Ka Yi Ja-gorar Sawayenka Da Ƙa’idodin Allah
“[Jehovah na] koya maka zuwa amfaninka.”—ISHAYA 48:17.
1. Ta yaya Mahaliccin ke ja-gorar mutane?
DA ’YAN kimiyya suke ƙoƙari su buɗe sirrin sararin samaniya, sun yi mamakin ƙarfi mai yawa da ke cikin sararin da ya gewaye mu. Ranarmu—matsakaiciyar tauraruwa—kowacce daƙiƙa tana fid da zafi mai yawa ƙwarai. Mahaliccin yana da iko kuma ya yi ja-gorar irin wannan halittu na samaniya masu girma da ikonsa marar iyaka. (Ayuba 38:32; Ishaya 40:26) Mu kuma fa, da aka ba mu ’yancin zaɓe, da ɗabi’a, tunani, da fahimtar al’amura na ruhaniya? Yaya Mahaliccinmu ya zaɓa ya yi mana ja-gora? Yana yi mana ja-gora cikin ƙauna da cikakken dokokinsa da ƙa’idodi masu girma, tare da lamirinmu da aka koyar sosai.—2 Samu’ila 22:31; Romawa 2:14, 15.
2, 3. A wane irin biyayya Allah ke farin ciki?
2 Allah yana farin ciki wajen halittu masu basira da suka zaɓa su yi masa biyayya. (Misalai 27:11) Maimakon ya sa muna yin biyayya babu tunani kamar ’yar tsana, Jehovah ya ba mu ’yancin zaɓe don mu tsai da shawara na yin abin da ke daidai.—Ibraniyawa 5:14.
3 Yesu wanda ya yi kwaikwayon Ubansa daidai, ya ce wa almajiransa: “Ku ne abokaina idan kun yi abin da na umurce ku. Ba ni ƙara ce da ku bayi ba.” (Yohanna 15:14, 15) A lokacin dā, bawa ba shi da wani zaɓe fiye da yin biyayya ga umurnin ubangidansa. A wata sassa kuma, ana ɗaura abota ta nuna halaye da ke sa zuciya farin ciki. Za mu iya zama abokan Jehovah. (Yaƙub 2:23) Ana ƙarfafa wannan abota ta ƙauna. Yesu ya haɗa biyayya ga Allah da ƙauna yayin da ya ce: “Idan mutum yana ƙaunata, za shi kiyaye maganata; Ubana kuwa za ya ƙaunace shi.” (Yohanna 14:23) Domin Uban yana ƙaunarmu kuma yana son ya yi mana ja-gora—Jehovah yana gayyatar mu mu yi rayuwa bisa ƙa’idodinsa.
Ƙa’idodin Allah
4. Ta yaya za ka kwatanta ƙa’idodi?
4 Menene ƙa’idodi? An ba da ma’anar ƙa’ida cewa “gaskiya ta musamman: cikakkiyar doka ce mai muhimmanci, koyarwa, ko kuma ra’ayi da wasu dokoki da koyarwa ke da tushe ko inda aka samo wasu.” (Webster’s Third New International Dictionary) Nazarin Littafi Mai Tsarki a hankali ya bayyana cewa Ubanmu na samaniya ya yi tanadin ƙa’idodi na musamman da ya shafi yanayi dabam dabam da fasalolin rayuwa. Ya yi hakan da amfaninmu na har abada a zuci. Wannan ya yi daidai da abin da mai hikima Sarki Sulemanu ya rubuta: “Ka ji, ya ɗana, ka karɓi batuttuwana: Shekarun ranka fa za su yawaita. Na koya maka cikin tafarkin hikima: na bishe ka cikin hanyoyin daidaita.” (Misalai 4:10, 11) Ƙa’idodi na musamman da Jehovah ya yi tanadinsa ya shafi dangantakarmu da shi da ’yan’uwanmu ’yan Adam, bautarmu, da rayuwarmu ta kullum. (Zabura 1:1) Bari mu bincika wasu cikin waɗannan ƙa’idodi na musamman.
