Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 3/1 pp. 19-24
  • Jehovah—Mai Ƙarfi Cikin Iko

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehovah—Mai Ƙarfi Cikin Iko
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ikon Allah Yana Bayyane Cikin Halitta
  • ‘Jehovah Mai Runduna, Mai Iko’
  • Jehovah Ya Bayyana Ikonsa Ma Bayinsa
  • Ikon Jehovah Ya Ba da Tabbaci na Cikar Alkawuransa
  • Jehobah “Mai Girma Ne”
    Ka Kusaci Jehobah
  • ‘Ka Biɗi Jehovah Da Kuma Ƙarfinsa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • “Almasihu Shi Ikon Allah” Ne
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Ku Ɗauki Misali Daga Wurin Allah” Wajen Amfani da Iko
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 3/1 pp. 19-24

Jehovah—Mai Ƙarfi Cikin Iko

“Bisa ga girman ikonsa, domin shi mai-ƙarfi ne cikin iko, ba wanda ba shi ko ɗaya.”—ISHAYA 40:26.

1, 2. (a) Akan wane tushen ƙarfi na zahiri dukanmu muka dangana? (b) Ka bayyana abin da ya sa Jehovah shi ne Tushe mafi girma na iko duka.

ƘARFI abu ne da yawancinmu muke ɗauka da rashin muhimmanci. Alal misali, da kyar mu kula da ƙarfin wutar lantarki da ke ba mu haske da kuma zafi ko kuma damar saka fulogi cikin wani abin da muke da shi da ke aiki da lantarki. Sai lokacin da aka ɗauke wuta muke gane cewa in ban da ita, biranen ’yan Adam za su daina aiki. Yawancin wutan lantarki da muke amfani da su sun zo ne daga matabbacin tushen ƙarfi na duniya—rana.a Kowace daƙiƙa wannan ƙarfin rana yana cin tan miliyan biyar na ƙarfi irin na nukiliya, yana ba ma duniya zafi da ke kiyaye rayuka.

2 Daga ina ne duk wannan ƙarfi na rana ya fito? Wanene ya gina wannan ƙarfin rana na samaniya? Jehovah Allah ne. Game da shi, Zabura 74:16 ya ce: “Kai ne ka shirya haske da rana.” I, Jehovah ne Tushe mafi girma na dukan iko, kamar yadda shi ne Tushe na rai duka. (Zabura 36:9) Bai kamata mu ɗauki ikonsa da rashin muhimmanci ba. Ta wurin annabi Ishaya, Jehovah ya tunatar mana mu duba halittu na sama, irin su rana da kuma taurari, kuma mu yi bimbini akan yadda suka soma wanzuwa. “Ku tada idanunku sama, ku duba ko wanene ya halicci waɗannan, wanda ya kawo rundunansu bisa ga lissafinsu: yana kiransu duka da sunansu; bisa ga girman ikonsa, domin shi mai-ƙarfi ne cikin iko, ba wanda ba shi ko ɗaya.”—Ishaya 40:26; Irmiya 32:17.

3. Ta yaya muke amfana daga nuni na ikon Jehovah?

3 Tun da shi ke Jehovah mai ƙarfi ne cikin iko, za mu kasance da gabagaɗi cewa rana za ta ci gaba da ba mu haske da ɗumi, abin da rayukanmu suka dangana akai. Amma, mun dangana ga ikon Allah ba kawai don bukatunmu na jiki ba. Fansarmu daga zunubi da mutuwa, begenmu na nan gaba, da kuma dogararmu ga Jehovah duk sun haɗu cikin nuna ikonsa. (Zabura 28:6-9; Ishaya 50:2) Littafi Mai-Tsarki na cike da misalai da sun tabbatar da ikon Jehovah na halitta da kuma fansa, na cetan mutanensa kuma da na halaka magabtansa.

Ikon Allah Yana Bayyane Cikin Halitta

4. (a) Ta yaya duba sama daddare ya taɓa Dauda? (b) Menene halittu na sama suka bayyana game da ikon Allah?

4 Manzo Bulus ya bayyana cewa ‘ana gane ikon madawwami ta wurin abubuwa da [Mahaliccinmu] ya yi.’ (Romawa 1:20) Ƙarnuka da suka gabata, Dauda mai zabura, wanda shi makiyayi ne ƙila sau da yawa ya duba sama daddare, ya gane darajar sararin samaniya da ikon Mahaliccinsa. Ya rubuta: “Sa’anda ina lura da sammanka, aikin yatsotsinka, wata kuma da taurari waɗanda ka sanya; wane abu ne mutum, da ka ke tuna da shi? Ɗan adam kuma da ka ke ziyartassa?” (Zabura 8:3, 4) Ko da bai san game da halitta na samaniya ba, Dauda ya gane cewa shi ba kome ba ne, in an gwada shi da Mahaliccin sararin samaniya namu mai faɗi. A yau, masu ilimin taurari sun san girman sararin samaniya da kuma ƙarfin da ya riƙe shi. Alal misali, sun gaya mana cewa kowace daƙiƙa, rana tana fid da ƙarfi da ya yi daidai da ƙarfin fashewar tan na TNT miliyan 100,000.b Ɗan kaɗan ne cikin ƙarfin nan ke isowa duniya; duk da haka wannan ya isa ya kiyaye dukan rai da ke bisa doron ƙasar. Har ila yau, rana ba ita ba ce tauraro da ya fi ƙarfi a sama. Wasu taurari a daƙiƙa guda kawai, suna fid da zafi da rana take fitarwa a kwana ɗaya. Sa’annan ka yi tunanin iko da Wanda ya halicce irin wannan halittu na sama yake da shi! Elihu ya faɗi daidai da ya ce: “Ubangiji! ya fi ƙarfinmu mu gane shi; mafifici ne shi cikin iko.”—Ayuba 37:23.

5. Wane tabbacin ƙarfin Jehovah muka gani a cikin ayyukansa?

5 Idan mun ‘biɗi ayyukan Allah’ yadda Dauda ya yi, za mu ga tabbacin ikonsa a ko’ina—cikin iska da raƙuman ruwa, a tsawa da walƙiya, cikin manyan koguna da manyan duwatsu. (Zabura 111:2; Ayuba 26:12-14) Ƙari ga haka, kamar yadda Jehovah ya tunatar ma Ayuba, dabobbi ma suna ba da shaida ga Ƙarfinsa. Ɗaya cikin waɗannan ita ce Dorina. Jehovah ya gaya ma Ayuba: “Ƙarfinsa yana cikin ƙungurunsa . . . Haƙarƙarinsa kamar kātākon baƙin ƙarfe ne.” (Ayuba 40:15-18) An san da ƙarfin ɓauna mai ban tsoro a lokuttan Littafi Mai-Tsarki, kuma Dauda ya yi addu’a a cece shi daga “bakin zaki; I, daga ƙahonin ɓauna.”—Zabura 22:21; Ayuba 39:9-11.

6. Menene ɓauna yake alamar ta a cikin Nassosi, kuma don me? (Duba hasiya.)

6 Saboda ƙarfinsa, an yi amfani da ɓauna a cikin Littafi Mai-Tsarki wajen nuna alamar ikon Jehovah.c Wahayin manzo Yohanna na kursiyin Jehovah ya kwatanta masu-rai huɗu, ɗaya cikinsu yana kama da ɓauna. (Ru’ya ta Yohanna 4:6, 7) Babu shakka, iko ɗaya ne cikin muhimman inganci guda huɗu na Jehovah da cherub suka kwatanta. Wasu kuma su ne ƙauna, hikima, da shari’a. Tun da shi ke iko muhimmin fasali na mutumtakar Allah ne, gane ikonsa sarai da kuma yadda yake amfani da shi zai jawo mu kurkusa da shi kuma zai taimake mu mu yi koyi da misalinsa ta yin amfani da kowane iko da muke da shi da kyau.—Afisawa 5:1.

‘Jehovah Mai Runduna, Mai Iko’

7. Ta yaya za mu iya tabbatar da cewa nagarta za ta ci nasara bisa mugunta?

7 A cikin Nassosi, an kira Jehovah “Allah Alƙadiru,” laƙabi da ke tunatar mana cewa ya kamata kada mu rena ikonsa ko mu yi shakkar ƙarfinsa na cin nasara bisa magabtansa. (Farawa 17:1; Fitowa 6:3) Zai iya zama kamar shirin abubuwa na Shaiɗan ya yi ƙarfi sosai, amma a idanun Jehovah “al’ummai suna kama da ɗiɗishin ruwa cikin guga, ana maishe su kuma kamar ƙura mai-labshi a bisa mizani.” (Ishaya 40:15) Muna godiya ga irin ikon nan na Allah, babu shakka cewa nagarta za ta ci nasara bisa mugunta. A lokacin da mugunta tana ko’ina za mu iya samun ta’aziya cewa “Ubangiji mai-runduna, Mai-iko na Isra’ila” zai kawar da mugunta har abada.—Ishaya 1:24; Zabura 37:9, 10.

8. Waɗanne runduna suke yi ma Jehovah hidima a samaniya, kuma wane alama muke da shi na ikonsu?

8 Furcin nan “Ubangiji mai-runduna,” wanda ya bayyana sau 285 a cikin Littafi Mai-Tsarki, wani abin tuni ne na ikon Allah. “Runduna” anan tana nuna halittun ruhu da yawa da Jehovah yake amfani da su. (Zabura 103:20, 21; 148:2) A cikin dare guda, ɗaya kawai cikin waɗannan mala’iku ya kashe sojojin Assuriya 185,000 da suke yi wa Urushalima burga. (2 Sarakuna 19:35) Idan mun gane ikon rundunar samaniya na Jehovah, ba zai yi wa ’yan hamayya sauƙi su tsoratar da mu ba. Annabi Iliya bai damu ba lokacin da runduna da yawa suna nemansa, ba kamar bawansa ba, ya gani da idanunsa na bangaskiya, ikon da rundunar samaniya mai yawa da ke goyon bayansa.—2 Sarakuna 6:15-17.

9. Me ya sa, kamar Yesu, ya kamata mu kasance da aminci a tsarewa na Allah?

9 Hakazalika Yesu ya san mala’iku da za su goyi bayansa lokacin da taron ’yan banza da suke da makamai suka tsare shi da takobi da kulki a lambun Jathsaimani. Bayan ya gaya ma Bitrus ya mayar da takobinsa gidansa, Yesu ya gaya masa cewa, idan yana bukata, Zai iya roƙon Ubansa ya aiko masa “rundunan mala’iku ya fi goma sha biyu.” (Matta 26:47, 52, 53) Idan muna da godiya irin wannan game da rundunar samaniya da ke hannun Allah, mu ma za mu dogara sosai ga goyon bayansa. Manzo Bulus ya rubuta: “Mi za mu ce da waɗannan al’amura fa? Idan Allah ke wajenmu, wa ke gāba da mu?”—Romawa 8:31.

10. Domin su wanene Jehovah yake amfani da ikonsa?

10 Ban da haka, muna da dalilin dogara ga tsarewan Jehovah. Ko yaushe yana yin amfani da ikonsa don sakamako mai kyau kuma cikin jituwa da wasu ingancinsa—shari’a, hikima, da ƙauna. (Ayuba 37:23; Irmiya 10:12) Yayin da kuwa mutane masu iko sau da yawa suna yin rauni ga talakawa da masu tawali’u don riban kansu, Jehovah ‘yana tada matalauci daga cikin turɓaya’ kuma ‘yana da iko garin yin ceto.’ (Zabura 113:5-7; Ishaya 63:1) Yadda Maryamu, uwar Yesu mai filako mara ɗaga kai ta fahimta, “Mai iko” wanda ba tare da son kai ba, yana nuna ikonsa domin waɗanda suke jin tsoronsa, yana sauƙar da masu girman kai amma yana ɗaukaka ƙasƙantattu.—Luka 1:46-53.

Jehovah Ya Bayyana Ikonsa Ma Bayinsa

11. Wace shaida ce ga ikon Allah Isra’ilawa suka gani a shekara ta 1513 K.Z.?

11 A lokutta da yawa, Jehovah ya bayyana ikonsa ma bayinsa. Ɗaya cikin irin lokuttan nan shi ne a Dutsen Sinai a shekara ta 1513 K.Z. A wannan shekarar, Isra’ilawa sun ga tabbaci mai girma na ikon Allah. Annoba goma da suka yi ɓarna sun bayyana ikon Jehovah mai girma da kuma rashin iko na allolin Masar. Ba da jimawa ba bayan haka, mu’ujizar ƙetare Jan Teku da kuma halaka rundunar Fir’auna ya ba da ƙarin tabbaci na ikon Allah. Watanni uku bayan haka, a ƙarƙashin Dutsen Sinai, Jehovah ya gayyace Isra’ilawa su zama ‘keɓaɓiyar taska a garesa daga cikin dukan al’umman duniya.’ Sai su kuma suka yi alkawari: “Abin da Ubangiji ya faɗi duka mu a yi.” (Fitowa 19:5, 8) Sai, Jehovah ya nuna ikonsa dalla-dalla. Tsakanin tsawa da walƙiya da ƙara mai ƙarfi na ƙaho, Dutsen Sinai ya yi hayaki kuma ya jijjiga. Mutanen, da suke tsaye da nisa, suka tsorata. Amma Musa ya gaya masu cewa ya kamata wannan abu da suka gani ya koya masu tsoro na ibada, tsoro da zai motsa su su yi biyayya ga Allahnsu na gaskiya kaɗai mai dukan iko, Jehovah.—Fitowa 19:16-19; 20:18-20.

12, 13. Wane yanayi ne ya sa Iliya ya bar aikinsa, kuma ta yaya Jehovah ya ƙarfafa shi?

12 Ƙarnuka da yawa bayan haka, a lokacin Iliya, Dutsen Sinai ya ga wani nuna iko na Allah. Annabin ya ga ikon Allah yana aiki. Allah ya “rufe sama” shekara uku da rabi, domin ridda na al’ummar Isra’ila. (2 Labarbaru 7:13) A farkon, hankaki suka ciyar da Iliya a kwarin ruwa na Cherith, bayan haka fulawa da mai na wata gwamruwa ya ƙaru a mu’ujizance don ya sami abinci. Jehovah ya ba Iliya ikon tada ɗan wannan gwamruwa da ya mutu. Daga bisani, a wata gwada Allahntaka mai girma a Dutsen Karmel, wuta ta sauƙo daga sama kuma ta cinye hadayar Iliya. (1 Sarakuna 17:4-24; 18:36-40) Duk da haka, ba da jimawa ba bayan wannan, Iliya ya tsorata kuma ya yi sanyin gwiwa lokacin da Jezebel ta yi burga za ta kashe shi. (1 Sarakuna 19:1-4) Ya gudu daga ƙasar, yana tunanin aikinsa na annabci ya ƙare. Don ya sake tabbatar masa kuma ya ƙarfafa shi, Jehovah da kansa ya nuna masa ikonsa cikin alheri.

13 Yayin da Iliya yana cikin kogo, ya ga abubuwa uku na mamaki da Jehovah yake iko da su: iska mai ƙarfi, girgizan ƙasa, kuma ta ƙarshe, wuta. Amma, lokacin da Jehovah yake ma Iliya magana, ya yi haka da “ƙaramar murya mara-ƙarfi.” Ya ƙara masa aiki da zai yi kuma ya gaya masa cewa, har ila da akwai mutane 7,000 masu aminci da suke bauta ma Jehovah cikin ƙasar. (1 Sarakuna 19:9-18) Idan kamar Iliya, mun yi sanyin gwiwa don ba ma yin nasara cikin hidimarmu, za mu iya mu roƙi Jehovah domin “mafificin girman iko”—iko da zai ƙarfafa mu mu ci gaba da wa’azin bishara babu fasawa.—2 Korinthiyawa 4:7.

Ikon Jehovah Ya Ba da Tabbaci na Cikar Alkawuransa

14. Menene sunan Jehovah kansa ya bayyana, kuma ta yaya ikonsa yake haɗe da sunansa?

14 Ikon Jehovah yana haɗe sosai da sunansa da kuma cika nufinsa. Sunan nan Jehovah da babu kamarsa, wanda yake nufin “Yana Sa Shi Zama,” ya bayyana cewa yana sa kansa shi zama Mai Cika alkawura. Babu wani abu da ko wani da zai iya hana Allah cika nufinsa, amma masu shakka za su iya tantamar cewa ba zai yiwu ba ya cika nufinsa. Yadda Yesu ya taɓa gaya ma manzanninsa “ga Allah dukan abu ya yiwu.”—Matta 19:26.

15. Ta yaya aka tunatar ma Ibrahim da Saratu cewa babu abin da ya fi ƙarfin Jehovah?

15 Alal misali, Jehovah ya yi ma Ibrahim da Saratu alkawari cewa zai sa zuriyarsu ta zama babban al’umma. Amma, shekaru da yawa ba su da ɗa. Sun tsufa sosai lokacin da Jehovah ya gaya masu cewa jim kaɗan alkawarin zai cika, sai Saratu ta yi dariya. A mayar da martani, mala’ikan ya ce: “Ko akwai abin da ya fi ƙarfin Ubangiji?” (Farawa 12:1-3; 17:4-8; 18:10-14) Ƙarnuka huɗu bayan haka, lokacin da Musa ya tara zuriyar Ibrahim—da yanzu babban al’umma ce—a Filin Moab, ya tunatar masu cewa Allah ya cika alkawarinsa. Musa ya ce: “Domin kuma [Jehovah] ya ƙaunaci ubanninka, domin wannan ya zaɓi zuriyassu a bayansu, kuma da zatinsa, da ikonsa mai-girma ya fishe ka daga ƙasar Masar; domin shi kori al’ummai daga gabanka, waɗanda suka fi ka girma da ƙarfi, shi shigo da kai, shi ba ka ƙasarsu abin gado, kamar da ya ke yau.”—Kubawar Shari’a 4:37, 38.

