Ka Riƙe ‘Begenka Na Ceto’ Da Kyau!
“Muna yafe . . . da bege na ceto, kwalkwali ke nan.”—1 TASSALUNIKAWA 5:8.
1. Ta yaya “bege na ceto” yake taimako wajen jurewa?
BEGEN za a cece shi, zai iya taimake mutum ya jure ko cikin yanayi mai tsanani ma. Wani wanda ya yi haɗari cikin jirgin ruwa da yake rataye a kan katako zai iya jurewa na doguwar lokaci idan ya san za a taimake shi ba da daɗewa ba. Hakanan, shekaru dubbai da suka gabata, begen ‘ceto na Jehovah’ ya taimake maza da mata masu bangaskiya a lokatan bala’i, kuma wannan begen bai taɓa kai wa ga kunya ba. (Fitowa 14:13; Zabura 3:8; Romawa 5:5; 9:33) Manzo Bulus ya kwatanta “bege na ceto” da “kwalkwali” na ɗamarar ruhaniya ta Kirista. (1 Tassalunikawa 5:8; Afisawa 6:17 ) Hakika, tabbacin cewa Allah zai cece mu yana tsare tunaninmu, yana taimakonmu mu zauna a faɗake duk da wahalarmu, hamayya, da kuma jaraba.
2. A waɗanne hanyoyi ne “bege na ceto” yake da muhimmanci a bauta ta gaskiya?
2 “Bege game da nan gaba ba halin duniyar arna ba ne,” mutane da suka kewaye Kiristoci a ƙarni na farko, in ji The International Standard Bible Encyclopedia. (Afisawa 2:12; 1 Tassalunikawa 4:13) Duk da haka, “bege na ceto” abu ne muhimmi a bauta ta gaskiya. Ta yaya? Na farko, ceton bayin Jehovah yana haɗe ga sunansa. Mai Zabura Asaph ya yi addu’a: “Ka yi mana taimako, ya Allah na cetonmu, domin darajar sunanka: Ka cece mu.” (Zabura 79:9; Ezekiel 20:9) Ƙari ga haka, gaskata alkawuran Jehovah na ba da albarka yana da muhimmanci wajen yin dangantaka mai kyau da shi. Bulus ya sa shi haka: “Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah sai shi ba da gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗansa.” (Ibraniyawa 11:6) Bugu da ƙari, Bulus ya yi bayani cewa ceton waɗanda suka tuba shi ne wani muhimmin dalilin da ya sa Yesu ya zo duniya. Ya furta: “Batun nan amintace ne, ya isa kowa shi karɓa, cewa, Kristi Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu-zunubi.” (1 Timothawus 1:15) Kuma manzo Bitrus ya nuna cewa ceto shi ne ‘ƙarshe [ko kuma sakamakon] bangaskiyarmu.’ (1 Bitrus 1:9) Babu shakka, daidai ne a yi begen ceto. Amma menene ceto? Kuma menene ake bukata don a same shi?
Menene Ceto?
3. Waɗanne irin ceto ne bayin Jehovah na dā suka gani?
3 A cikin Nassosin Ibrananci, “ceto” ko da yaushe yana nufin ceta ko kuma tsira daga zalunci ko daga mutuwar wulaƙanci, na ƙeta. Alal misali, a kiran Jehovah “mai-cetona,” Dauda ya ce: “Allah na dutsena ke nan, . . . mafakata kuma: Mai-cetona, kana cetona daga zilama mai-ƙarfi. Zan kira bisa Ubangiji, wanda ya isa a yi yabonsa: Da hakanan zan tsira daga hannun maƙiyana.” (2 Samuila 22:2-4) Dauda ya san cewa Jehovah yana sauraro idan amintattun bayinsa suka roƙi taimako.—Zabura 31:22, 23; 145:19.
4. Wane bege ne game da nan gaba bayin Jehovah kafin Kiristoci suke da shi?
4 Bayin Jehovah kafin lokacin Kiristoci, su ma suna da begen rayuwa ta nan gaba. (Ayuba 14:13-15; Ishaya 25:8; Daniel 12:13) Hakika, da yawa cikin alkawuran ceta da suke cikin Nassosin Ibrananci na annabci ne na ceto mafi girma—wanda zai kai ga rai na har abada. (Ishaya 49:6, 8; Ayukan Manzanni 13:47; 2 Korinthiyawa 6:2) A lokacin Yesu, Yahudawa da yawa sun yi begen rai na har abada, amma sun ƙi su karɓi Yesu wanda shi ne mabuɗin cim ma begensu. Yesu ya gaya wa shugabannan addinan lokacinsa: “Kuna bin cikin littattafai, domin kuna tsammani a cikinsu kuna da rai na har abada, su ne fa suna shaidata.”—Yohanna 5:39.
5. Menene ma’anar ceto gaba ɗaya?
5 Ta wurin Yesu, Allah ya bayyana ma’anar ceto gaba ɗaya. Ya haɗa da saki daga mallakar zunubi, daga garƙuwar addinin ƙarya, daga duniyar da take ƙarƙashin ikon Shaiɗan, daga tsoron mutane, har ma da tsoron mutuwa. (Yohanna 17:16; Romawa 8:2; Kolossiyawa 1:13; Ru’ya ta Yohanna 18:2, 4) Duka dai, ga amintattun bayin Allah, ceto daga Allah yana nufin fiye da ceto daga zalunci da kuma wahala amma yana nufin zarafin samun rai na har abada. (Yohanna 6:40; 17:3) Yesu ya koyar cewa, ga “ƙaramin garke,” ceto yana nufin za a tashe su zuwa rayuwa a sama su yi sarauta tare da Kristi a cikin Mulkinsa. (Luka 12:32) Ga sauran ’yan Adam, ceto yana nufin komowa ga kamiltaccen rai da kuma dangantaka da Allah wadda Adamu da Hauwa’u suka more kafin su yi zunubi. (Ayukan Manzanni 3:21; Afisawa 1:10) Rayuwa har abada a irin wannan yanayi na aljanna ita ce nufin Allah na asali ga ’yan Adam. (Farawa 1:28; Markus 10:30) Ta yaya dawowa ga irin yanayin nan zai yiwu?
Tushen Ceto—Fansar
6, 7. Menene matsayin Yesu a cikin cetonmu?
6 Ceto na har abada zai yiwu ta hadayar fansa ta Kristi ne kawai. Me ya sa? Littafi Mai-Tsarki ya yi bayani cewa lokacin da Adamu ya yi zunubi, ya ‘sayar’ da kansa da kuma yara da zai haifa, har da mu wa zunubi—wannan ya jawo bukatar fansa idan ’yan Adam za su sami wani muhimmin bege. (Romawa 5:14, 15; 7:14) Hadayar dabbobi a Dokar Musa alama ce ta cewa Allah zai ba da fansa ga dukan ’yan Adam. (Ibraniyawa 10:1-10; 1 Yohanna 2:2) Yesu ne hadayarsa ta cika waɗannan hotunan annabci. Mala’ikan Jehovah ya sanar kafin haihuwar Yesu: “Shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu.”—Matta 1:21; Ibraniyawa 2:10.
7 An haifi Yesu ta hanyar mu’ujiza ta budurwa Maryamu, kuma da yake Ɗan Allah ne, bai gāji mutuwa ba daga Adamu. Wannan gaskiyar tare da cikakken rayuwarsa ta aminci ta ba ransa tamani da ake bukata don a sayo ’yan Adam daga zunubi da kuma mutuwa. (Yohanna 8:36; 1 Korinthiyawa 15:22) Ba kamar dukan sauran mutane ba, ba a yi wa Yesu hukuncin kisa ba domin zunubi. Da son ransa ne ya zo duniya domin “shi bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28) Bayan ya yi hakan, Yesu da aka tashe shi daga matattu kuma aka naɗa shi sarauta yana da matsayin ya ceci dukan waɗanda suka cika farillan Allah.—Ru’ya ta Yohanna 12:10.
Menene Ake Bukata Domin a Sami Ceto?
8, 9. (a) Ta yaya Yesu ya amsa tambayar saurayi mai sarauta game da ceto? (b) Ta yaya Yesu ya yi amfani da wannan lokaci ya koyar da almajiransa?
8 Wani saurayi Ba’isra’ile mai dukiya mai sarauta ya taɓa tambayar Yesu: “Me zan yi domin in gāji rai na har abada?” (Markus 10:17) Tambayarsa ta nuna irin tunanin Yahudawa na lokacinsa—cewa Allah yana bukatar wasu kyawawan ayyuka kuma wai idan ka yi isashen waɗannan ayyukan, za ka sami ceto daga Allah. Amma irin wannan bauta, son kai ne yake motsa ta. Irin waɗannan ayyukan sun kasa ba da tabbataccen bege, tun da babu mutum ajizi da zai cika mizanan Allah.
9 Da yake amsa tambayar mutumin, Yesu ya tunatar da shi cewa ya kamata ya bi umurnan Allah. Da sauri kuwa saurayin mai sarauta ya gaya wa Yesu cewa ya kiyaye su tun daga ƙuruciya har yanzu. Amsarsa ta motsa Yesu ya ƙaunace shi. Yesu ya ce masa: “Abu ɗaya ka rasa: ka tafi, ka sayarda abin da ka ke da shi duka, ka ba fakirai, za ka sami wadata a sama: ka zo kuma, ka biyo ni.” Amma saurayin ya tafi yana baƙin ciki, “gama mai-arziki ne shi ainu.” Daga baya Yesu ya nanata wa almajiransa cewa yawan manne ma abin wannan duniyar yana hana hanyar samun ceto. Ya ƙara cewa babu wani wanda zai sami ceto domin ƙoƙarin kansa. Amma Yesu ya ci gaba ya tabbatar masu: “A wurin mutane ba shi yiwuwa, amma ga Allah ba haƙa ba ne: gama ga Allah abu duka ya yiwu.” (Markus 10:18-27; Luka 18:18-23) Ta yaya ceto zai yiwu?
10. Waɗanne abubuwa ne dole mu yi domin mu sami ceto?
10 Ceto kyauta ne daga wurin Allah, amma ba ya zuwa haka kawai. (Romawa 6:23) Da akwai wasu ainihin abubuwa da kowanenmu dole ya yi don ya cancanci karɓan kyautar. Yesu ya ce: “Gama Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” Kuma manzo Yohanna ya ƙara da cewa: “Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada; amma wanda ba ya yi biyayya ga Ɗan ba, ba za shi ganin rai ba.” (Yohanna 3:16, 36) Babu shakka, Allah yana bukatar bangaskiya da biyayya daga dukan wanda yake begen ya sami ceto na har abada. Ko waye dole ne ya tsai da shawarar karɓan fansa da kuma bin sawun Yesu.
11. Ta yaya mutum ajizi zai sami yardar Jehovah?
11 Tun da ba kamiltattu ba ne mu, ba shawarar zuciyarmu ba ce mu yi biyayya kuma ba ya yiwuwa mu yi cikakkiyar biyayya. Wannan shi ne dalilin da ya sa Jehovah ya yi tanadin fansa don ta rufe zunubanmu. Duk da haka, tilas ne mu ci gaba da ƙoƙarin rayuwa daidai da hanyoyin Allah. Kamar yadda Yesu ya gaya wa saurayi mai dukiya da sarauta, dole ne mu kiyaye umurnan Allah. Yin haka zai kawo yardan Allah ban da wannan ma zai kawo farin ciki, domin “dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba”; suna “wartsakewa.” (1 Yohanna 5:3; Misalai 3:1, 8) Duk da haka, ba shi da sauƙi a riƙe begen ceto.
‘Ku Dage Ƙwarai a Kan Bangaskiya’
12. Ta yaya begen ceto ya ƙarfafa Kiristoci su tsayayya wa jarabar lalata?
12 Almajiri Yahuda yana so ya rubuta wa Kiristoci na farko game da ‘ceto da suke riƙe da shi dukansu.’ Amma, hali na lalata da ya yi banga-banga ya tilasta shi ya yi gargaɗi wa ’yan’uwansa ‘su dage ƙwarai a kan bangaskiya.’ Hakika, don a sami ceto, ya wuce a ba da gaskiya kawai, a manne wa bangaskiyar Kirista na gaske, kuma yi biyayya lokacin da kome yake tafiya lau-lau. Ibadarmu ga Jehovah dole ne ta zama tana da ƙarfi sosai don ta taimake mu tsayayya wa rinjayar lalata. Duk da haka, lalata da fasikanci, rashin ɗa’a ga shugabannai, wariya, da kuma tantama ta rinjayi halayen ikklisiya na ƙarni na farko. Don ya taimake su su yi kokawa da waɗannan halaye, Yahuda ya yi gargaɗi wa ’yan’uwansa Kiristoci su sake riƙe burinsu a zuci: “Ƙaunatattu, cikin gina kanku bisa bangaskiyarku mafificin tsarki, kuna addu’a cikin Ruhu Mai-tsarki, ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Kristi zuwa rai na har abada.” (Yahuda 3, 4, 8, 19-21) Begen samun ceto zai ƙarfafa su wajen kokawarsu su kasance da tsabtacciyar ɗabi’a.
13. Ta yaya za mu nuna cewa ba mu ɗauki alherin Allah banza ba?
13 Jehovah Allah yana bukatar ɗabi’a mai kyau daga wurin waɗanda zai cece su. (1 Korinthiyawa 6:9, 10) Riƙe mizanan ɗabi’a na Allah, ba ya nufin kushe wa wasu. Ba mu ba ne za mu tsai da shawarar inda ’yan’uwanmu bil Adam ya dawwama. Allah ne zai yi wannan, kamar yadda Bulus ya gaya wa Hellenawa a Atina: “Ya sanya rana, inda za ya yi ma duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙaddara”—Yesu Kristi. (Ayukan Manzanni 17:31; Yohanna 5:22) Idan muna rayuwa da bangaskiya ga fansar Yesu ba mu da dalilin tsoron ranar shari’a da take zuwa. (Ibraniyawa 10:38, 39) Abu mafi muhimmanci shi ne “kada ku karɓi alherin Allah [sulhunmu da shi ta wurin fansa] banza” ta ƙyale kanmu mu jarabu zuwa yin munanan tunani ko kuma halaye. (2 Korinthiyawa 6:1) Ƙari ga haka, ta wurin taimaka wa wasu su sami ceto, muna nuna cewa ba mu ɗauki alherin Allah banza ba. Ta yaya za mu taimake su?
Yaɗa Begen Ceto
14, 15. Waye Yesu ya ba su aikin bisharar ceto?
14 Da ya ɗauko ayar annabi Joel, Bulus ya rubuta: “Dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” Sai ya daɗa cewa: “Ƙaƙa fa za su kira bisa ga wanda ba su bada gaskiya gareshi ba? kuma ƙaƙa za su bada gaskiya ga wanda ba su ji ba? ƙaƙa za su ji kuwa in ba mai-yin wa’azi ba?” A wasu ayoyi daga baya, Bulus ya nuna cewa bangaskiya ba ta zuwa haka kawai; maimakon haka, tana zuwa ta “wurin ji ne” wato, “maganar Kristi.”—Romawa 10:13, 14, 17; Joel 2:32.
15 Waye zai kai “maganar Kristi” ga al’ummai? Yesu ya bayar da wannan aikin ga almajiransa—waɗanda an riga an koya masu wannan “maganar.” (Matta 24:14; 28:19, 20; Yohanna 17:20) Lokacin da muke wa’azin Mulkin da kuma aikin almajirantarwa, muna yin abin da manzo Bulus ya rubuta ne, wannan karon ya ɗauko ne daga ayar Ishaya: “Ina misalin jamalin ƙafafu na masu-kawo bishara ta alheri!” Ko da mutane da yawa ba su karɓi bisharar da muka kawo masu ba, ƙafafunmu ‘jamali’ ne ga Jehovah.—Romawa 10:15; Ishaya 52:7.
16, 17. Waɗanne nufi biyu ne aikinmu na wa’azi yake cikawa?
16 Yin wannan aikin ya cika abubuwa biyu masu muhimmanci. Na farko, bisharar dole a yi wa’azinta saboda a ɗaukaka sunan Allah domin waɗanda suke son ceto su san inda za su juya don ceto. Bulus ya fahimci wannan ɓangaren aikin. Ya ce: “Gama haka Ubangiji ya umurce mu cewa, Na sanya ka domin hasken Al’ummai. Domin ka kawo ceto har iyakacin duniya.” Saboda haka, tun da yake mu almajiran Kristi ne, kowanne dole ya kai saƙon ceto ga mutane.—Ayukan Manzanni 13:47; Ishaya 49:6.
17 Na biyu, wa’azin bisharar ya kafa tushen shari’a na adalci na Allah. Game da wannan shari’ar, Yesu ya ce: “Amma sa’anda Ɗan mutum za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajarsa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi ya kan rarraba tumaki da awaki.” Ko da yake, shari’a da kuma rarraba tumaki da awaki za a yi su ne ‘sa’anda Ɗan mutum ya zo cikin darajarsa,’ aikin wa’azi yana ba wa mutane zarafi a yau na gano ’yan’uwan Kristi na ruhaniya don su yi aiki wajen tallafa masu domin nasu madawwamin ceto.—Matta 25:31-46.
Riƙe “Tabbatawar Bege”
18. Ta yaya za mu riƙe ‘begenmu na ceto’ da marmari?
18 Yin wa’azi da muke yi da ƙwazo hanya ce ɗaya ta taimaka mana mu riƙe begenmu da kyau. Bulus ya rubuta: “Muna kuwa so kowane ɗayanku shi nuna wannan ƙwazo zuwa ga tabbatawar bege har ƙarshe.” (Ibraniyawa 6:11) Bari kowannenmu, ya saka ‘kwalkwali, bege na ceto ke nan’ kuma mu dinga tuna cewa “Allah ba ya ƙaddara mu ga fushi ba, amma ga samun tsira ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi.” (1 Tassalunikawa 5:8, 9) Ya kamata mu bi gargaɗin Bitrus : “Ku natsu, kuna ɗamaracen gindin hankalinku, ku kafa begenku sarai a kan alherin da a ke kawo maku.” (1 Bitrus 1:13) Dukan waɗanda suka yi haka za su ga cikar ‘begensu na ceto’ gaba ɗaya!
19. Menene za mu bincika a cikin talifinmu na gaba?
19 A yanzu dai, yaya za mu ɗauki sauran lokaci da ya rage wa wannan tsarin? Ta yaya za mu yi amfani da wannan lokaci mu samo ceto wa kanmu da kuma wasu? Za mu bincika waɗannan tambayoyi a cikin talifinmu na gaba.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Me ya sa dole ne mu riƙe ‘begenmu na ceto’ da kyau?
• Menene ceto ya ƙunsa?
• Menene ya kamata mu yi domin mu sami kyautar ceto?
• Menene aikinmu na wa’azi yake cim ma daidai da nufin Allah?
[Hotuna a shafi na 20]
Ceto ya wuce tsira kawai daga halaka