka. Yesu ya ce: “Gaskiyar kuwa za ta ba ku ’yanci.” (Yohanna 8:32) Wasu addinai suna koyar da cewa idan mutum ya mutu, akwai abin da ke fita daga jikinsa ya ci gaba da rayuwa a wani wuri, amma ba abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ba ke nan. Kuma ba wanda yake shan wahala bayan ya mutu. Da yake matattu ba su san kome ba, ba za su iya mana mugunta ba. Don haka, ba ma bukatar mu bauta wa matattu ko mu yi wasu abubuwa don kada su yi fushi da mu. Kuma ba ma bukatar mu yi addu’a a madadinsu.

Wasu mutane sun ce za su iya magana da matattu. Amma hakan ba zai yiwu ba. Kuma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, matattu “ba su san kome ba.” Waɗanda suke ganin suna iya magana da matattu, suna magana ne da aljannu da suke yi kamar su ne mutanen da suka mutu. Don haka, sanin gaskiya game da matattu zai kāre mu daga aljannu. Jehobah ya gargaɗe mu kada mu kuskura mu yi magana da matattu don ya san cewa yin ma’amala da aljannu yana da haɗari.​—Karanta Maimaitawar Shari’a 18:​10-12.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da mutuwa, kuma hakan zai ƙarfafa bangaskiyarka ga Allah mai ƙauna da ba ya gana wa waɗanda suka mutu azaba.

Wani mutum da yaransa biyu suna zaune a kan benci sa’ad da ake binne matarsa. Abokai da danginsu sun taru suna ta’azantar da su kuma suna taimaka musu.

3. Ainihin abin da yake faruwa da matattu

A faɗin duniya, mutane suna da ra’ayi dabam-dabam game da abin da ke faruwa da mu bayan mun mutu. Babu shakka, ba dukan ra’ayoyin nan ba ne gaskiya.

  • Waɗanne ra’ayoyi ne mutane suke da su a yankinku game da matattu?

Don ku ga abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar, ku kalli BIDIYON nan.

BIDIYO: Wane Yanayi Ne Matattu Suke Ciki?​—Gajeren Bidiyo (1:19)

Hotuna: Hotuna daga bidiyon ‘Wane Yanayi Ne Matattu Suke Ciki?’​—Gajeren bidiyo.’ 1. Gawa a gadon asibiti. 2. Wani mutum yana zaune a tsakanin mutane biyu yana barci sa’ad da suke tafiya a jirgin kasa.

Ku karanta Mai-Wa’azi 3:​20, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kamar yadda ayar nan ta nuna, mene ne ke faruwa sa’ad da mutum ya mutu?

  • Akwai abin da ke ci gaba da rayuwa bayan mutum ya mutu?

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wani aminin Yesu mai suna Li’azaru. Yayin da kuke karanta Yohanna 11:​11-14, ku yi la’akari da abin da Yesu ya faɗa game da yanayin da Li’azaru yake ciki. Sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Da mene ne Yesu ya kwatanta mutuwa?

  • Me hakan ya nuna mana game da yanayin matattu?

  • Mene ne ra’ayinka a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da mutuwa?

4. Sanin gaskiya game da mutuwa yana taimaka mana

Idan muka san gaskiya game da mutuwa, ba za mu riƙa jin tsoron matattu ba. Ku karanta Mai-Wa’azi 9:​10, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Matattu za su iya mana mugunta ne?

Idan mun gaskata da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, ba za mu yarda da ƙaryar nan cewa wajibi ne mu kwantar da hankalin matattu ko kuma mu bauta musu ba. Ku karanta Ishaya 8:19 da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:​11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Yaya kake ganin Jehobah yake ji game da mutanen da ke bauta wa matattu ko suke neman taimakonsu?

Hotuna: Al’adu da ake daukaka matattu. 1. Wani mutum ya durkusa yana addu’a a gaban kabari kuma yana ba da hadayar abinci. 2. Mutane uku da suke rawan al’adarsu. 3. Wasu mutane sun yi layi sun rufe fuska da wani abu kuma suna dauke da kwarangwal a Ranar Tuna da Matattu.

Sanin gaskiya game da mutuwa yana ’yantar da mu daga al’adun da suke ɓata ran Jehobah

5. Sanin gaskiya game da mutuwa yana ta’azantar da mu

An koya wa mutane da yawa cewa idan suka mutu, za a yi musu hukunci don abubuwa marasa kyau da suka yi a dā. Amma abin farin ciki ne sanin cewa ba wanda yake shan wahala bayan ya mutu, ko da shi mugu ne sosai. Ku karanta Romawa 6:​7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Littafi Mai Tsarki ya ce idan mutum ya mutu, Allah ba zai kama shi da alhakin zunubansa ba. To, kana ganin mutumin da ya mutu yana shan wahala don zunuban da ya yi a dā ne?

Yayin da muke ƙara sanin Jehobah, hakan zai sa mu san cewa ba zai taɓa azabtar da waɗanda suka mutu ba. Ku karanta Maimaitawar Shari’a 32:4 da 1 Yohanna 4:​8, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Allah mai halaye masu kyau da aka ambata a ayoyin nan, zai taɓa azabtar da mutanen da suka mutu ne?

  • Shin sanin gaskiya game da matattu yana ta’azantar da kai? Me ya sa?

WASU SUN CE: “Ina tsoron wanda ya mutu domin zai iya dawowa ya yi min mugunta.”

  • Waɗanne nassosi ne za ka iya karanta wa mutumin da za su ƙarfafa shi?

TAƘAITAWA

Idan mutum ya mutu, ya daina wanzuwa. Matattu ba sa shan wahala kuma ba sa yi wa masu rai mugunta.

Bita

  • Mene ne ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu?

  • Ta yaya sanin gaskiya game da mutuwa yake taimaka mana?

  • Ta yaya sanin gaskiya game da mutuwa yake ta’azantar da mu?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga ko Littafi Mai Tsarki ya ce akwai abin da ke fita daga jikin mutum kuma ya ci gaba da rayuwa bayan mutumin ya mutu.

“Mene ne Ran Ɗan Adam?” (Talifin jw.org, English)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga ko Allah yana ƙona mutane a gidan wuta.

Da Gaske Za A Ƙona Mutane a Gidan Wuta? (3:07)

Ku karanta ƙasidar nan don ku ga abin da ya sa bai kamata mu ji tsoron matattu ba.

Ruhohin Matattu​—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske? (ƙasida)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wani mutum ya sami ta’aziyya bayan ya koyi gaskiya game da abin da ke faruwa sa’ad da muka mutu.

“Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Amsa Tambayoyina Ya Burge Ni” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Fabrairu, 2015)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba