Begen Tashin Matattu Yana Da iko
“Ina lissafta dukan abu hasara, . . . in san [Yesu Kristi], da ikon tashinsa.”—FILIBBIYAWA 3:8-10.
1, 2. (a) Shekaru da yawa da suka shige, yaya wani limami ya kwatanta tashin matattu? (b) Ta yaya za a yi tashin matattu?
A FARKON shekara ta 1890, ’yan jarida sun ba da rahoto game da huɗuba na musamman da wani limami ya bayar a Brooklyn, New York, U.S.A. Ya ce wai tashin matattu ya ƙunshi tara ƙasusuwa da kuma naman mutane da suka taɓa zama jikin mutum da kuma bayar da sabon rai, ko ya halaka da wuta ne ko a haɗari, ko dabban daji ne ya cinye ko kuma ya zama taki ma. Mai wa’azin ya ce a wasu sa’o’i 24 na rana, iska za ta zama baƙa domin tana ɗauke da hannaye, damutsai, ƙafafuwa, yatsu, ƙasusuwa, tsoka, da kuma fatun mutane biliyoyi da suka mutu. Ɓarin nan za su riƙa neman wancan ɓarin jiki. Sai kurwa ta zo daga sama da kuma jahannama don su shiga cikin waɗannan jiki da suka tashi daga matattu.
2 Ba hankali cikin zancen tashin matattu ta wurin tattara ɓangarorin jiki, kuma mutane ba su da kurwa da ba ta mutuwa. (Mai-Wa’azi 9:5, 10; Ezekiel 18:4) Jehovah, Allah mai ta da matattu, ba ya bukatar sake tattara ɓangarorin jiki da dā suke jikin mutum. Zai iya yin sabon jiki ga waɗanda aka tashe su. Jehovah ya ba wa Ɗansa Yesu Kristi, ikon ta da matattu, da damar samun rai madawwami. (Yohanna 5:26) Saboda haka Yesu ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya bada gaskiya gareni, ko ya mutu, za shi rayu.” (Yohanna 11:25, 26) Alkawari ne mai faranta rai! Yana taimaka mana mu jure wa gwaji har ma mu fuskanci mutuwa da amincinmu na Shaidun Jehovah.
3. Me ya sa Bulus ya kāre koyarwan tashin matattu?
3 Tashin matattu bai jitu da ra’ayin cewa mutane suna da kurwa da ba ta mutuwa ba—ra’ayin da ɗan falsafa na Helenanci Plato yake da shi. To, me ya faru lokacin da manzo Bulus ya yi wa manyan Hellenawa wa’azi a Tudun Arasa Atina, da ya yi magana game da Yesu, ya ce Allah ya ta da shi? Labarin ya ce: “Ananan sa’anda suka ji zancen tashin matattu, waɗansu suka yi ba’a.” (Ayukan Manzanni 17:29-34) Da yawa da suka ga Yesu Kristi da ya tashi suna da rai, kuma duk da ba’a, sun yi shaidar cewa ya tashi daga matattu. Malaman ƙarya da suke tarayya da ikklisiyar Korinta suka musanci tashin matattu. Saboda haka Bulus ya yi tsari mai ƙarfi ga wannan koyarwan Kirista a 1 Korinthiyawa sura ta 15. Nazarin wannan muhawararsa a hankali ya tabbatar cewa begen tashin matattu tabbatacce ne kuma ba wani abin musu.
Tabbaci Mai Ƙarfi na Tashin Yesu Daga Matattu
4. Wane tabbaci Bulus ya bayar na waɗanda suka ga tashin Yesu daga matattu?
4 Ka lura da yadda Bulus ya fara muhawararsa. (1 Korinthiyawa 15:1-11) Sai dai ko Korinthiyawan sun zama masu bi babu dalili, in ba haka ba za su riƙe bisharar ceto gam gam. Kristi ya mutu domin zunubanmu, aka binne shi, kuma aka tashe shi. Hakika, Yesu da ya tashi daga matattu ya bayyana wa Kefas (Bitrus), “kana ga goma sha biyu.” (Yohanna 20:19-23) Wasu 500 sun gan shi, wataƙila lokacin da yake ba da umurni: ‘Ku je, ku almajirantar.’ (Matta 28:19, 20) Yaƙub ya gan shi, kamar yadda dukan sauran manzanni amintattu suka gan shi. (Ayukan Manzanni 1:6-11) Yesu ya bayyana ga Shawulu a kusa da Dimashƙu “kamar ga wanda an haife shi bakwaini”—kamar dai an ɗauke shi zuwa rayuwar ruhu. (Ayukan Manzanni 9:1-9) Korinthiyawa sun zama masu bi domin Bulus ya yi masu wa’azi ne, kuma sun karɓi bisharar.
5. Yaya Bulus ya yi tunani yadda yake rubuce cikin 1 Korinthiyawa 15:12-19?
5 Ka lura da dalili da Bulus yake da shi. (1 Korinthiyawa 15:12-19) Tun da waɗanda suka shaida da idanunsu sun yi wa’azin cewa an tashi Kristi daga matattu, yaya kuma za a ce babu tashin matattu? Idan ba a ta da Yesu daga matattu ba, to ashe wa’azinmu da bangaskiyarmu duk banza ne, kuma mu maƙaryata ne waɗanda suka yi shaidan zur ga Allah cewa ya ta da Kristi. Idan ba za a ta da matattu ba, ‘ashe har yanzu muna cikin zunubanmu,’ kuma waɗanda suka mutu domin Kristi sun halaka ke nan. Bugu da ƙari, “idan cikin wannan rai kaɗai mun yi bege ga Kristi, mun fi dukan mutane ban tausayi.”
6. (a) Menene Bulus ya faɗa wajen ba da tabbacin tashin Yesu daga matattu? (b) Menene “maƙiyi na ƙarshe,” kuma ta yaya za a kawar da ita?
6 Bulus ya tabbatar da tashin Yesu daga matattu. (1 Korinthiyawa 15:20-28) Idan aka ta da Kristi ‘ ’ya’yan fari’ na waɗanda suke barci cikin mutuwa, za a ta da wasu ma. Kamar yadda mutuwa ta zo ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya Adamu, haka tashin matattu ma yake ta wurin mutum ɗaya—Yesu. Waɗanda na shi ne za a tashe su lokacin bayyanarsa. Kristi ya kawar da “dukan hukunci, da dukan sarauta, da dukan iko” da suke gaba da mulkin mallaka na Allah kuma ya yi Sarauta har sai Jehovah ya sarayar da kome ƙarƙashin ikonsa. Har “maƙiya na ƙarshe”—mutuwa da aka gāda daga Adamu—za a shafe ta ta wurin hadayar Yesu. Sai Kristi ya miƙa wa Allahnsa kuma Ubansa Mulkin, ya sarayar da kansa ‘domin Allah ya zama kome da kome.’
Baftisma Domin Matattu?
7. Su waye suka yi “baftisma saboda matattu,” kuma menene wannan yake nufi a gare su?
7 An tambayi abokan gaban tashin matattu: “Ƙaƙa waɗannan za su yi waɗanda a ke yi masu baftisma saboda matattu?” (1 Korinthiyawa 15:29) Bulus bai nufa cewa rayayyu suna yin baftisma a maimakon matattu ba, domin almajiran Yesu dole ne kowannensu ya yi koyi, ya gaskata, kuma ya yi baftisma. (Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 2:41) Shafaffu Kiristoci sun yi “baftisma saboda matattu” ta wurin nitso cikin rayuwa da za ta kai su ga mutuwa da tashi daga matattu. Irin wannan baftismar tana farawa lokacin da ruhun Allah ya saka begen sama a zukatansu kuma zai ƙare sa’anda aka tashe su daga matattu zuwa rayuwar ruhu da babu mutuwa a sama.—Romawa 6:3-5; 8:16, 17; 1 Korinthiyawa 6:14.
8. Menene Kiristoci za su iya tabbatawa da shi idan ma Shaiɗan da bayinsa suka kashe su?
8 Kamar yadda kalmomin Bulus suka nuna, begen tashin matattu ya sa Kiristoci suke jimre wa haɗari da mutuwa kullum domin aikin wa’azin Mulki. (1 Korinthiyawa 15:30, 31) Sun sani cewa Jehovah zai iya ya tashe su idan ya ƙyale Shaiɗan da bayinsa suka kashe su. Allah ne kaɗai zai iya halaka kurwansu, ko ransu, a Jahannama, wadda take nufin madawwamiyar halaka.—Luka 12:5.
Bukatar Zama a Farke
9. Idan begen tashin matattu zai zama da ikon ƙarfafa a rayuwarmu, dole mu guje wa menene?
9 Begen tashin matattu ya ƙarfafa Bulus. Sa’anda yake Afisus, magabtansa wataƙila sun jefa shi a wani fili ya yi faɗa da dabbar daji. (1 Korinthiyawa 15:32) Idan hakan ya faru, an cece shi, kamar yadda aka ceci Daniel daga zakuna. (Daniel 6:16-22; Ibraniyawa 11:32, 33) Tun da ya yi begen tashin matattu, Bulus ba shi da hali irin na ’yan riddan Yahuda a zamanin Ishaya. Suka ce: “Gara mu ci mu sha, gobe za mu mutu.” (Ishaya 22:13, Septuagint) Idan begen tashin matattu zai zama da ikon ƙarfafa a rayuwarmu kamar yadda ya yi a rayuwar Bulus, dole mu guje wa waɗanda ba su da halin kirki. “Kada ku yaudaru,” Bulus ya yi kashedi. “Zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Korinthiyawa 15:33) Hakika, wannan ƙa’ida ta shafi kowane ɓangaren rayuwa.
10. Ta yaya begenmu na tashin matattu zai ci gaba?
10 Ga waɗanda suke shakkar tashin matattu, Bulus ya ce: “Ku farka daga magagi zuwa adalci, ku bar zunubi; gama waɗansu ba su da sanin Allah: ina faɗin wannan domin in kunyatarda ku.” (1 Korinthiyawa 15:34) Wannan “zamani na ƙarshe,” muna bukatar mu yi ayyuka cikin jituwa da cikakken sanin Allah da kuma Kristi. (Daniel 12:4; Yohanna 17:3) Wannan zai sa begenmu na tashin matattu ya ci gaba.
Ta da Matattu da Wani Irin Jiki?
11. Ta yaya Bulus ya kwatanta tashin shafaffun Kiristoci daga matattu?
11 Bulus ya amsa wasu tambayoyi a gaba. (1 Korinthiyawa 15:35-41) Wataƙila don ya sa a yi shakkar tashin matattu, matambayi zai yi tambaya: “Ƙaƙa ake tada matattu? da wane irin jiki su ke zuwa?” Kamar yadda Bulus ya nuna, iri da aka shuka a ƙasa mutuwa yake yi ya canja ya zama tsiro. Hakanan, mutumin da ya zama ɗa a ruhu dole sai ya mutu. Kamar yadda shuka za ta tsiro daga iri ta zama sabuwar jiki, haka jikin shafaffun Kiristoci da aka tayar ya bambanta daga jiki mai tsoka na mutane. Ko da yake yana da jiki kamar wanda yake da shi kafin ya mutu, an tashe shi sabuwar halitta da jiki na ruhu da zai iya zama a sama. Waɗanda za a tashe su a duniya za a tashe su da jikin mutane.
12. Me ake nufi da furcin nan “jikuna na sama” da kuma “jikuna na duniya”?
12 Kamar yadda Bulus ya ce, jikin mutane ya bambanta daga na dabbobi. Har ma tsokar dabbobi ya bambanta da wasu dabbobi. (Farawa 1:20-25) “Jikuna na sama” na halittu na ruhu ya bambanta a daraja daga “jikuna na duniya” mai tsoka. Da akwai bambanci a darajar rana, wata, da kuma taurari. Amma shafaffu da aka ta da su daga matattu suna da daraja mafi girma.
13. In ji 1 Korinthiyawa 15:42-44, menene aka shuka kuma menene aka tayar?
13 Bayan ya faɗi bambanci, Bulus ya daɗa: “Hakanan kuma tashin matattu ya ke.” (1 Korinthiyawa 15:42-44) Ya ce: “Ana shukarsa cikin ruɓewa; ana tashinsa cikin rashin ruɓa.” A nan Bulus wataƙila yana nufin rukunin shafaffu ne. An shuka cikin ruɓewa lokacin mutuwa, an tashe shi cikin daraja, babu zunubi. Ko da yake duniya ta ci musu mutunci, an tayar da su zuwa rayuwa ta sama kuma a bayyane tare da Kristi cikin daraja. (Ayukan Manzanni 5:41; Kolossiyawa 3:4) A lokacin mutuwa an shuka cikin “jiki mai-nama” kuma an tayar cikin “jiki mai-ruhaniya.” Tun da wannan ya tabbata ga Kiristoci haifaffu daga ruhu, za mu iya tabbata cewa wasu za a ta da su zuwa rayuwa a duniya.
14. Ta yaya Bulus ya gwada Kristi da Adamu?
14 Sai Bulus ya gwada Kristi da Adamu. (1 Korinthiyawa 15:45-49) Adamu, mutum na fari, “ya zama rayayyen rai.” (Farawa 2:7) “Adamu na ƙarshe”—Yesu—“ya zama ruhu mai-rayarwa.” Ya ba da ransa hadayar fansa, da farko, domin mabiyansa shafaffu. (Markus 10:45) Da suke mutane, suna ‘kama da wanda aka halitta da turɓaya,’ amma lokacin da aka tashe su daga matattu suka zama kamar Adamu na ƙarshe. Hakika, hadayar Yesu za ta amfani dukan mutane masu biyayya, haɗe da waɗanda aka tashe su cikin duniya.—1 Yohanna 2:1, 2.
15. Me ya sa Kiristoci shafaffu ba a tashin su da jiki mai nama da jini, kuma yaya ake tashin su a lokacin bayyanuwar Yesu?
15 Lokacin da Kiristoci shafaffu suka mutu, ba a tada su cikin jiki mai nama. (1 Korinthiyawa 15:50-53) Jiki mai nama mai ruɓa da jini ba ya gadon mara ruɓa da kuma Mulkin sama. Wasu shafaffu ba za su bukaci jira da daɗewa ba cikin barcin mutuwa. Da sun gama ayyukansu a duniya cikin aminci lokacin bayyanar Yesu, za a ‘sauya kamaninsu, farat ɗaya, da ƙyiftawar ido.’ A take za a ta da su zuwa rayuwa ta ruhu cikin rashin ruɓa da daraja. A ƙarshe, ‘amaryar’ Kristi za su cika 144,000.—Ru’ya ta Yohanna 14:1; 19:7-9; 21:9; 1 Tassalunikawa 4:15-17.
Nasara Bisa Mutuwa!
16. In ji Bulus da kuma annabawa na fari, menene zai faru da mutuwa da aka gāda daga wurin Adamu mai zunubi?
16 Bulus cikin nasara ya sanar da cewa za a haɗiye mutuwa har abada. (1 Korinthiyawa 15:54-57) Lokacin da masu ruɓa da mutuwa suka zama marasa ruɓa da marasa mutuwa, waɗannan kalmomin za su cika: ‘An haɗiye mutuwa har abada.’ “Ya mutuwa, ina nasararki? Ya mutuwa, ina ƙarinki?” (Ishaya 25:8; Hosea 13:14) Ƙarin mutuwa zunubi ne, ikon zunubi kuma Shari’a ce, wadda take yi wa masu zunubi hukuncin kisa. Amma saboda hadaya da kuma tashi daga matattu na Yesu, mutuwa da aka gada daga wurin Adamu ba za ta sake yin nasara ba.—Romawa 5:12; 6:23.
17. Ta yaya kalmomin 1 Korinthiyawa 15:58 suke aikawa a yau?
17 “Domin wannan, ’yan’uwana, masoyana,” Bulus ya ce, “ku kafu yadda ba ku kawuwa, kullum kuna yawaita cikin aikin Ubangiji, da shi ke kun sani wahalarku ba banza ta ke ba cikin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 15:58) Waɗannan kalmomin sun shafi raguwan shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” na Yesu ko sun mutu a kwanaki na ƙarshen nan. (Yohanna 10:16) Hidimarsu ta shelar Mulki ba banza take ba, domin tashin matattu yana jiransu. Tun da bayin Jehovah ne mu, bari mu shagala cikin aikin Ubangiji yayin da muke jirar ranar da za mu ce cikin farin ciki: “Ya mutuwa, ina nasararki?”
Begen Tashin Matattu Ya Cika!
18. Yaya ƙarfin begen Bulus ga tashin matattu?
18 Kalmomin Bulus da suke rubuce cikin 1 Korinthiyawa sura 15 sun ba da tabbacin cewa begen tashin matattu yana da iko a rayuwarsa. Ya tabbata cewa Yesu ya tashi daga matattu kuma wasu ma za su taso daga kabari. Kana da irin wannan tabbaci mai ƙarfi haka? Bulus ya mai da abin duniya ‘juji mai yawa’ kuma ‘ya lissafa dukan abu hasara’ domin ya ‘san Kristi da kuma ikon tashinsa daga matattu.’ Manzon ya yarda ya mutu kamar yadda Kristi ya mutu da begen ya sami ‘tashin farko daga matattu.’ Wanda mabiyan Yesu shafaffu 144,000 suka samu wannan. Hakika, an ta da su zuwa rayuwar ruhu a sama, sai kuma “sauran matattu” a za tashe su a duniya.—Filibbiyawa 3:8-11; Ru’ya ta Yohanna 7:4; 20:5, 6.
19, 20. (a) Waɗanne mutane ne da aka yi rubutu game da su cikin Littafi Mai-Tsarki za a tashe su a duniya? (b) Wa ka ke sauraron tashinsa daga matattu?
19 Begen tashi daga matattu ya zama tabbata mai ɗaukaka ga shafaffu waɗanda suka kasance da aminci har mutuwarsu. (Romawa 8:18; 1 Tassalunikawa 4:15-18; Ru’ya ta Yohanna 2:10) Waɗanda suka tsira daga “babban tsananin” za su ga cikar begen tashin matattu a duniya lokacin da ‘teku zai ba da matattu da ke cikinsa, mutuwa kuma da Hades su ba da waɗanda suke cikinsu.’ (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 13, 14; 20:13) Tsakanin waɗanda za a tashe su zuwa rai a duniya da akwai Ayuba, wanda ya yi rashin yara maza bakwai da mata uku. Ka ga yadda zai yi farin cikin yi musu maraba—kuma za su yi murnar ganin suna da ƙarin ’yan’uwa bakwai maza da mata uku kyawawa!—Ayuba 1:1, 2, 18, 19; 42:12-15.
20 Lalle zai zama albarka ce lokacin da Ibrahim, Saratu, Ishaƙu da Rifkatu—hakika da wasu da yawa, har da ‘dukan annabawa’—aka tashe su zuwa rai a duniya! (Luka 13:28) Ɗaya cikin waɗannan annabawa shi ne Daniel wanda aka yi masa alkawarin tashin matattu a ƙarƙashin mulkin Almasihu. Daniel ya huta cikin kabari na wajen shekara 2,500 amma da ikon tashin matattu, ba da daɗewa ba zai tashi ‘cikin rabonsa’ wanda ɗaya ne “cikin sarakuna cikin dukan duniya.” (Daniel 12:13; Zabura 45:16) Abin farin ciki ne ka yi maraba kuma ga babanka, mamarka, ɗanka, ’yarka, ko kuma wasu ƙaunatattu naka da abokiyar gaba mutuwa ta ɗauke su!
21. Me ya sa ya kamata mu yi kirki babu jinkiri?
21 Wasu abokannan mu da ƙaunatattu wataƙila sun bauta wa Jehovah na shekaru da yawa kuma yanzu sun tsufa. Tsufa zai sa ya yi musu wuya su cika ƙalubale na rayuwa. Ƙauna ce idan muka ba su taimako da suke bukata a yanzu! Da haka ba za mu yi nadama a wata hanya ba idan mutuwa ta ɗauke su. (Mai-Wa’azi 9:11; 12:1-7; 1 Timothawus 5:3, 8) Za mu tabbata cewa Jehovah ba zai manta da kirkin da muka yi wa wasu ba, ko yaya shekarunsu da kuma yanayinsu. Bulus ya ce: “Yayinda mu ke da dama fa, bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.”—Galatiyawa 6:10; Ibraniyawa 6:10.
22. Har sai begen tashin matattu ya cika, menene ya kamata mu ƙuduri anniyar yi?
22 Jehovah ne “Uban jiyejiyanƙai, Allah na dukan ta’aziyya.” (2 Korinthiyawa 1:3, 4) Kalmarsa tana yi mana ta’aziyya kuma tana taimakonmu mu yi wa wasu ta’aziyya da ikon tashin matattu. Har sai mun ga cikar begen ta wajen ta da matattu a duniya, bari mu zama kamar Bulus, wanda ya ba da gaskiya ga tashin matattu. Bari mu zama musamman ma kamar Yesu wanda begensa ga ikon Allah na ta da matattu ya cika. Waɗanda suke cikin kabarbaru ba da daɗewa ba za su ji muryar Yesu kuma su fito. Bari wannan ya yi mana ta’aziyya kuma ya kawo mana farin ciki. Amma bisa kome, bari mu yi wa Jehovah godiya, wanda ya sa nasara ya kasance bisa mutuwa ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi.
Mecece Amsarka?
• Wane shaida ne Bulus ya bayar na waɗanda suka shaida tashin Yesu daga matattu?
• Menene “maƙiyi na ƙarshe,” kuma ta yaya za a kawar da ita?
• Ga Kiristoci shafaffu, menene aka shuka kuma menene aka tayar?
• Wanene da aka yi maganarsa cikin Littafi Mai-Tsarki za ka so ka gani lokacin da aka ta da su zuwa rai a duniya?
[Hoto a shafi na 14]
Manzo Bulus ya kāre zancen tashin matattu da kyau
[Hotuna a shafi na 18]
Tashin Ayuba, iyalinsa, da kuma wasu da yawa zai zama abin murna ƙwarai!