Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 5/1 pp. 8-13
  • Sabonta Dukan Abubuwa —Kamar Yadda Aka Annabta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sabonta Dukan Abubuwa —Kamar Yadda Aka Annabta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Makamantan Littattafai
  • Sabuwar Duniya—Za Ka Kasance A Can?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Sabuwar Duniya Bisa Ga Alkawarin Allah
    Ka Zauna A Faɗake!
  • Annabcin Rayuwarmu Ta Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 5/1 pp. 8-13

Sabonta Dukan Abubuwa —Kamar Yadda Aka Annabta

“Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce, Duba, sabonta dukan abu ni ke yi. Ya ce kuma, . . . waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.” —Ru’ya Ta Yohanna 21:5.

1, 2. Me ya sa wasu mutane suke jinkiri da ya dace game da bincika abin da ke a gaba?

KA TAƁA cewa ko tunanin, ‘Wa ya san gobe?’ Za ka iya gane dalilin da ya sa mutane suke jinkirin faɗin abin da zai faru a nan gaba ko ma sun yarda da waɗanda suke da’awar suna faɗin abin da zai faru a nan gaba. Mutane ba su da iyawar da za su faɗi daidai abin da zai faru a watanni ko kuma shekaru da suke gaba.

2 Jaridar Forbes ASAP wadda aka keɓe don batun lokaci. A cikinta mai ba da tarihi a TV, Robert Cringely ya rubuta: “Lokaci yana ci ma dukanmu mutunci, amma ba waɗanda suke shan wulaƙanci a hannun lokaci fiye da masu faɗin abin da ke gaba. Ƙoƙarin faɗin abin da ke gaba wasa ne da kusan kullum ba ma cin nasara. . . . Duk da haka, waɗanda wai su gwanaye ne sai ci gaba suke da faɗin abin da zai faru.”

3, 4. (a) Me wasu suka yarda da shi game da sabon alif? (b) Waɗanne abubuwa ne na gaske wasu suke tsammani game da nan gaba?

3 Wataƙila ka lura da yadda aka mai da hankali sosai ga batun sabon alif, kamar dai mutane da yawa suna tunani game da gaba. A farkon shekara da ta gabata, jaridar Maclean ta ce: “Shekara ta 2000 za ta zama wata shekara ce kawai a kalandar yawancin ’yan Canada, amma wataƙila za ta yi karo da sabuwar farawa ta gaske.” Shehun Malami Chris Dewdney na Jami’ar New York ya ba da wannan dalili na gaskatawa: “Alif yana nufin za mu iya wanke hannayenmu daga ƙarni na yawan bala’i.”

4 Wannan ya yi kama da tunani ne kawai na inda a ce? A Canada kashi 22 ne kawai cikin ɗari na waɗanda aka tambaya “sun yarda cewa shekara ta 2000 za ta kawo sabuwar farawa ga duniya.” Hakika, kusan rabi “suna tsammanin hargitsi a duniya”—yaƙin duniya—cikin shekara 50. Babu shakka, da yawa sun fahimci cewa sabon alif ba zai iya kawar da damuwarmu ba, ya sabonta dukan abubuwa. Sir Michael Atiyah, shugaban Royal Society na Britaniya na dā, ya rubuta: “Irin canji da ake samu da wuri-wuri . . . yana nuna cewa ƙarni na ashirin da ɗaya zai kawo babbar matsala ga dukan wayewar mu. Matsalar yawan jama’a, karancin arziki, gurɓata mahalli, da kuma talauci da ya mamaye duniya, duk sun taru a kanmu, al’amura ne da ke neman mu warware su da hanzari.”

5. A ina za mu sami amsa ta gaskiya game da abin da ke zuwa a nan gaba?

5 Kana iya mamaki cewa, ‘Tun da yake mutane ba za su iya faɗin abin da zai zo mana a nan gaba ba, ba sai kawai mu mance da abin da ke gaba ba?’ Amsar ita ce, a’a! Gaskiya ne, mutane ba za su iya faɗin daidai abin da ke gaba ba, amma kada ku ce babu wanda zai iya. To wa zai iya, kuma me ya sa za mu yarda da abin da ke zuwa a nan gaba? Za ka sami amsoshi masu gamsarwa ga waɗannan tambayoyi cikin wasu annabce-annabce huɗu. An rubuta su ne cikin littafin da aka fi karantawa da mutane suke da shi, kuma wanda aka fi rashin fahimta da kuma wanda aka fi yin banza da shi—Littafi Mai-Tsarki. Ko yaya ka ke tunanin Littafi Mai-Tsarki, ko yaya ka ke ji kana da saninsa, zai amfane ka idan ka yi la’akari da waɗannan tamanai huɗu masu muhimmanci. Sun faɗi abu mai kyau da zai zo a nan gaba. Bugu da ƙari, waɗannan muhimman annabce-annabce huɗu sun zana yadda rayuwarka da ta masoyanka za ta iya zama a nan gaba.

6, 7. A wane lokaci ne Ishaya ya yi annabci, kuma ta yaya annabcinsa ya sami cika ta ban mamaki?

6 An sami na farkon a cikin Ishaya, sura ta 65. Kafin ka karanta, ka fahimci yanayin a zuciyarka—lokacin da aka rubuta wannan da abubuwan da ta yi zance a kansu. Annabin Allah Ishaya, wanda ya rubuta waɗannan kalmomi, ya rayu fiye da ƙarni guda kafin sarautar Yahudiya ta zo ƙarshenta. Ƙarshenta ya zo ne lokacin da Jehovah ya janye kāriyarsa daga Yahudawa marasa aminci, ya ƙyale Babiloniyawa su halaka Urushalima su kwashe mutanenta zuwa hijira. Wannan ya faru ne fiye da shekara ɗari bayan Ishaya ya annabta hakan.—2 Labarbaru 36:15-21.

7 Don a cika tushen tarihin, ku tuna cewa da ja-gorar Allah ne Ishaya ya annabta sunan Cyrus na Pashiya wanda ma ba a haife shi ba, wanda a ƙarshe ya hamɓare Babila. (Ishaya 45:1) Cyrus ya gyara wa Yahudawa hanya suka koma ƙasarsu a shekara ta 537 K.Z. Abin mamaki, Ishaya ya faɗi komawar nan kamar yadda muka karanta a sura ta 65. Ya mai da hankali ne ga yanayi da Isra’ilawa za su iya morewa a ƙasarsu.

8. Wane farin ciki na nan gaba ne Ishaya ya annabta, kuma wane furci ne yake da muhimmanci?

8 Mun karanta a Ishaya 65:17-19: “Ga shi, sababbin sammai da sabuwar duniya ni ke halitta: ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba. Amma sai ku yi murna ku yi farinciki har abada da abin da ni ke halittawa; gama, ga shi, na halitta Urushalima abin murna, mutanenta kuma abin farinciki. Zan yi farinciki domin Urushalima kuma, in yi murna domin mutanena: ba za a ƙara jin motsin hawaye a cikinta ba, ko muryar kuka.” Babu shakka, Ishaya ya kwatanta yanayi ne da suka fi waɗanda Yahudawa da suka zauna cikin Babila kyau. Ya annabta yin murna da farin ciki. Yanzu ka lura da wannan furcin “sababbin sammai da sabuwar duniya.” Wannan shi ne na farko cikin aukuwa huɗu na wannan furcin cikin Littafi Mai-Tsarki, kuma waɗannan matani huɗu za su shafe rayuwarmu na nan gaba sosai, har ma sun faɗe su.

9. Ta yaya cikar Ishaya 65:17-19 ta shafi Yahudawa na dā?

9 Cikar Ishaya 65:17-19 na lokacin ya shafe Yahudawa na dā waɗanda, kamar yadda Ishaya ya faɗa daidai, sun komo ƙasarsu, inda suka sake kafa bauta mai tsarki. (Ezra 1:1-4; 3:1-4) Ka gane cewa, sun komo ƙasa a cikin duniyar nan ce, ba a wani waje a samaniya ba. Fahimtar wannan zai taimake mu mu gane abin da Ishaya yake nufi da sababbin sammai da sabuwar duniya. Ba za mu yi kame-kame ba kamar yadda waɗansu suke yi, game da annabce-annabce mai harshen damo na Nostradamus ko wasu mutane masu faɗin abin da ke zuwa a nan gaba. Littafi Mai-Tsarki kansa ya bayyana abin da Ishaya yake nufi.

10. Yaya za mu fahimci sabuwar “duniya” da Ishaya ya annabta?

10 A cikin Littafi Mai-Tsarki ba ko yaushe ba ne “duniya” take nufin duniyarmu. Alal misali, Zabura 96:1 ta ce a zahiri: “A raira ga Ubangiji, ku dukan duniya.” Mun san cewa doron ƙasar nan tamu—wajen zama da kuma teku mai bala’in girma—ba za su iya rera waƙa ba. Mutane ne suke iya rera waƙa. Hakika, Zabura 96:1 tana nufin mutanen duniya ne.a Amma Ishaya 65:17 ma ya ambaci “sababbin sammai.” Idan “duniya” tana nufin sabuwar tarayyar mutane ne a ƙasar Yahudawa, to menene “sababbin sammai” ɗin?

11. Menene furcin nan “sababbin sammai” yake nufi?

11 Cyclopedia of Biblical, Theological, and Ecclesiastica Literature, na M’Clintock da Strong ya ce: “Dukan inda aka yi amfani da sama a cikin wahayi na annabci, sama tana nufin . . . dukan taron masu iko . . . waɗanda suke bisa kuma suke sarautar mutane, kamar yadda sama ta zahiri take bisa duniya kuma take sarautar duniya.” Game da haɗaɗɗiyar furcin nan “sama da duniya,” Cyclopedia ya yi bayani cewa ‘a harshen annabci, furcin yana nufin yanayin iko dabam dabam ne na mutane. Sama ita ce mai sarauta; duniya kuwa ita ce ake mallaka, mutanen da masu sarauta suke mallakarsu.’

12. Ta yaya Yahudawa na dā suka sami “sabobin sammai da sabuwar duniya”?

12 Yayin da Yahudawa suka komo ƙasarsu, suka sami abin da za a iya kira sabon shirin abubuwa. Suna da sababbin rukunin masu sarauta. Zerubbabel, tattaɓa-kunnen Sarki Dauda, shi ne gwamna, kuma Joshua shi ne babban firist. (Haggai 1:1, 12; 2:21; Zechariah 6:11) Waɗannan sune suka zama “sababbin sammai.” Bisa menene? Waɗannan “sababbin sammai” suna bisa “sabuwar duniya,” tsabtaceccen tarayyar mutane da suka komo ƙasarsu domin su sake gina Urushalima da haikalinta don bauta wa Jehovah. Shi ya sa, a zahiri akwai sababbin sammai da sabuwar duniya a cikar da ta shafi Yahudawa a lokacin.

13, 14. (a) Wane aukuwa na wannan furcin “sababbin sammai da sabuwar duniya” ya kamata mu bincika? (b) Me ya sa annabcin Bitrus yake da muhimmanci a wannan lokacin?

13 Ka mai da hankali, don ka fahimci abin da ake nufi. Wannan ba ƙoƙarin fassara Littafi Mai-Tsarki ba ne ba kuma muna duba tarihin dā kawai ba ne. Za ka iya ganin wannan ta wajen zuwa wata aukuwan wannan furci “sabobin sammai da sabuwar duniya.” A 2 Bitrus sura ta 3, za ku ga wannan aukuwa kuma ku ga yadda ta shafi rayuwarmu a nan gaba.

14 Manzo Bitrus ya rubuta wasiƙarsa fiye da shekara 500 bayan Yahudawa suka komo ƙasarsu. Bitrus da yake ɗaya daga cikin manzannin Yesu, ya yi rubutu ne zuwa ga mabiyan Kristi, “Ubangiji” da aka ambata a 2 Bitrus 3:2. A aya ta 4, Bitrus ya ambata ‘alkawarin bayyanuwar’ Yesu, da ya sa annabcin ya zama da muhimmanci a yau. Tabbaci masu yawa sun nuna cewa tun daga Yaƙin Duniya na I, Yesu ya bayyana, wato yana da ikon Sarauta cikin Mulkin Allah na samaniya. (Ru’ya ta Yohanna 6:1-8; 11:15, 18) Wannan yana da ma’ana ta musamman saboda wani abin da Bitrus ya annabta a wannan surar.

15. Ta yaya annabcin Bitrus game da “sababbin sammai” yake neman cika?

15 Mun karanta a 2 Bitrus 3:13: “Bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci ya ke zaune.” Wataƙila ka riga ka san cewa Yesu wanda yanzu yake sama, shi ne Masarauci na musamman a cikin “sababbin sammai.” (Luka 1:32, 33) Ko da yake, wasu ayoyi na Littafi Mai-Tsarki sun nuna cewa ba shi kaɗai yake sarauta ba. Yesu ya yi alkawari cewa manzanninsa da waɗansu kamarsu za su sami wuri a sama. A cikin littafin Ibraniyawa, manzo Bulus ya kwatanta waɗannan da cewa “masu-tarayya na kira basamaniya.” Kuma Yesu ya ce waɗanda suke cikin wannan rukuni za su zauna bisa kursiyai tare da shi a sama. (Ibraniyawa 3:1; Matta 19:28; Luka 22:28-30; Yohanna 14:2, 3) Abin da ake nufi shi ne cewa waɗansu za su yi mulki tare da Yesu a sababbin sammai. To menene Bitrus yake nufi da furcin nan “sabuwar duniya”?

16. Wace “sabuwar duniya” ce ta riga ta kasance?

16 Kamar yadda yake a cikar ta dā—komowar Yahudawa zuwa ƙasarsu—cikar ta yanzu na 2 Bitrus 3:13 ya ƙunshi mutane waɗanda suka miƙa kai ga mulkin sababbin sammai. Za ka sami miliyoyi a yau da suka miƙa kai da farin ciki ga mulkin nan. Waɗannan suna amfana daga tsarin ilimantarwansa kuma suna ƙoƙari su bi dokokinsa da ke cikin Littafi Mai-Tsarki. (Ishaya 54:13) Waɗannan sune suka zama tushen “sabuwar duniya” wato sun kafa tarayyar jama’a daga dukan al’ummai, harsuna, da ƙabilu, kuma suna aiki tare a miƙa kai ga Sarki, Yesu Kristi da ke sarauta. Gaskiya da take da muhimmanci kuwa ita ce za ka iya zama cikin waɗannan!—Mikah 4:1-4.

17, 18. Me ya sa kalmomin 2 Bitrus 3:13 ke ba mu dalilin sa rai a abin da ke nan gaba?

17 Kada ka ji, kamar wannan shi ne ƙarshen al’amura, ka ce ba mu da ƙarin bayani game da abin da ke a nan gaba. Babu shakka, yayin da muka bincika mahallin 2 Bitrus sura ta 3, za ka ga alamun canji mai girma a nan gaba. A ayoyi 5 da 6, Bitrus ya rubuta game da Rigyawar kwanakin Nuhu, Tufana da ta kawo ƙarshen muguwar duniya ta dā can. A aya ta 7, Bitrus ya ambata cewa “sammai da su ke yanzu, da duniya kuma,” sarauta da kuma mutane da yawa, ajiyayyu ne don “ranar shari’a da hallakar mutane masu-fajirci.” Wannan ya tabbatar da cewa furcin nan “sammai da duniya” ba ya nufin duniyarmu, amma mutane da kuma sarautarsu.

18 Bitrus ya yi bayani daga baya cewa ranar Jehovah da ke zuwa za ta kawo tsabtacewa mai girma, wanda zai gyara hanya don sababbin sammai da sabuwar duniya da aka ambata a aya ta 13. Ka lura da ƙarshen wannan ayar—“inda adilci ya ke zaune.” Wannan bai nuna cewa akwai canje-canje da yawa masu kyau da za su auku ba? Wannan bai tada tsammanin ainihin sababbin abubuwa ba, lokaci da mutane za su sami farin ciki mai yawa a rayuwarsu fiye da yadda suke samu a yau? Idan ka fahimci haka, to, ka sami fahimi ke nan cikin abin da Littafi Mai-Tsarki ya faɗa, fahimi da mutane kalilan ne suka samu.

19. A wane yanayi ne littafin Ru’ya ta Yohanna ta yi nuni ga “sababbin sammai da sabuwar duniya” da suke zuwa?

19 Amma bari mu ci gaba. Mun riga mun duba aukuwan wannan furcin “sababbin sammai da sabuwar duniya,” a cikin Ishaya sura ta 65, da kuma wani a 2 Bitrus sura ta 3. Yanzu ka juya zuwa ga Ru’ya ta Yohanna sura ta 21, wadda take ɗauke da aukuwa na huɗu na wannan furcin a cikin Littafi Mai-Tsarki. Har ila yau, fahimtar yanayin zai taimaka. A cikin surori biyu kafin Ru’ya ta Yohanna sura ta 19, mun ga an kwatanta yaƙi sarai cikin alama—amma ba yaƙi tsakanin al’ummai biyu da suke abokan gāba ba ne. A ɓangare ɗaya “Kalmar Allah” ce. Laƙabi wanda wataƙila ka san Yesu Kristi da shi. (Yohanna 1:1, 14) Yana sama, kuma wannan wahayin ya nuna shi tare da rundunarsa na yaƙi na samaniya. Da wa suke yaƙi? Surar ta ambaci “sarakuna,” “jarumawa,” da kuma mutane iri-iri, “ƙanana da manya.” Wannan yaƙi ya shafi ranar Jehovah da ke zuwa, na halaka mugunta. (2 Tassalunikawa 1:6-10) A gaba, Ru’ya ta Yohanna sura ta 20 ta soma da kwatancin yadda za a cire “tsofon maciji [wanda] shi ne Iblis da Shaiɗan.” Wannan ya shirya fagen bincika Ru’ya ta Yohanna sura ta 21.

20. Ru’ya ta Yohanna 21:1 ta nuna wane muhimmin canji ne da za a yi a nan gaba?

20 Manzo Yohanna ya soma da kalmomi masu ban sha’awa: “Na ga sabuwar sama da sabuwar duniya kuma: gama sama ta fari da duniya ta fari sun shuɗe; teku kuma ba shi.” Bisa ga abin da mun gani a Ishaya sura ta 65 da 2 Bitrus sura ta 3, za mu iya tabbata cewa, wannan ba ya nufin sauya sama ta zahiri da doron ƙasa, tare da tekun cikinta. Kamar yadda surori na farko suka nuna, za a cire miyagun mutane da sarautarsu, haɗe da sarki mara ganuwa Shaiɗan. Hakika, abin da aka yi alkawarinsa a nan shi ne sabon shirin abubuwa da ya shafi mutane na duniya.

21, 22. Ga waɗanne albarka ne Yohanna ya tabbatar mana, kuma menene share hawaye yake nufi?

21 Za a tabbatar mana da wannan yayin da mun ci gaba cikin wannan annabci mai girma. Ƙarshen aya ta 3 ta faɗi lokaci da zai zama Allah yana tare da mutane, zai mai da hankalinsa ga mutane da suke yin nufinsa. (Ezekiel 43:7) Yohanna ya ci gaba a ayoyi 4, 5: “[Jehovah] za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe. Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce, Duba, sabonta dukan abu ni ke yi. Ya ce kuma, Ka rubuta: gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.” Annabci ne mai faranta rai!

22 Bari mu dakata mu ɗanɗana abin da Littafi Mai-Tsarki yake annabtawa a nan. ‘Allah za ya share dukan hawaye daga idanunsu.’ Wannan ba ya nufin hawayen da yake wanke idanu masu tausayi, ko kuma hawayen murna. A’a, hawayen da Allah zai share, hawaye ne da wahala, baƙin ciki, cin mutunci, ɓacin rai, da kuma azaba suke kawowa. Ta yaya za mu tabbatar da haka? Lallai, wannan alkawarin mai ban sha’awa na Allah ya haɗa share hawaye da ‘mutuwa, baƙin zuciya, da kuma azaba da ba za su ƙara kasancewa ba.’—Yohanna 11:35.

23. Annabcin Yohanna ya ba da tabbacin ƙarshen wane irin yanayi?

23 Wannan bai ba da tabbacin cewa, za a halaka ciwon daji, gazawar jiki, da kuma bugun zuciya ba? Wanene cikinmu bai yi rashin wani wanda yake ƙauna don wani ciwo, haɗari, ko bala’i ba? Allah a nan ya yi alkawarin cewa mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba, wanda ya nuna cewa yaran da wataƙila za a haife su a wannan lokacin ba za su zo duniya da tsammanin su manyanta har su tsufa ba—su mutu kuma. Wannan annabcin har wa yau yana nufin ƙaban ƙashi, kaluluwan ciki, ciwon ido mai kawo makanta, har ma da amosanin ido—wanda ya fi damun tsofaffi, ba za su ƙara kasancewa ba.

24. Ta yaya “sabuwar sama da sabuwar duniya” za su zama albarka, kuma menene har ila yau za mu bincika ?

24 Babu shakka za ka yarda da cewa baƙin zuciya da kuma kuka za su ragu in an cire mutuwa, tsufa, da cuta. Duk da haka, yaya batun talauci da yake halaka mutane a hankali, zaluntar yara, da kuma wariya irin ta zalunci don tushe ko launin fata? Idan waɗannan abubuwa—da suka zama ruwan dare a yau—suka ci gaba, baƙin ciki da kuka ba za su ƙare ba. Saboda haka, waɗannan abubuwa da suke kawo baƙin ciki a yau ba za su lalace rayuwa a ƙarƙashin “sabuwar sama da sabuwar duniya.” Canji ne ƙwarai! Yanzu dai, mun riga mun bincika aukuwa guda uku cikin huɗu na wannan furcin “sababbin sammai da sabuwar duniya” a cikin Littafi Mai-Tsarki. Har yanzu da akwai guda wanda yake ɗaure da waɗanda muka bincika kuma ya nanata abin da ya sa muke da dalilin zuba ido mu ga lokaci da kuma yadda Allah zai cika alkawarinsa na “sabonta dukan abu.” Talifi na gaba zai bincika wannan annabcin da kuma ma’anarsa ga farin cikinmu.

[Hasiya]

a The New English Bible ya furta wannan ayar haka: “Ku rera waƙa wa UBANGIJI, dukan mutane na bisa duniya.” The Contemporary English Version ya ce: “Kowa bisa wannan duniya, rera waƙar yabo ga UBANGIJI.” Wannan ya yi daidai da fahimtar cewa, “sabuwar duniya” da Ishaya ya faɗa, yana nufin mutanen Allah da suka koma ƙasarsu ne.

Menene Ka Tuna?

• A wane yanayi guda uku Littafi Mai-Tsarki ya annabta “sababbin sammai da sabuwar duniya”?

• Ta yaya cikan “sababbin sammai da sabuwar duniya” ya shafi Yahudawa na dā?

• Wace cika ce aka fahimta game da “sababbin sammai da sabuwar duniya” da Bitrus ya ambata?

• Ta yaya Ru’ya ta Yohanna sura ta 21 ta yi nuni ga gaba mai kyau?

[Hoto a shafi na 10]

Kamar yadda Jehovah ya faɗa, Cyrus ya gyara hanya wa Yahudawa su koma ƙasarsu a shekara ta 537 K.Z.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba