Abin Da Mulkin Allah Zai Yi
“Mulkinka ya zo, a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.”—MATIYU 6:10.
1. Menene Mulkin Allah da ke zuwa zai nufa?
LOKACIN da Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a don Mulkin Allah, ya san cewa zuwan mulkin zai kawo ƙarshen dubban shekaru na sarautar ’yan Adam na ’yanci daga Allah. A duk lokacin, ba a yin nufin Allah a duniya gabaki ɗayanta. (Zabura 147:19, 20) Amma bayan da aka kafa Mulkin a sama, za a yi nufin Allah a ko’ina. Lokaci mai ban tsoro na canji daga sarautar ’yan Adam zuwa na Mulkin Allah na samaniya yana kusatowa sosai.
2. Menene zai nuna canji daga sarautar ’yan Adam zuwa Mulkin Allah?
2 Abin da zai nuna wannan canji shi ne lokacin da Yesu ya kira “matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.” (Matiyu 24:21) Littafi Mai Tsarki bai faɗi tsawon lokaci da za ta ci ba, amma bala’in da za su faru lokacin za su yi muni fiye da kome da aka taɓa gani a duniya. A somawa ta matsananciyar wahalar, wani abu zai faru da zai ba yawancin mutane a duniya mamaki sosai: halakar dukan addinan ƙarya. Wannan ba zai ba Shaidun Jehovah mamaki ba, domin tun da daɗewa suna sauraron wannan. (Wahayin Yahaya 17:1, 15-17; 18:1-24) Matsananciyar wahalar za ta ƙare a Armageddon lokacin da Mulkin Allah zai rugurguje dukan tsarin Shaiɗan.—Daniyel 2:44; Wahayin Yahaya 16:14, 16.
3. Yaya Irmiya ya kwatanta abin da zai faru da waɗanda suka yi rashin biyayya?
3 Menene wannan yake nufi ga mutane “waɗanda suka ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar” game da Mulkin samaniya a hannun Kristi? (2 Tasalonikawa 1:6-9) Annabcin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ga masifa tana tahowa daga al’umma zuwa al’umma, hadiri kuma yana tasowa daga dukan manisantan wurare na duniya. Waɗanda Ubangiji ya kashe a wannan rana, za su zama daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a tattara gawawwakinsu a binne ba. Za su zama taki ga ƙasa.”—Irmiya 25:32, 33.
Ƙarshen Mugunta
4. Me ya sa ya dace Jehovah ya kawo ƙarshen wannan mugun tsari?
4 Shekaru dubbai yanzu, Jehovah Allah ya ƙyale mugunta, ya isa da mutane masu zuciyar kirki su ga cewa sarautar ’yan Adam bala’i ce. Alal misali, a ƙarni na 20 kaɗai, fiye da mutane miliyan 150 aka kashe a yaƙe-yaƙe, zanga-zanga, da wasu hargitsi da mutane suke yi, in ji wata majiya. An ga muguntar ’yan Adam musamman a lokacin Yaƙin Duniya na II yayin da aka kashe mutane miliyan 50, da yawa cikinsu sun yi mutuwar wulakanci a sansanin Nazi. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta, a zamaninmu ‘mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni suke yi.’ (2 Timoti 3:1-5, 13) A yau, lalata, laifi, mugunta, ɓatanci, da kuma rena mizanan Allah sun cika ko’ina. Saboda haka, ya dace sosai Jehovah ya kawo ƙarshen wannan mugun tsarin.
5, 6. Ka kwatanta mugunta da ta wanzu a Kan’ana ta dā.
5 Yanayin yanzu yana kama da na Kan’ana a cikin shekara 3,500 da suka shige. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sun yi wa gumakansu dukan abar ƙyamar da Ubangiji ke ƙi, har sun ƙona wa gumakansu ’ya’yansu mata da maza.” (Maimaitawar Shari’a 12:31) Jehovah ya gaya wa al’ummar Isra’ila: “Saboda muguntar waɗannan al’ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku.” (Maimaitawar Shari’a 9:5) Henry H. Halley Ɗan tarihin Littafi Mai Tsarki ya lura: “Bautar Ba’al, Ashtarot, da wasu allolin Kan’anawa ya haɗa da kisa mafi ban ƙyama; haikalansu wuraren mugunta ne.”
6 Halley ya nuna yadda muguntarsu take da yawa, gama a cikin ɗaya irin wurare masu yawan nan, ’yan tona ƙasa sun “gano tuluna da yawa da ke ɗauke da raguwar yara da aka yi hadaya da su ga Ba’al.” Ya ce: “Duk wuraren suka zama makabartar jarirai. . . . Kan’anawa suna bauta ta yawan lalata, kamar ka’ida na addini a gaban allolinsu; sa’annan kuma ta wurin kisan yaransu ’yan farinsu hadayu ne ga waɗannan alloli. Kamar dai, Kan’anawa sun zama irin su Saduma da Gwamarata ne sosai. . . . Ya kamata irin abin ban ƙyamar nan da kuma hali irin na dabban nan su sake wanzuwa kuwa? . . . ’Yan tonan ƙasa da suka tono kangon biranen Kan’anawa sun yi mamaki da Allah bai halaka su da wuri ba kafin lokacin da ya yi hakan.”
Gadān Duniya
7, 8. Ta yaya Allah zai tsabtacce wannan duniyar?
7 Yadda Allah ya tsabtacce Kan’ana, jim kaɗan zai tsabtacce dukan duniya ya kuma ba da duniya ga waɗanda suka yi nufinsa. “Mutane adalai, masu kamewa, su ne za su zauna ƙasarmu. Amma Allah zai fizge mugaye daga ƙasar.” (Karin Magana 2:21, 22) Mai zabura kuma ya ce: “A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe . . . Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar, su ji daɗin cikakkiyar salama.” (Zabura 37:10, 11) Za a kuma cire Shaiɗan, don “kada ya ƙara yaudarar al’ummai, har dai shekarun nan dubu su ƙare.” (Wahayin Yahaya 20:1-3) Hakika, “duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.”—1 Yahaya 2:17.
8 A kammala bege mai girma na waɗanda suke so su zauna har abada a duniya, Yesu ya ce: “Albarka tā tabbata ga masu tawali’u, domin za su gaji duniya.” (Matiyu 5:5) Kamar dai yana maganar Zabura 37:29, wadda ta annabta: “Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar, su gāje ta har abada.” Yesu ya san cewa nufin Jehovah ne mutane masu zuciyar kirki su zauna cikin aljanna ta duniya har abada. Jehovah ya ce: “Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda ke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.”—Irmiya 27:5.
Sabuwar Duniya ta Ban Mamaki
9. Wace irin duniya ce Mulkin Allah zai kawo?
9 Bayan Armageddon, Mulkin Allah zai kawo “sabuwar ƙasa” ta ban mamaki inda “adalci zai yi zamansa.” (2 Bitrus 3:13) Lalle sauƙaƙawa ce mai girma ga waɗanda suka tsira daga Armageddon a cire wannan mugun tsarin abubuwa na zalunci! Za su yi farin cikin shiga sabuwar duniya ta adalci a ƙarƙashin Mulkin gwamnati ta samaniya, da albarka mai girma da nufin madawwamin rai a zuci!—Wahayin Yahaya 7:9-17.
10. Waɗanne mummunan abubuwa ne ba za su ƙara kasancewa ba a sarautar Mulki?
10 Mutane ba za su ƙara jin tsoron yaƙi, aikata laifi, yunwa, ko kuma dabbobi masu kai hari ba. “Zan yi alkawarin salama da [mutanena]. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar . . . Itatuwan saura za su yi ’ya’ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani. Za su zauna lafiya a ƙasarsu.” “Za su mai da takubansu garemani, māsunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace. Al’umma ba za ta ƙara fita zuwa yaƙi ba, ba za su ƙara koyon yaƙi ba. Kowa zai zauna gindin kurangar inabinsa da gindin ɓaurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi.”—Ezekiyel 34:25-28; Mika 4:3, 4.
11. Me ya sa za mu kasance da gaba gaɗi cewa cututtuka za su ƙare?
11 Ciwo, baƙin ciki, da mutuwa za a kawar da su. “Ba wanda zai zauna a ƙasarmu har ya ƙara yin kukan yana ciwo, za a kuma gafarta dukan zunubai.” (Ishaya 33:24) “[Allah] zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce. . . . ‘Kun ga, ina yin kome sabo.’ ” (Wahayin Yahaya 21:4, 5) Lokacin da yake duniya, Yesu ya nuna zai iya yin waɗannan abubuwa da iko da Allah ya ba shi. Da taimakon ruhu mai tsarki, Yesu ya yi tafiya a dukan ƙasar yana warkar da guragu da kuma masu ciwo.—Matiyu 15:30, 31.
12. Wane bege ne matattu suke da shi?
12 Yesu ya yi fiye da haka. Ya tashi matattu. Yaya mutane masu tawali’u suka yi? Yayin da ya tashi ’yar shekara 12, iyayenta “kuwa mamaki ya kama su.” (Markus 5:42) Wannan wani misali ne na abin da Yesu zai yi a duka duniya a ƙarƙashin sarautar Mulki, lokacin “za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (Ayyukan Manzanni 24:15) Ka yi tunanin mamaki mai girma da za a yi lokacin da za a mai da rukuni biye da rukuni na matattu zuwa rai kuma su sake haɗuwa da ƙaunatattunsu! Babu shakka za a yi aikin ilimantarwa mai girma a kula da Mulkin domin “ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji kamar yadda tekuna ke cike da ruwa.”—Ishaya 11:9.
An Kunita Ikon Mallakar Jehovah
13. Yaya za a nuna ikon Allah na sarauta?
13 A ƙarshen shekara dubu na sarautar Mulki, za a mai da azanci da jiki na iyalin ’yan Adam zuwa kamilcewa. Duniya duka za ta zama gonar Adnin, aljanna ke nan. Za a samu salama, farin ciki, kwanciyar hankali, da kuma jam’iyyar ’yan Adam mai kyau. Ba a taɓa ganin irin wannan a tarihin ’yan Adam ba kafin sarautar Mulki. Lalle wannan zai nuna bambanci na ƙwarai tsakanin shekaru dubbai da suka shige na sarautar zalunci na mutane da kuma sarautar shekara dubu mai ɗaukaka na Allah na Mulkin samaniya! Za a nuna gaba ɗaya cewa sarautar Allah ta Mulkinsa ya fi kyau a kome. Ikon Allah na sarauta, ikon mallakarsa, za a kunita gaba ɗaya.
14. Menene zai faru wa ’yan tawaye yayin da shekara dubu ta ƙare?
14 A ƙarshen shekara dubu, Jehovah zai ƙyale mutane kamiltattu su nuna wanda suka zaɓa za su bauta masa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za “a saki Shaiɗan daga ɗaurinsa.” Zai kuma yi ƙoƙarin ya yaudare mutane, wasu kuma za su zaɓi ’yanci daga Allah. Don kada ‘wahala ta taso kuma,’ Jehovah zai halaka Shaiɗan, aljanunsa, da duka waɗanda suka yi tawaye ga ikon mallakar Jehovah. Ba wanda zai ce ba a ba mutane da aka halaka har abada a lokacin zarafi ba, ko a ce mummunar tafarkinsu domin ajizanci ne ba. A’a, za su zama kamar Adamu da Hauwa’u kamiltattu, waɗanda da son rai suka zaɓi su yi tawaye ga sarautar Jehovah na adalci.—Wahayin Yahaya 20:7-10; Nahum 1:9.
15. Wace dangantaka ce amintattu za su yi da Jehovah?
15 A wata sassa, yawancin mutane za su zaɓa su ɗaukaka ikon mallakar Jehovah. Tun da an halaka duk ’yan tawaye, masu adalci za su tsaya a gaban Jehovah, da yake sun jimre gwajin ƙarshe na aminci. Jehovah zai amince da waɗannan amintattu ’ya’yansa maza da mata. Sai su koma dangantaka da Adamu da Hauwa’u suka yi da Allah kafin su yi tawaye. Sa’annan, Romawa 8:21 za ta cika: “Za a ’yantar da halitta kanta [mutane] ma daga bautar ruɓewa domin ta sami ’yancin nan na ɗaukaka na ’ya’yan Allah.” Annabi Ishaya ya annabta: “Ubangiji zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum.”—Ishaya 25:8.
Begen Rai na Har Abada
16. Me ya sa daidai ne a yi sauraron ladar rai na har abada?
16 Abu mai girma yana jiran masu aminci, sun san cewa Allah zai ba su abubuwan ruhaniya da abin duniya a yawalce har abada! Mai zabura ya faɗi daidai da ya ce: “Yana kuwa ba su isasshe, yakan biya bukatarsu [da ya dace] duka.” (Zabura 145:16) Jehovah ya ƙarfafa waɗanda suke aji na duniya su kasance da begen rai cikin Aljanna, kamar ɓangaren bangaskiyarsu a gare shi. Gaskiya ce cewa batun ikon mallakar Jehovah ya fi muhimmanci, bai gaya wa mutane su bauta masa ba tare da zaton samun lada ba. Duk cikin Littafi Mai Tsarki, aminci ga Allah da begen rai madawwami suna haɗe tare kamar ɓangare ne da dole ya kasance cikin bangaskiya ta Kirista ga Allah. “Wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa.”—Ibraniyawa 11:6.
17. Ta yaya Yesu ya nuna cewa daidai ne begenmu ya kiyaye mu?
17 Yesu ya ce: “Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.” (Yahaya 17:3) A nan ya haɗa sanin Allah da nufe-nufensa da albarka da wannan zai kawo. Alal misali, lokacin da wani mai laifi ya gaya wa Yesu ya tuna da shi in ya shiga cikin Mulkinsa, Yesu ya ce: “Za ka kasance tare da ni a Firdausi.” (Luka 23:43) Bai gaya wa mutumin ya kasance da bangaskiya kawai ba ko da bai samu lada ba. Ya san cewa Jehovah yana son bayinsa su kasance da begen rai madawwami a cikin aljanna ta duniya zai kiyaye su yayin da suke fuskantar gwaji dabam dabam a wannan duniya. Sauraron ladar, taimako da wajibi ne ga Kirista ya jimre.
Abin da Zai Faru a nan Gaba ga Mulkin
18, 19. Menene zai faru wa Sarkin da kuma Mulkin a ƙarshen Sarauta ta Shekara Dubu?
18 Da yake Mulkin, gwamnati ce a matsayi na biyu da Jehovah ya yi amfani da shi ya kawo duniya da mutane da suke zama ciki zuwa kamilcewa kuma ya sulhunta da su, wane aiki ne Sarki Yesu Kristi da sarakuna da firistoci 144,000 za su yi bayan Shekara Dubu? “Sa’an nan sai ƙarshen, sa’ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko. Domin kuwa lalle ne ya yi mulki, har ya take dukkan maƙiyansa.”—1 Korantiyawa 15:24, 25.
19 Lokacin da Kristi ya mayar wa Allah Mulkin, yaya za a fahimci nassosi da ya yi magana cewa zai dawwama? Abin da Mulkin ya cim ma zai kasance har abada. Za a ɗaukaka Kristi har abada saboda aikin da ya yi a kunita ikon mallaka na Allah. Amma da yake sa’annan an cire zunubi da mutuwa gaba ɗaya, an fanshe ’yan Adam, ba za a bukaci Mai Fansa kuma ba. Sa’annan kuma zai zamana an cika Sarauta ta Shekara Dubu sarai; saboda haka ba za a bukaci gwamnati da take matsayi na biyu ta kasance tsakanin Jehovah da mutane masu biyayya kuma ba. Da haka, “Allah ya tabbata shi ne kome da kome.”—1 Korantiyawa 15:28.
20. Yaya za mu san abin da zai faru a nan gaba ga Kristi da 144,000?
20 Wane aiki ne Kristi da abokan sarautarsa za su yi a gaba bayan Sarauta ta Shekara Dubu ta ƙare? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Duk da haka, mun tabbata cewa Jehovah zai ba su ƙarin gata na hidima da yawa a duk cikin halittarsa. Bari dukanmu a yau mu ɗaukaka ikon mallakar Jehovah mu samu rai madawwami, don a gaba, mu rayu mu san aikin da Jehovah zai ba Sarkin da sarakuna da firistoci abokansa, haɗe da duka sararin samaniya na ban mamaki!
Darussa don Maimaitawa
• A ƙarshe wace sarauta ce take matsowa kusa?
• Yaya Allah zai yi shari’ar mugaye da masu adalci?
• Wane yanayi ne zai kasance cikin sabuwar duniya?
• Ta yaya za a kunita ikon mallakar Jehovah sosai?
[Hotuna a shafi na 15]
“Za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka”
[Hoto a shafi na 16]
Amintattu za su koma ga dangantaka mai kyau da Jehovah