Su Wanene Masu Hidima Na Allah A Yau?
“Iyawarmu daga Allah take, domin shi ne ya iyar mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari.”—2 KORANTIYAWA 3:5, 6.
1, 2. Wane hakki ne duka Kiristoci na ƙarni na farko suka sa hannu, yaya abubuwa suka canja?
A ƘARNI na farko a Zamaninmu, dukan Kiristoci sun sa hannu cikin hakki da take da muhimmanci—farilla ta yin wa’azin bishara. Dukansu shafaffu ne kuma masu hidima na sabon alkawari. Wasu suna da ƙarin hakki, irinsu koyarwa a cikin ikilisiya. (1 Korantiyawa 12:27-29; Afisawa 4:11) Iyaye suna da farillai masu girma cikin iyali. (Kolosiyawa 3:18-21) Amma duka suna sa hannu cikin muhimmin aikin wa’azi. A cikin Helenanci na asali na Nassosin Kirista, wannan hakki di·a·ko·niʹa ne—aiki, ko kuma hidima.—Kolosiyawa 4:17.
2 Da shigewar lokaci, abubuwa suka canja. Wani rukuni ya taso, da aka san da su limamai, waɗanda suka ajiye wa kansu gatar yin wa’azi. (Ayyukan Manzanni 20:30) Limaman kalilan ne cikin waɗanda suke kiran kansu Kiristoci. Yawancin aka san su da ’yan zauna ku ji. Yayin da an koyar wa ’yan zauna ku ji cewa suna da wasu farillai, haɗe da ba da kyauta don gudanar da limamai, yawancinsu sun zama masu ji kawai a batun yin wa’azi.
3, 4. (a) Yaya mutane a Kiristendam suke zama masu hidima? (b) Wanene ake ɗauka mai hidima a cikin Kiristendam, me ya sa abubuwa suka bambanta tsakanin Shaidun Jehovah?
3 Limamai suna da’awa su masu hidima ne (daga mai hidima, fassarar kalmar Latin di·aʹko·nos ne, “bawa”).a Domin haka suna sauke karatu daga kwaleji ko kuma taron ƙarawa juna sani sai a naɗa su ministoci. The International Standard Bible Encyclopedia ya ce: “ ‘Naɗa’ da ‘naɗawa’ suna nuni ga matsayi na musamman da ake ba wa ministoci da firistoci ta al’adu da aka kafa, da ya ƙunshi nanata ikon shelar Kalmar ko kuma a gudanar da al’adar addini, ko a yi dukansu.” Wanene ke naɗa ministocin? The New Encyclopædia Britannica ya ce: “A cocin da suka ci gaba da riƙe matsayin bishop, minista mai naɗawa ko yaushe bishop ne. A cocin mabiya Presbytery, ministocin ne suke naɗawa.”
4 Saboda haka, a cocin Kiristendam, gata na zama mai hidima na da iyaka sosai. Amma ba haka yake tsakanin Shaidun Jehovah ba. Me ya sa? Domin ba haka yake a ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko ba.
Su Wanene Ainihin Masu Hidima na Allah?
5. Bisa ga Littafi Mai Tsarki, waɗanda suke hidima sun ƙunshi su wanene?
5 Bisa ga Littafi Mai Tsarki, duka masu bauta wa Jehovah—na sama da na duniya—masu hidima ne. Mala’iku suna wa Yesu hidima. (Matiyu 4:11; 26:53; Luka 22:43) Mala’iku ma an “aika su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima.” (Ibraniyawa 1:14; Matiyu 18:10) Yesu mai hidima ne. Ya ce: “Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar.” (Matiyu 20:28; Romawa 15:8) Saboda haka, tun da yake mabiyan Yesu za su “bi hanyarsa,” ba abin mamaki ba ne su ma dole su zama masu hidima.—1 Bitrus 2:21.
6. Yaya Yesu ya nuna cewa almajiransa ya kamata su zama masu hidima?
6 Kafin ya hau sama, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku.” (Matiyu 28:19, 20) Almajiran Yesu za su zama masu almajirantarwa—masu hidima. Sababbin almajirai za su koyi su kiyaye duk iyakar abubuwa da Yesu ya umarta, haɗe da umurni na su je su almajirtar. Namiji ko tamace, babba ko yaro, almajirin Yesu Kristi na gaskiya zai zama mai hidima.—Yowel 2:28, 29.
7, 8. (a) Waɗanne nassosi ne suka nuna cewa duka Kiristoci na gaskiya masu hidima ne? (b) Waɗanne tambayoyi aka yi game da naɗawa?
7 Cikin jituwa da wannan, a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., duka almajiran Yesu, maza da mata, duk suna maganar “manyan al’amuran Allah.” (Ayyukan Manzanni 2:1-11) Ƙari ga haka, manzo Bulus ya rubuta: “Da zuci mutum ke gaskatawa ya sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa ya sami ceto.” (Romawa 10:10) Bulus ya yi wannan magana ba ga ajin limamai ba, amma “ga dukan ƙaunatattun Allah da ke Roma [ta dā].” (Romawa 1:1, 7) Hakanan ma, duka ‘tsarkaka da ke Afisa, amintattu cikin Almasihu Yesu’ za su “kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafun[su].” (Afisawa 1:1; 6:15) Duka waɗanda suka saurari wasiƙar da aka aika wa Ibraniyawa za su ‘tsaya da ƙarfi a kan bayyana yarda ga sa zuciyar nan tasu.’—Ibraniyawa 10:23.
8 Amma yaushe mutum yake zama mai hidima? A wata sassa, yaushe ake naɗa shi? Kuma wa ke naɗa shi?
Naɗa Mai Hidima—Yaushe?
9. Yaushe aka naɗa Yesu, kuma wanene ya naɗa shi?
9 Game da ko yaushe kuma wa ke naɗa mutum, yi la’akari da misalin Yesu Kristi. Ba shi da satifiket na naɗi ko kuma digiri daga wasu makarantu don a nuna cewa shi mai hidima ne, kuma ba mutum ne ya naɗa shi ba. To, me ya sa za mu iya cewa shi mai hidima ne? Domin kalmomin Ishaya da aka hura sun cika a kansa: “Ruhun Ubangiji na tare da ni, domin yā shafe ni ni yi wa matalauta bishara.” (Luka 4:17-19; Ishaya 61:1) Waɗannan kalmomi babu shakka sun nuna cewa an ba Yesu aikin bishara. Wa ya sa shi? Tun da yake ruhun Jehovah Allah ne ya shafe shi ya yi aikin, a bayyane yake cewa Jehovah Allah ne ya naɗa shi. Yaushe wannan ya faru? Ruhun Jehovah ya sauƙo kan Yesu lokacin da ya yi baftisma. (Luka 3:21, 22) Saboda haka, lokacin da ya yi baftisma ne aka naɗa shi.
10. Daga wanene Kirista mai hidima yake ‘cancanta sosai’?
10 Me kuma za a ce game da mabiyan Yesu na ƙarni na farko? Matsayinsu na masu hidima ma ya zo daga wajen Jehovah. Bulus ya ce: “Iyawarmu daga Allah take, domin shi ne ya iyar mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari.” (2 Korantiyawa 3:5, 6) Ta yaya Jehovah ya iyar masu bauta masa su zama masu hidima? Yi la’akari da misalin Timoti, wanda Bulus ya kira “bawan Allah kuma na al’amarin bisharar Almasihu.”—1 Tasalonikawa 3:2.
11, 12. Ta yaya Timoti ya yi girma na zama mai hidima?
11 Kalmomi na biye da aka aika wa Timoti ya taimake mu mu fahimci yadda ya zama mai hidima: “Amma kai kuwa ka zauna kan abin da ka koya, ka kuma haƙƙaƙe, gama ka san wurin waɗanda ka koye su, da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu.” (2 Timoti 3:14, 15) Tushen bangaskiyar Timoti, wanda zai motsa shi ya yi magana a fili, shi ne sani na Nassosi. Yin karatu ne kawai na mutum ake bukata don wannan? A’a. Timoti na bukatar taimako don ya samu cikakken sani da fahimta ta ruhu na abin da ya karanta. (Kolosiyawa 1:9) Da haka an ‘tabbatar da [Timoti] ya gaskata.’ Tun da yake ya san Littattafai ‘tun yana ɗan ƙaramin yaro,’ waɗanda suka koya masa da farko ƙila mamarsa ce da kakarsa, ubansa babu shakka ba mai bi ba ne.—2 Timoti 1:5.
12 Amma zama mai hidima da Timoti ya yi, ya ƙunshi fiye da haka. Abu ɗaya shi ne, bangaskiyarsa ta ƙarfafa ta wajen yin cuɗanya da Kiristoci a ikilisiyoyi da ke kusa da shi. Ta yaya muka sani? Domin lokacin da Bulus ya sadu da saurayi Timoti da farko, “shi kuwa ’yan’uwa da ke Listira da Ikoniya na yabonsa.” (Ayyukan Manzanni 16:2) Ƙari ga haka, a waɗannan kwanaki wasu ’yan’uwa sun rubuta wasiƙu zuwa ga ikilisiyoyi don su ƙarfafa su. Masu kula suna ziyararsu don su gina su. Irin waɗannan tanadodi na taimakon Kiristoci kamar Timoti su ci gaba a ruhaniya.—Ayyukan Manzanni 15:22-32; 1 Bitrus 1:1.
13. Yaushe aka naɗa Timoti ya zama mai hidima, me ya sa za ka ce ci gabansa na ruhaniya bai tsaya a wurin ba?
13 Saboda umurnin Yesu da ke rubuce a Matiyu 28:19, 20, za mu tabbata cewa a wani lokaci bangaskiyar Timoti ta motsa shi ya yi koyi da Yesu kuma ya yi baftisma. (Matiyu 3:15-17; Ibraniyawa 10:5-9) Wannan alamar keɓe kan Timoti ne ga Allah da dukan zuciyarsa. Da ya yi baftisma, Timoti ya zama mai hidima. Daga lokacin, rayuwarsa, ƙarfinsa, da kome da yake da shi na Allah ne. Wannan sashe na musamman ne a bautarsa, “tsarkakkan hidima.” Amma, Timoti bai tsaya kawai da ɗaukaka na zama mai hidima ba. Ya ci gaba da girma a ruhaniya, ya zama mai hidima na Kirista da ya manyanta. Wannan haka ne domin Timoti ya yi cuɗanya na kusa da Kiristoci manya kamar Bulus, nazari na kansa, da kuma aikin wa’azi da ya yi da ƙwazo.—1 Timoti 4:14; 2 Timoti 2:2; Ibraniyawa 6:1.
14. A yau, yaya wanda ‘yake da zuciyar kirki na samun rai madawwami’ yake ci gaba zuwa zama mai hidima?
14 A yau, naɗi don hidima na Kirista yana kama da hakkan. Waɗanda suke da ‘zuciyar kirki na samun rai madawwami,’ an taimake su su koyi game da Allah da nufe-nufensa ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki. (Ayyukan Manzanni 13:48) Mutumin ya koya ya yi amfani da ka’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarsa ya kuma yi addu’a mai ma’ana ga Allah. (Zabura 1:1-3; Karin Magana 2:1-9; 1 Tasalonikawa 5:17, 18) Yana tarayya da wasu masu bi kuma ya yi amfani da tanadodi da shirye-shirye da “amintaccen bawan nan mai hikima” ya yi. (Matiyu 24:45-47; Karin Magana 13:20; Ibraniyawa 10:23-25) Da haka yana ci gaba a tsarin koyarwa da aka shirya.
15. Menene yake faruwa yayin da mutum ya yi baftisma? (Dubi hasiya kuma.)
15 Bayan haka, ɗalibin Littafi Mai Tsarki, da ya riga ya gina ƙauna ga Jehovah Allah da bangaskiya mai ƙarfi a cikin hadayar fansa, zai so ya keɓe kansa gabaɗaya ga Ubansa na samaniya. (Yahaya 14:1) Yana yin wannan keɓewa a cikin addu’arsa sai kuma ya yi baftisma, alama a fili na abin da ya yi a ɓoye. Baftisma da ya yi, bikin naɗa shi ne domin daga lokacin ne aka san da shi bawa da ya keɓe kai sarai, di·aʹko·nos, na Allah. Dole ya kasance a ware daga duniya. (Yahaya 17:16; Yakubu 4:4) Ya miƙa jikinsa “hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah” babu ragi ko domin wani lada ba. (Romawa 12:1)b Shi mai hidima ne na Allah, yana yin koyi da Kristi.
Mecece Hidima ta Kirista?
