Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 31
  • Mene ne Mulkin Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Mulkin Allah?
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Abin da Mulkin Allah Zai Yi
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Mene Ne Mulkin Allah?
    Albishiri Daga Allah!
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 31
Darasi na 31. Yesu Kristi a matsayinsa na Sarki yana tsaye a gaban daukakar Jehobah.

DARASI NA 31

Mene ne Mulkin Allah?

Hoto
Hoto
Hoto

Saƙo mafi muhimmanci da ke Littafi Mai Tsarki shi ne game da Mulkin Allah. Jehobah zai yi amfani da Mulkin don ya mai da duniya ta zama aljanna. Mene ne Mulkin Allah? Ta yaya muka san cewa ya soma sarauta? Mene ne ya riga ya cim ma? Kuma me zai yi mana a nan gaba? Darasin nan da kuma biyu da ke gaba za su amsa tambayoyin nan.

1. Mene ne Mulkin Allah, kuma waye ne Sarkin?

Mulkin Allah gwamnati ce da Jehobah ya kafa. Sarkin Mulkin, wato Yesu Kristi zai yi sarauta daga sama. (Matiyu 4:17; Yohanna 18:36) Littafi Mai Tsarki ya ce: Yesu “zai yi mulki . . . har abada.” (Luka 1:​32, 33) Yesu Sarkin Mulkin Allah, zai yi sarauta bisa dukan duniya.

2. Su wane ne za su yi mulki tare da Yesu?

Yesu ba zai yi sarauta shi kaɗai ba. Mutane daga “kowace zuriya, da yare, da kabila, da al’umma . . . za su kuma yi mulki a kan duniya.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:​9, 10) Mutane nawa ne za su yi mulki tare da Yesu? Miliyoyin mutane sun zama mabiyan Yesu tun lokacin da ya zo duniya har wa yau, amma mutane 144,000 ne kawai za su yi mulki tare da Yesu a sama. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:​1-4.) Sauran Kiristoci za su yi rayuwa a duniya.​—Zabura 37:29.

3. Me ya sa Mulkin Allah ya fi gwamnatin ’yan Adam?

Ko da yake masu mulki za su so s yi iya ƙoƙarinsu wajen yin abubuwa masu kyau, ba su da ikon yin dukan abubuwan da suke so su yi. A kwana a tashi, wasu za su karɓi mulkin, ƙila masu son kai ne da ba sa tausayin talakawansu. Amma babu wanda zai karɓi mulki daga wurin Sarkin Mulkin Allah, wato Yesu. Domin Allah ya kafa “mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba.” (Daniyel 2:44) Yesu zai yi sarauta bisa dukan duniya, kuma ba zai nuna son kai ba. Shi mai ƙauna da alheri da adalci ne, kuma zai koya wa mutane su riƙa nuna wa juna ƙauna da alheri da kuma adalci.​—Karanta Ishaya 11:9.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga abin da ya sa Mulkin Allah ya fi duk wani gwamnatin ’yan Adam.

Yesu Kristi yana sarauta bisa duniya daga sama. Masu sarauta tare da shi suna zaune a bayansa. Daukakar Jehobah tana haskakawa a bayansu.

4. Mulkin Allah zai yi sarauta bisa duniya

Yesu Kristi yana da ikon yin mulki fiye da duk wani da ya taɓa mulki. Ku karanta Matiyu 28:​18, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane bambanci ne yake tsakanin sarautar Yesu da na ’yan Adam?

Akan canja gwamnatocin ’yan Adam yau da kullum, kuma kowannensu yana mulki bisa wata ƙasa. Amma Mulkin Allah kuma fa? Ku karanta Daniyel 7:​14, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Tun da “ba za a taɓa halaka” Mulkin Allah ba, hakan ya burge ka kuwa? Me ya sa?

  • Ta yaya za mu amfana idan Mulkin Allah ya soma sarauta bisa duniya?

5. Wajibi ne a canja gwamnatocin ’yan Adam

Me ya sa Mulkin Allah zai sauya na ’yan Adam? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: Mene ne Mulkin Allah?​—Gajeren Bidiyo (1:​41)

  • Mene ne sakamakon sarautar ’yan Adam?

Ku karanta Mai-Wa’azi 8:​9, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana ganin ya kamata Mulkin Allah ya sauya na ’yan Adam ne? Me ya sa?

6. Waɗanda za su yi sarauta a Mulkin Allah sun san yanayinmu

Sarkinmu Yesu ya taɓa rayuwa a duniya, don haka, ya san “kasawarmu.” (Ibraniyawa 4:15) Mata da maza 144,000 da Jehobah ya zaɓa don su yi mulki da Yesu, sun fito ne “daga kowace zuriya, da yare, da kabila, da al’umma.”​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:9.

  • Da yake Yesu da abokan mulkinsa sun san matsalolin da muke fuskanta, hakan ya ƙarfafa ka kuwa? Me ya sa?

Shafaffu maza da mata daga lokatai da wurare dabam-dabam.

Jehobah ya zaɓi maza da mata da suka fito daga wurare dabam-dabam su yi mulki tare da Yesu

7. Dokokin Mulkin Allah sun fi na ’yan Adam

Gwamnatocin ’yan Adam suna kafa dokokin da suke ganin za su taimaka wa mutane da kuma kāre su. A Mulkin Allah ma akwai dokokin da wajibi ne talakawan mulkin su bi. Ku karanta 1 Korintiyawa 6:​9-11, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ya kake ganin duniya za ta kasance a lokacin da kowa zai riƙa bin dokokin Allah?a

  • Kana ganin yadda Jehobah ya ce talakawan Mulkinsa su riƙa bin dokokinsa ya dace? Me ya sa?

  • Me ya nuna cewa mutanen da ba sa bin dokokin Allah za su iya canjawa?​—Ka duba aya ta 11.

Wani dan sanda yana tsai da motoci a wata mararraba. Mutane masu shekaru dabam-dabam suna tafiya a kan titi.

Gwamnatocin ’yan Adam suna kafa dokokin da suke ganin za su taimaka wa mutane da kuma kāre su. Mulkin Allah yana da dokokin da suka fi amfana da kuma kāre talakawansa

WANI YANA IYA CEWA: “Mene ne Mulkin Allah?”

  • Me za ka ce wa mutumin?

TAƘAITAWA

Mulkin Allah gwamnati ce da aka kafa a sama kuma za ta yi mulki bisa dukan duniya.

Bita

  • Su waye ne za su yi sarauta a Mulkin Allah?

  • A wace hanya ce Mulkin Allah ya fi na ’yan Adam?

  • Waɗanne abubuwa ne Jehobah yake so talakawan Mulkinsa su yi?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga wurin da Yesu ya ce Mulkin Allah yake.

“Shin Mulkin Allah a Zuciyarka Yake?” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga dalilin da ya sa Shaidun Jehobah suka zaɓi su riƙe amincinsu ga Mulkin Allah maimakon na ’yan Adam.

Sun Goyi Bayan Mulkin Allah (1:43)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutane 144,000 da Jehobah ya zaɓa don su yi mulki tare da Yesu.

“Su Waye Za Su Je Sama?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya tabbatar ma wata mata da ke kurkuku cewa Allah zai sa a daina rashin adalci a duniya.

“Yadda Na Sami Amsa Game da Rashin Adalci” (Awake!, Nuwamba 2011, English)

a Za a tattauna wasu daga cikin dokokin nan a Sashe na 3.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba