Ja-gora Daga Allah A Zaɓar Wadda Za A Aura
“Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.”—ZABURA 32:8.
1. Waɗanne abubuwa ne suke da muhimmanci domin aure mai kyau?
MAKAƊA suka soma kiɗa. Zabiya ta soma waƙa mai daɗi. Ya sa kiɗan ya yi daɗi. Mutane biyu suna sauke kwalaye masu nauyi na kayan kasuwa daga babbar mota, ɗaya yana jefo wa ɗayan kwalayen, shi kuma yana cafe su yana ajiyewa bi da bi. Misalan nan biyu kamar ba su da wani wuya. Amma, wa zai yi su ba tare da ya gwada ba, ba tare da abokin aikin da ya dace ba, musamman ma ba tare da ja-gora ko gargaɗi da ya dace ba. Hakazalika, aure mai kyau kamar ya faru ne kawai. Amma, shi ma ya dangana ne a kan abokiyar aure da ta dace, a kan haɗin kai, kuma musamman shawara mai kyau. Hakika, ja-gora da ta dace tana da muhimmanci.
2. (a) Waye ya kafa tsarin aure, da wane nufi? (b) Yaya ake shirya wasu aure?
2 Daidai ne samari da ’yan mata su yi tunani game da waɗanda za su aura—abokin aure a rayuwa. Tun lokacin da Jehovah Allah ya kafa aure, auren namiji da ta mace hanyar rayuwa ce. Amma mutum na farko, Adamu, ba shi ya zaɓi matarsa ba. Jehovah ne cikin ƙauna ya ba shi. (Farawa 2:18-24) Ya nufa ma’aurata na farko su yalwata domin a ƙarshe duniya ta cika da mutane. Bayan wannan gami na farko, iyayen ango da amarya ne suke shirin aure, wani lokaci sai bayan sun waiwace waɗanda za su yi auren. (Farawa 21:21; 24:2-4, 58; 38:6; Joshua 15:16, 17) Yayin da a wasu ƙasashe da al’adu har ila ana zaɓa wa wasu wanda za su aura, mutane da yawa a yau suna zaɓar wadda za su aura da kansu.
3. Ta yaya ya kamata a zaɓi wadda za a aura?
3 Yaya ya kamata a zaɓi wadda za a aura? Sifar mutum ce take rinjayar wasu—abin da suka gani ya yi musu kyau, abin sha’awa ga ido. Wasu suna neman abin duniya, wanda zai kula da su sosai da wanda zai biya bukatunsu da sha’awarsu. Amma kowanne cikin waɗannan kawai zai kai ga dangantaka ta farin ciki mai gamsarwa kuwa? “Tagomashi yana da rikici, jamali kuma abin banza ne,” in ji Misalai 31:30, “amma mace mai-tsoron Ubangiji za a yabe ta.” Akwai muhimmin darasi cikin wannan: Ka tuna da Jehovah yayin da ka ke zaɓan wadda za ka aura.
Ja-gora Mai Kyau Daga Allah
4. Wane taimako Allah ya yi mana game da zaɓar wadda za a aura?
4 Ubanmu na sama mai ƙauna Jehovah, ya ba da rubucacciyar Kalmarsa ta yi mana ja-gora a dukan al’amura. Ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi.” (Ishaya 48:17) Don haka, ba abin mamaki ba ne a ga ja-gora a kan kari cikin Littafi Mai Tsarki game da zaɓan wadda za a aura. Jehovah yana son aurenmu ya kasance na dindindin kuma na farin ciki. Saboda haka, ya yi mana taimako don mu fahimci kuma mu yi amfani da waɗannan shawarwari. Ba abin da za mu tsammani daga Mahaliccinmu mai ƙauna ke nan ba?—Zabura 19:8.
5. Menene yake da muhimmanci idan za a sami farin ciki mai daɗewa cikin aure?
5 Lokacin da Jehovah ya kafa tsarin aure, nufinsa ne aure ya zama gami na dindindin. (Markus 10:6-12; 1 Korinthiyawa 7:10, 11) Shi ya sa yake “ƙyamar kisan aure,” sai a kan “fasikanci” kaɗai. (Malachi 2:13-16; Matta 19:9) Domin wannan, zaɓar wadda za a aura ita ce mataki da ta fi muhimmanci da za mu ɗauka kuma ba za mu ɗauke ta da wasa ba. Ba yawan shawarwari ne ba ke kawo farin ciki ko kuma baƙin ciki. Yayin da zaɓe mai kyau zai ƙara kyautata rayuwar mutum kuma ya sa ta gamsu, zaɓe da ba shi da kyau zai iya kawo baƙin ciki har abada. (Misalai 21:19; 26:21) Domin farin ciki ya ci gaba, yana da muhimmanci mu yi zaɓe da kyau kuma mu kasance da yardan rai a wa’adi mai daɗewa, domin Allah ya kafa aure ya zama tarayya da zai ci gaba cikin jituwa da haɗin kai.—Matta 19:6.
6. Me ya sa samari da ’yan mata ne musamman suke bukatar mai da hankali yayin da suke zaɓan wadda za su aura, kuma yaya za su iya tsai da shawara cikin hikima?
6 Samari da ’yan mata musamman suna bukatar su mai da hankali kada kyakkyawar sifar mutum da sha’awa mai ƙarfi su rinjayi fahiminsu wajen zaɓan wadda za su aura. Hakika dangantaka da ke bisa irin waɗannan abubuwa kawai, za ta kawo raini ko kuma ƙiyayya ba da daɗewa ba. (2 Samu’ila 13:15) A wata sassa, za mu koyi ƙauna mai jimrewa yayin da mun zo ga sanin abokiyar aurenmu da kuma fahimtar kanmu da kyau. Muna bukatar mu sani cewa abin da ya fi mana kyau ƙila ba abin da zuciyarmu da farko take sha’awa ba ne. (Irmiya 17:9) Shi ya sa ja-gorar Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki take da muhimmanci sosai. Yana taimakonmu mu fahimci yadda za mu iya tsai da shawara cikin hikima a rayuwa. Mai Zabura ya faɗi game da Jehovah cewa: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.” (Zabura 32:8; Ibraniyawa 4:12) Yayin da aure zai iya gamsar da bukatarmu na ƙauna da cuɗanya, yana kawo matsaloli kuwa da ke bukatar manyanta da fahimi.
7. Me ya sa wasu ba sa bin gargaɗin Littafi Mai Tsarki game da zaɓan wadda za su aura, har ila yau wannan zai kai ga me?
7 Hikima ce mu yi biyayya ga abin da Tushen aure ya ce a batun zaɓan wadda za mu aura. Duk da haka, wataƙila muna ƙin gargaɗi da ke daga Littafi Mai Tsarki da iyayenmu ko da dattawa Kirista suka ba mu. Muna jin ba su fahimce mu sosai ba, kuma sha’awa mai ƙarfi ta zuciya za ta iya sa mu mu bi nufin zuciyarmu. Amma, yayin da muka fuskanci ainihin rayuwa, za mu yi da-na-sani cewa ba mu bi gargaɗi mai kyau ba da aka ba mu don amfaninmu. (Misalai 23:19; 28:26) Za mu iya iske kanmu cikin aure da babu ƙauna, da yara da ba za mu iya kula da su ba, wataƙila ma da abokin aure mara bi. Zai zama abin baƙin ciki kuwa idan tsari da zai kawo mana farin ciki ya zama tushen baƙin ciki mai yawa!
Ibada—Taimako na Musamman
8. Ta yaya ibada take taimaka wa aure ya jure kuma ya kawo farin ciki?
8 Babu shakka, soyayya ta kan taimaka a sa aure ya kasance da ƙarfi. Ƙa’ida ɗaya da mutane biyu suke bi ya fi muhimmanci a sa aure ya jure kuma ya kawo farin ciki. Ibada ga Jehovah Allah tana mulmula gami na dindindin kuma tana ɗaukaka haɗin kai a hanyar da babu wani abin da zai iya. (Mai-Wa’azi 4:12) Yayin da ma’aurata Kirista suka kafa rayuwarsu a kan bauta ta gaskiya na Jehovah, suna haɗe a ruhaniya, a hankali, da kuma a ɗabi’a. Suna nazarin Kalmar Allah tare. Suna addu’a tare, kuma waɗannan suna sa zuciyarsu ta zama ɗaya. Suna zuwa taron Kirista tare kuma suna zuwa hidimar fage tare. Dukan waɗannan na taimakawa wajen kafa gami na ruhaniya da ke jawo su kurkusa da juna. Mafi muhimmanci kuma, yana kawo albarkar Jehovah.
9. Menene Ibrahim ya yi game da nema wa Ishaƙu mata, da wane sakamako?
9 Domin ibadarsa, uban iyali mai aminci, Ibrahim ya nemi ya faranta wa Allah rai yayin da lokaci ya kai ya zaɓa wa ɗansa Ishaƙu mata. Ibrahim ya ce wa baransa da ya amince da shi: “Zan rantsarda kai kuma game da Ubangiji, Allah na sama, Allah na duniya, ba za ka ɗauka ma ɗana mata daga cikin ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda ni ke zaune a wurinsu: amma za ka tafi garina, zuwa wajen dangina, can za ka ɗauka ma ɗana Ishaƙu mata. . . . [Jehovah] za ya aike mala’ikansa a gabanka, za ka ɗauki ma ɗana mata daga can kuma.” Rifkatu ta zama mace ta musamman, wadda Ishaƙu ya ƙaunace ta sosai.—Farawa 24:3, 4, 7, 14-21, 67.
10. Waɗanne farillai na Nassi aka ɗaura wa magidanta da kuma mata?
10 Idan mu Kiristoci ne da ba su yi aure ba, ibada za ta taimake mu mu koyi halaye da za su taimake mu cika farillai na Nassi game da aure. Waɗannan ne suke cikin farillai na magidanta da na mata da manzo Bulus ya nuna: “Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji . . . Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta . . . Ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu . . . Sai ku kuma kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” (Afisawa 5:22-33) Yadda muka gani, hurarun kalmomin Bulus sun nanata bukatar ƙauna da ladabi. Bin wannan gargaɗin ya ƙunshi tsoron Jehovah. Yana bukatar wa’adi da zuciya ɗaya a duk lokatai masu kyau da marasa kyau. Kiristoci da suke tunanin yin aure ya kamata su iya ɗaukan wannan hakki.
Tsai da Shawarar Lokacin da Za Ka Yi Aure
11. (a) Wane gargaɗi ne game da lokacin da za a yi aure ke cikin Nassi? (b) Wane misali ne ya nuna hikimar bin gargaɗin Littafi Mai Tsarki da ke rubuce a 1 Korinthiyawa 7:36?
11 Sanin lokacin da muke a shirye mu yi aure yana da muhimmanci. Tun da yake wannan ya bambanta daga mutum zuwa mutum, Nassi bai faɗi wata shekara ba. Amma, ya nuna ya fi kyau mu jira sai mun ‘zarce lokacin muguwar sha’awa’ lokacin da sha’awar jima’i mai ƙarfi tana iya rinjayar tunanin kirki. (1 Korinthiyawa 7:36) “Lokacin da na ga abokane na suna fita zance kuma suna aure, yawancinsu suna shekarunsu na goma sha, yana da wuya wani lokaci a bi wannan gargaɗin,” in ji Michelle. “Amma na gane cewa wannan gargaɗin daga wurin Jehovah ne, yana gaya mana abin da zai amfane mu ne. Da na ke jira, na iya mai da hankali a kan dangantakata da Jehovah kuma domin na fahimci rayuwa, wanda ba za ka samu ba a shekarunka na goma sha. Shekaru bayan haka, na kasance a shirye na bi da hakki da kuma matsaloli da ke cikin aure.”
12. Me ya sa yake da kyau kada a yi hanzarin aure lokacin da ake matasa?
12 Waɗanda suka yi hanzarin aure da suke matasa sau da yawa suna ganin cewa bukatunsu da sha’awoyinsu sun canja yayin da suka manyanta. Lokacin sai su gane cewa abubuwa da a dā suke gani da sha’awa ba su da muhimmanci kuma. Wata matashiya Kirista ta kafa zuciyarta a yin aure lokacin da take shekara 16. Kakarta ta yi aure a daidai wannan shekara, yadda mamarta ta yi. Lokacin da wani saurayi da take so ta aura bai aure ta a lokacin, ta zaɓi wani kuma da yake son ya yi hakan. Daga baya, ta yi da-na-sani sosai game da hanzarin shawara da ta yi.
13. Waɗanda suka yi aure lokacin da ba su kai ba sau da yawa suna rashi a waɗanne fasaloli?
13 Yayin da ka ke tunanin aure, yana da muhimmanci ka fahimci dukan abin da ya ƙunsa. Yin aure lokacin da ba a kai ba zai kawo matsaloli da yawa da ma’aurata da su matasa ne wataƙila ba su kai su iya bi da shi ba. Za su iya rashin ilimi da manyanta da ke da muhimmanci a bi da wahalar aure da kuma renon yara. Ya kamata a yi aure sai kaɗai lokacin da muke shirye a jiki, a hankali, da kuma a ruhaniya mu soma dangantaka mai jurewa.
14. Me ake bukata don a warware yanayi mai wuya a cikin aure?
14 Bulus ya rubuta cewa waɗanda suka yi aure “za su sha wahala a cikin jiki.” (1 Korinthiyawa 7:28) Matsaloli za su taso domin mutane biyun sun bambanta, kuma ra’ayoyi za su bambanta. Saboda ajizancin ’yan Adam, zai yi wuya mu cika hakkinmu na Nassi cikin tsarin aure. (1 Korinthiyawa 11:3; Kolossiyawa 3:18, 19; Titus 2:4, 5; 1 Bitrus 3:1, 2, 7) Yana bukatar manyanta da kuma ruhaniya mai ƙarfi don a nemi kuma a bi ja-gorar Allah a warware yanayi mai wuya cikin ƙauna.
15. Wane aiki ne iyaye za su iya kasancewa da shi a shirya yaransu don aure? Ka ba da misali.
15 Iyaye za su iya shirya yaransu don aure ta taimaka musu su fahimci muhimmancin bin ja-gorar Allah. Ta yin amfani da Nassosi da kyau da littattafai na Kirista, iyaye za su iya taimakon yaransu su sani, ko su ko kuma wadda suke so su aura suna shirye su ɗauki wa’adin aure.a Blossom ’yar shekara goma sha takwas ce tana son wani saurayi a cikin ikilisiyarsu. Shi majagaba mai hidima na cikakken lokaci ne, suna so su yi aure. Amma iyayenta sun gaya mata ta jira na shekara guda, suna jin har ila ta kasa. Blossom daga baya ta rubuta: “Ina godiya cewa na saurari wannan shawara ta hikima. Cikin shekara guda, na ƙara manyanta kuma na soma ganin cewa wannan saurayin ba shi da inganci na nagarin abokin aure. Daga baya ya bar ƙungiyar, na tsira daga abin da da zai zama bala’i a rayuwata. Abu mai girma ne samun iyaye masu hikima waɗanda za a dogara ga fahiminsu!”
‘Yi Aure Sai dai Cikin Ubangiji’
16. (a) Yaya za a gwada Kiristoci game da ‘yin aure cikin Ubangiji’? (b) Lokacin da aka jarabce su su auri mara bi, me ya kamata Kiristoci su yi tunani a kai?
16 Ja-gorar Jehovah ga Kiristoci a bayyane yake: ‘Yi aure sai dai cikin Ubangiji.’ (1 Korinthiyawa 7:39) Za a iya gwada iyaye Kirista da yaransu game da wannan. Ta yaya? Matasa za su so su yi aure, amma ƙila babu waɗanda za su aura a cikin ikilisiyar. Aƙalla dai, kamar haka yake. Ƙila maza kaɗan ne idan aka gwada da mata a wani yanki, ko kuma babu wani da ya dace a wurin. Saurayi da bai keɓe kansa ba a cikin ikilisiyar zai iya nuna yana son wata budurwa Kirista (ko kuma budurwa ta nuna tana son saurayi Kirista), kuma ga matsi don a taka mizanai da Jehovah ya kafa. A irin wannan yanayi, zai yi kyau mu yi tunani a kan misalin Ibrahim. Hanya ɗaya da ya riƙe dangantakarsa mai kyau da Allah shi ne ta ganin cewa ɗansa Ishaƙu ya auri mai bauta wa Jehovah da gaske. Ishaƙu ma ya yi hakan game da ɗansa Yakubu. Wannan ya bukaci ƙoƙari daga dukan waɗanda ya shafe su, amma yana faranta wa Allah rai kuma yana kawo albarkarsa.—Farawa 28:1-4.
17. Me ya sa a auri mara bi bala’i ne, wane dalili mafi muhimmanci ne ya sa za a ‘yi aure sai dai cikin Ubangiji’?
17 A yanayi kalilan mara bi ɗin daga baya yakan zama Kirista. Amma, aure ga mara bi sau da yawa ya kasance bala’i. Waɗanda suka yi karkiya marar dacewa ba sa bin imani, mizanai, ko makasudai ɗaya. (2 Korinthiyawa 6:14) Wannan zai kawo lahani a kan sadarwa da farin ciki na aure. Alal misali, wata mace Kirista tana baƙin ciki sosai cewa bayan taro mai ƙarfafa, ba za ta iya komawa gida ta tattauna abubuwa na ruhaniya da maigidanta mara bi ba. Hakika, abu mafi muhimmanci ‘yin aure cikin Ubangiji’ batu ne na kasance da aminci ga Jehovah. Yayin da mun bi Kalmar Allah, zuciyarmu ba ta hukunta mu, domin muna yin abin da ya “gamshe shi.”—1 Yohanna 3:21, 22.
18. Lokacin da ka ke tunanin aure, ga waɗanne al’amura masu muhimmanci ya kamata ka mai da hankali, kuma don me?
18 Lokacin da ka yi tunanin aure, hali da kuma ruhaniyar wadda ka ke so ka aura ya kamata ya zama damuwa na farko. Mutumtakar Kirista, tare da ƙaunar Allah da kuma ba da dukan zuciyarmu gare shi, ya fi amfani sosai fiye da yadda mutum yake da kyau a jiki. Waɗanda suke fahimta kuma suke cika farillansu na zama abokan aure masu ƙarfi a ruhaniya suna more amincewar Allah. Kuma ƙarfi mafi girma da ma’aurata za su iya samu zai zo daga ibada ta haɗin kai ga Mahalicci da kuma amincewa da ja-gorarsa sosai. Ta wannan hanyar ana girmama Jehovah, kuma auren ya soma da tushe na ruhaniya mai ƙarfi da zai kawo gami mai daɗewa.
[Hasiya]
a Dubi Hasumiyar Tsaro na 15 ga Fabrairu, 1999 (Turanci), shafofi 4-8.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa ake bukatar ja-gorar Allah a zaɓan abokin aure mai dacewa?
• Ta yaya ibada za ta taimaka wajen ƙarfafa gamin aure?
• Ta yaya iyaye za su shirya yaransu don aure?
• Me ya sa yake da muhimmanci a ‘yi aure sai dai cikin Ubangiji’?
[Hotuna a shafi na 9]
Yin amfani da gargaɗin Allah a zaɓan wadda za ka aura zai kawo farin ciki sosai
[Hotuna a shafi na 10]
Albarka mai girma tana zuwa daga ‘yin aure sai dai cikin Ubangiji’