Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 11/1 pp. 19-24
  • Ra’ayin Allah Game Da Ɗabi’a Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ra’ayin Allah Game Da Ɗabi’a Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kyauta Daga Wajen Mahalicci Mai Ƙauna
  • Hani Daga Allah
  • Amfana Daga Dokokin Allah na Ɗabi’a
  • An Albarkaci Yusufu Domin Ɗabi’arsa
  • Ayuba Ya Yi ‘Alkawari da Idanunsa’
  • Budurwa Mara Aibi
  • Wani Bawa da Ya Yi Biyayya ga Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Jehobah Yana Taimaka Maka don Ka Yi Nasara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • An Jefa Yusufu A Kurkuku
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ya Kāre, Ya Tanadar Kuma Ya Jimre
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 11/1 pp. 19-24

Ra’ayin Allah Game Da Ɗabi’a Mai Tsarki

“Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.”—ISHAYA 48:17.

1, 2. (a) Yaya galibin mutane suke ɗaukar jima’i? (b) Wane ra’ayi Kiristoci suke da shi game da jima’i?

A YAU, a ɓangarori da yawa na duniya, tarbiyya ana ɗaukanta batu ne na kai. Mutane suna ɗaukan jima’i hanya ce ta nuna soyayya da za su iya yi duk lokacin da suka ga dama, ba abin da za a bari ga aure ba ne kawai. Suna jin cewa idan babu wanda zai ji rauni, daidai ne kowa ya yi halin da ya ga dama. A nasu ra’ayi, bai kamata a hukunta mutane ba game da tarbiyya, musamman ma idan ya zo ga zancen jima’i.

2 Waɗanda suka zo ga sanin Jehovah suna da ra’ayi dabam. Suna bin sharuɗan Nassosi domin suna ƙaunar Jehovah kuma suna so su faranta masa rai. Sun fahimci cewa Jehovah yana ƙaunarsu kuma yana ja-gorarsu domin amfanin kansu ne, ja-gorar da za ta amfane su da gaske kuma ta sa su farin ciki. (Ishaya 48:17) Tun da Allah ne tushen rai, daidai ne da suke zuba masa ido domin ja-gora game da yadda za su yi amfani da jikinsu, musamman ma a wannan batu da yake da alaƙa da ba da rai ga wasu.

Kyauta Daga Wajen Mahalicci Mai Ƙauna

3. Menene aka koya wa mutane da yawa a Kiristendam game da jima’i, kuma yaya wannan koyarwar take idan aka gwada da koyarwar Littafi Mai Tsarki?

3 Dabam da duniya ta yau da ba ta addini ba, wasu a cikin Kiristendam sun koyar da cewa jima’i abin kunya ne, zunubi ne, wai kuma “zunubi na ainihi” na lambun Adnin ruɗin da Hauwa’u ta yi wa Adamu na jima’i ne. Wannan ra’ayin ya fanɗare daga abin da hurarrun Nassosi suka ce. Labarin Littafi Mai Tsarki ya kira ma’aurata na farko “mutumin da matarsa.” (Farawa 2:25) Allah ya gaya musu su haifi ’ya’ya, yana cewa: “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya.” (Farawa 1:28) Ba zai kasance da kan gado ba a ce Allah ya umurci Adamu da Hauwa’u su haifi ’ya’ya kuma a ce ya hore su domin sun yi haka.—Zabura 19:8.

4. Me ya sa Allah ya ba wa mutane iyawar yin jima’i?

4 A umurnin da aka ba iyayenmu na farko, wanda aka maimaita wa Nuhu da ’ya’yansa, mun ga ainihin dalilin jima’i: don a haifi ’ya’ya. (Farawa 9:1) Ko da yake, Kalmar Allah ta nuna cewa bayinsa ma’aurata ba a wajabce su da yin jima’i kawai domin ƙoƙarin su haifi ’ya’ya ba. Irin wannan saduwar takan biya bukatu na motsin zuciya da na jiki kuma ta zama dalilin farin ciki ga ma’aurata. Hanya ce da za su nuna soyayya ga juna.—Farawa 26:8, 9; Karin Magana 5:18, 19; 1 Korantiyawa 7:3-5.

Hani Daga Allah

5. Waɗanne hani ne Allah ya yi ga ayyukan jima’i na mutane?

5 Ko da yake jima’i kyauta ne daga Allah, ba za a yi shi kawai ba babu kamewa ba. Wannan umurnin ya shafi har masu aure. (Afisawa 5:28-30; 1 Bitrus 3:1, 7) An haramta yin jima’i da wadda ba matarka ba. Littafi Mai Tsarki ya yi magana takamaimai a kan wannan batu. A Dokar da Allah ya ba al’ummar Isra’ila, an ce: “Kada ka yi zina.” (Fitowa 20:14) Daga baya, Yesu ya haɗa “fasikanci,” “zina” da “mugayen tunani” da suke fitowa daga zuciyar mutum, su suke ƙazamtar da shi. (Markus 7:21, 22) An hure manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci a Korintos: “Ku guji fasikanci.” (1 Korantiyawa 6:18) A wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa, Bulus ya rubuta: “Kowa ya girmama aure. Gādon aure kuwa ya zauna marar dauɗa, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su.”—Ibraniyawa 13:4.

6. A cikin Littafi Mai Tsarki, menene wannan kalmar “fasikanci” ya ƙunsa?

6 Me ake nufi da kalmar nan “fasikanci”? An juya ta daga kalmar Helenanci ne por·neiʹa, wadda wani lokaci ana amfani da ita ga jima’i tsakanin mutane da ba su yi aure ba. (1 Korantiyawa 6:9) A wasu wurare, kamar su Matiyu 5:32 da kuma Matiyu 19:9, kalmar tana da ma’ana mai girma kuma takan nufi zina, jima’i tsakanin dangi, da kuma jima’i da dabba. Jima’i kuma tsakanin mutane da ba su yi aure ba, kamar su tsotsan azzakari da kuma luwaɗi, da shashafa azzakarin wani, ana iya ce da su por·neiʹa. Dukan irin waɗannan ayyukan an haramta su—ko kai tsaye ko kuma ta sharaɗi—cikin Kalmar Allah.—Littafin Firistoci 20:10, 13, 15, 16; Romawa 1:24, 26, 27, 32.a

Amfana Daga Dokokin Allah na Ɗabi’a

7. Ta yaya muke amfana ta wajen kasancewa da tsabta ta ɗabi’a?

7 Yin biyayya ga umurnin Jehovah game da jima’i kaluɓale ne ƙwarai ga mutane ajizai. Mashahurin ɗan falsafa na Yahudawa na ƙarni na 12 mai suna Maimonides ya rubuta: “Babu wani hani a cikin Attaura [Dokar Musa] da yake da wuyan bi kamar saduwa da kuma yin jima’i da aka haramta.” Duk da haka, idan mun bi Allah, mu za mu amfana ƙwarai da gaske. (Ishaya 48:18) Alal misali, biyayya ga wannan umurnin yana taimako wajen kāre mu daga cututtuka da ake ɗauka ta wajen jima’i, wanda waɗansu cikinsu ba su da magani kuma suna iya kisa.b An kāre mu daga ɗaukar cikin shege. Amfani da hikima ta Allah yakan kawo tsabtacaccen lamiri. Yin haka za mu daraja kanmu kuma wasu za su daraja mu, har danginmu, matanmu, ’ya’yanmu, da kuma ’yan’uwanmu Kiristoci maza da mata. Hakanan kuma yana sa mu ɗaukaka hali mai kyau game da jima’i wanda zai ƙara farin ciki a cikin aure. Wata Kirista ta rubuta: “Gaskiya ta Kalmar Allah ita ce kāriya mafi kyau da muke da ita. Ina jiran in yi aure, kuma lokacin da na yi, zan yi fahariyar gaya wa Kirista da na aura ban yi fasikanci ba.”

8. Ta waɗanne hanyoyi ne halayenmu masu kyau za su ɗaukaka bauta mai tsarki?

8 Ta halaye masu kyau, za mu iya ƙaryata kushe bauta ta gaskiya da ake yi kuma mu jawo mutane zuwa wajen Allah da muke bauta masa. Manzo Bitrus ya rubuta: “Ku yi halin yabo a cikin al’ummai, don duk sa’ad da suke kushenku, wai ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah ran da alheri ya sauko musu.” (1 Bitrus 2:12) Idan ma waɗanda ba sa bauta wa Jehovah suka ƙi su yabi halayenmu masu kyau, za mu tabbata cewa Ubanmu na sama yana gani, yana yarda, har ma yana farin ciki ganin muna ƙoƙari mu bi umurninsa.—Karin Magana 27:11; Ibraniyawa 4:13.

9. Me ya sa za mu dogara ga umurnan Allah, ko da ba mu fahimci dalilinsu ba? Ka kwatanta.

9 Bangaskiya ga Allah ta ƙunshi tabbacin cewa ya san abin da ya fi mana kyau, idan ma ba mu fahimci dalilan da ya sa ya umurce mu a hanyar da ya yi ba. Ka yi la’akari da misalin da yake daga Dokar Musa. Wani umurni game da zangon sojoji shi ne ana bukatar a binne ba haya a bayan zangon. (Maimaitawar Shari’a 23:13, 14) Wataƙila Isra’ilawan sun yi mamakin irin wannan umurnin; wataƙila wasu ma sun ga cewa umurnin ba shi da amfani. Tun daga lokacin, kimiyyar ƙwayoyin rai ta fahimci cewa wannan dokar ta taimaka wajen tsabtacce magudana daga gurɓacewa kuma ta ba da kāriya daga cututtuka da ƙwari suke yaɗawa. Hakazalika, da akwai dalilai na ruhaniya, na zaman jama’a, na motsin zuciya, na jiki, da kuma na hankali da ya sa Allah ya ce jima’i sai a gādon aure. Bari mu bincika misalai kaɗan a cikin Littafi Mai Tsarki na waɗanda suka bi ɗabi’a mai kyau.

An Albarkaci Yusufu Domin Ɗabi’arsa

10. Wacece ta yi ƙoƙari ta yaudare Yusufu, kuma yaya ya amsa?

10 Mai yiwuwa ka san labarin Littafi Mai Tsarki na Yusufu, ɗan Yakubu. Yana ɗan shekara 17 ya zama bawan Fotifar, shugaban masu tsaron fadan Fir’auna na Masar. Jehovah ya albarkaci Yusufu, kuma ba da jimawa ba aka naɗa shi shugaba a gidan Fotifar. Lokacin da ya cika shekara 20, “Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani.” Ya kwashe wa matar Fotifar hankali, sai ta yi ƙoƙari ta yaudare shi. Yusufu ya gaya mata matsayinsa, ya yi mata bayani cewa in ya yarda zai ci amanar maigidansa kuma zai yi wa “Allah zunubi.” Me ya sa Yusufu ya yi tunani a wannan hanyar?—Farawa 39:1-9.

11, 12. Ko da yake babu rubucacciyar doka daga Allah da ta hana fasikanci da kuma zina, me ya sa tilas ne Yusufu ya yi tunani yadda ya yi?

11 Babu shakka, shawarar da Yusufu ya yi ba domin yana tsoron cewa mutane za su san abin da ya yi ba ne. Iyalin Yusufu suna da nisa sosai, kuma babansa yana tsammanin ya riga ya mutu. Idan Yusufu ya yi fasikanci, iyalinsa ba za su taɓa sani ba. Irin wannan zunubin wataƙila a ɓoye wa Fotifar da bayinsa maza, tun da akwai lokatan da ba sa zama a gida. (Farawa 39:11) Duk da haka, Yusufu ya san cewa irin wannan halin ba za a ɓoye wa Allah ba.

12 Yusufu wataƙila ya yi tunani ne a kan abin da ya sani game da Jehovah. Babu shakka ya san abin da Jehovah ya ce a lambun Adnin: “Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa, sun zama ɗaya.” (Farawa 2:24) Bugu da ƙari, mai yiwuwa Yusufu ya san abin da Jehovah ya gaya wa sarkin Filistiyawa wanda ya yi ƙoƙarin yaudarar kakar Yusufu Saratu. Jehovah ya gaya wa sarkin: “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce. . . . Ni na hana ka ka aikata zunubin, don haka ban yarda maka ka shafe ta ba.” (Farawa 20:3, 6; tafiyar tsutsa tamu ce) Ko da yake Jehovah bai ba da rubucacciyar doka ba, yadda yake ji game da aure a fayyace yake. Hankalin Yusufu, tare da muradinsa na son ya faranta wa Jehovah rai, ya sa ya ƙi lalata.

13. Me ya sa wataƙila bai yiwu Yusufu ya guje wa matar Fotifar ba?

13 Amma matar Fotifar, ta nace, tana yi masa magana “yau da gobe” ya kwana da ita. Me ya sa Yusufu bai guje matar ba kawai? To, ga bawa dai, yana da ayyuka da zai yi kuma ba abin da zai yi ya canja yanayinsa. Tabbaci daga masu haƙa ƙasa ya nuna cewa tsarin gidajen Masarawa ya tilasta wucewa ta tsakiyar gida kafin a kai rumbuna. Saboda haka, ƙila bai yiwu Yusufu ya guje wa matar Fotifar ba.—Farawa 39:10.

14. (a) Me ya sami Yusufu bayan ya gudu daga matar Fotifar? (b) Ta yaya Jehovah ya albarkaci Yusufu domin amincinsa?

14 Rana ta kai da suka kasance su biyu ne kawai a gida. Matar Fotifar ta kama Yusufu ta ce: “Ka kwana da ni.” Ya gudu. Ƙi da ya yi, ya yi wa matar ciwo, sai ta yi masa sharri wai ya yi ƙoƙarin ya yi mata fyaɗe. Menene sakamakon haka? Jehovah ya ba shi lada ne nan take saboda amincinsa? A’a. Aka jefa Yusufu a gidan yari aka sa masa mari. (Farawa 39:12-20; Zabura 105:18) Jehovah ya ga rashin gaskiyar da aka yi masa, daga baya ya ɗaukaka Yusufu daga gidan yari zuwa fada. Ya zama na biye da sarki a ƙasar Masar kuma aka albarkace shi da mata da ’ya’ya. (Farawa 41:14, 15, 39-45, 50-52) Bugu da ƙari, labarin amincin Yusufu an rubuta shi shekara 3,500 da suka shige domin bayin Allah su bincika tun daga lokacin. Albarka kuwa daga kiyaye dokokin Allah na adalci! Hakazalika, a yau ba kullum ne za mu ga amfanin amintacciyar ɗabi’a ba, amma za mu iya tabbata cewa Jehovah yana gani kuma zai albarkace mu a lokacinsa.—2 Tarihi 16:9.

Ayuba Ya Yi ‘Alkawari da Idanunsa’

15. Wane ‘alkawari Ayuba ya yi da idanunsa’?

15 Ayuba wani ne mai aminci. Lokacin gwaji da Iblis ya yi masa, Ayuba ya bincika rayuwarsa ya ce yana shirye ya sha horo, idan ya taka mizanan Jehovah a kan jima’i, ɗaya cikin wasu abubuwa. Ayuba ya ce: “Na yi alkawari da idanuna, me zai sa in ƙyafaci budurwa?” (Ayuba 31:1) Da wannan, Ayuba yana nufin cewa a aniyarsa ya ci gaba da aminci ga Allah, ya riga ya shawarta zai guje wa yin sha’awar mata. Hakika, zai ga mata a rayuwar yau da kullum kuma wataƙila ya taimake su idan suna bukatar taimako. Amma ƙyafatar budurwa domin jima’i bai ƙyale kansa ga wannan ba. Kafin gwajinsa ya soma, mutum ne mai arziki ƙwarai, “ya fi kowa a ƙasar gabas.” (Ayuba 1:3) Duk da haka, bai yi amfani da dukiya ya rinjayi mata da yawa ba. A bayyane ya ke sarai, bai yi amfani da damar yin lalata da budurwoyi ba.

16. (a) Me ya sa Ayuba abin koyi ne mai kyau ga Kiristoci masu aure? (b) Ta yaya halin maza a zamanin Malakai ya bambanta da na Ayuba, yau kuma fa?

16 Saboda haka, a lokacin farin ciki da kuma lokaci mai wuya, Ayuba ya nuna aminci a zancen ɗabi’a. Jehovah ya lura da haka kuma ya albarkace shi ƙwarai. (Ayuba 1:10; 42:12) Ayuba abin koyi ne ga ma’aurata Kiristoci, maza da mata! Babu mamaki da Jehovah yake ƙaunarsa haka! Akasin haka, halin mutane da yawa a yau ya yi daidai da abin da ya faru a zamanin Malakai. Wannan annabin ya kwatanta yadda magidanta da yawa suke sake matansu, sau da yawa domin su auri budurwa. Bagaden Jehovah ya cika da hawayen mata da aka sake su, kuma Allah ya la’anci waɗanda suka ci “amanar” abokiyar zamansu.—Malakai 2:13-16.

Budurwa Mara Aibi

17. Ta yaya Bashulamiya take kama da “lambu mai katanga”?

17 Bashulamiya ita ce mai riƙe aminci ta uku. Yarinya ce kyakkyawa, ba yaro makiyayi ne kaɗai ya yi sha’awarta ba amma har mai arziki sarkin Isra’ila, Sulemanu. A duk cikin labari mai kyau na Waƙar Waƙoƙi, Bashulamiyar ta kasance babu aibi, saboda haka, waɗanda suke kusa da ita suka ba ta daraja. Sulemanu da ta ƙi, aka hure shi da rubuta labarin. Makiyayi da take ƙauna shi ma ya ba ta daraja domin ɗabi’arta. Wani lokacin ya yi bimbini cewa Bashulamiyar kamar “lambu mai katanga” take. (Waƙar Waƙoƙi 4:12) A Isra’ila ta dā, kyawawan lambu sun ƙunshi tsiro iri iri na ciyayi, fure masu ƙanshi, da kuma manya manyan itatuwa. Irin waɗannan lambuna ana kewaye su da katanga sai dai ta ƙofa da ake rufewa ne kawai za a iya shiga. (Ishaya 5:5) Ga makiyayin, ɗabi’ar Bashulamiyar da kuma ƙaunarta suna kama da irin wannan lambun da yake da gwanin kyau. Ba ta da aibi ko kaɗan. Soyayyarta tana ba wa wanda zai zama mijinta ne kawai.

18. Menene labarin Yusufu, Ayuba, da kuma Bashulamiya ya tunasar da mu?

18 A aminci wajen ɗabi’a, Bashulamiya ta kafa misali mai kyau ga Kiristoci mata a yau. Jehovah ya ji daɗin tarbiyyar yarinya Bashulamiyar kuma ya albarkace ta kamar yadda ya albarkaci Yusufu da kuma Ayuba. Domin yi mana ja-gora, aka rubuta labaransu na aminci a cikin Kalmar Allah. Ko da yake ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na kasance da aminci a yau ba a rubuta su cikin Littafi Mai Tsarki, Jehovah yana da “littafin tarihin” domin waɗanda suke ƙoƙari su yi nufinsa. Kada mu manta cewa Jehovah yana “kasa kunne” kuma yana murna yayin da muka nace domin mu kasance masu tsarki a ɗabi’armu.—Malakai 3:16.

19. (a) Yaya ya kamata mu ɗauki tsabta ta ɗabi’a? (b) Menene za a tattauna a talifi na biye?

19 Ko da yake marasa bangaskiya za su yi ba’a, muna farin ciki a biyayyarmu ga Mahaliccinmu mai ƙauna. Muna da tarbiyya mafi kyau, tarbiyya ta ibada. Aba ce da ya kamata mu yi fahariya da ita, abar adanawa. Ta wajen ɗabi’a mai tsarki, za mu iya samun albarkar Allah kuma mu ci gaba da begen samun rai madawwami da albarka. Me za mu yi mu riƙe ɗabi’a mai tsarki, a hanyar da za ta yiwu? Talifinmu na gaba zai tattauna wannan muhimmiyar tambayar.

[Hasiya]

a Duba Hasumiyar Tsaro, ta Turanci fitar 15 ga Maris, 1983, shafuffuka 29-31.

b Abin baƙin ciki kuwa, akwai yanayin da Kirista mara laifi takan kamu da cuta da ake ɗauka ta wajen jima’i daga mijinta da ba mai bi ba ne wanda bai bi umurnin Allah ba.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Menene Littafi Mai Tsarki ya koyar game da jima’i?

• Menene kalmar nan “fasikanci” ta ƙunsa a cikin Littafi Mai Tsarki?

• Ta yaya muke amfana ta wajen riƙe ɗabi’a mai tsarki?

• Me ya sa Yusufu, Ayuba, da kuma budurwa Bashulamiya abin koyi ne ga Kiristoci a yau?

[Hoto a shafi na 21]

Yusufu ya guje wa lalata

[Hoto a shafi na 22]

Bashulamiya kama take da “lambu mai katanga”

[Hoto a shafi na 23]

Ayuba ya yi ‘alkawari da idanunsa’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba