Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 2/1 pp. 20-24
  • Kana Cikin Waɗanda Allah Yake Ƙauna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Cikin Waɗanda Allah Yake Ƙauna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Koya Daga Misalin Ƙauna ta Yesu
  • Ka Bi Sabuwar Doka
  • Dangantaka da Za a Daraja Ta
  • “Ku Ba na Duniya Ba Ne”
  • Ka Kasance Cikin Ƙaunar Uban da na Ɗan
  • Darussa Daga “Almajirin Nan da Yesu Yake Ƙauna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Me Ya Sa Muke Halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 2/1 pp. 20-24

Kana Cikin Waɗanda Allah Yake Ƙauna?

“Wanda ya ke da dokokina, yana kuwa kiyaye su, shi ne yana ƙaunata: wanda yana ƙaunata kuma za ya zama ƙaunatacen Ubana.”—YOHANNA 14:21.

1, 2. (a) Ta yaya Jehovah ya nuna ƙaunarsa ga ’yan Adam? (b) Menene Yesu ya kafa a daren 14 ga Nisan, 33 A.Z.?

JEHOVAH yana ƙaunar halittarsa mutane. Hakika, yana ƙaunar mutane ƙwarai, “har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Sa’ad da lokacin Bikin Tuna mutuwar Kristi ya kusa, Kiristoci na gaskiya ya kamata su san fiye da dā cewa Jehovah “ya ƙaunace mu, ya aike Ɗansa kuma shi zama kafara ta zunubanmu.”—1 Yohanna 4:10.

2 A daren 14 ga Nisan, 33 A.Z., Yesu da kuma manzanninsa 12 sun taru a ɗaki a bene a Urushalima su yi bikin Ƙetarewa, su tuna ceton Isra’ilawa daga Masar. (Matta 26:17-20) Bayan sun gama wannan bikin na Yahudawa, sai Yesu ya sallami Yahuda Iskariyoti, ya kafa abincin maraice da ya zama Bikin Tuna mutuwar Kristi na Kiristoci.a Ya yi amfani da ishara, ko kuma alamun, gurasa marar yisti da kuma jar giya, jikinsa na zahiri da kuma jininsa, Yesu ya sa manzannin 11 da suka rage su ci wannan jibi na tarayya. Bayanin yadda ya yi, marubutar Lingila, Matta, Markus, da kuma Luka, sun bayyana shi dalla-dalla, da kuma manzo Bulus wanda ya kira shi ‘jibin maraice na Ubangiji.’—1 Korinthiyawa 11:20; Matta 26:26-28; Markus 14:22-25; Luka 22:19, 20.

3. A waɗanne hanyoyi masu muhimmanci labarin manzo Yohanna na sa’o’in Yesu na ƙarshe da almajiransa a ɗakin bene ya bambanta daga na wasu?

3 Amma, manzo Yohanna bai ambaci ba da gurasa da giya ba, wataƙila domin a sa’ad da ya rubuta Lingilarsa (kusan shekara ta 98 A.Z.), tsarin ya riga ya kafu sosai a tsakanin Kiristoci na farko. (1 Korinthiyawa 11:23-26) Duk da haka, Yohanna ne kawai aka hure shi ya ba mu wasu bayani masu muhimmanci game da abin da Yesu ya ce da abin da ya yi kafin, da kuma bayan, ya kafa Bikin Tuna mutuwarsa. Wannan bayani mai ban sha’awa ya cika surori biyar na Lingilar Yohanna. Bai bar wata shakka ba game da irin mutane da Allah yake ƙauna. Bari mu bincika Yohanna sura 13 zuwa 17.

Ka Koya Daga Misalin Ƙauna ta Yesu

4. (a) Ta yaya Yohanna ya nanata jigon taron Yesu da almajiransa sa’ad da ya kafa Abin Tuni? (b) Wane dalili ne guda mai muhimmanci da ya sa Jehovah ya ƙaunaci Yesu?

4 Ƙauna ita ce babban jigo a cikin dukan waɗannan surori da suka ƙunshi furcin ban kwana ta Yesu ga mabiyansa. Hakika, kalmomi iri-iri na “ƙauna” sun bayyana a wajen sau 31. Ƙauna mai zurfi ta Yesu ga Ubansa, Jehovah, da kuma ga almajiransa babu inda suka bayyana sarai fiye da waɗannan surorin. Ƙaunar Yesu ga Jehovah za a iya gani a cikin dukan Linjila game da rayuwarsa, amma a ta Yohanna ce kawai Yesu ya furta cewa: “Ina ƙaunar Uba.” (Yohanna 14:31) Yesu kuma ya ce Jehovah yana ƙaunarsa kuma ya bayyana dalilin haka. Ya ce: “Kamar yadda Ubana ya ƙaunace ni, ni kuma na ƙaunace ku; ku zauna cikin ƙaunata. Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata: kamar yadda na kiyaye dokokin Ubana, ina zaune kuwa cikin ƙaunatasa.” (Yohanna 15:9, 10) Hakika, Jehovah yana ƙaunar Ɗansa domin cikakkiyar biyayyarsa. Darasi ne mai kyau ga dukan mabiyan Yesu Kristi!

5. Ta yaya Yesu ya nuna ƙaunarsa ga almajiransa?

5 Ƙauna mai zurfi na Yesu ga mabiyansa an nanata ta a farkon labarin Yesu da Yohanna ya bayar na taronsa na ƙarshe da manzannin. Yohanna ya ba da labari: “Ananan tun idin faska ba ya yi ba, Yesu domin ya sani sa’atasa ta zo da za ya fita daga cikin wannan duniya, shi tafi wurin Uban, tun da ya yi ƙaunar nasa da ke cikin duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.” (Yohanna 13:1) A wannan maraice na abin tuni, ya koyar da su darasi da ba za su manta ba na yin hidima ga wasu cikin ƙauna. Ya wanke ƙafafunsu. Wannan abu ne da kowanne cikinsu da zai so ya yi ga Yesu da kuma ’yan’uwansu, amma suka ƙi ƙememe. Yesu ya yi wannan aikin na tawali’u sai kuma ya ce wa almajiransa: “Idan fa ni, Ubangiji da Malami, na wanki sawayenku, ya kamata ku kuma ku wanki na juna. Gama na yi muku kwatanci, domin ku kuma ku yi kamar yadda na yi muku.” (Yohanna 13:14, 15) Kiristoci na gaskiya ya kamata su so kuma su yi farin cikin yin hidima ga ’yan’uwansu.—Matta 20:26, 27, hasiya ta NW; Yohanna 13:17.

Ka Bi Sabuwar Doka

6, 7. (a) Wane bayani ne mai muhimmanci Yohanna ya bayar dalla-dalla game da kafa Abin Tuni? (b) Wace sabuwar doka ce Yesu ya bai wa almajiransa, kuma menene sabo game da ita?

6 Labarin Yohanna ne game da abin da ya faru a ɗakin bene a daren 14 ga Nisan kawai ya faɗi takamaiman fitar Yahuda Iskariyoti. (Yohanna 13:21-30) Idan aka kawo dukan labaran Linjilar ya nuna cewa bayan wannan maci amana ya tafi ne, Yesu ya kafa Bikin Tuna mutuwarsa. Sai ya yi magana da manzanninsa masu aminci na ɗan lokaci, ya yi musu ban kwana kuma ya ba su umurnai. Sa’ad da muke shirin mu halarci Bikin Tuni, ya kamata mu nuna ƙauna ga abin da Yesu ya faɗa a wannan lokaci, musamman ma domin muna so mu kasance tsakanin waɗanda Allah yake ƙauna.

7 Umurni na farko da Yesu ya bai wa almajiransa bayan ya kafa Bikin Tuna mutuwarsa wani sabon abu ne. Ya ce: “Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Mecece sabuwa game da wannan dokar? Jim kaɗan a maraicen, Yesu ya bayyana batun, yana cewa: “Umurnina ke nan, ku yi ƙaunar juna, kamar yadda ni na ƙaunace ku. Ba wanda ya ke da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, mutum shi bada ransa domin abokansa.” (Yohanna 15:12, 13) Dokar Musa ta umurci Isra’ilawa su ‘yi ƙaunar maƙwabcinsu kamar ransu.’ (Leviticus 19:18) Amma umurnin Yesu ya wuce nan. Kiristoci za su yi ƙaunar juna kamar yadda Kristi ya ƙaunace su, suna shirye su sadaukar da ransu domin ’yan’uwansu.

8. (a) Mecece ƙauna ta sadaukarwa ta ƙunsa? (b) Ta yaya Shaidun Jehovah suke nuna ƙauna ta sadaukarwa a yau?

8 Lokacin Bikin Tuni, lokaci ne da ya kamata mu binciki kanmu, ɗai-ɗai da kuma a ikilisiya, mu ga ko muna da wannan alama mai bambance Kiristanci na gaskiya—ƙauna irin ta Kristi. Irin wannan ƙaunar mai sadaukarwa za ta iya nufin, kuma a wasu lokatai ma ta nufa cewa, Kiristoci sun ba da ransu maimakon su ci amanar ’yan’uwansu. A koyaushe, ta ƙunshi kasance a shirye mu sadaukar da namu burin domin mu taimaki kuma mu yi hidima wa ’yan’uwanmu da kuma wasu. Manzo Bulus misali ne mai kyau game da wannan. (2 Korinthiyawa 12:15; Filibbiyawa 2:17) An san Shaidun Jehovah a dukan duniya domin ruhunsu na sadaukarwa, suna taimakon ’yan’uwansu da kuma maƙwabtansu da ba da kansu su gaya wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki.b—Galatiyawa 6:10.

Dangantaka da Za a Daraja Ta

9. Domin mu riƙe dangantakarmu mai tamani da Allah da kuma Ɗansa, menene muke farin cikin yi?

9 Babu wani abin da ya fi mana tamani fiye da Jehovah da Ɗansa, Kristi Yesu su ƙaunace mu. Amma domin mu samu wannan ƙaunar, dole ne mu yi wani abu. A wannan dare na ƙarshe da almajiransa, Yesu ya ce: “Wanda ya ke da dokokina, yana kuwa kiyaye su, shi ne yana ƙaunata: wanda yana ƙaunata kuma za ya zama ƙaunatacen Ubana, ni ma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gareshi kuma.” (Yohanna 14:21) Tun da muna tamanin dangantakarmu da Allah da kuma Ɗansa, muna yin biyayya ga dokokinsu da farin ciki. Wannan ya haɗa da sabuwar dokar cewa mu nuna ƙauna ta sadaukar da kai da kuma umurnin da Kristi ya bayar bayan tashiwarsa daga matattu “mu yi ma jama’a wa’azi,” mu yi ƙoƙari mu “almajirtad” da dukan waɗanda suka karɓi bisharar.—Ayukan Manzanni 10:42; Matta 28:19, 20.

10. Waɗanne dangantaka ne masu tamani aka bai wa shafaffu da kuma “waɗansu tumaki”?

10 Daga baya a wannan dare, da yake amsa tambayar da Yahuda (Taddawus) mai aminci ya yi masa, Yesu ya ce: “Idan mutum yana ƙaunata, za shi kiyaye maganata; Ubana kuwa za ya ƙaunace shi, mu zo wurinsa, mu yi zamanmu tare da shi.” (Yohanna 14:22, 23) Har lokacin da suke duniya ma, Kiristoci shafaffu, da aka gayyace su su yi sarauta da Kristi a sama, suna da wata irin dangantaka ta kusa da Jehovah da kuma Ɗansa. (Yohanna 15:15; 16:27; 17:22; Ibraniyawa 3:1; 1 Yohanna 3:2, 24) Amma abokanansu “waɗansu tumaki,” waɗanda begensu rai ne na har abada a duniya, su ma suna da dangantaka mai tamani da “makiyayinsu,” Yesu Kristi, da kuma Allahnsu, Jehovah, idan suka kasance masu biyayya.—Yohanna 10:16; Zabura 15:1-5; 25:14.

“Ku Ba na Duniya Ba Ne”

11. Wane gargaɗi Yesu ya yi wa almajiransa?

11 A lokacin taro na ƙarshe da almajiransa masu aminci kafin mutuwarsa, Yesu ya yi musu gargaɗi: Idan Allah yana ƙaunar mutum, duniya za ta ƙi shi. Ya ce: “Idan duniya ta ƙi ku, kun sani ta rigaya ta ƙi ni tun ba ta ƙi ku ba. Da na duniya ne ku, da duniya ta yi ƙaunar nata; amma domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zaɓe ku daga cikin duniya, saboda wannan duniya tana ƙinku. Ku tuna da magana wadda na faɗa muku, Bawa ba ya fi ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mini tsanani, su a yi muku tsanani kuma; idan suka kiyaye maganata, su a kiyaye taku kuma.”—Yohanna 15:18-20.

12. (a) Me ya sa Yesu ya yi wa almajiransa gargaɗi cewa duniya za ta ƙi su? (b) Me zai yi kyau mu yi bimbini a kai sa’ad da lokacin Abin Tuni ya kusa?

12 Yesu ya yi wannan gargaɗin ne saboda waɗannan manzanni 11 da kuma dukan Kiristoci na gaskiya bayansu kada su yi sanyin gwiwa ba domin ƙiyayyar duniya. Ya daɗa cewa: “Waɗannan abubuwa na faɗa muku domin kada a sa ku ku yi tuntuɓe. Za su fitarda ku daga cikin majami’u; i, sa’a tana zuwa, idan dukan wanda za ya kashe ku, za ya zace yana yi ma Allah hidima. Waɗannan abu fa za su yi, domin ba su san Uban ba, ba su san ni kuma.” (Yohanna 16:1-3) Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa irin kalmar aikatau da aka yi amfani da ita a nan “tuntuɓe” tana nufin “a sa mutum ya kasance da rashin yarda kuma ya yi watsi da wanda ya kamata ya amince da shi kuma ya yi masa biyayya; a sa ya bauɗe.” Sa’ad da lokacin Abin Tuni ya kusa, dukanmu ya kamata mu yi bimbini bisa tafarkin rayuwar amintattu, na dā da na yanzu, kuma mu yi koyi da misalinsu na jimiri a lokacin gwaji. Kada ka ƙyale hamayya ko kuma tsanantawa su sa ka yi watsi da Jehovah da kuma Yesu, amma ka ƙudura niyyar amincewa da su kuma ka yi musu biyayya.

13. Menene Yesu ya roƙa domin mabiyansa a addu’arsa ga Ubansa?

13 A addu’arsa ta ƙarshe kafin ya bar ɗakin bene a Urushalima, Yesu ya gaya wa Ubansa: “Na ba su maganarka; duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. Ba na yin addu’a ka ɗauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga Mugun. Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:14-16) Za mu iya tabbata cewa Jehovah yana kula da waɗanda yake ƙauna, ya ƙarfafa su sa’ad da suke ware kansu daga duniya.—Ishaya 40:29-31.

Ka Kasance Cikin Ƙaunar Uban da na Ɗan

14, 15. (a) Ga menene Yesu ya kwatanta kansa, akasarin wace ‘lalatacciyar kuringa’? (b) Su waye ne “reshe” na “kuringa mai-gaskiya”?

14 A lokacin tattaunawa ta kud da kud da ya yi da almajiransa masu aminci a daren 14 ga Nisan, Yesu ya kwatanta kansa da “kuringar anab mai-gaskiya,” akasarin ‘kuringar anab da ta lalace’ na Isra’ila marar aminci. Ya ce: “Ni ne kuringar anab mai-gaskiya, Ubana kuwa mai-noma ne.” (Yohanna 15:1) Ƙarnuka da farko, annabi Irmiya ya rubuta waɗannan kalmomi na Jehovah ga mutanensa da suka bauɗe: “Na dasa ka kuringa mai-daraja . . . yaya fa ka juya ka zama mini lalatacen dashe na wata baƙuwar kuringa?” (Irmiya 2:21) Kuma annabi Hosea ya rubuta: “Isra’ila kuringa ce mai-yabanya, wadda tana fidda ’ya’yanta . . . Zuciyarsu ta rabu biyu.”—Hosea 10:1, 2.

15 Maimakon ba da ’ya’ya na bautar gaskiya, Isra’ila ta faɗā cikin ridda kuma ta ba da ’ya’ya ga kanta. Kwanaki uku kafin taronsa na ƙarshe da almajiransa masu aminci, Yesu ya gaya wa shugabannin Yahudawa masu riya: “Ina ce muku, Za a amshe muku mulkin Allah, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Matta 21:43) Wannan sabuwar al’ummar “Isra’ila ta Allah” ce da ta ƙunshi shafaffun Kiristoci 144,000 waɗanda aka kwatanta su da “reshe” na “kuringa mai-gaskiya,” Kristi Yesu.—Galatiyawa 6:16; Yohanna 15:5; Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3.

16. Menene Yesu ya aririci manzanni 11 amintattu su yi, kuma menene za a ce game da raguwar amintattun a wannan lokaci na ƙarshe?

16 Yesu ya gaya wa manzanninsa 11 da suke tare da shi a ɗakin bene: “Kowane reshe a cikina wanda ba ya bada ’ya’ya ba, ya kan kawashe shi: kowane reshe kuma da ya bada ’ya’ya, ya kan tsarkake shi domin shi daɗa bayarda ’ya’ya. Ku zauna cikina, ni ma a cikinku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada ’ya’ya don kansa ba, sai dai yana zaune cikin kuringar anab; hakanan kuwa ku ba ku iya ba, sai dai kuna zaune cikina.” (Yohanna 15:2, 4) Tarihin zamani na mutanen Jehovah ya nuna cewa amintattun raguwar shafaffun Kiristoci sun kasance cikin haɗin kai da Shugabansu, Kristi Yesu. (Afisawa 5:23) Sun karɓi tsabtacewa da rarragewa. (Malachi 3:2, 3) Tun shekara ta 1919, sun ba da ’ya’ya na Mulki a yalwace, da farko wasu shafaffun Kiristoci, tun daga shekara ta 1935 kuma, “taro mai-girma” mai ci gaba na abokan shafaffun.—Ru’ya ta Yohanna 7:9; Ishaya 60:4, 8-11.

17, 18. (a) Waɗanne kalmomin Yesu ne suka taimaki shafaffu da kuma waɗansu tumaki su kasance a cikin ƙaunar Jehovah? (b) Ta yaya halartar Abin Tuni zai taimake mu?

17 Kalmomin da Yesu ya ƙara sun shafe dukan shafaffu Kiristoci da abokanansu: “Inda a ke ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya dayawa; hakanan kuma za ku zama almajiraina. Kamar yadda Ubana ya ƙaunace ni, ni kuma na ƙaunace ku; ku zauna cikin ƙaunata. Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata: kamar yadda na kiyaye dokokin Ubana, ina zaune kuwa cikin ƙaunatasa.”—Yohanna 15:8-10.

18 Dukanmu muna so mu kasance cikin ƙaunar Allah, kuma wannan yana motsa mu mu zama Kiristoci masu ba da ’ya’ya. Muna yin haka ta wajen yin amfani da dukan zarafi mu yi wa’azin “bishara kuwa ta mulki.” (Matta 24:14) Muna yin dukan iyakacin ƙoƙarinmu mu nuna “ɗiyar ruhu” a rayuwarmu. (Galatiyawa 5:22, 23) Halartar Bikin Tuna mutuwar Kristi za ta ƙarfafa mu a aniyarmu mu yi haka, domin za a tunasar da mu ƙauna mai girma ta Allah da ta Kristi a gare mu.—2 Korinthiyawa 5:14, 15.

19. Wane ƙarin taimako ne za a tattauna a talifi na gaba?

19 Bayan ya kafa Abin Tunin, Yesu ya yi alkawarin cewa Ubansa zai aiko wa mabiyansa amintattu da ‘mataimaki, ruhu mai tsarki.’ (Yohanna 14:26) Yadda wannan ruhun ya taimake shafaffu da kuma waɗansu tumaki su kasance cikin ƙaunar Jehovah za a bincika a talifi na gaba.

[Hasiya]

a Don shekara ta 2002, kamar yadda aka yi ƙirge na Littafi Mai Tsarki, 14 ga Nisan za ta fara bayan faɗuwar rana, ranar Jumma’a, 28 ga Maris. Wannan maraice, Shaidun Jehovah a dukan duniya za su taru su yi bikin tuna mutuwar Ubangiji, Yesu Kristi.

b Ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, da Shaidun Jehovah suka buga, babi na 19 da na 32.

Tambayoyin Maimaitawa

• Wane darasi mai amfani ne game da hidima cikin ƙauna Yesu ya koya wa almajiransa?

• Game da menene lokacin Abin Tuni lokaci ne da ya dace domin bincika kanmu?

• Me ya sa bai kamata mu yi tuntuɓe ba domin gargaɗin Yesu game da ƙiyayya da kuma tsanantawa daga duniya?

• Wanene “kuringa mai-gaskiya”? Su waye ne “reshe,” kuma menene ake bukata a gare su?

[Hoto a shafi na 21]

Yesu ya koya wa manzanninsa darasi da ba za a taɓa manta ba na hidima cikin ƙauna

[Hotuna a shafuffuka na 21, 22]

Almajiran Kristi suna biyayya da dokarsa na su nuna ƙauna ta sadaukar da kai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba