Sabuwar Duniya—Za Ka Kasance A Can?
“Na sani babu abin da ya fi masu, kamar su yi murna, su kama aika nagarta dukan kwanakin ransu. Kowane mutum kuma shi ci, shi sha, shi ji daɗi cikin dukan aikinsa; wannan kyautar Allah ne.”—MAI-WA’AZI 3:12, 13.
1. Me ya sa za mu gaskata da abin da ke zuwa nan gaba?
MUTANE da yawa suna tunanin cewa Allah Maɗaukaki Duka matsananci ne, mai zalunci. Duk da haka, matani nan na saman gaskiya ne wanda za ka samu cikin Kalmarsa da ya hure. Cikin jituwa da cewa “Allah mai-albarka” ne da ya saka iyayenmu na fari cikin aljanna a duniya. (1 Timothawus 1:11; Farawa 2:7-9) Lokacin da muke neman fahimi game da abin da ke zuwa nan gaba da Allah ya yi alkawari ga mutanensa, kada mu yi mamakin koyon yanayi da zai kawo mana morewa na dindindin.
2. Waɗanne abubuwa ne ka ke sauraro?
2 A cikin talifi da ya shige, mun bincika aukuwa uku inda Littafi Mai-Tsarki ya annabta “sababbin sammai da sabuwar duniya.” (Ishaya 65:17) Ɗaya cikin waɗannan annabcin an rubuta a Ru’ya ta Yohanna 21:1. Ayoyi da suka biyo baya sun faɗi game da lokaci da Allah Maɗaukaki Duka zai canja yanayin duniya ya zama mai kyau sosai. Zai share hawayen baƙin ciki. Mutane ba za su ƙara mutuwa don tsufa, ciwo, ko haɗari ba. Makoki, kuka, da kuma azaba za su shuɗe. Kai, bege ne mai kyau! Amma za mu iya tabbata cewa zai zo, kuma wane tasiri wannan tsammanin zai yi a kan mu a yanzu?
Dalilai na Gaba gaɗi
3. Me ya sa za mu dogara ga alkawuran Littafi Mai-Tsarki game da nan gaba?
3 Ka lura da yadda Ru’ya ta Yohanna 21:5 ta ci gaba. Ta faɗi abin da Allah ya ce, a zaune a kan kursiyinsa na sama: “Duba, sabonta dukan abu ni ke yi.” Wannan alkawarin Allah ya fi dukan wani furcin ’yancin kai, ko wani ’yancin dama na zamani, ko kuma wani abu da mutane suke so su cim ma a nan gaba. Furci ne daga wanda za a iya dogara da Shi wanda Littafi Mai-Tsarki ya ce “ba shi iya yin ƙarya.” (Titus 1:2) Babu shakka, za ka ji ya kamata mu dakata a nan, mu more armashin wannan kamiltaccen bege da kuma dogara ga Allah. Amma ba ma bukatar dakatawa. Da akwai ƙarin abubuwa da za mu koya game da abin da ke zuwa a gabanmu.
4, 5. Waɗanne annabce-annabce na Littafi Mai-Tsarki ne da aka riga aka bincika za su ƙara ƙarfafanmu game da abin da ke zuwa a nan gaba?
4 Ka yi waswasi game da abin da talifi da ya gabata ya kafa game da alkawarin Littafi Mai-Tsarki na sababbin sammai da sabuwar duniya. Ishaya ya faɗi game da wani sabon shiri, kuma annabcinsa ya cika lokacin da Yahudawa suka komo ƙasarsu suka sake kafa bauta mai-tsarki. (Ezra 1:1-3; 2:1, 2; 3:12, 13 ) Amma dai, wannan shi ne kawai dukan abin da annabcin Ishaya yake nufi? Ko kaɗan! Abin da ya annabta zai sake cika a hanya mafi girma a lokaci da yake zuwa a gaba can da nesa. Me ya sa muka faɗi haka? Saboda abin da muka karanta a 2 Bitrus 3:13 da Ru’ya ta Yohanna 21:1-5. Waɗannan matanai suna nufin sababbin sammai da sabuwar duniya waɗanda za su amfane Kiristoci a dukan duniya ne.
5 Kamar yadda aka ambata da farko, Littafi Mai-Tsarki ya yi amfani da furcin nan “sababbin sammai da sabuwar duniya” sau huɗu. Mun bincika uku cikinsu kuma mun kai ga kammala da take da ƙarfafa. Kai tsaye kuwa, Littafi Mai-Tsarki ya annabta cewa Allah zai kawar da mugunta da kuma waɗansu abubuwa da suke kawo wahala, kuma zai ƙara wa mutane albarka a cikin sabon shiri da ya yi alkawarinsa.
6. Menene annabci na huɗu da ya ambata “sababbin sammai da sabuwar duniya” ya faɗa?
6 Bari mu bincika sauran aukuwa ɗaya na furcin nan “sababbin sammai da sabuwar duniya,” a Ishaya 66:22-24: “Gama, yadda sababbin sammai da sabuwar duniya, waɗanda zan yi, za su dawama a gabana, in ji Ubangiji, hakanan kuma zuriyarku da sunanku za su dawama. Za ya zama kuma, daga wani sabon wata zuwa wani, daga wata asabar kuma zuwa wata asabar, dukan masu-rai za su zo su yi sujada a gabana, in ji Ubangiji. Za su fita, su yi kallon gawayen mutane waɗanda sun yi mini laifi: gama tsutsarsu ba za ta mutu ba, wutarsu kuma ba za a bice ta ba: za su zama abin ƙyama kuwa ga dukan masu-rai.”
7. Me ya sa za mu kammala da cewa Ishaya 66:22-24 zai cika a kwanaki masu zuwa?
7 Wannan annabci ya cika tsakanin Yahudawa da suka sake mallakar ƙasarsu, amma da akwai wata cika kuma. Wannan za ta zama shekaru da yawa bayan da aka rubuta wasiƙar Bitrus ta biyu da littafin Ru’ya ta Yohanna, don sun yi maganar ‘sabuwar sama da sabuwar duniya.’ Za mu saurari cika ta ƙarshe mafi girma a cikin sabon shiri. Ka yi la’akari da wasu yanayi da za mu yi tsammanin moransu.
8, 9. (a) A wace hanya ce mutanen Allah za su ci gaba da ‘dawwama’? (b) Menene ma’anar annabcin da ya ce bayin Jehovah za su yi bauta “daga wani sabon wata zuwa wani, daga wata asabar kuma zuwa wata asabar”?
8 Ru’ya ta Yohanna 21:4 ta ce mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba. Matani na Ishaya 66 ya jitu da wannan. Za mu ga cewa a aya ta 22, Jehovah ya san cewa sababbin sammai da sabuwar duniya ɗin ba na ɗan lokaci ba ne, waɗanda suke da ƙarshe. Bugu da ƙari, mutanensa za su jure; za su ‘dawwama’ a gabansa. Abin da Allah ya riga ya yi wa mutanensa zaɓaɓu ya ba mu dalilin gaba gaɗi. Kiristoci na gaskiya sun fuskanci mugun tsanantawa, har ma an yi ƙoƙari a shafe su. (Yohanna 16:2; Ayukan Manzanni 8:1) Duk da haka, ko abokan gāba masu ƙarfi na mutanen Allah, kamar su Nero da ya mallaki Daular Roma da kuma Adolf Hitler ma, ba su iya shafe amintattun bayin Jehovah waɗanda suke ɗauke da sunansa ba. Jehovah ya tsare ikklisiyar zaɓaɓɓunsa, kuma mun tabbata cewa zai ci gaba da tsare ta.
9 Hakanan ma, waɗanda suke da aminci ga Allah sashi na sabuwar duniya, tarayyar masu bautar gaskiya a cikin sabuwar duniya, za su ci gaba da tsayawa kowannensu, domin suna yi wa Mahaliccin dukan abubuwa bauta mai tsarki. Wannan bautar ba wadda za a yi ta jefi-jefi ko kawai ana yi ne ba. Dokar Allah, da aka ba Isra’ila ta hannun Musa, ta nuna yadda za a yi bauta kowanne wata, in an ga sabon wata, kowane mako, a ranar Asabarci. (Leviticus 24:5-9; Littafin Lissafi 10:10; 28:9, 10; 2 Labarbaru 2:4) Saboda haka Ishaya 66:23 ya annabta bauta wa Allah da ake yi a kai a kai, wadda take ci gaba, mako zuwa mako da kuma wata zuwa wata. Rashin yarda da wanzuwar Allah da kuma riya ta addini ba za ta kasance a lokacin ba. “Dukan masu-rai za su zo su yi sujada a gaban” Jehovah.
10. Me ya sa za ka tabbata cewa miyagun mutane ba za su lalata sabuwar duniya dindindin ba?
10 Ishaya 66:24 ya tabbatar mana cewa salama da adalci na sabuwar duniya ba za su taɓa shiga haɗari ba. Miyagun mutane ba za su lalata su ba. Ka tuna cewa 2 Bitrus 3:7, 10 ya ce aba da ke gabanmu ita ce “ranar shari’a da hallakar mutane masu-fajirci.” Waɗanda za su zo ƙarshensu masu-fajirci ne. Ba kamar yadda yake kullum a yaƙin mutane, inda ’yan farin hula suke mutuwa fiye da sojoji ba. Alƙali Mai Girma ya tabbatar mana cewa ranarsa za ta zama ta halaka mutane masu-fajirci ne.
11. Menene Ishaya ya nuna cewa kowa da ya juya wa Allah baya da kuma bautarsa zai fuskanta a nan gaba?
11 Masu adalci da suka tsira za su ga cewa kalmomin annabci na Allah gaskiya ne. Aya ta 24 ta faɗi cewa ‘gawayen mutane waɗanda sun yi laifi’ wa Jehovah za su zama alamar shari’arsa. Kalmomin da Ishaya ya yi kwatanci da su, zai zama da mamaki. Duk da haka, ya yi daidai da tarihi. Bayan garun Urushalima ta dā wurin zuba juji ne, a wasu lokutta kuma don gawawwakin masu-laifi da aka kashe aka ga ba su cancanta a yi jana’izarsu ba.a Tsutsotsi da kuma wutar da ke wajen za su halaka jujin da kuma gawawwakin. Babu shakka, kwatancin Ishaya yana nuna ƙarshen shari’ar Jehovah bisa masu laifi ne.
Abin da Shi da Kansa Ya Yi Alkawari
12. Ishaya ya ba da wane ƙarin bayani ne game da rayuwa a cikin sabuwar duniyar?
12 Ru’ya ta Yohanna 21:4 ta gaya mana wasu abubuwa da ba za su kasance ba a cikin sabon shiri da ke zuwa. Amma kuma, menene zai kasance a lokacin? Yaya rayuwa za ta zama? Za mu iya samun ɗan fahimi? Sosai ma kuwa. Ishaya sura 65 ya annabta yanayi da za mu more idan muka sami tagomashin Jehovah mu rayu a lokacin, wato a ƙarshe, zai halicci waɗannan sabuwar sama da sabuwar duniya. Waɗanda aka albarkace su da waje na dindindin a cikin sabuwar duniyar ba za su tsufa ba balle su mutu. Ishaya 65:20 ya ba mu wannan tabbaci: “Ba za a ƙara ganin jariri mai-kwanaki kaɗan ba gaba nan, ko tsoho wanda ba ya cika kwanakinsa ba: gama yaro za ya mutu yana shekara ɗari, mai-zunubi kuwa wanda ya ke da shekara ɗari za ya zama la’antace.”
13. Ta yaya Ishaya 65:20 ya ba mu tabbacin cewa mutanen Allah za su more kwanciyar rai?
13 Lokacin da wannan ya cika da fari a kan mutanen Ishaya, yana nufin cewa jarirai da suke cikin ƙasar suna da kāriya. Babu abokan gāba da suke shigowa, kamar yadda Babila ta taɓa yi, don su kwashe jarirai su kuma kashe maza a ƙuruciyarsu. (2 Labarbaru 36:17, 20) A cikin sabuwar duniyar, mutane za su zauna lafiya, cikin kwanciyar rai, su more rayuwa. Idan mutum ya zaɓi ya yi wa Allah tawaye, ba za a ƙyale shi ya ci gaba da rayuwa ba. Allah zai cire shi. Me za a ce idan ɗan tawaye mai zunubin shekararsa ɗari ne? Zai mutu ‘kamar yaro’ idan aka gwada da rai na har abada.—1 Timothawus 1:19, 20; 2 Timothawus 2:16-19.
14, 15. Bisa ga Ishaya 65:21, 22, ga waɗanne ayyuka masu albarka ne ka sa rai?
14 Maimakon ya tsaya kawai game da yadda za a cire mai zunubi da gangan, Ishaya ya kwatanta yanayin rayuwa da zai kasance a cikin sabuwar duniyar. Ka sa kanka cikin wannan yanayin. Abin da za ka fara gani da idanunka na zuci, abubuwa na kusa da gida ne. Ishaya ya mai da hankali akan wannan a ayoyi 21 da 22: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba; gama kamar yadda kwanakin itace su ke, hakanan kwanakin mutanena za su zama, zaɓaɓuna kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.”
15 Idan ba ka iya gini ba ko ba ka taɓa yin lambu ba, annabcin Ishaya ya nuna cewa ilimi yana jiranka. Ba za ka so ka koya ba ta wurin taimakon malamai, wataƙila ma maƙwabta masu kirki waɗanda da farin ciki za su taimake ka? Ishaya bai faɗi ko gidanka zai zama mai babbar taga da labule ba, don ka ji daɗin shan iska, ko kuma mai tagar gilas wanda za ka lura da canjawar yanayi. Za ka gina gidanka, da rufi mai gangara don ya tare ruwan sama da kuma dasƙararriyar iska? Ko kuma dai yanayin zai sa ka yi rufi da ke shimfiɗe—irin waɗanda suke a Gabas ta Tsakiya—rufin da za ka iya tara iyalinka don abinci mai daɗi da kuma taɗi?—Kubawar Shari’a 22:8; Nehemiah 8:16.
16. Me ya sa za ka yi tsammanin sabuwar duniya ta zama tana da gamsarwa na dindindin?
16 Abu mafi muhimmanci, fiye da sanin abin da zai faru dalla-dalla shi ne cewa za ku sami gidan kanku. Zai zama naka—ba kamar yau ba da za ka yi wahalar gini, amma sai wani ya amfana. Ishaya 65:21 ya ce za ka dasa kuma ka ci amfaninta. Wannan ya taƙaita yanayin sarai. Za ka gamsu da duk ƙoƙarce-ƙoƙarcenka, da amfanin ayyukan hannunka. Za ka yi haka na tsawon lokaci—“kamar yadda kwanakin itace suke.” Wannan babu shakka ya dace da kwatancin nan “sabonta dukan abu”!—Zabura 92:12-14.
17. Wane alkawari ne iyaye za su ga yana da ban ƙarfafa?
17 Idan kuma mahaifi ne kai, waɗannan kalmomin za su taɓa zuciyarka: “Ba za su yi aiki a banza ba, ba kuwa za su haifi ’ya’ya ga razana ba labari; gama zuriyar masu-albarka na Ubangiji ne su, ’ya’yansu kuma za su kasance tare da su. Za ya zama kuma, kamin su kira, in amsa; tun suna cikin magana kuma, in ji.” (Ishaya 65:23, 24) Ka san baƙin cikin ‘haihuwa ga razana’? Ba sai mun lissafa matsalolin da yara suke da shi da ke sa iyaye da kuma wasu damuwa ba. Game da wannan, dukanmu mun ga iyaye da sun shagala cikin nasu sana’o’i, ayyuka, ko nishaɗi da suke ba da lokaci kaɗan kawai don yaransu. Akasarin haka, Jehovah ya ba mu tabbacin zai ji mu kuma ya biya bukatunmu, har ma ya yi tsammaninsu.
18. Me ya sa za ka yi tsammanin jin daɗin dabbobi a sabuwar duniya?
18 Lokacin da ka ke tunani game da abin da za ka more a sabuwar duniya, ka ƙaga yanayin a zuci na abin da kalmomin annabci na Allah ya ce: “Kerkeci da ɗan rago za su yi kiwo tare, zaki kuma za ya ci ciyawa kamar sā: ƙura kuwa za ta zama abincin maciji. Ba za su ciwutar, ba kuwa za su yi ɓarna cikin dukan dutsena mai-tsarki ba, in ji Ubangiji.” (Ishaya 65:25) ’Yan zane-zane sun yi ƙoƙari su zana wannan yanayin, amma wannan ba zane ba ne kawai da suka zana da gwanintarsu ba. Wannan yanayin zai zama gaskiya. Salama za ta kasance tsakanin mutane kuma zai yi daidai da salama tsakanin dabbobi. Masana kimiyyar ƙwayoyin rai da yawa da masu son dabbobi suna ɓad da shekaru mafi kyau na rayuwarsu don su koyi kaɗan daga cikin iri-irin dabbobi kalilan, wataƙila ma iri ɗaya kawai. Akasarin haka, ka yi tunanin abin da za ka iya koya lokacin da dabbobin ba su cika da tsoron mutane ba. A lokacin za ka iya zuwa wurin tsuntsaye da kuma ƙananan halittu da suke zama a daji ko kuma kurmi—i, ka lura, ka koya daga wajensu kuma ka more su. (Ayuba 12:7-9) Za ka iya yin wannan cikin lafiya, babu haɗari daga mutum ko kuma dabba. Jehovah ya ce: “Ba za su ciwutar, ba kuwa za su yi ɓarna cikin dukan dutsena mai-tsarki ba.” Wannan canji ne ƙwarai da gaske daga abin da muke ji da gani a yau!
19, 20. Me ya sa mutanen Allah suka bambanta daga yawancin mutane a yau?
19 Kamar yadda aka faɗa da farko, mutane ba za su iya annabta abin da zai faru a nan gaba daidai ba, duk da damuwa game da sabon alif. Wannan ya bar mutane da yawa cikin halin kakanikayi, a rikice, ko kuma cikin fid da zuciya. Peter Emberley, darektan jami’ar Canada, ya rubuta: “[Manyan mutane] da yawa suna fuskantar muhimman tambayoyin rayuwa. Wanene ni? Menene nake fama in samu? Wace wasiyya ce zan bar wa tsara ta gaba? Suna ƙoƙari don su sami kwanciyar rai da kuma ma’ana a rayuwarsu a shekarun warɓa.”
20 Za ka gane dalilin da ya sa wannan ya zama haka ga waɗansu da yawa. Wataƙila su biɗi more rayuwa ta wajen hutu ko kuma wasanni masu faranta rai. Duk da haka, ba su san abin da yake zuwa a nan gaba ba, saboda haka, rayuwa ta zama ba ta da muhimmanci, tsari, ko kuma ma’ana ta gaske. Yanzu ka duba bambancin rayuwarka da ta su daga abin da muka bincika. Ka san cewa a cikin sababbin sammai da sabuwar duniya da Jehovah ya yi alkawarinsa, za mu iya duba, mu ce daga zuciyarmu, ‘Allah ya sabonta dukan abu da gaske!’ Ta yaya za mu more wannan!
21. Wane abu makamanci muka gani a Ishaya 65:25 da Ishaya 11:9?
21 Ba ƙetare doka ba ne, mu yi tunanin muna cikin sabuwar duniya ta Allah. Ya gayyace mu, har ma ya aririce mu, mu bauta masa cikin gaskiya yanzu kuma mu cancanci samun rai lokacin da ‘ba za su ciwutar, ba kuwa za su yi ɓarna cikin dukan dutsensa ba.’ (Ishaya 65:25) Ka san cewa Ishaya ya yi magana da ta kusanci haka da farko, kuma ya haɗa da abin da tabbas ne don mu more sabuwar duniya da gaske? Ishaya 11:9 ya ce: “Ba za su yi ciwutarwa ba; ba kuwa za su yi ɓarna ko’ina cikin dutsena mai-tsarki ba: gama duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.”
22. Binciken annabce-annabcen huɗu na Littafi Mai-Tsarki zai ƙarfafa mu mu ƙuduri aniyar yin menene?
22 ‘Sanin Jehovah.’ Lokacin da Allah ya sabonta dukan abu, mazaunan duniya ma za su sami cikakken saninsa da kuma na nufinsa. Wannan ya ƙunshi fiye da koya daga halittar dabbobi. Ya ƙunshi hurarren Kalmarsa. Alal misali, ka yi waswasi game da yawan abubuwan da muka gani daga binciken annabce-annabce huɗu kawai da suka ambaci “sababbin sammai da sabuwar duniya.” (Ishaya 65:17; 66:22; 2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 21:1) Kana da kyakkyawan dalilin na karatun Littafi Mai-Tsarki kullum. Wannan ɗaya ne daga abin da ka ke yi kullum? Idan ba ka yi, wane gyara za ka iya yi don kowace rana ka karanta wasu abubuwa da Allah ya ce? Za ka ga cewa ban da more sabuwar duniya, za ka sami ƙarin farin ciki yanzu, kamar yadda mai Zabura ya yi.—Zabura 1:1, 2.
[Hasiya]
a Duba Insight on the Scriptures, Littafi na 1, shafi 906, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa za mu iya cewa abin da Ishaya 66:22-24 ya annabta yana zuwa a nan gaba ne?
• Menene musamman muke sa rai mu gani tsakanin abin da aka faɗa a annabcin da yake Ishaya 66:22–24 da kuma Ishaya 65:20-25?
• Wane dalili ne muke da shi na gaba gaɗi game da abin da ke zuwa a gabanmu?
[Hotuna a shafi na 15]
Ishaya, Bitrus, da kuma Yohanna sun annabta fannonin “sababbin sammai da sabuwar duniya”