Yaya Muhimmancin Tsabta Take?
TSABTA tana nufin aba dabam ga mutane dabam dabam. Alal misali, sa’ad da uwa ta ce wa yaro ƙarami ya wanke hannunsa da fuskarsa, zai yi tunanin cewa saka hannunsa a bakin famfo da kuma jika leɓansa ya isa. Amma uwarsa ta san bai isa ba. Sai ta ɗauke shi ta mai da shi wajen da ruwan yake ta wanke masa hannu da fuska da ruwa da sabulu—duk da hayaniyarsa!
Hakika, mizanin tsabta ba daidai ba ne a dukan duniya, mutane suna girma da ra’ayoyi dabam dabam na tsabta. A dā, filayen makaranta da suke da tsabta a ƙasashe da yawa suna taimakon ɗalibai su koyi tsabta. A yau, wasu makarantu suna cike da juji sai ka ce bola maimakon wajen wasa da kuma koyo. To, cikin aji kuma fa? Darren, wani ma’aikaci a babbar makaranta a Australiya, ya lura cewa: “A yau muna ganin juji har a cikin aji ma.” Wasu ɗalibai suna ganin umurnin “Ka ɗauka” ko kuma “Ka tsabtace” kamar ana yi musu horo ne. Matsalar ita ce wasu malamai suna amfani da tsabtacewa wajen horo.
A wani ɓangare kuma, manya ma ba sa ba da misali mai kyau na tsabta, ko a rayuwa ta yau da kullum ko kuma a hanyar kasuwanci. Alal misali, yawancin wajen taron jama’a ana bari da datti ba kyaun gani. Wasu masana’anta suna gurɓata mahalli. Gurɓata mahalli, ba masana’antu da kuma kasuwa ba ne suke jawowa, amma mutane ne. Ko da yake wataƙila haɗama ce ainihin sanadin matsalar gurɓata mahalli a dukan duniya da kuma illarta, ɓangaren matsalar sakamakon rashin tsabta ne na mutane. Wani darekta janar dā na ƙungiyar Commonwealth ta Australiya ta goyi bayan wannan sa’ad da ta ce: “Dukan wani batun kiwon lafiya ya dangana ne bisa tsabtar dukan mutane.”
Duk da haka, wasu suna jin cewa tsabta ra’ayi ne na mutane saboda haka bai kamata ya dami kowa ba. Shin haka ne da gaske?
Tsabta tana da muhimmanci ƙwarai sa’ad da ta shafi abincinmu—ko muna saya ne a kasuwa, ko muna ci ne a gidan abinci, ko muna ci ne a gidan wani aboki. Ana bukatar tsabta ƙwarai daga waɗanda suke dafa ko kuma bayar da abincin da muke ci. Hannaye masu datti—nasu ko namu—za su iya kasancewa sanadin yawancin cututtuka. To, asibiti fa—fiye da ko’ina, ita ce wajen da muke bukatar mu ga tsabta? The New England Journal of Medicine ya ba da rahoto cewa rashin wanke hannu tsakanin likitoci da nas-nas shi ne dalilin majiyyata a asibiti suke kamuwa da cututtuka da suke cin dala biliyan goma kowacce shekara wajen magani. Muna fata babu wanda zai saka mu cikin haɗari domin rashin tsabtarsa.
Batu ne kuma mai tsanani idan wani—da gangan ko kuma domin rashin sanin ya kamata—ya gurɓata mana ruwan sha. Babu damuwa ne mu yi tafiya babu takalmi a kan yashin bakin teku inda ake ganin allurai da ’yan ƙwaya da wasu suka yi amfani da su suka jefar? Wataƙila tambaya mai muhimmanci a gare mu ita ce: Ana yin tsabta a gidanmu?
Suellen Hoy, a littafinta Chasing Dirt, ta yi tambaya: “Muna nan tsab-tsab kamar yadda muka saba?” Ta amsa: “Wataƙila, a’a.” Ta ce canji a yanayin rayuwa shi ne ainihin dalilin. Sa’ad da mutane ba sa yawan zama a gida, sai su biya wani kawai ya tsabtace musu gida. Saboda haka, tsabtar mahalli bai kasance al’amari mai muhimmanci ba. “Ba na tsabtace wajen wanka—kai na nake tsabtacewa,” in ji wani mutum. Aƙalla, idan gidana yana da datti, tsab-tsab nake.”
Amma, tsabta ta wuce yadda muke a zahiri. Ta ƙunshi tarbiyya mai kyau na rayuwa. Ta ƙunshi tunani da zuciya da ya shafi ɗabi’a da kuma bauta. Bari mu ga yadda hakan ya kasance.