16. Menene wasu hakkin Timoti na mai hidima?
16 Menene hidimar Timoti ta ƙunsa? Yana da ayyuka na musamman abokin tafiyar Bulus. Lokacin da ya zama dattijo, Timoti ya yi aiki tuƙuru a koyarwa da kuma ƙarfafa ’yan’uwa Kiristoci. Amma sashe na musamman na hidimarsa, yadda yake da Yesu da Bulus, shi ne wa’azin bishara da almajirantarwa. (Matiyu 4:23; 1 Korantiyawa 3:5) Bulus ya gaya wa Timoti: “Kai kuwa, sai ka natsu cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.”—2 Timoti 4:5, tafiyar tsutsa tamu ce.
17, 18. (a) A wace hidima Kiristoci suke sa hannu? (b) Yaya aikin wa’azi yake da muhimmanci ga Kirista mai hidima?
17 Haka yake da Kiristoci masu hidima a yau. Suna hidima a fili, aikin bishara, suna kai wasu ga ceto bisa hadayar Yesu da koya wa masu tawali’u su kira sunan Jehovah. (Ayyukan Manzanni 2:21; 4:10-12; Romawa 10:13) Suna tabbatarwa daga Littafi Mai Tsarki cewa Mulkin shi ne kawai begen mutane da suke wahala kuma suna nuna cewa ko a yanzu ma abubuwa za su fi kyau idan muka rayu bisa ka’ida ta ibada. (Zabura 15:1-5; Markus 13:10) Amma mai hidima Kirista ba ya neman kawar da matsalolin jama’a. Maimako, yana koyar da cewa ‘bin Allah da ya ke, shi ne ke da alkawarin rai na yanzu da na nan gaba.’—1 Timoti 4:8.
18 Gaskiya, yawancin masu hidima suna da ƙarin hanyoyi na hidima, wanda ƙila zai bambanta daga na wani Kirista. Da yawa suna da hakki na iyali. (Afisawa 5:21–6:4) Dattawa da bayi masu hidima suna da ayyuka a cikin ikilisiya. (1 Timoti 3:1, 12, 13; Titus 1:5; Ibraniyawa 13:7) Kiristoci da yawa suna taimakawa wajen gina Majami’un Mulki. Wasu suna da gata mai girma na yin aiki a ɗaya cikin iyalin Bethel na Watch Tower Society. Amma duka Kiristoci masu hidima suna sa hannu a wa’azin bishara. Ba a barin kowa. Sa hannu a wannan aikin ne yake nuna cewa mutum tabbatacce, Kirista ne mai hidima.
Halin Kirista Mai Hidima
19, 20. Wane irin hali ne dole Kirista mai hidima ya koya?
19 Yawanci ministocin Kiristendam suna tsammani za a ba su daraja na musamman, suna ɗaukan laƙabi irinsu “rafuren” (reverend) da “fada” ( father). Amma Kirista mai hidima ya san cewa Jehovah ne kaɗai ya cancanci a ji tsoronsa sosai. (1 Timoti 2:9, 10) Ba Kirista mai hidima da yake neman irin wannan daraja mai girma ko kuma yake biɗan wani laƙabi na musamman ba. (Matiyu 23:8-12) Ya san cewa ma’ana na musamman na di·a·ko·niʹa “hidima” ce. Aikatau da aka haɗa da shi wasu lokatai ana amfani da shi cikin Littafi Mai Tsarki game da hidima wadda mutum yake wa kansa, irinsu ba mutane abinci. (Luka 4:39; 17:8; Yahaya 2:5) Ko da an ɗaukaka yadda aka yi amfani da shi a hidima ta Kirista, di·aʹko·nos har ila bawa ne.
20 Saboda haka, babu Kirista mai hidima da yake da dalilin ɗaga kai. Kiristoci masu hidima na gaskiya—har da waɗanda suke da hakki na musamman a cikin ikilisiya—bayi masu tawali’u ne. Yesu ya ce: “Duk wanda ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. Wanda duk kuma ke so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku.” (Matiyu 20:26, 27) Lokacin da yake nuna wa almajiransa hali mai kyau da za su koya, Yesu ya wanke ƙafafunsu, ya yi aikin bawa mafi ƙanƙanta. (Yahaya 13:1-15) Wannan hidima ce ta tawali’u! Saboda haka, Kiristoci masu hidima suna bauta wa Jehovah Allah da Yesu Kristi cikin tawali’u. (2 Korantiyawa 6:4; 11:23) Suna nuna ƙasƙantar rai a yi wa juna hidima. Lokacin da suke wa’azin bishara, suna wa maƙwabtansu marasa bi hidima ba tare da son kai ba.—Romawa 1:14, 15; Afisawa 3:1-7.
Ka Jure a Hidima
21. Yaya aka saka wa Bulus don jimrewa a hidima?
21 A wajen Bulus, zama mai hidima na bukatar jimiri. Ya gaya wa Kolosiyawa cewa ya sha wuya sosai don ya yi musu wa’azin bishara. (Kolosiyawa 1:24, 25) Amma saboda ya jimre, mutane da yawa sun karɓi bishara kuma sun zama masu hidima. An haife su sun zama ’ya’yan Allah da ’yan’uwan Yesu Kristi, da zaton zama halitta ta ruhu tare da shi a sama. Lalle wannan lada ce mai girma don jimiri!
22, 23. (a) Me ya sa Kiristoci masu hidima a yau suke bukatar jimiri? (b) Wace albarka mai girma ce take zuwa daga jimiri na Kirista?
22 Waɗanda da gaske masu hidima na Allah ne suna bukatar jimiri a yau. Da yawa suna kokawa kullum don rashin lafiya ko kuma ciwo domin tsufa. Iyaye suna aiki tuƙuru—yawancinsu ba tare da abokin aure ba—don su yi renon yaransu. Da gaba gaɗi, yara suna tsayayya wa rinjaya da ba ta da kyau da suka kewaye su a makaranta . Kiristoci da yawa suna fuskantar tattalin arziki mai tsanani. Mutane da yawa suna shan adawa ko kuma fuskanci wahala saboda ‘zamanin ƙarshe da ake shan wuya ƙwarai’ na yau! (2 Timoti 3:1) Hakika, kusan masu hidima na Jehovah miliyan shida a yau za su iya faɗa tare da manzo Bulus: “Ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matuƙar jurewa.” (2 Korantiyawa 6:4) Kiristoci masu hidima ba su fid da zuciya ba. Za a yaba musu ƙwarai don jimrewarsu.
23 Ƙari ga haka, yadda yake da Bulus, jimiri yana kawo albarka mai girma. Ta wajen jurewa, muna adana dangantakarmu ta kusa da Jehovah kuma muna faranta masa rai. (Karin Magana 27:11) Muna ƙarfafa bangaskiyarmu kuma muna almajirantarwa, muna ƙara ga ’yan’uwanci na Kirista. (1 Timoti 4:16) Jehovah ya kiyaye masu hidimarsa ya kuma albarkaci hidimarsu a waɗannan kwanaki na ƙarshe. A sakamakon wannan an tara 144,000 na ƙarshe, kuma ƙarin miliyoyi suna da gaba gaɗin bege na more rai madawwami a aljanna a duniya. (Luka 23:43; Wahayin Yahaya 14:1) Gaskiya, hidima ta Kirista nuna jinƙan Jehovah ne. (2 Korantiyawa 4:1) Bari dukanmu mu ɗauke shi da tamani kuma mu yi godiya saboda amfaninsa zai kasance har abada.—1 Yahaya 2:17.
[Hasiya]
a Kalmar Helenanci di·aʹko·nos ita ce tushen kalmar “dikon,” matsayi ne a coci. A coci inda mata sun iya zama dikon, za a iya kiransu dikoniya.
b Ko da Romawa 12:1 yana nuni ne musamman ga shafaffu Kiristoci, ka’idar ma ga “waɗansu tumaki” ne. (Yahaya 10:16) Waɗannan ‘suna bin Jehovah su yi masa hidima, suna ƙaunar sunan Jehovah, don su zama bayinsa.’—Ishaya 56:6.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Wane hakki ne duka Kiristoci na farko suke da shi?
• Yaushe kuma wanene ke naɗa Kirista mai hidima?
• Wane hali ya kamata Kirista mai hidima ya koya?
• Me ya sa ya kamata Kirista mai hidima ya jure in yana fuskantar wahala?
[Hotuna a shafuffuka na 14, 15]
An koya wa Timoti Kalmar Allah tun yana ɗan yaro. Ya zama mai hidima da aka naɗa lokacin da ya yi baftisma
[Hoto a shafi na 16]
Baftisma alamar keɓe kai ga Allah ce kuma nuna an naɗa mutum ya zama mai hidima ne
[Hoto a shafi na 18]
Kiristoci masu hidima suna so su yi bauta