Jehovah Yana Ƙarfafa Masu Kasala
“[Jehovah] yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.”—ISHAYA 40:29.
1. Ka kwatanta ƙarfi da abubuwa da Allah ya halitta suke da shi.
ƘARFIN Jehovah ba shi da iyaka. Kuma abubuwa da ya halitta suna da ƙarfi sosai! Atam ɗan mitsitsi—dutsen da aka gina kome da shi—mitsitsi ne sosai da ɗigon ruwa yana ɗauke da atam biliyan biliyan har guda ɗari.a Dukan rai a duniya ya dangana ne a kan ƙarfi da yake samu daga ayyukan atam bisa rana. Amma yaya yawan ƙarfi da ake bukata daga rana don rayuwa a duniya? Duniya tana samun ƙarfi kaɗan ne kawai da rana take bayarwa. Duk da haka, ƙarfi kaɗan na Rana da yake sauka Duniya ya fi ƙarfi da ake amfani da shi a kamfanoni na dukan duniya sosai da sosai.
2. Ainihi, menene Ishaya 40:26 ya ce game da ikon Jehovah?
2 Ko mun yi tunani a kan atam ko kuma mun juya hankalinmu ga sararin samaniya mara iyaka, iko mai ban mamaki na Jehovah yana burge mu. Babu shakka da ya ce: “Ka dubi sararin sama a bisa! Wanene ya halicci taurarin da kake gani? Shi wanda yake musu ja-gora kamar sojoji, ya sani ko su guda nawa ne, yana kiran dukansu, kowanne da sunansa! Ikonsa da girma yake, ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba!” (Ishaya 40:26) Hakika, Jehovah “ikonsa da girma yake,” kuma shi ne Tushen ‘ƙarfi’ da aka yi amfani da shi wajen saka sararin samaniya ta wanzu.
Ana Bukatar Ƙarfi Fiye da na Kullum
3, 4. (a) Waɗanne abubuwa ne za su iya sa mu yi kasala? (b) Wace tambaya ce take bukatar bincike?
3 Yayin da ƙarfin Allah ba shi da iyaka, mutane suna kasala. Ko’ina da muka je, muna ganin mutane da suka kasala. Suna farkawa a kasalance, su je aiki ko makaranta a kasalance, kuma su kwanta barci ba kawai a kasalance ba amma da gajiya. Wasu suna alla-alla su samu zuwa wani wuri su samu ɗan hutu da suke bukata ƙwarai. Mu bayin Jehovah ma muna kasalancewa, domin rayuwarmu ta ibada tana bukatar ƙoƙari sosai. (Markus 6:30, 31; Luka 13:24; 1 Timoti 4:8) Da wasu abubuwa da yawa da suke janye mana ƙarfi.
4 Ko da yake mu Kiristoci ne, ba a kāre muke ba daga wasu matsaloli da galibin mutane suke fuskanta. (Ayuba 14:1) Ciwo, rashin kuɗi, ko kuma wasu wahalolin rayuwa suna iya sa mutum ya karaya, da kuma raunanar da take jawowa. Ƙari ga waɗannan kaluɓalen su ne gwaji da waɗanda ake tsananta musu don adalci suke fuskanta. (2 Timoti 3:12; 1 Bitrus 3:14) Domin matsi na kullum daga duniya da kuma hamayya ga aikinmu na wa’azin Mulki, wasu cikinmu wataƙila su naunaya har su ji kamar su rage hanzari a hidimar Jehovah. Ƙari ga haka, a ƙoƙarin ya sa mu rashin aminci ga Allah, Shaiɗan Iblis yana yin amfani da dukan zarafin da yake da shi. To, ta yaya za mu samu ƙarfi na ruhaniya da muke bukata don kada mu yi kasala mu daina?
5. Me ya sa ake bukatar fiye da ƙarfin mutane domin a yi hidimar Kirista?
5 Domin ƙarfi na ruhaniya, dole mu dogara ga Jehovah, Mahalicci mafi ƙarfi duka. Manzo Bulus ya nuna cewa hidimar Kirista za ta bukaci fiye da ƙarfi na kullum na mutane ajizai. Ya rubuta: “Wannan wadata da muke da ita kuwa cikin kasake take, wato jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.” (2 Korantiyawa 4:7) Shafaffu Kiristoci suna yin “aikin shelar sulhuntawa” tare da taimakon abokanansu waɗanda suke da begen zama a duniya. (2 Korantiyawa 5:18; Yahaya 10:16; Wahayin Yahaya 7:9) Tun da mu mutane ajizai muna yin aikin Allah kuma muna fuskantar tsanantawa, ba za mu iya yinsa da namu ƙarfi kawai ba. Jehovah yana taimaka mana ta wajen ruhunsa mai tsarki, ta haka raunanarmu tana ɗaukaka ikonsa. Kuma muna samun ta’aziyya ta wajen tabbacin da ya bayar “Ubangiji, . . . zai kiyaye mutanen kirki”!—Zabura 37:17.
‘Jehovah Shi ne Ƙarfinmu’
6. Ta yaya Nassosi suka ba mu tabbacin cewa Jehovah shi ne Tushen ƙarfinmu?
6 Ubanmu na samaniya “ikonsa da girma yake” kuma babu wuya zai iya ƙarfafa mu. Hakika an gaya mana: “[Jehovah] yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya. Har da waɗanda suke yara ma, sukan ji kasala, Samari sukan siƙe su fāɗi, Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa’ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, sa’ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.” (Ishaya 40:29-31) Domin ƙarin matsi, wani lokaci sai mu ji mun gaji kamar mai gudu wanda ƙafafunsa kamar ba za su iya ɗaukan shi zuwa gaba ba. Amma ƙarshen wannan gudu na rai yana nan gaba, kuma kada mu karaya. (2 Tarihi 29:11) Magabcinmu, Iblis, yana zagayawa kamar “zaki mai ruri,” kuma yana so ya hana mu. (1 Bitrus 5:8) Kada mu manta cewa ‘Jehovah shi ne ƙarfinmu kuma shi ne makāriyarmu,’ kuma ya yi tanadin abubuwa da yawa don ‘ya ba wanda ya kasala ƙarfi.’—Zabura 28:7.
7, 8. Wane tabbaci ne da akwai cewa Jehovah ya ƙarfafa Dauda, Habakuk, da kuma Bulus?
7 Jehovah ya ba Dauda ƙarfin da yake bukata ya ci gaba duk da tangarɗa mai girma da ya fuskanta. Da cikakken bangaskiya da tabbaci, Dauda ya rubuta: “Idan Allah yana wajenmu, za mu yi nasara, zai kori abokan gābanmu.” (Zabura 60:12) Jehovah kuma ya ƙarfafa Habakuk saboda ya cika aikinsa na annabci. Habakuk 3:19 ta ce: “Ubangiji Allah shi ne ƙarfina, ya sa ƙafafuna su zama kamar na bareyi, ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin maɗaukakan wurare.” Abin lura kuma misalin Bulus ne, wanda ya rubuta: “Zan iya yin kome albarkacin [Allah] wannan da yake ƙarfafata.”—Filibiyawa 4:13.
8 Kamar Dauda, Habakuk, da kuma Bulus, ya kamata mu ba da gaskiya a iyawar Allah ya ƙarfafa mu kuma a cikin ikonsa ya cece mu. Sanin cewa Ubangiji Jehovah Mamallaki Duka shi ne Tushen “ƙarfi,” bari yanzu mu bincika wasu hanyoyin da za mu samu ƙarfi na ruhaniya daga tanadi mai yawa da ya yi.
Tanadi na Ruhaniya don Ya Ƙarfafa Mu
9. Wane aiki littattafan Kiristoci suke yi wajen ciyar da mu?
9 Nazari mai kyau na Nassosi da taimakon littattafan Kirista zai iya ƙarfafa mu kuma ya raya mu. Mai Zabura ya rera waƙa: “Albarka ta tabbata ga mutumin . . . [wanda] yana jin daɗin karanta shari’ar Allah, yana ta nazarinta dare da rana. Yana kama da itacen da ke a gefen ƙorama, yakan ba da ’ya’ya a kan kari, ganyayensa ba sa yin yaushi, yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.” (Zabura 1:1-3) Kamar yadda dole ne mu ci abinci na zahiri domin mu samu ƙarfin jiki, dole ne mu ci abinci na ruhaniya da Allah ya yi tanadinsa ta Kalmarsa da kuma littattafan Kirista don mu adana ƙarfi na ruhaniya. Saboda haka, nazari mai ma’ana da kuma waswasi suna da muhimmanci.
10. Yaushe za mu samu lokacin nazari da waswasi?
10 Hakika waswasi bisa “zurfafan al’amuran Allah” suna ba da lada ƙwarai. (1 Korantiyawa 2:10) Amma yaushe za mu iya samun lokacin waswasi? Ɗan Ibrahim Ishaku “a gabatowar maraice, sai . . . ya fita saura ya yi tunani.” (Farawa 24:63-67) Mai Zabura Dauda ya yi ‘tunanin Allah cikin dare farai.’ (Zabura 63:6) Za mu iya mu yi nazarin Kalmar Allah kuma mu yi waswasi a kai da safe, da maraice, da dad dare—kai, a kowanne lokaci. Irin wannan nazarin da kuma waswasi suna kai wa ga wata tanadin ruhaniya na Jehovah na ba da ƙarfi—addu’a.
11. Me ya sa za mu ba wa addu’a a kai a kai muhimmanci ƙwarai?
11 Addu’a a kai a kai ga Allah yana taimakawa wajen ƙarfafa mu. Saboda haka mu “nace da addu’a.” (Romawa 12:12) Wani lokaci, muna bukatar mu yi takamaiman roƙo na hikima da kuma ƙarfin da ake bukata don mu jure wa gwaji. (Yakubu 1:5-8) Bari mu yi godiya ga Allah kuma mu yaba masa lokacin da muka lura da cikar nufinsa ko kuma muka ga cewa ya ƙarfafa mu mu ci gaba a hidimarsa. (Filibiyawa 4:6, 7) Idan muka kasance kusa da Jehovah cikin addu’a, ba zai taba ƙyale mu ba. Dauda ya rera waƙa, “na sani Allah ne mai taimakona.”—Zabura 54:4.
12. Me ya sa za mu roƙe Allah ruhunsa mai tsarki?
12 Ubanmu na samaniya yana ƙarfafa mu kuma yana ba mu ƙarfi ta wajen ruhunsa mai tsarki, ko kuma ƙarfin ikonsa. Bulus ya rubuta: ‘Na durƙusa a gaban Uban . . . ina addu’a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta Ruhunsa.’ (Afisawa 3:14-16) Ya kamata mu yi addu’a domin ruhu mai tsarki, da tabbacin cewa Jehovah zai albarkace mu da shi. Yesu ya yi tambaya: Idan yaro ya roƙi a ba shi kifi, wane uban da yake da ƙauna zai danƙa masa maciji? Hakika, babu. Saboda haka, ya kammala da cewa: “To, ku da kuke [masu zunubi ta haka] mugaye [sosai ko kuma kaɗan] ma kuka san yadda za ku ba ’ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.” (Luka 11:11-13) Bari mu yi addu’a da irin wannan tabbacin kuma kullum mu tuna cewa amintattun bayin Allah za a iya “ƙarfafa [su] matuƙa” da iko ta wajen ruhunsa.
Ikilisiya Tana Taimako Wajen Ƙarfafawa
13. Yaya ya kamata mu ɗauki taron Kirista?
13 Jehovah yana ƙarfafa mu ta wajen taro na Kirista a ikilisiya. Yesu ya ce: “Inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.” (Matiyu 18:20) Lokacin da Yesu ya yi wannan alkawarin, yana magana ne a kan al’amari da yake bukatar hankalin waɗanda suke ja-gora a cikin ikilisiya. (Matiyu 18:15-19) Duk da haka, kalmominsa sun shafi dukan taronmu, manyan taro, da kuma taron gunduma, waɗanda ake buɗe su kuma a rufe su da addu’a cikin sunansa. (Yahaya 14:14) Saboda haka gata ce a halarci waɗannan taron Kirista, ko mutane kaɗan ne a wajen ko dubbai. Saboda haka bari mu nuna godiyarmu ga waɗannan taron da aka tsara su su ƙarfafa mu a ruhaniya kuma su tada mu a tsimi mu yi ƙauna da nagarin aiki.—Ibraniyawa 10:24, 25.
14. Wace fa’ida muke samu daga ƙoƙarce-ƙoƙarcen dattawa Kiristoci?
14 Dattawa Kiristoci suna ba da taimako na ruhaniya da kuma ƙarfafawa. (1 Bitrus 5:2, 3) Bulus ya taimaka wa ikilisiyoyi da ya yi wa hidima kuma ya ƙarfafa su, kamar yadda masu kula masu ziyara suke yi a yau. Hakika, ya yi ɗokin saduwa da ’yan’uwansa mabiya saboda su ƙarfafa juna. (Ayyukan Manzanni 14:19-22; Romawa 1:11, 12) Mu nuna godiyarmu kullum ga dattawanmu da wasu Kiristoci masu ja-gora, waɗanda suke ɗaukan nauyi mai yawa wajen ƙarfafa mu a ruhaniya.
15. Ta yaya ’yan’uwa mabiya a cikin ikilisiyarmu suke zama ‘abin taimako wajen ƙarfafawa’?
15 ’Yan’uwa mabiya da suke ikilisiyarmu za su iya zama ‘abin taimako wajen ƙarfafawa.’ (Kolosiyawa 4:10, 11) Da yake su ‘abokane ne na gaskiya’ za su iya taimaka mana a lokatan wahala. (Karin Magana 17:17) Alal misali, lokacin da aka sallami bayin Allah 220 daga sansanin fursuna na Sachsenhausen a ƙarƙashin tsarin ’yan Nazi a shekara ta 1945, suka fuskanci tafiya a ƙar na mil 120. Sun yi tafiyar tare, mafiya ƙarfi su jawo mafiya raunana a wasu amalanke. Menene sakamakon haka? A tafiyar mutuwa da mutane fiye da 10,000 daga sansanin suka mutu, babu Mashaidin Jehovah ko ɗaya da ya mutu. Irin waɗannan labarai da aka rubuta suna cikin littattafan Watch Tower, har da Yearbook of Jehovah’s Witnesses da kuma Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, sun tabbatar da cewa Allah yana ƙarfafa mutanensa, saboda kada su zama gajiyayyu.—Galatiyawa 6:9.b
Ƙarfafa Daga Hidimarmu ta Fage
16. Ta yaya sa hannun a hidima a kai a kai yake ƙarfafa ruhaniyarmu?
16 Fita wa’azin Mulki a kai a kai yana ƙarfafa mu a ruhaniya. Irin wannan aikin yana taimaka mana mu mai da hankali ga Mulkin Allah kuma mu saka albarkar dawwama har abada a zuci. (Yahuza 20, 21) Alkawuran Nassosi da muke magana a kai a hidimarmu suna sa mu bege kuma za su iya sa mu ƙuduri aniyya kamar yadda annabi Mika ya yi, wanda ya ce: “Mu za mu bi Ubangiji Allahnmu [Jehovah] har abada abadin.”—Mika 4:5.
17. Waɗanne shawarwari aka bayar game da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida?
17 Dangantakarmu da Jehovah tana ƙarfafawa yayin da muka yi amfani sosai da Nassosi wajen koyar da wasu. Alal misali, lokacin da ka ke nazari na gida da taimakon littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, yana da amfani a karanta dukan nassosi da aka rubuta kuma a tattauna su. Wannan zai taimaki ɗalibin kuma ya ƙarfafa fahiminmu na ruhaniya. Idan ɗalibin ya iske shi da wuya ya fahimci wani ra’ayi na Littafi Mai Tsarki ko kuma wani kwatanci da aka yi, za a iya yin amfani da sashe fiye da ɗaya na nazari don a kammala wani babi a littafin nan Sanin. Lalle abin farin ciki ne ƙwarai mu shirya sosai kuma mu ƙara ƙoƙari mu taimake wasu su matso ga Allah!
18. Ka kwatanta yadda ake amfani da littafin nan Sanin sosai.
18 Kowacce shekara, ana amfani da littafin nan Sanin ƙwarai wajen taimakon dubbai su zama keɓaɓɓun bayin Jehovah, kuma wannan ya ƙunshi mutane da yawa waɗanda ba su da sani na Littafi Mai Tsarki. Alal misali, lokacin da yake yaro, wani mutumin Hindu a Sri Lanka ya ji wata Mashaidiya tana maganar Aljanna. Shekaru daga baya ya tunƙare ta, ba da daɗewa ba mijinta ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Hakika, wannan saurayin yana zuwa don nazarin kullum, har suka gama littafin nan Sanin a cikin ɗan lokaci. Ya fara halartar dukan taro, ya raba gari da addininsa na dā, ya zama mai shelar Mulki. Lokacin da ya yi baftisma, ya riga yana nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da wani idon sani.
19. Yayin da muka ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da farko, menene za mu tabbata?
19 Ƙwallafa rai ga ayyukan Mulki tana kawo mana farin ciki mai ƙarfafawa. (Matiyu 6:33) Ko da yake muna fuskantar gwaji iri iri, muna ci gaba da shelar bisharar da murna da kuma himma. (Titus 2:14) Da yawa cikinmu suna cika hakkinsu na aikin majagaba na cikakken lokaci, kuma wasu suna hidima a inda ake bukatar masu wa’azi sosai. Ko muna yaɗa al’amuran Mulki ta wannan hanyar ko, ta wasu hanyoyi, mun tabbata cewa Jehovah ba zai manta da ayyukanmu da kuma ƙauna da muka yi wa sunansa ba.—Ibraniyawa 6:10-12.
Ku Ci Gaba Cikin Ƙarfin Jehovah
20. Ta yaya za mu nuna cewa muna zuba wa Jehovah ido ya ba mu ƙarfi?
20 Ko ta yaya, bari mu nuna cewa mun saka rai ga Jehovah kuma mun zuba masa ido don ya ba mu ƙarfi. Za mu iya yin haka ta wajen ba da kanmu ga tanadi na ruhaniya da yake yi ta wajen “amintaccen bawan nan.” (Matiyu 24:45) Nazari na kanmu da na ikilisiya na Kalmar Allah da taimakon littattafan Kirista, addu’a daga zuci, taimako na ruhaniya daga dattawa, misalai masu kyau na amintattun ’yan’uwa mabiya, da kuma wa’azi a kai a kai a hidima suna tsakanin tanadin da suke ƙarfafa dangantakarmu da Jehovah kuma suke ba mu ikon ci gaba a hidimarmu mai tsarki.
21. Ta yaya manzo Bitrus da Bulus suka furta bukatar ƙarfi da Allah yake bayarwa?
21 Duk da ajizancinmu na ’yan Adam, Jehovah zai ƙarfafa mu mu yi nufinsa idan muka dogara a gare shi don taimako. Sanin cewa muna bukatar irin wannan taimakon, manzo Bitrus ya rubuta: “Duk mai yin hidima, ya yi da ƙarfin da Allah ya ba shi.” (1 Bitrus 4:11) Bulus ya nuna dogararsa ga ƙarfi da Allah yake bayar da ya ce: “Ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa’ad da nake rarrauna, a sa’an nan ne nake da ƙarfi.” (2 Korantiyawa 12:10) Bari mu nuna irin wannan tabbacin kuma mu ɗaukaka Ubangiji Jehovah Mamallaki Duka, wanda yake ba wa gajiyayye ƙarfi.—Ishaya 12:2.
[Hasiya]
a Wannan lambar, ta tsarin ƙirge na Amurka, shi ne lambar da sifiri 20 suke bin 1.
b Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa mutanen Jehovah suke bukatar fiye da ƙarfi na kullum?
• Wane tabbaci ne da akwai na Nassosi cewa Allah yana ƙarfafa bayinsa?
• Waɗanne tanadi ne na ruhaniya Jehovah ya yi don ya ƙarfafa mu?
• Ta yaya za mu nuna cewa muna zuba wa Allah ido don ya ƙarfafa mu?
[Hoto a shafi na 22]
Dangantakarmu da Jehovah tana yin ƙarfi yayin da muka yi amfani da Littafi Mai Tsarki muka koya wa wasu