Taimaka Wa Gwauraye Mata Cikin Gwadawarsu
ƊAYA cikin labarai da aka fi sani na gwauraye mata shi ne labarin Littafi Mai Tsarki na Ruth da surukarta, Naomi. Matan dukan su gwauraye ne. Ba kawai Naomi ta yi rashin mijinta ba amma kuma da yaranta maza biyu, wanda ɗaya cikinsu ne mijin Ruth. Domin suna zama cikin jama’a manoma da ake dogara ga maza sosai, yanayinsu lalle mai tsanani ne.—Ruth 1:1-5, 20, 21.
Amma kuwa, Naomi tana da abuya ta musamman kuma mai ta’azantarwa, surukarta Ruth, wadda ta ƙi ta ƙyale ta. A kwana a tashi, Ruth ta zama wadda ta “fi ’ya’ya bakwai a gare [Naomi]”—ba kawai domin tana ƙaunarta ƙwarai ba amma kuma domin ƙaunarta ga Allah. (Ruth 4:15) Lokacin da Naomi ta ce Ruth ta koma wajen danginta Mowabawa da kuma abokai, Ruth ta amsa da furci mafi kyau na aminci da aka taɓa rubutawa: “Inda za ki tafi duka, nan za ni; inda za ki sauka, nan zan sauka: danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna: wurin da kika mutu, nan kuma in mutu, a kuma binne ni: Ubangiji ya sāka mini har ma gaba da wannan, idan ba mutuwa kaɗai ta raba ni da ke.”—Ruth 1:16, 17.
Halin Ruth bai faɗi gaban Jehovah Allah banza ba. Ya albarkaci ƙaramin iyalin da Naomi ce da Ruth, daga baya kuma Ruth ta auri Ba’israile Boaz. Naomi ce kuma ta yi renon yaronsu, wanda ya zama kakan Yesu Kristi, sai ka ce nata. Wannan tarihin misalin yadda Jehovah yake son gwauraye mata da suke matsowa kurkusa da shi kuma suke dogara a gareshi. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa yana daraja waɗanda suke ƙaunar gwauraye mata cikin wahalarsu. Saboda haka, yaya mu a yau za mu iya toƙara wa gwauraye mata da suke tsakaninmu?—Ruth 4:13, 16-22; Zabura 68:5.
Takamaimai Amma Kada a Mallaka
Yayin da ake ba da taimako ga gwauruwa, zai fi kyau ya zama a bayyane kuma takamaimai ban da mallakarsu. Ka guje wa furcin nan, “Ki gaya mini idan kina bukatar wani abu.” Daidai yake da gaya wa wani da ke jin sanyi da kuma yunwa, ‘Ka tafi lafiya, ka ji ɗumi’ ba tare da taimaka masa ba. (Yaƙub 2:16) Mutane da yawa ba za su biɗi taimako ba lokacin da suke bukatar wani abu; maimako, su yi ta shan wahalarsu babu magana. Don a taimaki irin waɗannan mata ana bukatar fahimi, a fahimci bukatunsu. A wata sassa, cika son shan gaba—kana sarrafa rayuwar gwauruwar—zai iya ɓata mata rai ko kuma sa ta jayayya. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya nanata bukatar mu daidaita a sha’aninmu da wasu. Ko da ya ƙarfafa mu mu kasance da marmari mai kyau wajen wasu, ya tunasar da mu kada mu zama masu shisshigi.—Filibbiyawa 2:4; 1 Bitrus 4:15.
Ruth ta kasance da hali da ya daidaita wajen Naomi. Yayin da ta manne cikin aminci ga surukarta, Ruth ba ta matsa mata ko kuma ta mallake ta ba. Ta ɗauki matakai na hikima, irin na nemo wa Naomi abinci da kuma wa kanta, amma ta bi umurnin Naomi.—Ruth 2:2, 22, 23; 3:1-6.
Hakika, bukatar mutane ta bambanta daga wani zuwa wani sosai. Sandra, da aka ambata a farko ta ce: “Na sami abin da nike bukata cikin wahala ta—ƙaunatattun abokai masu kyau da suka zo waje na.” Amma kuma Elaine, da aka ambata a farko, tana son ita kaɗai ta kasance. Saboda haka, don mutum ya taimaka, yana bukatar ya fahimta kuma daidaita tsakanin yadda mutumiyar take son a bar ta ta huta da kuma abin da take son a taimake ta yi.
Taimako Daga Iyalin
Iyali mai kyau, mai ƙauna, idan akwai, za ta iya taimaka a tabbatar da gwauruwar cewa za ta iya jimrewa. Ko da yake wasu cikin iyali za su iya ba da taimako fiye da wasu, duka dai za su iya taimakawa. “Idan kowacce gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, bari su koya su fara gwada ibada wajen iyalin gida nasu, su sāka ma iyayensu: gama wannan abin karɓa ne a wurin Allah.”—1 Timothawus 5:4.
A fannoni da yawa, ba za a bukaci taimakon kuɗi ba ko ‘sākawa’ ma. Wasu gwauraye mata suna da isashen kuɗi na kula da bukatunsu wasu kuma sun isa jihar ta kula da su, a ƙasashen da akwai irin tsarin. Amma a inda gwauraye mata suke da bukata, waɗanda suke cikin iyalin ya kamata su taimaka. Idan gwauruwa ba ta da dangi na kusa da za su taimaka ko kuma dangin ba su iya ba da taimako ba, Nassi ya ƙarfafa ’yan’uwa masu bi su taimake ta: “Addini mai-tsarki mara-ɓāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum shi ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu.”—Yaƙub 1:27.
Waɗanda suke bin waɗannan ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki suna “bada girma ga gwauraye” da gaske. (1 Timothawus 5:3) Ba wa mutum girma yana nufin yin ladabi ga mutumin. Mutane da ake ba su girma, sukan ji suna da daraja, ana ƙaunarsu kuma ana daraja su. Ba kawai wai wasu suna taimakawa don dai su cika wani nawaya ne ba. Ko da yake Ruth ita ma gwauruwa ce na ɗan lokaci, ta daraja Naomi sosai ta wurin kasance a shirye kuma cikin ƙauna ta kula da bukatu na jiki da kuma na jiye-jiye da Naomi take da shi. Hakika, bai daɗe ba halin Ruth ya sa ta yi suna mai kyau, har da mijin da zai aure ta ya ce mata: “Dukan mazaunan gari sun sani macen kirki ce ke.” (Ruth 3:11, hasiyana NW) Amma ƙaunar Naomi ga Allah, yadda ita ba mai fitina ba ce da kuma yadda take son Ruth da gaske babu shakka shi ya sa ya kasance da sauƙi Ruth ta taimake ta. Lalle Naomi misali ce mai kyau ga gwauraye mata a yau!
Matsa Kusa da Allah
Babu shakka cewa waɗanda suke cikin iyali da kuma abokai ba za su iya kawar da rashi da mutuwar abokin aure ya jawo ba. Saboda wannan yana da muhimmanci mai baƙin cikin ya jawo kurkusa musamman ga “Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” (2 Korinthiyawa 1:3, 4) Ka yi la’akari da misalin Hannatu, gwauruwa mai ibada shekararta 84 a lokacin da aka haife Yesu.
Lokacin da mijin Hannatu ya mutu bayan shekara bakwai kawai na aure. “[Hannatu] ba ta rabuwa da haikali, tana sujjada tare da azumi da addu’o’i dare da rana.” (Luka 2:36, 37) Jehovah ya ba da lada kuwa ga ibadar Hannatu? E! Ya nuna mata ƙaunarsa a hanya ta musamman ya yarda mata ta ga jaririn da zai yi girma ya zama Mai Ceton duniya. Lalle wannan ya burge ta kuma ya yi wa Hannatu ta’aziyya! Babu shakka, ta shaida gaskiyar Zabura 37:4: “Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji kuma; za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.”
Allah Yana Aiki ta Wajen ’Yan’uwa Kirista
Elaine ta ce: “Na yi ciwon jiki na dogon lokaci bayan mutuwar David, sai ka ce ana suka ta da wuƙa a haƙarƙari ta. Ca nake rashin narkewar abinci ne. Wata rana ya yi tsanani sosai har da na so na je wajen likita. Sai wata ’yar’uwa kuma abuyata mai fahimi ta ce wataƙila baƙin cikina ne kuma ta ƙarfafa ni na nemi taimako daga wajen Jehovah da kuma ta’aziyya. Na yi na’am da shawararta nan da nan kuma na yi addu’a daga zuci, na ce Jehovah ya taimake ni cikin baƙin cikina. Kuma ya yi hakan!” Elaine ta samu sauƙi, kuma ba da daɗewa ba ciwon jikin ya warke.
Dattawan ikilisiya musamman za su iya ba da taimako mai kyau na alheri ga gwauraye mata da suke baƙin ciki. Ta wajen yin tanadin taimako da kuma ta’aziyya ta ruhaniya da gudun zuciya da kuma hanyar fahimta, dattawa za su iya su taimaka musu su tsaya kusa da Jehovah duk da gwajinsu. Yadda bukata ta kama, dattawa suna iya taimaka a shirya yadda za su sami taimako na ababan jiki. Irin waɗannan dattawa masu juyayi, masu fahimi sukan zama da gaske “maɓoya daga iska.”—Ishaya 32:2; Ayukan Manzanni 6:1-3.
Ta’aziyya ta Dindindin Daga Sabon Sarki na Duniya
Wanda Hannatu tsohuwa ta yi murnan ganinsa shekara dubu biyu da ta shige yanzu ya zama Sarki Almasihu na Mulkin Allah na sama. Wannan gwamnati ba da daɗewa ba za ta kawar da dukan abubuwan da ke haddasa baƙin ciki, har da mutuwa. Domin wannan Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4 ya ce: “Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane . . . Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” Ka lura cewa wannan ayar ta yi zance game da “mutane”? I, mutane za a ’yantar da su daga mutuwa da ke jawo dukan baƙin ciki da kuma kuka.
Amma da akwai albishiri mai daɗi kuma har ila yau! Littafi Mai Tsarki ya yi alkawarin tashin matattu. “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa [Yesu], su fito kuma.” (Yohanna 5:28, 29) Kamar Li’azaru, wanda Yesu ya ta da daga matattu, za su fito mutane, ba halittu na ruhu ba. (Yohanna 11:43, 44) Waɗanda kuwa suka yi ‘nagargarun ayyuka’ za a kawo su ga kamilcewa na ’yan Adam kuma su kansu su ɗanɗana kula ta uba daga Jehovah yayin da ‘zai buɗe hannuwansa ya biya dukan muradin kowanne abu mai rai.’—Zabura 145:16.
Waɗanda sun yi rashin wanda suke ƙauna da suka sa bangaskiyarsu cikin wannan tabbacaccen bege ya zama musu tushen ta’aziyya mai girma. (1 Tassalunikawa 4:13) Saboda haka idan ke gwauruwa ce, ki tabbata kina “addu’a ba fasawa” domin ta’aziyya da kuma taimakon da ki ke bukata kullum don ki iya kulawa da wasu hakkinki. (1 Tassalunikawa 5:17; 1 Bitrus 5:7) Kuma kowacce rana ki sayi lokaci don karanta Kalmar Allah domin tunanin Allah ya ta’azantar da ke. Idan ki ka yi waɗannan abubuwa, za ki ga yadda ke kanki duk da gwaji da kuma matsalolin da ki ke fuskanta ke gwauruwa, Jehovah zai iya taimaka maki da gaske ki sami salama.
[Bayanin da ke shafi na 5]
Taimako yana nufin a bambance tsakanin sanin lokacin da mutum ke bukatar kaɗaita da kuma kasancewa a shirye lokacin da ake bukatarmu
[Hoto a shafi na 7]
Allah ya albarkaci tsohuwa gwauruwa Hannatu