5. Ka ba da misalan wasu ƙa’idodi na musamman.
5 Game da dangantakarmu da Jehovah, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:37) Ƙari ga haka, Allah ya yi tanadin ƙa’idodi game da yadda za mu bi da ’yan’uwanmu ’yan Adam, kamar su Ƙa’idar Ja-gora: “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi muku, ku yi musu hakanan kuma.” (Matta 7:12; Galatiyawa 6:10; Titus 3:2) Game da bauta, an yi mana gargaɗi: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Game da fasalin rayuwarmu ta kullum, manzo Bulus ya ce: “Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.” (1 Korinthiyawa 10:31) Akwai wasu ƙa’idodi da yawa a Kalmar Allah.
6. Ta yaya ƙa’idodi ya bambanta da dokoki?
6 Ƙa’idodi suna aikawa, muhimmiyar gaskiya ce, Kiristoci masu hikima sun koya su so su. Jehovah ya hure Sulemanu ya rubuta: “Ka kasa kunne ga zantattukana: ka karkato kunnenka ga batutuwana. Kada su gushe ma idanunka: Ka tsare su a tsakiyar zuciyarka. Gama rai ne su ga masu-samunsu, lafiya kuma ga dukan jikinsu.” (Misalai 4:20-22) Ta yaya ƙa’idodi ya bambanta daga dokoki? Ƙa’idodi ne ke kafa tushen dokoki. Takamammun dokoki, don wani lokaci na musamman ko yanayi ne, amma ƙa’idodi ba su da lokaci. (Zabura 119:111) Ƙa’idodin Allah ba yayin dā ba ne ko su wuce. Huraren kalmomi na annabi Ishaya sun kasance gaskiya: “Ciyawa ta kan yi yaushi, fure shi yanƙwane, amma maganar Ubangiji za ta tsaya har abada.”—Ishaya 40:8.
Ka Yi Tunani Kuma Ka Yi Aiki Bisa Ƙa’idodi
7. Ta yaya Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu yi tunani kuma mu yi aiki bisa ƙa’idodi?
7 A kai a kai, “maganar Ubangiji” na ƙarfafa mu mu yi tunani kuma mu yi aiki bisa ƙa’idodi. Yayin da aka ce ma Yesu ya taƙaita Dokar, ya yi furci biyu da suka fita sarai—ɗaya ya nanata ƙauna ga Jehovah, ɗayan kuma ya mai da hankali ga ƙaunar maƙwabci. (Matta 22:37-40) A yin haka, Yesu ya ɗan yi ƙaulin magana da ƙa’idar Dokar Musa ta faɗa, da ke Kubawar Shari’a 6:4, 5: “Ubangiji Allahnmu Ubangiji ɗaya ne: kuma za ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka.” Hakika, Yesu ya tuna da ƙa’idar Allah da ke Leviticus 19:18. A ƙarshen littafin Mai-Wa’azi da ke a bayane, kuma gajere, kalmomin Sarki Sulemanu ya ba da misalin dokokin Allah da yawa: “Wannan shi ne ƙarshen zancen; duk an rigaya an ji: ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum. Gama Allah za ya kawo kowane aiki wurin shari’a, da dukan asirin rai, domin shi raba, ko nagari ne, ko mugu.”—Mai-Wa’azi 12:13, 14; Mikah 6:8.
8. Me ya sa kāriya ce mu kasance da fahimi na ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?
8 Samun cikakken fahimi na irin wannan ƙa’idodi zai taimaka mana mu fahimci kuma yi amfani da ƙarin takamammun ƙa’idodi. Bugu kan ƙari, idan ba mu fahimci ƙa’idodi sosai ba kuma mun amince da su ba, ba za mu iya yanke shawara mai kyau ba kuma bangaskiyarmu za ta jijjiga da sauri. (Afisawa 4:14) Idan mun kafa irin wannan ƙa’idodi a azancinmu da zuciya, za mu kasance a shirye mu yi amfani da su a tsai da shawara. Idan mun yi amfani da su da fahimi, suna kawo cin nasara.—Joshua 1:8; Misalai 4:1-9.
9. Me ya sa ba ko yaushe ba ne yake da sauƙi a fahimci kuma a yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?
9 Fahimi da yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba shi da sauƙi kamar bin dokoki da aka kafa. Da yake mu ajizai ne muna iya guje wa ƙoƙari da ake bukata na yin tunani a kan ƙa’idodi. Za mu fi son sukunin doka sa’ad da muke fuskantar mu tsai da shawara ko yi zaɓe. Wani lokaci muna iya neman shawara daga Kirista da ya manyanta—wataƙila dattijo a ikilisiya—da tsammanin samun doka takamaimai da ta shafi yanayinmu. Amma, Littafi Mai Tsarki ko littattafan Littafi Mai Tsarki wataƙila ba su yi tanadin doka takamaimai ba, ko ma an ba mu wani, ba za ta shafi dukan lokaci ba da dukan yanayi. Za ka iya tuna cewa wani mutum ya gaya wa Yesu: “Malam, ka ce ma ɗan’uwana shi raba gādo da ni.” Maimakon ya ba da doka da sauri don ya raba jayayya tsakanin ’yan’uwa, Yesu ya ba shi ƙa’ida a kan galibin abubuwa: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi.” Da haka Yesu ya yi tanadin ja-gora da ke da amfani a lokacin kuma ya kasance haka a yanzu.—Luka 12:13-15.
10. Ta yaya yin hali da ya yi daidai da ƙa’idodi ke bayyana muradin zuciyarmu?
10 Wataƙila ka ga mutane da suke yin biyayya ga dokoki dole, don suna tsoron horo. Daraja ga ƙa’idodi ba ta haɗa da irin wannan halin ba. Ƙa’idodi na motsa waɗanda yake musu ja-gora su yi biyayya daga zuciya. Hakika, yawancin ƙa’idodi ba sa horon waɗanda ba sa bin sa nan da nan ba. Wannan yana ba mu zarafi mu bincika abin da ya sa muke wa Jehovah biyayya, abin da motsuwar zuciyarmu take. Mun samu misali a yadda Yusufu ya ƙi yaudarar matar Potiphar cewa ya yi lalata da ita. Ko da Jehovah bai ba da rubutacciyar doka ba game da zina tukuna kuma babu horo daga Allah a kan kwana da matar wani, Yusufu ya san da ƙa’idodin Allah game da aminci cikin aure. (Farawa 2:24; 12:18-20) Za mu gani daga amsarsa cewa irin ƙa’idodin ya taɓa shi sosai: “Ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah kuma?”—Farawa 39:9.
11. A waɗanne wurare Kiristoci suke son ƙa’idodin Jehovah su yi musu ja-gora?
11 A yau, Kiristoci suna son a yi musu ja-gora da ƙa’idodin Jehovah game da batutuwa na kai, irinsu zaɓan abokane, nishaɗi, kaɗe-kaɗe, da littattafai. (1 Korinthiyawa 15:33; Filibbiyawa 4:8) Yayin da muka ƙara sani, fahimi, da daraja Jehovah da mizanansa, lamirinmu, hankalinmu, za su taimaka mana mu yi amfani da ƙa’idodin Allah a kowane yanayi da za mu fuskanta, har ma a batutuwa na kanmu. Da yake ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki na yi mana ja-gora, ba za mu nemi kuskure ba a dokokin Allah; ba kuwa za mu yi koyi da waɗanda suke ƙoƙarin su ga har yaya za su yi nisa ba tare da karya wata doka ba. Mun gane cewa irin wannan tunani na kasawa kuma yana da lahani.—Yaƙub 1:22-25.
12. Menene mabuɗi domin ƙa’idodin Allah ya yi mana ja-gora?
12 Kiristoci da sun manyanta sun fahimci cewa mabuɗin bin ƙa’idodin Allah shi ne son su sani yadda Jehovah yake ji game da wani batu. “Ya ku masu-ƙaunar Ubangiji,” mai Zabura ya yi gargaɗi, “ku ƙi mugunta.” (Zabura 97:10) A lissafa wasu abubuwa da Allah ya ce ba su da kyau, Misalai 6:16-19 ta ce: “Akwai abu shida waɗanda Ubangiji ya ƙi: I, har bakwai ma waɗanda ransa ya ke ƙyamarsu: Idanu masu-alfarma, harshe mai-ƙarya, hannuwa masu-zubda jinin mara-laifi: Zuciya mai-tsiro da miyagun tunani, ƙafafu masu-saurin gudu gari yin ƙeta: Mai-shaidan zur wanda ya ke furtawa da ƙarya, da mai-shirkan annamimanci tsakani ’yan’uwa.” Yayin da son yin tunani a kan yadda Jehovah yake ji game da irin wannan abubuwa na musamman ke ja-gorar rayuwarmu, rayuwa daidai da ƙa’idodi sai ta zama abin da muke yi kullum.—Irmiya 22:16.
Ana Bukatar Muradi Mai Kyau
13. Wane irin tunani Yesu ya nanata a Huɗubarsa Bisa Dutse?
13 Sani da yin amfani da ƙa’idodi kuma na tsare mu daga yin bauta ta wofinci, marar tushi. Akwai bambanci tsakanin bin ƙa’idodi da nace wa yin biyayya ga dokoki. Yesu ya nuna wannan dalla-dalla a Huɗuba Bisa Dutse. (Matta 5:17-48) Ka tuna cewa masu sauraron Yesu Yahudawa ne, saboda haka ya kamata Dokar Musa ta yi wa halinsu ja-gora. Amma da gaske suna da murɗaɗɗen ra’ayi game da Dokar. Suka kai ga nanata baƙaƙen Dokar fiye da dalilinta. Kuma sun mai da hankali ga al’adunsu, suna saka wannan gaba da koyarwar Allah. (Matta 12:9-12; 15:1-9) Saboda haka, ba a koya wa mutanen su yi tunani bisa ƙa’idodi ba.
14. Ta yaya Yesu ya taimaki masu sauraronsa su yi tunani bisa ƙa’idodi?
14 Akasin haka, Yesu ya haɗa ƙa’idodi a wurare biyar na tarbiyya a Huɗubarsa Bisa Dutse: fushi, aure da kashe aure, alkawari, ramako, da ƙauna da ƙiyayya. A kowanne, Yesu ya nuna amfanin bin ƙa’ida. Da haka Yesu ya ɗaukaka mizanan ɗabi’a ga mabiyansa. Alal misali, a batun zina, ya ba mu ƙa’ida da ke ja-gorar ba kawai ayyukanmu ba amma kuma tunaninmu da sha’awoyinmu: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.”—Matta 5:28.
15. Ta yaya za mu guje halin manne wa doka?
15 Wannan misali ya nuna cewa kada mu mance da nufi da ma’anar ƙa’idodin Jehovah. Kada mu yi ƙoƙari mu samu tagomashin Allah ta halinmu na waje. Yesu ya fallasa irin wannan hali na rashin gaskiya ta yin nuni ga jinƙai da ƙaunar Allah. (Matta 12:7; Luka 6:1-11) Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, za mu guje wa yin ƙoƙari mu yi rayuwa (ko bukaci wasu su yi rayuwa) ta zumamin dokoki da zai gaya mana abin da za mu yi ko abin da ba za mu yi ba da ba ya cikin koyarwar Littafi Mai Tsarki. Za mu fi damuwa da ƙa’idodi na ƙauna da biyayya ga Allah fiye da bauta ta waje.—Luka 11:42.
Sakamako na Farin Ciki
16. Ka ba da misalan ƙa’idodi da ke goyon bayan wasu dokokin Littafi Mai Tsarki.
16 Yayin da muke ƙoƙari mu yi wa Jehovah biyayya, yana da muhimmanci mu gane cewa dokokinsa suna bisa ƙa’idodi ta musamman. Alal misali, Kiristoci za su guji bautar gumaka, lalata, da wasa da jini. (Ayukan Manzanni 15:28, 29) Menene ya goyi bayan Kirista a kan waɗannan batutuwa? Allah ya cancanci mu bauta masa shi kaɗai; mu kasance da aminci ga abokiyar aurenmu; kuma Jehovah ne Mai Ba da Rai. (Farawa 2:24; Fitowa 20:5; Zabura 36:9) Fahimtar waɗannan ƙa’idodi na sa ya kasance da sauƙi mu karɓi kuma mu bi dokoki game da wannan.
17. Wane sakamako mai kyau ne ke zuwa daga fahimta da yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?
17 Yayin da muka gane ƙa’idodin kuma muka yi amfani da su, mun fahimci cewa don amfaninmu ne. Albarka ta ruhaniya da mutanen Allah suke morewa, amfani na gaske ne sau da yawa ke bin ta. Alal misali, waɗanda ba sa shan taba, da suke rayuwa ta ɗabi’a, da waɗanda suke daraja tsarkin jini suna guje wa faɗa cikin wasu cututtuka. Hakanan ma, rayuwa cikin jituwa da gaskiya da muka koya daga Littafi Mai Tsarki zai amfane mu a tattalin arziki, yadda muke bi da mutane, a rayuwar iyali. Kowane cikin albarkar na nuna amfanin mizanan Jehovah, cewa suna aikawa da gaske. Amma samun irin wannan fa’idodi ba shi ne dalili na musamman na yin amfani da ƙa’idodin Allah ba. Kiristoci na gaskiya na yi wa Jehovah biyayya domin suna ƙaunarsa ne, domin ya cancanci bautarsu, kuma domin abin da ya dace su yi ne.—Ru’ya ta Yohanna 4:11.
18. Idan muna son mu zama Kiristoci da suka yi nasara, menene ya kamata ya yi mana ja-gora a rayuwa?
18 Barin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki su yi mana ja-gora a rayuwa na kai wa ga rayuwa mafi kyau, wanda da kanta za ta jawo wasu zuwa hanyar Allah. Mafi muhimmanci, tafarkin rayuwarmu na girmama Jehovah. Mun fahimci cewa Jehovah Allah ne mai ƙauna da gaske wanda yake son abu mafi kyau dominmu. Sa’ad da muke tsai da shawara daidai da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muka ga yadda Jehovah ke mana albarka, muna jin muna kusa da shi. Hakika, muna ƙara gina dangantaka ta ƙauna da Ubanmu na samaniya.
Ka Tuna?
• Mecece ƙa’ida?
• Ta yaya ƙa’idodi suka bambanta daga dokoki?
• Me ya sa yake da amfani mu yi tunani kuma mu yi aiki a kan ƙa’idodi?
[Akwati a shafi na 10]
An gaya wa Wilson, wani Kirista daga Ghana cewa kwanaki kaɗan za a kore shi daga aiki. A ranarsa ta ƙarshe wajen aiki, aka gaya masa ya wanke motar darekta na kamfanin. Sa’ad da Wilson ya samu kuɗi a motar, shugabansa ya gaya masa cewa Allah ya aiko kuɗin ne domin za a kore Wilson ranar. Amma, yin amfanin da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki na yin gaskiya, Wilson ya mai da wa darektar kuɗin. Abin ya burge darektan kuma ba shi mamaki, ba kawai ya ba Wilson aiki na dindindin ba amma ya ƙara masa matsayi zuwa ɗaya cikin manya na kamfanin.—Afisawa 4:28.
[Akwati a shafi na 11]
Rukia mace ce daga Albania a shekarunta na 60. Domin rashin jituwa na iyali, ba ta magana da ɗan’uwanta na fiye da shekara 17. Ta soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah kuma ta koyi cewa Kiristoci na gaskiya za su kasance da salama da wasu, ba za su yi gaba da su ba. Ta yi addu’a dukan dare, zuciyarta tana tsinkewa ta je gidan ɗan’uwanta. ’Yar ɗan’uwan ta buɗe ƙofa. Cikin mamaki, ta tambayi Rukia: “Wa ya mutu? Me ki ke yi a nan?” Rukia ta ce tana son ta ga ɗan’uwanta. Ta bayyana masa cewa koyo game da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma Jehovah ya motsa ta ta sulhunta da ɗan’uwanta. Bayan hawaye da rungumar juna, suka yi bikin wannan sake haɗuwa ta musamman!—Romawa 12:17, 18.
[Hoto a shafi na 13]
[Hoto a shafi na 13]
[Hoto a shafi na 13]
[Hoto a shafi na 13]
“Sa’anda ya ga taron mutane, ya hau cikin dutse: da ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa: ya fa buɗe bakinsa, ya yi ta koya musu.”