Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 1/1 pp. 15-17
  • Dattawa—Ku Koyar da Wasu Su Ɗauki Hakki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dattawa—Ku Koyar da Wasu Su Ɗauki Hakki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Bi Misalin Jehovah
  • Kada Ku Ji Tsoron Bayar da Aiki
  • Dattawa, Ku Koyar da Wasu!
  • Mene Ne Aikin Bawa Mai Hidima
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Mu Yi Godiya don Mazan da Aka Ba Mu Kyauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Bayi Masu Hidima?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Jehobah Yana Koyar Da Makiyaya Don Garkensa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 1/1 pp. 15-17

Dattawa—Ku Koyar da Wasu Su Ɗauki Hakki

A IKILISIYOYI na Shaidun Jehovah a dukan duniya, ana bukatar maza da gaggawa da za su iya hidima a matsayin masu kula. Dalilai uku ne suka kawo hakan.

Na farko, Jehovah yana cika alkawarinsa ya mai da “ƙanƙanin . . . al’umma mai-ƙarfi.” (Ishaya 60:22) Domin alherinsa, kusan sababbin almajirai miliyan ɗaya aka yi wa baftisma da suka zama Shaidun Jehovah a cikin shekara uku da ta shige. Ana bukatar maza masu sanin ya kamata domin su taimaki waɗannan sababbi da suka yi baftisma su ci gaba su manyanta a Kiristanci.—Ibraniyawa 6:1.

Na biyu, wasu da suke hidimar dattawa na shekaru da yawa, tsufa ko kuma rashin lafiya ya tilasta musu su rage nauyin aiki da suke ɗauka a ikilisiya.

Na uku, wasu cikin dattawa masu ƙwazo suna hidima a Kwamitin Hulɗa da Asibitoci, Kwamitin Gine-Gine na Yanki, ko kuma Kwamitin Majami’ar Manyan Taro. Wasu sun bukaci su daidaita yanayinsu a ayyukansu ta wajen tuɓe wasu hakkokinsu a ikilisiya.

Ta yaya za a biya wannan bukatar ta ƙwararrun maza? Koyarwa ita ce magani. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci dattawa su koyar da “mutane masu-aminci, waɗanda za su iya su koya ma waɗansu kuma.” (2 Timothawus 2:2) In ji wani ƙamus, kalmar aikatau “koya” tana nufin “a ilimantar saboda ya dace, ya ƙware, ya gwaninta.” Bari mu bincika yadda dattawa za su iya su koyar da wasu su zama ƙwararrun maza.

Ku Bi Misalin Jehovah

Yesu Kristi babu shakka ya ‘dace, ƙwararre ne, kuma gwani ne’ a aikinsa—kuma ba abin mamaki ba ne! Jehovah Allah ne kansa ya koyar da shi. Waɗanne abubuwa ne suka sa koyarwar ta yi kyau? Yesu ya ambaci abubuwa uku, kamar yadda suke rubuce a Yohanna 5:20: “Uban [1] yana ƙaunar Ɗan, kuma [2] yana nuna masa dukan abin da yana yi da kansa; [3] ayyukan da sun fi waɗannan girma za ya nuna masa kuma.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Bincika kowannen waɗannan abubuwa zai ba da fahimi a batun koyarwa.

Ka lura cewa Yesu da farko ya ce: “Uban yana ƙaunar Ɗan.” Daga farkon halitta, da nasaba mai kyau tsakanin Jehovah da Ɗansa. Misalai 8:30 ta ƙara bayani a kan wannan nasabar: “Sa’annan ina nan [Yesu] wurinsa [Jehovah Allah], gwanin mai-aiki ne: kowace rana ni ne abin daularsa, kullum ina farinciki a gabansa.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Yesu bai yi shakka a zuciyarsa ba cewa Jehovah yana “daularsa.” Kuma Yesu bai ɓoye farin cikinsa ba sa’ad da yake aiki a gefen Ubansa. Yana da kyau ƙwarai idan dangataka mai kyau ta kasance tsakanin dattawa Kiristoci da kuma waɗanda suke koyar da su!

Abu na biyu da Yesu ya ambata shi ne cewa Uban “yana nuna masa dukan abin da yana yi da kansa.” Waɗannan kalmomin sun tabbatar da abin da Misalai 8:30 ya ce, wato, Yesu ‘ya kasance a gefen’ Jehovah sa’ad da ake halittar dukan halitta. (Farawa 1:26) Dattawa za su iya bin wannan misali mai kyau ta wajen aiki kusa kusa da bayi masu hidima, su nuna musu yadda za su bi da ayyukansu ta hanya mai kyau. Ba sababbin waɗanda aka naɗa bayi masu hidima ba ne kawai suke bukatar a ci gaba da koyar da su. Yaya game da waɗannan ’yan’uwa masu aminci waɗanda suke biɗan aikin dattijo na shekaru da yawa amma ba a naɗa su ba? (1 Timothawus 3:1) Ya kamata dattawa su ba da takamaiman shawara ga irin waɗannan mutane saboda su san inda za su yi gyara.

Alal misali, bawa mai hidima zai kasance mai aminci, ba ya makara, kuma yana da ƙwazo a aikinsa. Zai kasance kuma malami ne mai kyau. A ɓangarori da yawa yana aiki mai kyau a cikin ikilisiya. Amma ba zai fahimci cewa yana nuna zafin hali ba a sha’aninsa da wasu Kiristoci. Dattawa suna bukatar su nuna “tawali’u na hikima.” (Yaƙub 3:13) Ba zai kasance alheri ba ga dattijo ya yi magana da bawa mai hidima, ya bayyana masa matsalar, kuma ya ba da takamammun misalai, kuma ya ba da shawara domin gyara? Idan dattijon ya ‘gyara gargaɗinsa da gishiri,’ za a karɓi maganarsa da kyau. (Kolossiyawa 4:6) Hakika, bawa mai hidimar zai sa aikin dattijon ya yi daɗi ta wajen karɓan dukan gargaɗi da aka yi masa.—Zabura 141:5.

A wasu ikilisiyoyi, dattawa suna koyar da bayi masu hidima a kai a kai. Alal misali, suna tafiya tare da bayi masu hidima sa’ad da za su ziyarci mara lafiya ko kuma tsoho. A wannan hanyar bawa mai hidimar zai fahimci aikin kiwo. Hakika, da abubuwa da yawa da bawa mai hidima zai yi ya yi girma a ruhaniya.—Duba akwati na gaba mai jigo “Abin da Bayi Masu Hidima Za Su Iya Yi.”

Abu na ukun da ya sa koyarwa da Yesu ya yi, ya yi kyau shi ne cewa Jehovah ya koyar da shi da tunanin ci gabansa a nan gaba. Yesu ya ce game da Ubansa cewa zai nuna wa Ɗan “ayyukan da sun fi waɗannan girma.” Ilimi da Yesu ya samu sa’ad da yake duniya ya taimaka masa ya koyi halaye da za su taimaka wajen cika wasu ayyuka a nan gaba. (Ibraniyawa 4:15; 5:8, 9) Alal misali, Yesu zai karɓi hakkin babban aiki ba da jimawa ba—na ta da matattu da kuma yi wa biliyoyin mutane hukunci da yanzu matattu ne!—Yohanna 5:21, 22.

Sa’ad da suke koyar da bayi masu hidima, dattawa a yau ya kamata su tuna da bukatu na nan gaba. Zai kasance da akwai dattawa da bayi masu hidima isashe da za su biya bukatun yanzu, amma haka zai kasance idan aka kafa sabuwar ikilisiya? Idan kuma aka kafa sababbin ikilisiyoyi fa? A cikin shekara uku da ta shige, akwai fiye da sababbin ikilisiyoyi 6,000 a dukan duniya. Ana bukatar adadi mai yawa na dattawa da bayi masu hidima su biya bukatun waɗannan sababbin ikilisiyoyi!

Dattawa, kuna koyi da misalin Jehovah wajen gina dangantaka mai kyau da mutane da kuke koyar da su? Kuna koya musu yadda za su yi aikinsu kuwa? Kuna tunanin bukatu na nan gaba? Bin misalin Jehovah a yadda ya koyar da Yesu zai kasance albarka ga mutane da yawa.

Kada Ku Ji Tsoron Bayar da Aiki

Ƙwararrun dattawa da suka saba da ɗaukan ayyuka da yawa masu nauyi za su riƙa jinkirin bai wa wasu iko. Wataƙila sun yi ƙoƙarin yin haka a dā amma bai kasance da albarka ba. Saboda haka, za su koyi hali na, ‘idan kana son a yi aiki da kyau, to, ka yi shi da kanka.’ Amma halin ya jitu ne da nufin Jehovah, da aka furta a cikin Nassosi, cewa maza masu fahimi sosai su koyar da waɗanda ba su da fahimi sosai?—2 Timothawus 2:2.

Manzo Bulus bai ji daɗi ba da abokin tafiyarsa, Yohanna Markus, ya yi watsi da aikinsa a Famfiliya ya koma gida. (Ayukan Manzanni 15:38, 39) Duk da haka, Bulus bai ƙyale wannan ci baya ya kashe masa gwiwa ba daga koyar da wasu. Ya sake zaɓan wani saurayi, Timothawus, ya koyar da shi aikin wa’azi a ƙasashen waje.a (Ayukan Manzanni 16:1-3) A Biriya wasu ’yan wa’azi a ƙasashen waje sun fuskanci hamayya mai tsanani da ya kasance ba daidai ba Bulus ya ci gaba da zama a wajen. Sai ya danka sabuwar ikilisiya a hannun Sila, ɗan’uwa da ya ƙware, da kuma Timothawus. (Ayukan Manzanni 17:13-15) Babu shakka cewa Timothawus ya koyi abubuwa da yawa daga wurin Sila. Daga baya, sa’ad da Timothawus ya kai ya samu ƙarin hakki, Bulus ya aike shi zuwa Tassaluniki ya ƙarfafa ikilisiyar da take wajen.—1 Tassalunikawa 3:1-3.

Dangantaka tsakanin Bulus da Timothawus ba kamar na ’yan kasuwa ba ne, wanda babu nasaba. Suna da gami mai kyau tsakaninsu. Sa’ad da yake rubuta wa ikilisiyoyi a Koranti, Bulus ya ce game da Timothawus, wanda yake shirin ya aika can, “ɗana cikin Ubangiji, ƙaunatacce, mai-aminci kuwa.” Kuma ya daɗa cewa: “[Timothawus] shi tuna maku da al’amurana da ke cikin Kristi.” (1 Korinthiyawa 4:17, tafiyar tsutsa tamu ce.) Timothawus ya bi abin da Bulus ya koyar da shi, ya zama ƙwararre a cika aikinsa. Matasa da yawa sun zama ƙwararrun bayi masu hidima, dattawa, ko kuma masu kula masu ziyara domin sun amfana daga koyarwa da dattawa da suka nuna damuwa waɗanda suka nuna suna ƙaunarsu, kamar yadda Bulus ya yi ga Timothawus.

Dattawa, Ku Koyar da Wasu!

Babu shakka, annabci da ke a Ishaya 60:22 yana cikawa a yau. Jehovah yana mayar da “ƙanƙanin . . . ya zama al’umma mai-ƙarfi.” Domin al’ummar ta kasance da “ƙarfi,” dole ne ta kasance da tsari mai kyau. Dattawa, me ya sa ba za ku bincika hanyoyi ba da za a ƙara koyar da keɓaɓɓun mutane da suka cancanci hakan? Ku tabbata cewa kowanne bawa mai hidima yana sane da gyara da yake bukata domin ya ci gaba. Ku kuma ’yan’uwa da ku ka yi baftisma, ku yi amfani da koyarwa da kuka samu. Ku yi amfani da zarafi ku ƙara iyawarku, ilimi, da kuma fahimi. Babu shakka Jehovah zai albarkaci wannan tsarin taimako na ƙauna.—Ishaya 61:5.

[Hasiya]

a Daga baya, Bulus ya sake aiki da Yohanna Markus.—Kolossiyawa 4:10.

[Akwati a shafi na 16]

Abin da Bayi Masu Hidima Za Su Iya Yi

Ko da yake ya kamata dattawa su koyar da bayi masu hidima, da abubuwa da yawa da bayi masu hidima za su iya yi don su ci gaba a ruhaniya.

—Bayi masu hidima su kasance masu ƙwazo kuma masu aminci wajen yin aikinsu. Kuma ya kamata su koyi hali mai kyau na yin nazari. Ci gaba ya dangana ga nazari da kuma bin abin da aka koya.

—Yayin da bawa mai hidima yana shirya jawabi da zai gabatar a taron Kirista, kada ya ɓata lokaci ya nemi shawara daga ƙwararren dattijo game da yadda ya kamata ya bayar da jawabin.

—Bawa mai hidima zai iya gaya wa dattijo ya lura da yadda ya gabatar da jawabi na Littafi Mai Tsarki kuma ya ba da shawara domin gyara.

Bayi masu hidima ya kamata su nema, su karɓa, kuma su bi shawara daga dattawa. A wannan hanyar, ci gabansu “ya bayyanu ga kowa.”—1 Timothawus 4:15.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba