Tambayoyi Daga Masu Karatu
Shin ajizancin budurwa Maryamu ya shafi cikin da ta yi na Yesu ne?
Game da “haihuwar Yesu,” hurarren tarihi ya ce: “Sa’anda aka yi tashi tsakanin uwatasa Maryamu da Yusufu, tun ba su gamu ba, aka iske tana da juna biyu daga wurin Ruhu Mai-tsarki.” (Matta 1:18) Hakika, ruhu mai tsarki na Allah ya yi aiki mai muhimmanci a cikin Maryamu.
To, Maryamu kuma fa? Ƙwan maniyyinta, ya yi wani aiki ne wajen cikinta? Game da dukan alkawura da aka yi wa—Ibrahim, Ishaƙu, Yakubu, da Yahuda, da kuma Sarki Dauda—kakannin Maryamu—ɗan da za a haifa dole ne ya zama zuriyarsu da gaske. (Farawa 22:18; 26:24; 28:10-14; 49:10; 2 Samu’ila 7:16) Ta yaya wannan ɗan da Maryamu za ta haifa zai kasance magaji ga waɗannan alkawura na Allah? Lallai ya zama ainihin ɗanta.—Luka 3:23-34.
Mala’ikan Jehovah ya bayyana ga budurwa Maryamu, yana cewa: “Kada ki ji tsoro, Maryamu, gama kin sami tagomashi wurin Allah. Ga shi kuwa, za ki yi ciki, za ki haifi ɗa, za ki ba shi suna Yesu.” (Luka 1:30, 31) Ɗaukan ciki yana bukatar ƙwan maniyyi ya kasance wanda zai iya zama yaro. Hakika, Jehovah Allah ya sa ƙwan a cikin Maryamu ya zama yaro, ya cim ma wannan ta wajen ƙaurar da ran Ɗansa makaɗaici daga duniya ta ruhu zuwa duniyarmu.—Galatiyawa 4:4.
Shin yaro da mace ajiza ta yi cikinsa a wannan hanyar zai kasance kamiltacce kuma marar zunubi a cikin jikinsa na zahiri? Ta yaya dokar gadō take aiki sa’ad da aka gama kamilta da ajizanci? Ka tuna cewa ruhu mai tsarki ne aka yi amfani da shi wajen ƙaurar da kamiltaccen rai na Ɗan Allah da ya kawo cikin. Wannan ya kawar da dukan wani ajizancin da yake ƙwan maniyyin Maryamu, ta haka ya ƙirƙiro tsarin jinsi da ya kasance kamiltacce tun daga farkonsa.
Ko yaya dai, mun tabbata cewa aikin ruhu mai tsarki na Allah a wannan lokacin ya tabbatar da nasara na nufin Allah. Mala’ika Jibrailu ya yi wa Maryamu bayani: “Ruhu Mai-tsarki za ya auko miki, ikon Maɗaukaki kuma za ya inuwantarda ke: domin wannan kuwa abin nan da za a haifa, za a ce da shi mai-tsarki, Ɗan Allah.” (Luka 1:35) Hakika, ruhu mai tsarki na Allah ya yi katanga saboda babu ajizanci ko kuma mugun rinjaya da zai aibantar da ɗan tayi da yake girma a ciki.
A bayyane yake, albarkacin Ubansa ne na sama Yesu ya sami kamiltaccen rai na mutane, ba daga wani mutum ba. Jehovah ya ‘shirya jiki’ ga Yesu—daga cikinsa zuwa gaba—wanda da gaske “mara-ƙazanta, raɓaɓɓe ne da masu-zunubi.”—Ibraniyawa 7:26; 10:5.
[Hoto a shafi na 9]
“Za ki yi ciki, za ki haifi ɗa”