A Ina Ƙaunarka Ta Tsaya?
“Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.”—MATIYU 22:39.
1. Idan muna ƙaunar Jehovah, me ya sa dole ne mu ƙaunaci maƙwabcinmu?
DA AKA tambayi Yesu wannene mafi girma cikin doka, ya amsa: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.” Sai ya ɗauko na biyu makamancin na farkon: “Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.” (Matiyu 22:37, 39) Hakika, ƙaunar maƙwabci lamba ce ta Kiristoci. Babu shakka, idan muna ƙaunar Jehovah, dole ne mu ƙaunaci maƙwabcinmu. Me ya sa? Domin muna nuna ƙaunarmu ga Allah ta yin biyayya da Kalmarsa, kuma Kalmarsa ta umarce mu mu ƙaunaci maƙwabcinmu. Saboda haka, idan ba mu ƙaunaci ’yan’uwanmu maza da mata ba, ƙaunarmu ga Allah ba za ta zama ta gaske ba.—Romawa 13:8; 1 Yahaya 2:5; 4:20, 21.
2. Wacce irin ƙauna ce ya kamata mu kasance da ita ga maƙwabcinmu?
2 Da Yesu ya ce mu ƙaunaci maƙwabcinmu, yana magana ne fiye da abokantaka. Kuma yana maganar ƙauna ce dabam da wadda take tsakanin iyalai ko kuma tsakanin mace da namiji. Yana magana ne game da irin ƙaunar da Jehovah yake da ita wa bayinsa waɗanda suka keɓe kai kuma waɗanda suke ƙaunarsa. (Yahaya 17:26; 1 Yahaya 4:11, 19) Marubuci Bayahude—wanda, kamar yadda Yesu ya lura, yana magana da basira—ya yarda da abin da Yesu ya ce ƙaunar Allah ta kamata ta kasance da “dukkan zuciya, da dukkan hankali da dukkan ƙarfi.” (Markus 12:28-34) Ya amsa daidai. Ƙauna da Kirista ya gina wajen Allah da kuma maƙwabci ta ƙunshi jiye-jiyenmu hankalinmu. Ana jin ta a zuci kuma hankali yake yi mata ja-gora.
3. (a) Ta yaya Yesu ya koyar da “masanin Attaura” cewa ya kamata ya samu ƙarin fahimi game da waɗanda yake gani maƙwabtansa ne? (b) Ta yaya misalin Yesu ya shafi Kiristoci a yau?
3 Kamar yadda Luka ya ba da rahoto, lokacin da Yesu ya ce ya kamata mu ƙaunaci ɗan’uwanmu, “wani masanin Attaura” ya yi tambaya: “To, wanene ɗan’uwa nawa?” Yesu ya amsa da wani misali. Wani mutum aka yi masa fashi, aka yi masa mugun dūka, aka bar shi rai ga hannun Allah a gefen hanya. Wani firist da kuma wani Balawe suka biyo ta wannan hanyar. Dukansu suka ƙyale shi. A ƙarshe, hanya ta kawo wani Basamariye, ya ga mutumin da aka yi wa rauni, ya yi masa kirki. Wanne ne cikin mutanen nan uku ya zama maƙwabcin mutumin da aka ji wa rauni? Amsar a bayyane take. (Luka 10:25-37) Wataƙila masanin Attaurar ya firgita da ya ji Yesu ya ce Basamariye zai iya zama maƙwabci mai kyau fiye da firist da kuma Balawe. Hakika, Yesu ya taimaki mutumin ne ya ƙaunaci maƙwabcinsa a babbar hanyar. Kiristoci ma suna ƙauna a wannan hanyar. Ka yi la’akari da dukan waɗanda suke ƙauna.
Ƙauna Cikin Iyali
4. A ina Kirista yake nuna ƙauna da farko?
4 Kiristoci suna ƙaunar waɗanda suke iyalinsu—mata suna ƙaunar mazansu, maza suna ƙaunar matansu, iyaye suna ƙaunar yaransu. (Mai Hadishi 9:9; Afisawa 5:33; Titus 2:4) Gaskiya ce, da akwai ƙauna a iyalai da yawa. Duk da haka, rahotannin kisan aure, ci wa mata ko miji mutunci, ƙyaliya ko kuma ci wa yara mutunci ya nuna cewa iyalai suna fuskantar alhini a yau, kuma ƙauna kawai na iyali ba za ta isa ta riƙe su tare ba. (2 Timoti 3:1-3) Domin iyalai su ci nasara a rayuwar iyali, Kiristoci suna bukatar nuna irin ƙaunar da Jehovah da kuma Yesu Kristi suke da shi.—Afisawa 5:21-27.
5. Ga wanene iyaye suke zuba ido domin taimako wajen renon ’ya’yansu, kuma menene sakamakon haka ga mutane da yawa?
5 Iyaye Kiristoci suna ganin ’ya’yansu amana ce daga Jehovah, kuma suna zuba masa ido wajen taimako domin renon yaran. (Zabura 127:3-5; Karin Magana 22:6) A wannan hanyar suna koyar ƙauna ta Kirista, wadda take taimakonsu su kāre ’ya’yansu daga rinjaya mai lalata da matasa suke faɗawa ciki. Sakamakon haka, iyaye Kiristoci sun yi murna kusan irin na wata uwa a Netherlands. Bayan ta ga baftismar ɗanta—ɗaya daga cikin mutane 575 da suka yi baftisma a Netherlands bara—ta rubuta wannan: “A wannan lokacin, jari na na shekara 20 da ya shige ya ba da riba. Dukan lokaci da kuma ƙarfi—tare da baƙin ciki, ƙoƙari, da azaba—yanzu an manta.” Ta yi farin ciki da cewa ɗanta da son ransa ya zaɓi ya bauta wa Jehovah. Adadin masu shela 31,089 da suka ba da rahoto a Netherlands bara ya haɗa da yawa da suka koyi su ƙaunaci Jehovah daga iyayensu.
6. Ta yaya ƙauna ta Kirista za ta taimaka a ƙarfafa gamin aure?
6 Bulus ya kira ƙauna “wadda dukkan kammala ke ƙulluwa a cikinta,” kuma za ta iya kiyaye aure har a lokatai na wahala. (Kolosiyawa 3:14, 18, 19; 1 Bitrus 3:1-7) Da wani mutum a Rurutu, wani ƙaramin tsibiri da yake nisan mil 450 daga Tahiti, ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah, matarsa ta yi hamayya ƙwarai. A ƙarshe, ta kwashi yaransu, ta bar shi, ta koma da zama a Tahiti. Duk da haka, ya nuna ƙaunarsa ta wajen aika musu kuɗi a kai a kai kuma yana yin waya ya tambaya ko akwai wani abin da ita da yaran suke bukata. Ta haka ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya cika hakkinsa na Kirista. (1 Timoti 5:8) Yana addu’a kullum iyalinsa su sake haɗuwa, a ƙarshe matarsa ta komo. Da ta dawo, ya bi da ita cikin “ƙauna, da jimiri, da kuma tawali’u.” (1 Timoti 6:11) Ya yi baftisma a shekara ta 1998, ya yi murna ƙwarai da matarsa ta yarda ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki daga baya. Wannan nazarin ɗaya ne cikin 1,351 da aka tafiyar cikin yankin da yake ƙarƙashin reshen da yake Tahiti a bara.
7. In ji wani mutum a Jamus, menene ya ƙarfafa aurensa?
7 A Jamus wani mutum ya yi hamayya da marmarin matarsa a gaskiyar Littafi Mai Tsarki kuma ya gaskata cewa Shaidun Jehovah suna so su ruɗe ta ne. Daga baya, ya rubuta zuwa ga Mashaidiya da ta fara magana da matarsa: “Na gode da ki ka gabatar da matata ga Shaidun Jehovah. Da farko, na damu domin na ji abubuwa da yawa da ba su da kyau game da su. Amma yanzu, da na halarci taronsu da matata, na fahimci cewa na yi kuskure. Na san cewa gaskiya nake sauraro, kuma ya ƙarfafa aurenmu ƙwarai.” Shaidun Jehovah 162,932 da suke Jamus—da kuma 1,773 da suke tsibiri da suke ƙarƙashin reshen Tahiti—sun haɗa da iyalai da yawa da suke haɗe cikin ƙaunar Allah.
Ƙauna ga ’Yan’uwanmu Kiristoci
8, 9. (a) Wanene ya koya mana mu ƙaunaci ’yan’uwanmu, kuma menene ƙauna take motsa mu mu yi? (b) Ka ba da misalin yadda ƙauna za ta taimaki ’yan’uwa su taimake kansu.
8 Bulus ya gaya wa Kiristoci na Tasalonika: “Ku kanku Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.” (1 Tasalonikawa 4:9) Hakika, waɗanda ‘Jehovah ya koya musu’ suna ƙaunar juna. (Ishaya 54:13) Suna furta ƙaunarsu a kan aikatawa yadda Bulus ya nuna yayin da ya ce: “Ku bauta wa juna da ƙauna.” (Galatiyawa 5:13; 1 Yahaya 3:18) Alal misali, suna yin haka lokacin da suke ziyarci ’yan’uwa da suke rashin lafiya, suna ƙarfafa masu baƙin ciki, suna tallafa wa raunannu. (1 Tasalonikawa 5:14) Ƙaunarmu ta gaske ta Kirista ta tallafa wajen girmar aljannarmu ta ruhaniya.
9 A ikilisiyar Ancón—ɗaya cikin ikilisiyoyi 544 a Ecuador—’yan’uwan sun nuna ƙaunarsu a zahiri. Lalacewar tattalin arziki ya bar su babu aiki ko kuɗi, sai masu shela suka shawarta su nemi kuɗi ta wajen sayar da abinci ga masunta lokacin da suke dawo daga kamun dare. Kowa ya sa hannu, har da yara. Sukan fara da ƙarfe 1:00 na dare saboda su gama girki da ƙarfe 4:00 na asubar fari lokacin da masuntan suka dawo. Kuɗin da ’yan’uwan suka samu suka raba a tsakaninsu bisa ga bukatunsu. Irin wannan taimakon ya nuna ƙaunar gaske ta Kirista.
10, 11. Ta yaya za mu nuna ƙauna ga ’yan’uwan da ba mu san su ba ma?
10 Ko da yake, ƙaunarmu ba ta tsaya ga Kiristoci da muka sani ba kawai. Manzo Bulus ya ce: ‘Ku ƙaunaci dukan ’yan’uwa.’ (1 Bitrus 2:17) Muna ƙaunar dukan ’yan’uwanmu maza da mata domin dukansu masu bauta wa Jehovah Allah ne tare da mu. Lokacin hargitsi zai ba mu zarafin nuna wannan ƙaunar. Alal misali, a cikin shekarar hidima ta 2000, ambaliya mai tsanani ta share Mozambique, kuma yaƙin basasa da yake ci gaba a Angola ya talautar da mutane da yawa. ’Yan’uwa da yawa da adadinsu 31,725 ne a Mozambique da kuma 41,222 a Angola su ma wannan abin ya shafe su. Saboda haka, Shaidu a Afirka ta Kudu da take maƙwabtaka da su sun aika musu da kayayyaki da yawa don su sauƙaƙa wa ’yan’uwansu wahalarsu. Gudummawa da suka bayar na “yalwarsu” da son rai ya nuna ƙaunarsu.—2 Korantiyawa 8:8, 13-15, 24.
11 Ana ganin ƙauna kuma a lokacin da ’yan’uwa a ƙasashe dabam dabam suka ba da kyauta domin gina Majami’un Mulki da Majami’un Babban Taro a ƙasashen da ba su da arziki. Solomon Islands misali ne a wannan. Duk da rashin kwanciyar hankali, Solomon Islands sun sami ƙarin masu shela kashi 6 bisa ɗari a bara da ƙolin 1,697. Suna shirin gina Majami’ar Babban Taro. Ko da yake da yawa cikin ’yan ƙasan suna gudu daga ƙasar, waɗanda suka ba da kai suka zo daga Australia su taimaka wajen ginin. A ƙarshe, waɗanda suka ba da kai dole su koma, amma sai da suka koya wa ’yan’uwa ’yan ƙasan yadda za su gama harshashen. An shigo da garun majami’ar daga Australia, kuma gama wannan kyakkyawan gini na bauta—a lokacin da an yi banza da wuraren da ake neman a yi gini—zai zama wa’azi ne mai kyau ga sunan Jehovah kuma ga ƙaunar ’yan’uwan.
Kamar Allah, Muna Ƙaunar Duniya
12. Ta yaya za mu yi koyi da Jehovah a halinmu ga waɗanda ba sa cikin imaninmu?
12 Ƙaunarmu ga iyalinmu da kuma ’yan’uwancinmu ne kawai? A’a, sai idan mu ba masu ‘koyi da Allah’ ba. Yesu ya ce: “Ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.” (Afisawa 5:1; Yahaya 3:16) Kamar Jehovah Allah, muna aikin ƙauna wajen duka—haɗe da waɗanda ba sa bin imaninmu. (Luka 6:35, 36; Galatiyawa 6:10) Game da wannan musamman, muna wa’azin bishara ta Mulki kuma muna gaya wa wasu babbar ƙauna da Allah ya nuna saboda su. Wannan zai kasance ceto ga kowanne da ya saurara.—Markus 13:10; 1 Timoti 4:16.
13, 14. Waɗanne labarai ne na ’yan’uwa da suka nuna ƙauna ga waɗanda ba Shaidu ba ne, har da takura wa kansu?
13 Ka yi la’akari da majagaba na musamman guda huɗu a Nepal. An aika su wani birni a kudu maso yammacin ƙasar, kuma cikin shekaru biyar da suka shige, sun nuna ƙaunarsu ta wajen wa’azi cikin haƙuri a birnin da kuma ƙauyuka da suke nesa. Don su kewaye yankinsu, sau da yawa suna tafiya sa’o’i da yawa a kan kekuna a lokacin zafi sosai. Ƙaunarsu da “naciyarsu ga aikata nagarta,” ya ba da lada da aka kafa rukunin nazarin littafi a ɗaya daga cikin ƙauyukan. (Romawa 2:7) A Maris 2000, mutane 32 suka zo su saurari jawabi ga jama’a daga mai ziyara da yake kula da da’irar. Nepal tana da masu shela 430 a bara—ƙarin kashi 9 bisa ɗari. A bayyane yake Jehovah yana ba da albarka ga ƙwazo da kuma ƙauna na waɗannan ’yan’uwa a wannan ƙasar.
14 A Colombia majagaba na musamman na ɗan lokaci suka je su yi wa’azi a tsakanin Indiyawa da ake kira Wayuu. Don su yi haka, dole su koyi sabuwar yare, amma damuwarsu ta ƙauna ta sami albarka da mutane 27 suka halarci jawabi ga jama’a duk da ruwan sama mai yawa da aka yi. Ƙwazo ta ƙauna da waɗannan majagaba suka nuna ya ƙara ƙashi 5 bisa ɗari da aka yi a Colombia da kuma adadin masu shela 107,613. A Denmark wata ’yar’uwa tsohuwa tana so ta yi shelar bishara tare da wasu, amma ta naƙasa. Amma bai hana ta ba, tana saduwa da mutane da suke da marmari ta wajen rubuta musu wasiƙa. A yanzu, tana rubuta tattaunawa da mutane 42 kuma tana tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki 11. Tana ɗaya daga cikin adadin masu shela 14,885 da suka ba da rahoto a Denmark a bara.
Ƙaunaci Magabtanka
15, 16. (a) Yaya Yesu ya ce zurfin ƙaunarmu zai zama? (b) Ta yaya ’yan’uwa waɗanda suke da izini suka bi da wani cikin ƙauna da ya yi tuhuma ta ƙarya a kan Shaidun Jehovah?
15 Yesu ya gaya wa masanin Attaura cewa Basamariye ma zai iya zama maƙwabci. A Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ci gaba kuma da ya ce: “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan’uwanka, ka ƙi magabcinka.’ Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin Sama.” (Matiyu 5:43-45) Har lokacin da wani yake hamayya da mu, muna ƙoƙarin mu “rinjayi mugunta da nagarta.” (Romawa 12:19-21) Idan zai yiwu, mu raba aba mafi muhimmanci da muke da ita da shi, gaskiyar.
16 A Ukraine wani talifi a cikin jaridar Kremenchuk Herald ya yi maganar Shaidun Jehovah wai ɗarika ce mai haɗari. Wannan ba abin wasa ba ne domin a Turai wasu suna maganar Shaidun Jehovah a wannan hanyar domin su rinjayi mutane a hana ayyukan Shaidun. Saboda haka, aka tunkari editan aka ce ya buga wani talifi ya gyara abin da aka ce a talifin. Ya yarda, amma da fitarsa, ya buga wata magana cewa talifi na ainihi an buga shi bisa gaskiya ne. ’Yan’uwa waɗanda suke da izini suka tunkaro shi da ƙarin bayani. A ƙarshe, editan ya fahimci cewa talifi na ainihin ba daidai ba ne, sai ya buga talifi da ya ƙaryata na farkon. Bi da shi da gaskiya da kuma kirki hanya ce ta ƙauna na magance wannan yanayin, kuma hakan ya kai ga sakamako mai kyau.
Ta Yaya Za Mu Koyi Ƙauna?
17. Me ya nuna cewa ba ko yaushe ba ne zai yi sauƙi mu nuna ƙauna ga wasu?
17 Lokacin da aka haifi jariri, iyayensa nan da nan za su ƙaunace shi. Bi da manya cikin ƙauna ba ko yaushe ba ne yake da sauƙin yi hakanan ba. Wataƙila saboda haka ne Littafi Mai Tsarki ya gaya mana a kai a kai mu yi ƙaunar juna—abu ne da dole mu koya. (1 Bitrus 1:22; 4:8; 1 Yahaya 3:11) Yesu ya san cewa za a gwada ƙaunarmu da ya ce ya kamata mu gafarta wa ɗan’uwanmu sau “bakwai har sau saba’in.” (Matiyu 18:21, 22) Bulus ma ya aririce mu mu riƙa “jure wa juna.” (Kolosiyawa 3:12, 13) Babu shakka da aka gaya mana: “Ku nace wa ƙauna”! (1 Korantiyawa 14:1) Ta yaya za mu yi wannan?
18. Menene zai taimake mu mu koyi yin ƙaunar wasu?
18 Da farko, mu riƙa tunawa da ƙauna da muke da ita ga Jehovah Allah. Wannan abu ne da zai motsa mu mu ƙaunaci maƙwabcinmu. Me ya sa? Domin idan muka yi hakan, wannan yana kawo ɗaukaka da yabo ga Ubanmu na samaniya. (Yahaya 15:8-10; Filibiyawa 1:9-11) Na biyu, za mu iya mu yi ƙoƙari mu ga abubuwa kamar yadda Jehovah yake ganinsu. Kowane lokaci da muka yi zunubi, mun yi zunubi ne ga Jehovah; duk da haka, sau da yawa yana gafarta mana kuma yana ƙaunarmu. (Zabura 86:5; 103:2, 3; 1 Yahaya 1:9; 4:18) Idan muka koyi ra’ayin Jehovah, za mu so mu ƙaunaci wasu kuma mu gafarta musu laifuffukansu a gare mu. (Matiyu 6:12) Na uku, za mu bi da wasu kamar yadda muke so su bi da mu. (Matiyu 7:12) Muna bukatar gafartawa sau da yawa, domin ajizancinmu. Alal misali, idan muka faɗi abin da ya yi wa wasu ciwo, muna sa rai za su tuna cewa kowa yana zunubi da harshensa a wasu lokatai. (Yakubu 3:2) Idan muna son mutane su bi da mu cikin ƙauna, ya kamata mu ma muna bi da su cikin ƙauna.
19. Ta yaya za mu nemi taimakon ruhu mai tsarki wajen koyon ƙauna?
19 Na huɗu, za mu iya biɗan taimakon ruhu mai tsarki domin ƙauna ɓangare ne na ’ya’yan ruhu mai tsarki. (Galatiyawa 5:22, 23) Abokantaka, ƙauna ta iyali, da kuma soyayya sau da yawa a take ne. Amma muna bukatar taimakon ruhun Jehovah domin mu koyi ƙauna da Jehovah yake da ita, ƙauna da take magami mai kyau ne. Za mu iya neman taimakon ruhu mai tsarki ta wajen karanta hurarren Littafi Mai Tsarki. Alal misali, idan muka yi nazarin rayuwar Yesu, za mu ga yadda ya bi da mutane, kuma za mu iya yin koyi da shi. (Yahaya 13:34, 35; 15:12) Ƙari ga haka, za mu iya roƙon Jehovah ya ba mu ruhu mai tsarki, musamman a yanayi da ya kasance mana da wuya mu nuna ƙauna. (Luka 11:13) A ƙarshe, za mu iya biɗan ƙauna ta wajen manne wa ikilisiyar Kirista. Kasancewa tare da ’yan’uwa maza da mata da suke da ƙauna zai taimake mu mu koyi ƙauna.—Karin Magana 13:20.
20, 21. Wace nuna ƙauna ce da ta fi Shaidun Jehovah suka yi a shekarar hidima ta 2000?
20 Bara, adadin masu shelar bishara 6,035,564 ne a dukan duniya. Shaidun Jehovah sun ba da sa’o’i 1,171,270,425 wajen neman mutanen da za su gaya wa bisharar. Ƙauna ce ta sa suka jimre wa zafi, ruwan sama, sanyi, lokacin da suke wannan aikin. Ƙauna ce ta motsa su suka yi magana da abokanan makarantarsu da kuma na aiki da kuma su tunkari baƙi a kan titi da kuma wasu wurare. Da yawa cikin waɗanda Shaidun suka ziyarta ba su da marmari, kaɗan daga cikinsu sun yi hamayya. Amma dai, wasu sun nuna marmari, saboda haka an koma ziyara 433,454,049 kuma an yi nazarin Littafi Mai Tsarki 4,766,631.a
21 Wannan lalle nuna ƙauna da Shaidun Jehovah suke da shi ga Allahnsu ne da kuma maƙwabtansu! Wannan ƙauna ba za ta taɓa yin sanyi ba. Mun tabbata cewa shekarar hidima ta 2001 za ta ga wa’azi mafi yawa ga ’yan Adam. Bari albarkar Jehovah ta ci gaba bisa amintattun kuma masu ƙwazo masu bauta masa, bari ‘duk abin da za su yi, su yi shi da ƙauna’!—1 Korantiyawa 16:14.
[Hasiya]
a Domin cikakken bayani game da rahoton shekarar hidima ta 2000, dubi taswira da take shafuffuka 28-31.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Waye muke koyi da shi lokacin da muka ƙaunaci maƙwabcinmu?
• Ina ya kamata ƙaunarmu ta kai?
• Waɗanne labarai ne suka nuna ƙauna ta Kirista?
• Ta yaya za mu koyi ƙauna?
[Hotuna a shafi na 25]
Ƙauna ta Kirista za ta iya riƙe iyali
[Hotuna a shafi na 27]
Ƙauna ta motsa mu mu gaya wa wasu begenmu