16. Me ya sa Sadukiyawa suka faɗa cikin kuskuren ƙin gaskatawa da tashin matattu?

16 Ƙarnuka bayan haka, Yesu ya hukunta Sadukiyawa, waɗanda ba su gaskata da tashin matattu ba. Me ya sa suka ƙi gaskatawa da alkawarin Allah cewa zai tada da matattu? Yesu ya gaya masu: “Rashin sanin Litattafai da ikon Allah [ne].” (Matta 22:29) Nassosi sun tabbatar mana cewa ‘dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryar Ɗan mutum, su fito kuma.’ (Yohanna 5:27-29) Idan mun san abin da Littafi Mai-Tsarki ya ce game da tashin matattu, gabagaɗinmu cikin ikon Allah zai sa mu yarda cewa matattu za su tashi. Allah zai “haɗiye mutuwa har abada . . . gama Ubangiji ya faɗi.”—Ishaya 25:8.

17. A wace rana ce ta gaba gaskatawa da Jehovah a hanya ta musamman za ta zama da muhimmanci?

17 A nan gaba, lokaci zai zo da kowa cikinmu zai gaskata ikon ceto na Allah a hanya ta musamman. Shaiɗan Iblis zai faɗā ma mutanen Allah, waɗanda za su zama kamar ba wanda yake tsare su. (Ezekiel 38:14-16) Sa’annan Allah zai nuna ikonsa mai ƙarfi sabili da mu, kuma kowa za su sani cewa shi Jehovah ne. (Ezekiel 38:21-23) Yanzu ne lokacin da za mu gina bangaskiya da gabagaɗi ga Allah Mai Iko Duka don kada mu yi shakka a wannan lokaci na musamman.

18. (a) Waɗanne fa’idoji muke samu daga yin bimbini akan ikon Jehovah? (b) Wace tambaya ce za a bincika a cikin talifi na gaba?

18 Babu shakka, akwai dalilai da yawa don yin bimbini akan ikon Jehovah. Yayin da muke bimbini game da ayyukansa, mukan motsu cikin tawali’u mu yaba ma Mahaliccinmu Mai Girma kuma mu yi godiya cewa yana amfani da ikonsa a hanya ta hikima da kuma mai kyau. Ba za mu taɓa tsorata ba idan mun dogara ga Jehovah mai runduna. Bangaskiyarmu cikin alkawarinsa ba za ta jijjiga ba. Amma, ka tuna, cewa an halicce mu cikin sifar Allah. Saboda haka, mu ma muna da iko—ko da ba sosai ba ne. Ta yaya za mu iya yin koyi da Mahaliccinmu a hanyar da muke nuna ikonmu? Za a bincika wannan a cikin talifi na gaba.

[Hasiya]

a Yawancin mutane a duniya suna yarda cewa irin man nan da ake samu daga shuƙe-shuƙe kamar fetur da kuma kwal—tushe na musamman na ƙarfin wutar lantarki—suna samun ƙarfi daga rana.

b Akasarin haka, bom na nukiliya da ya fi ƙarfi da aka taɓa gwadawa yana da ƙarfin fashewar nakiya da ya yi daidai da tan na TNT.

c Ɓauna da aka nuna a cikin Littafi Mai-Tsarki mai yiwuwa ɓaunar jeji mai dogon kaho da ake kira a (Latin urus) ne. Shekara dubu biyu da suka shige, an samu waɗannan dabbobi a Gaul (yanzu Faransa), kuma Julius Caesar ya rubuta kwatancin nan game da su: “Waɗannan uri sun kusan kai giwa girma, amma halinsu, launi, da kuma yadda suke, ɓauna ne. Suna da ƙarfi sosai, kuma suna gudu sosai: suna kashe mutum ko dabba da suka gani.”

Za Ka Iya Amsa Waɗannan Tambayoyi?

• Ta yaya halitta ta tabbatar da ikon Jehovah?

• Waɗanne runduna ne Jehovah zai iya yin amfani da su don ya toƙara ma mutanensa?

• A waɗanne lokutta ne Jehovah ya nuna ikonsa?

• Wane tabbaci muke da shi cewa Jehovah zai cika alkawuransa?

[Hotuna a shafi na 21]

“Ku tada idanunku sama, ku duba ko wanene ya halicci waɗannan?”

[Inda aka Dauko]

Hoto daga Malin, © IAC/RGO 1991

[Hotuna a shafi na 24]

Yin bimbini game da ikon Jehovah yana gina bangaskiya cikin alkawuransa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba