Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 4/1 pp. 26-31
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehovah Da Zuciya Da Ta Kahu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehovah Da Zuciya Da Ta Kahu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ci Gaba da Neman Cikakken Ilimi
  • Ka Tuna da Tubarka da Kuma Juyowa
  • Kada Ka Manta da Keɓe Kanka da Kuma Baftisma
  • Naka Nufin na da Muhimmanci
  • Za Ka Iya Kiyaye Zuciya da ta Kahu
  • Ka Ci Gaba da Bauta da Zuciya da ta Kahu
  • Kana Rayuwa Daidai Da Keɓe Kai Da Ka Yi Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Za Ka Keɓe Kanka Ga Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • ‘Ku Tafi Fa, Ku Almajirtar, Kuna Yi Musu Baftisma’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 4/1 pp. 26-31

Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehovah Da Zuciya Da Ta Kahu

“Zuciyata ta kahu, ya Allah, zuciyata ta kahu.”—ZABURA 57:7.

1. Me ya sa za mu kasance da tabbaci irin na Dauda?

JEHOVAH zai iya sa mu kahu cikin bangaskiya ta Kirista domin mu iya manne wa Kiristanci na gaskiya mu bayinsa da muka keɓe kai. (Romawa 14:4) Saboda haka, za mu kasance da tabbaci irin na mai Zabura Dauda, wanda ya motsa ya rera waƙa: “Zuciyata ta kahu, ya Allah.” (Zabura 108:1) Idan zuciyarmu ta kahu, za mu motsa mu cika keɓe kanmu ga Allah. Kuma mu zuba masa idanu don ja-gora da kuma ƙarfi, za mu zama kafaffu, masu ƙuduri da tabbaci na masu riƙe aminci, muna “yawaita cikin aikin Ubangiji.”—1 Korinthiyawa 15:58.

2, 3. Mecece manufar kashedin Bulus da ke a 1 Korinthiyawa 16:13?

2 A cikin wani kashedi ga mabiyan Yesu a Koranti na dā amma da ke da amfani ga Kiristoci na zamanin yau, manzo Bulus ya ce: “Ku yi tsaro, ku tsaya da ƙarfi cikin imani, ku mazakuta, ku ƙarfafa.” (1 Korinthiyawa 16:13) A Helenanci kowanne cikin waɗannan dokoki mai ci yanke ne, yana ƙarfafa a ci gaba da aiki. Mecece manufar wannan kashedi?

3 Za mu iya ‘yin tsaro’ a ruhaniya ta yin hamayya da Iblis kuma mu kasance kusa da Allah. (Yaƙub 4:7, 8) Dogararmu ga Jehovah na taimakonmu mu ci gaba da haɗa kanmu mu ‘tsaya da ƙarfi cikin imanin Kirista.’ Mu—haɗe da mata da yawa da ke tsakaninmu—muna “mazakuta” ta bauta wa Allah da gaba gaɗi masu shelar Mulki. (Zabura 68:11) Muna “ƙarfafa” ta wurin neman ƙarfi kullum daga Ubanmu na samaniya don mu yi nufinsa.—Filibbiyawa 4:13.

4. Me ke kai wa ga yin baftismarmu ta Kirista?

4 Muna tsayawa domin imani na gaskiya yayin da muka keɓe kai babu ragi ga Jehovah kuma nuna alamar ta nitsewa cikin ruwa. Amma me ya kai mu ga yin baftisma? Da farko mun samu sani na Kalmar Allah. (Yohanna 17:3) Wannan yana sa bangaskiya kuma ya motsa mu zuwa tuba, mu nuna baƙin ciki a kan laifinmu na dā. (Ayukan Manzanni 3:19; Ibraniyawa 11:6) Sai kuma juyowarmu, domin mun juya daga ayyukan mugunta don mu bi rayuwa da ta jitu da nufin Allah. (Romawa 12:2; Afisawa 4:23, 24) Keɓewar kai da zuciya ɗaya cikin addu’a ga Jehovah zai biyo shi. (Matta 16:24; 1 Bitrus 2:21) Mun roƙi Allah don lamiri mai kyau kuma an yi mana baftisma alamar keɓe kanmu gare shi. (1 Bitrus 3:21) Idan mun tuna da matakin nan zai taimake mu mu lura da bukatar ci gaba da ƙoƙari mu cika keɓe kanmu kuma mu ci gaba da bauta wa Jehovah da zuciya da ta kahu.

Ka Ci Gaba da Neman Cikakken Ilimi

5. Me ya sa za mu ci gaba da samun ilimi na Nassi?

5 Don mu cika keɓe kanmu ga Allah, dole ne mu ci gaba da samun ilimi na Nassi mai gina bangaskiya. Abin farin ciki ne mu ci abinci na ruhaniya yayin da muka sarƙu da gaskiyar Allah da farko! (Matta 24:45-47) “Abincin” masu daɗi ne—kuma suna ba mu lafiya a ruhaniya. Yanzu akwai muhimmancin mu ci gaba da cin abinci na ruhaniya don mu kiyaye zuciya da ta kahu na bayin Jehovah da sun keɓe kansu.

6. Yaya aka taimake ka ka yi godiya daga zuciya ga fahimta gaskiyar Littafi Mai Tsarki?

6 Ana bukatar ƙoƙari don a samu ƙarin ilimin Nassosi. Kama yake da neman ɓoyayyiyar dukiya—abin da ke bukatar ƙoƙari. Lallai yana da albarka a samu “sanin Allah”! (Misalai 2:1-6) Lokacin da mai shelar Mulki ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da farko, ƙila ya ko ta yi amfani da littafi nan Sanin da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Ƙila ya ɗauki ɗan lokaci kafin ku gama kowanne babi, mai yiwuwa ma fiye da sashe ɗaya. Ka amfana yayin da aka karanta kuma aka tattauna nassosin da aka rubuta. Idan wani darasi ya yi maka wuya, ana yi maka bayani. Wanda yake yin nazari da kai a Littafi Mai Tsarki yana shiryawa sosai, ya yi addu’a don ruhun Allah, kuma ya taimake ka ka yi godiya daga zuciya domin gaskiyar.

7. Me ke sa mutum ya ƙware don ya koya wa wasu gaskiyar Allah?

7 Ƙoƙarin nan ya dace, domin Bulus ya rubuta: “Shi wanda ya ke koyayye cikin magana bari shi yi tarayya da mai-koyarwa cikin dukan arzuka.” (Galatiyawa 6:6) A nan matani na Helenanci ya nuna cewa an koyar da koyarwar Kalmar Allah zuwa cikin azanci da zuciya na wanda ‘ake koya masa ta baki.’ Yadda aka koya maka haka zai sa ka ƙware ka zama mai koyar da wasu kuma. (Ayukan Manzanni 18:25) Don ka cika keɓe kanka, dole ne ka kiyaye lafiyarka ta ruhaniya da kuma kahuwa ta ci gaba da nazarin Kalmar Allah.—1 Timothawus 4:13; Titus 1:13; 2:2.

Ka Tuna da Tubarka da Kuma Juyowa

8. Ta yaya zai yiwu a kiyaye halaye na ibada?

8 Ka tuna da sauƙi da ka samu lokacin da ka koyi gaskiya, ka tuba, kuma ka tabbata da gafarar Allah a kan bangaskiya cikin hadayar fansa ta Yesu? (Zabura 32:1-5; Romawa 5:8; 1 Bitrus 3:18) Hakika ba za ka so ka koma cikin rayuwa ta zunubi ba. (2 Bitrus 2:20-22) Cikin abubuwan da zai taimake ka, addu’a a kai a kai ga Jehovah za ta taimake ka ka kiyaye halaye na ibada, ka cika keɓewar kanka, kuma ka ci gaba da bauta wa Jehovah cikin aminci.—2 Bitrus 3:11, 12.

9. Bayan ka juya daga ayyuka na zunubi, wane tafarki za ka biɗa?

9 Da yake ka juya daga ayyuka na zunubi, ka ci gaba da biɗan taimakon Allah don ka riƙe zuciyarka a kafe. Kamar kana kan hanya ce da ba daidai ba, amma ka bincika tabbatacciyar taswira sai ka fara yin tafiya a hanyar da ke daidai. Kada ka bijire a hanyar. Ka ci gaba da dogara ga ja-gorar Allah, kuma ka ƙudura ka zauna a kan hanyar rai.—Ishaya 30:20, 21; Matta 7:13, 14.

Kada Ka Manta da Keɓe Kanka da Kuma Baftisma

10. Waɗanne darussa ya kamata mu tuna da su game da keɓewar kanmu ga Allah?

10 Ka tuna cewa ka keɓe kai ga Jehovah cikin addu’a, kana tunanin bauta masa har abada cikin aminci. (Yahuda 20, 21) Keɓewa yana nufin a ware, don tsarkaken nufi. (Leviticus 15:31; 22:2) Keɓe kanka ba wani abu ne na ɗan lokaci ko kuma yarjejeniya da mutane ba. Keɓe kai karƙo ne ga Mamallakin Dukan Halitta, kuma cika hakkin, yana bukatar aminci ga Allah don samun rai. Hakika, ‘ko mun mutu ko muna da rai, mu na Jehovah ne.’ (Romawa 14:7, 8) Kasancewarmu da farin ciki ya dangana ga yadda muke ba da kai ga yin nufinsa da kuma ci gaba da bauta masa da zuciya da ta kahu.

11. Me ya sa ya kamata ka tuna da baftismarka da muhimmancinta?

11 Ka tuna kullum cewa baftismarka alamar keɓewar kanka da zuciya ɗaya ne ga Allah. Ba baftisma da aka tilasta maka ba ne domin kai ka tsai da shawarar. Yanzu a shirye kake ka cika aikinka cikin jituwa da nufin Allah a duk rayuwarka? Ka roƙi Allah don lamiri mai kyau kuma a yi maka baftisma alamar keɓe kanka gare shi. Ka kiyaye wannan lamiri mai kyau a cika keɓewar kanka, kuma albarka mai yawa na Jehovah za ta zo wajenka.—Misalai 10:22.

Naka Nufin na da Muhimmanci

12, 13. Yaya nufinmu yake da alaƙa da keɓe kai da yin baftisma?

12 Keɓe kai da baftisma sun kawo albarka mai yawa ga miliyoyin mutane a duk duniya. Yayin da mun keɓe kanmu ga Allah ta yin baftisma cikin ruwa, mun mutu ke nan game da tafarkinmu na dā amma ba game da nufinmu ba. Mu waɗanda aka koyar da su masu bi, mun yi namu nufin ne yayin da muka keɓe kai cikin addu’a ga Allah kuma muka yi baftisma. Tafarkin keɓe kai da yin baftisma na bukatar mu iya sanin abin da nufin Allah yake nufi kuma mu ƙudura mu yi shi. (Afisawa 5:17) Da haka muna yin koyi da Yesu, wanda ya yi nufinsa lokacin da ya bar aikin sassaƙa, ya yi baftisma, kuma ya keɓe kansa ga yin nufin Ubansa na samaniya sosai.—Zabura 40:7, 8; Yohanna 6:38-40.

13 Jehovah Allah ya nufa cewa Ɗansa zai ‘kamilta ta wurin wahala.’ Saboda haka ya bukaci Yesu ya yi nufinsa a jimre wa wahalar cikin aminci. Domin haka, ya yi “addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai-zafi da hawaye . . . , da aka amsa masa kuma saboda tsoronsa mai-ibada.” (Ibraniyawa 2:10, 18; 5:7, 8) Idan muka nuna irin wannan tsoro na daraja Allah, mu ma za a ‘ji kukanmu,’ kuma za mu tabbata cewa Jehovah zai sa mu zama Shaidunsa da sun keɓe kai da suke da aminci.—Ishaya 43:10.

Za Ka Iya Kiyaye Zuciya da ta Kahu

14. Me ya sa ya kamata mu karanta Littafi Mai Tsarki kowacce rana?

14 Me zai taimake ka ka kiyaye zuciya da ta kahu kuma ka cika keɓe kanka ga Allah? Da nufin samun ƙarin sani daga Kalmar Allah, ka karanta Littafi Mai Tsarki kullum. Wannan shi ne abin da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” suke ariritar mu a kai a kai. Irin gargaɗin nan ana ba mu domin cika keɓe kanmu yana bukatar mu ci gaba da yin tafiya cikin gaskiyar Allah. Idan ƙungiyar Jehovah tana koyar da ƙarya da saninsu, ba za a taba gaya wa Shaidun Jehovah da kuma waɗanda ake musu wa’azi su yi karatun Littafi Mai Tsarki kowacce rana ba.

15. (a) Me ya kamata a yi la’akari da shi sa’ad da ake tsai da shawara? (b) Me ya sa za a iya cewa aikin albashi na Kirista aikinsa na biyu ne?

15 Yayin da ka ke tsai da shawara, kullum ka bincika yadda za ta iya shafar cika keɓewarka ga Jehovah. Mai yiwuwa batun aikinka ne. Kana ƙoƙari ka sa aikin ya taimake ka don ka ci gaba da bauta ta gaskiya? Ko da yake masu ɗaukan mutane a aiki sun lura cewa Kiristoci da sun keɓe kai ana iya dogara da su kuma suna da ƙwazo, sun kuma lura cewa Shaidun Jehovah ba su da dogon buri na cin gaba cikin duniya, ba sa gasa da wasu don samun matsayi mafi girma a aiki. Wannan haka yake domin ba nufin Shaidun ba ne su yi arziki, su yi suna, su samu ɗaukaka, ko kuma iko. Abu mafi muhimmanci ga waɗanda suke cika keɓe kansu ga Allah shi ne yin nufinsa. Aikin da suke yi don ya taimake su biyan bukatar rayuwa, aiki ne na biyu, yana a matsayi na biyu. Kamar manzo Bulus, aikinsu na musamman, shi ne hidimar Kirista. (Ayukan Manzanni 18:3, 4; 2 Tassalunikawa 3:7, 8; 1 Timothawus 5:8) Kana sa abin Mulki farko a rayuwarka?—Matta 6:25-33.

16. Me za mu iya yi idan alhini na sa ya zama da wuya mu cika keɓe kanmu ga Allah?

16 Wasu ƙila alhini dabam dabam sun kusa sha kansu kafin su koyi gaskiya. Amma yanzu zuciyarsu tana cike da farin ciki, da godiya, da kuma ƙauna ga Allah domin sun sami bege na Mulki! Tuna da irin albarka da sun samu tun lokacin zai iya taimakonsu su cika keɓe kansu ga Jehovah. A wata sassa, idan alhini mai yawa game da matsaloli na rayuwar wannan zamanin na barazanar shaƙe ‘kalmar Allah,’ kamar yadda ƙayoyi ke hana iri daga yin girman ba da ’ya’ya fa? (Luka 8:7, 11, 14; Matta 13:22; Markus 4:18, 19) Idan ka lura cewa wannan ya soma faruwa maka ko iyalinka, ka zuba alhininka a kan Jehovah kuma zai taimake ka ka ƙara ƙauna da kuma godiya. Idan ka zuba nauyinka a kansa, zai kiyaye ka kuma ya ba ka ƙarfi ka ci gaba da bauta masa da farin ciki da kuma zuciya da ta kahu.—Zabura 55:22; Filibbiyawa 4:6, 7; Ru’ya ta Yohanna 2:4.

17. Yaya yake yiwuwa a jimre da gwaji mai tsanani?

17 Ka ci gaba da yin addu’a ga Jehovah Allah a kai a kai, kamar yadda ka yi lokacin da kake keɓe kai gare shi. (Zabura 65:2) Yayin da ka fuskanci gwaji na yin laifi mai tsanani, ka biɗi ja-gorar Allah da taimakonsa don ka bi ja-gorar. Ka tuna da bukatar bangaskiya, domin Yaƙub ya rubuta: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima [a jimre da gwaji], bari shi yi roƙo ga Allah, wanda ya ke bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi. Amma bari shi yi roƙo da bangaskiya, ba da shakkar komi ba: gama mai-shakka yana kama da raƙumin teku, wanda iska yana korassa, yana jijigarsa kuma. Gama kada wannan mutum shi yi tsammani za shi karɓi komi daga wurin Ubangiji; mutum mai-zuciya biyu ke nan, mara-tsayawa a cikin dukan al’amuransa.” (Yaƙub 1:5-8) Idan gwaji ya zama yana da wuya, za mu iya tabbata da wannan: “Babu wata jaraba ta same ku sai irin da mutum ya iya jimrewa: amma Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.”—1 Korinthiyawa 10:13.

18. Me za mu iya yi idan wani zunubi mai tsanani na raunana ƙudurinmu mu cika keɓe kanmu ga Jehovah?

18 Idan akwai wani zunubi na ɓoye da ke damun lamirinka kuma na raunana tsai da shawararka ka cika keɓe kanka ga Allah fa? Idan ka tuba, za ka iya samun ta’aziyya a sanin cewa Jehovah ‘ba zai yi banza da karyayyar zuciya mai tuba ya raina ta ba.’ (Zabura 51:17) Ka nemi taimakon dattawa Kiristoci masu ƙauna, da sanin cewa su—a yin koyi da Jehovah—ba za su yi banza da batun mai da ka ga dangantaka mai kyau da Ubanka na ruhaniya ba. (Zabura 103:10-14; Yaƙub 5:13-15) Sai kuma ta sabonta ƙarfi na ruhaniya da zuciya da ta kahu, za ka iya miƙe tafarkin sawayenka kuma ya yiwu ka cika keɓe kanka ga Allah.—Ibraniyawa 12:12, 13.

Ka Ci Gaba da Bauta da Zuciya da ta Kahu

19, 20. Me ya sa yake da muhimmanci mu cika keɓe kanmu?

19 A cikin waɗannan miyagun zamani, dole ne mu yi aiki sosai don mu cika keɓe kanmu kuma mu ci gaba da bauta wa Allah da zuciya da ta kahu. Yesu ya ce: “Wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira.” (Matta 24:13) Tun da yake muna cikin “miyagun zamanu,” a koyaushe ƙarshen na iya zuwa. (2 Timothawus 3:1) Ban da haka ma, babu wani cikinmu da yake da tabbacin kasancewa da rai gobe. (Yaƙub 4:13, 14) Saboda haka yana da muhimmanci mu ci gaba da cika keɓe kanmu a yau!

20 Manzo Bitrus ya nanata wannan a cikin wasiƙarsa ta biyu. Ya nuna cewa yadda marasa ibada suka halaka cikin Rigyawan, haka ma duniya ta alama, ko kuma jam’iyyar miyagun mutane, za su halaka cikin “ranar Ubangiji.” Saboda haka Bitrus ya yi kashedi: “Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma?” Ya kuma aririce su: “Ku . . . , ƙaunatattu, domin kun rigaya kun sani, ku yi hankali kada ya zama a janye ku bisa ga kuskure na [malaman ƙarya da mutane masu fajirci] har ku fāɗi daga cikin tsayawarku.” (2 Bitrus 3:5-17) Lallai abin baƙin ciki ne ƙwarai wanda ya yi baftisma ya bijire zuwa ƙarshen ransa ko ranta cewa ba ta riƙe kahuwar zuciya ba!

21, 22. Yaya kalmomin Zabura 57:7 suka cika a batun Dauda da kuma na Kiristoci na gaskiya?

21 Ƙudurinka na son cika keɓe kanka ga Allah zai iya ƙarfafa ka idan ka tuna da rana ta farin ciki ta baftismarka kuma ka biɗi taimakon Allah domin kalmomi da kuma ayyukanka su faranta masa zuciya. (Misalai 27:11) Jehovah ba ya taɓa ba mutanensa kunya ba, kuma ya kamata mu kasance da aminci gare shi. (Zabura 94:14) Ya nuna juyayi da jinƙai a lalata ƙullin magabtan kuma ya ceci Dauda. A nuna godiyarsa ga wannan, Dauda ya yi shelar ƙarfafa, da kahuwar ƙaunarsa ga Mai Cetonsa. Cikin motsa rai na ƙwarai ya rera waƙa ya ce: “Zuciyata ta kahu, ya Allah, zuciyata ta kahu: zan rera, i, zan rera yabbai.”—Zabura 57:7.

22 Kamar Dauda, Kiristoci na gaskiya ba su jijjiga cikin ibadarsu ga Allah ba. Cikin zukata da suka kahu, suna cewa cetonsu da tsirarsu daga Jehovah ne, wanda suke rera masa waƙar yabo. Idan zuciyarka ta kahu, za ta dogara ga Allah, kuma ta wurin taimakonsa za ka iya cika keɓe kanka. Hakika, za ka iya kasancewa kamar “mai-adalci” wanda mai Zabura ya rera waƙa: “Ba za ya ji tsoron mugun labari ba: zuciyatasa a kafe ta ke, yana dogara ga Ubangiji.” (Zabura 112:6, 7) Da bangaskiya ga Allah da kuma dogara ta ƙwarai gare shi, za ka iya cika keɓe kanka kuma ka ci gaba da bauta wa Jehovah da zuciya da ta kahu.

Ka Tuna?

• Me ya sa ya kamata mu ci gaba da samun cikakken sanin Littafi Mai Tsarki?

• Me ya sa ya kamata mu tuna da tuba da kuma juyowarmu?

• Menene amfanin tuna da keɓe kanmu da kuma baftisma?

• Me zai taimake mu mu ci gaba da bauta wa Jehovah da zuciyar da ta kahu?

[Hotuna a shafi na 29]

Kana kiyaye lafiyarka ta ruhaniya ta wurin karanta Kalmar Allah kowacce rana?

[Hoto a shafi na 29]

Idan muka sa hidimar Kirista muhimmin aikinmu zai taimake mu mu ci gaba da bauta wa Jehovah da zuciya da ta kahu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba