Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 8/1 pp. 26-31
  • “Ayyuka Masu-girma Na Allah” Sun Motsa Su

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ayyuka Masu-girma Na Allah” Sun Motsa Su
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sun Motsa don Aiki!
  • Kalmar Allah Tana da Iko
  • Sun Motsa Su Bi Mizanan Jehovah
  • ‘Kada Ka Yi Ƙaunar Duniya’
  • Ka Yi La’akari da Irin Kayan da Kake Sakawa da Kuma Adonka
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Tufafinka Suna Daukaka Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • ‘Na Riga Na Ba da Gaskiya’
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Me Ya Sa Muke Saka Tufafin da Ya Dace Zuwa Taronmu?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 8/1 pp. 26-31

“Ayyuka Masu-girma Na Allah” Sun Motsa Su

“Muna jinsu suna zance cikin harsunanmu ayyuka masu-girma na Allah.”—AYUKAN MANZANNI 2:11.

1, 2. Wane abin mamaki ne ya faru a Urushalima a ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z.?

AWATA ranar Lahadi da safe a shekara ta 33 A.Z., abin mamaki ya faru a rukunin maza da mata, almajiran Yesu Kristi da suka taru a wani gida a Urushalima. “Ba labari, sai wani motsi kamar na hucin iska mai-ƙarfi ya fito sama, duk ya gama gida wurinda su ke zaune. Harsuna kuma mararraba da juna, kamar na wuta, suka bayyanu garesu . . .. Aka cika dukansu da Ruhu Mai-tsarki, suka soma zance da waɗansu harsuna.”—Ayukan Manzanni 2:2-4, 15.

2 Taro mai girma ya taru a gaban gidan. Cikinsu da Yahudawa baƙi, “mutane masu tsoron Allah” da suka zo Urushalima su yi bikin idin Fentakos. Sun yi mamaki domin kowannensu ya ji almajiran suna magana da harshensu game da “ayyuka masu-girma na Allah.” Yaya wannan ya kasance haka tun da waɗanda suke magana daga Galili suka fito?—Ayukan Manzanni 2:5-8, 11.

3. Wane saƙo ne manzo Bitrus ya gabatar wa taron jama’a a Fentakos?

3 Ɗaya cikin waɗanda suka fito daga Galili manzo Bitrus ne. Ya bayyana cewa ’yan makonni da suka wuce, miyagun mutane sun kashe Yesu Kristi. Amma Allah ya ta da Ɗansa daga matattu. Bayan haka, Yesu ya bayyana ga almajiransa da yawa, har da Bitrus da wasu da suke wajen. Kwanaki goma ne bayan Yesu ya haura sama. Shi ne ya zubo ruhu mai tsarki a kan almajiransa. Wannan yana da wata ma’ana ce ga waɗanda suke bikin Fentakos? Hakika. Mutuwar Yesu ta shirya musu hanyar da za su samu gafarar zunubansu su sami “Ruhu Mai-tsarki kyauta kuma” idan sun yi bangaskiya cikinsa. (Ayukan Manzanni 2:22-24, 32, 33, 38) Saboda haka yaya waɗancan masu kallon suka mai da martani ga “ayyuka masu-girma na Allah” da suka ji? Kuma yaya wannan labarin zai taimake mu mu sake duba hidimarmu ga Jehovah?

Sun Motsa don Aiki!

4. Wane annabci na Joel ne ya cika a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z.?

4 Da suka sami ruhu mai tsarki, almajiran a Urushalima ba su ɓata lokaci ba a yaɗa bisharar ceto ga wasu, suka soma da taron jama’a da suka taru a safiyar. Wa’azinsu ya cika annabci mai girma, da Joel, ɗan Pethuel ya rubuta tun farkon ƙarni na takwas: “Zan zuba ruhuna a bisa dukan masu-rai; ’ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su ga mafarkai, majiya-ƙarfinku za su ga ru’yai: kuma a bisa bayina maza da mata zan zuba ruhuna cikin waɗancan kwanaki . . . , kafin babbar rana mai-ban razana ta Ubangiji ta zo.”—Joel 1:1; 2:28, 29, 31; Ayukan Manzanni 2:17, 18, 20.

5. A wane azanci ne Kiristoci na ƙarni na farko suka yi annabci? (Dubi hasiya.)

5 Wannan yana nufin cewa Allah zai ta da tsara na annabawa, maza da mata, kamarsu Dauda, Joel, da Deborah, don su faɗi abubuwa da za su auku a nan gaba? A’a. Kiristoci ‘ ’ya’ya maza da mata, bayi maza da mata’ za su yi annabci yana nufin cewa ruhun Jehovah zai motsa su su sanar da “ayyuka masu-girma” da Jehovah ya yi da kuma waɗanda zai yi. Saboda haka za su zama kakakin Mafi Girma Duka.a Menene jama’ar suka yi?—Ibraniyawa 1:1, 2.

6. Da jin jawabin Bitrus, menene da yawa cikin jama’ar suka motsa su yi?

6 Bayan da jama’ar suka ji bayanin Bitrus, da yawa suka motsa zuwa aiki. Suka ‘karɓi maganarsa’ da zuciya ɗaya “aka yi musu baftisma: a cikin wannan rana fa aka ƙara musu masu-rai wajen talata.” (Ayukan Manzanni 2:41) Domin su Yahudawa ne na jiki da Yahudawa shigaggu, da farko suna da sanin muhimman Nassosi. Wannan, tare da bangaskiya cikin abin da suka koya daga Bitrus, ya isa a yi musu baftisma “cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki.” (Matta 28:19) Bayan baftismarsu “suka lizima a cikin koyarwar manzanni.” A lokacin kuma suka soma gaya wa wasu game da sabuwar imaninsu. Hakika, “yau da gobe kuma, suka riƙa zuwa cikin haikali da zuciya ɗaya, . . .. suna yabon Allah, suna da tagomashi wurin dukan mutane.” Sakamakon wannan aikin wa’azin, “Ubangiji kuma yana tattarawa yau da gobe waɗanda a ke cetonsu.” (Ayukan Manzanni 2:42, 46, 47) A ƙasashe yawancin inda waɗannan sababbin almajirai suke da zama, aka samu ikilisiyoyin Kirista. Babu shakka ƙaruwar, domin himmarsu ne a yin wa’azin “bisharar,” yayin da suka koma gida.—Kolossiyawa 1:23.

Kalmar Allah Tana da Iko

7. (a) Menene yake jawo mutane daga dukan al’ummai ga ƙungiyar Jehovah a yau? (b) Waɗanne alamu na ƙaruwa kake gani cikin fage na dukan duniya da kuma a yankinku? (Dubi hasiya.)

7 Waɗanda a yau suke da burin zama bayin Allah fa? Su ma suna bukatar su yi nazarin Kalmar Allah a hankali. A yin haka, za su zo ga sanin Jehovah cewa shi Allah ne “cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” (Fitowa 34:6; Ayukan Manzanni 13:48) Sun koyi game da tanadin Jehovah na fansa ta wurin Yesu Kristi, wanda jinin da ya zubar ya wanke su daga dukan zunubi. (1 Yohanna 1:7) Sun kuma koya game da ƙudurin Allah ya sa “tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:15) Ƙauna ga Tushen “ayyuka masu-girma” ɗin nan na cika zuciyarsu, kuma suna motsa su su yi wa’azin wannan gaskiya mai tamani. Sai suka zama bayin Allah da suka keɓe kansu suka yi baftisma suka ci gaba da “ƙaruwa kuma cikin sanin Allah.”b—Kolossiyawa 1:10b; 2 Korinthiyawa 5:14.

8-10. (a) Ta yaya labarin wata mace ya tabbatar da cewa Kalmar Allah tana da “iko”? (b) Menene wannan labarin ya koya maka game da Jehovah a yadda yake bi da bayinsa? (Fitowa 4:12)

8 Sanin da bayin Allah suke samu daga nazari na Littafi Mai Tsarki ba na sama sama ba ne. Sanin nan ya motsa zuciyarsu, yana sake tunaninsu, kuma yana zama cikinsu. (Ibraniyawa 4:12) Alal misali, wata mace sunanta Camille, da take aikin kula da tsofaffi. Wata tsohuwa da take kula da ita Martha, Mashaidiyar Jehovah ce. Da yake Martha ta taɓu, tana bukatar a kula da ita koyaushe. Ana bukatar a tuna mata ta ci abinci—har sai an tuna mata kafin ta haɗiye abincin. Amma akwai abu ɗaya cikin zuciyar Martha da ba ta manta ba, menene wannan?

9 Wata rana Martha ta ga Camille tana kuka domin wasu matsalolin da take da su. Martha ta sa mata hannu a kafaɗa ta gayyace ta ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Amma mutuniya kamar Martha za ta iya tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki kuwa? Hakika! Ko da yake ta manta da kusan kome, Martha ba ta manta da Allahnta mai girma ba; ba ta kuwa manta da gaskiya mai tamani da ta koya daga Littafi Mai Tsarki ba. A lokacin nazarin, Martha ta gaya wa Camille ta karanta kowanne sakin layi, ta buɗe Nassosin, ta karanta tambayoyin na ƙarƙashin shafin, kuma ta ba da amsar. Wannan ya ci gaba na ɗan lokaci, kuma ko da yake Martha tana da kasawa, Camille ta ci gaba a koyonta na Littafi Mai Tsarki. Martha ta gane ya dace Camille ta yi tarayya da wasu da suke son su bauta wa Allah. Domin wannan, ta ba wa ɗalibarta riga da takalma, saboda Camille ta yi adon kirki yayin da ta halarci taro na farko a Majami’ar Mulki.

10 Yadda Martha ta damu, misalinta, da kuma tabbacinta ya motsa Camille. Ta kammala cewa duk abin da Martha take koya mata daga Littafi Mai Tsarki suna da muhimmanci, tun da yake Martha ta manta da kome sai abin da ta koya daga Nassosi ne kawai ba ta manta ba. Bayan haka, sa’ad da aka canja wa Camille wajen aiki, sai ta fahimci ya dace ta ɗauki mataki. A lokaci na farko, ta je Majami’ar Mulki, ta saka riga da kuma takalma da Martha ta ba ta, kuma ta ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Camille ta ci gaba kuma ta yi baftisma.

Sun Motsa Su Bi Mizanan Jehovah

11. Ƙari ga kasancewa da himma a aikin wa’azi, ta yaya za mu nuna cewa saƙon Mulkin ya motsa mu?

11 A yau, akwai fiye da miliyan shida na Shaidun Jehovah waɗanda kamar Martha da Camille yanzu ke wa’azin “bisharar mulkin” a dukan duniya. (Matta 24:14; 28:19, 20) “Ayyuka masu-girma na Allah” ne ke motsa su sosai kamar Kiristoci na ƙarni na farko. Sun fahimci cewa suna da gatar ɗaukan sunan Jehovah kuma zai zuba musu ruhunsa. Saboda haka, suna iyakacin ƙoƙarinsu su “yi tafiya wadda ta cancanta ga Ubangiji, [suna] gamshe shi sarai,” a yin amfani da mizanansa a kowanne fannin rayuwarsu. Tsakanin wasu abubuwa, wannan ya haɗa da girmama mizanan Allah a yin ado da kuma saka tufafi.—Kolossiyawa 1:10a; Titus 2:10.

12. Wane gargaɗi ainihi a kan ado da saka tufafi muka samu a 1 Timothawus 2:9, 10?

12 Hakika, Jehovah ya kafa mizanai game da adonmu. Manzo Bulus ya nuna wasu farillan Allah game da batun nan. “Mata su yafa tufafi na ladabi tare da tsantsani da hankali; ba da tubkakken gashi ba, ko da zinariya ko da lu’ulu’ai, ko da tufafi masu-yawan tamani; amma ta wurin kyawawan ayyuka abinda ya dace ga mata masu-shaidan ibada ke nan.”c Me muka koya daga waɗannan kalmomin?—1 Timothawus 2:9, 10.

13. (a) Me ake nufi da “tufafi na ladabi”? (b) Me ya sa za mu ce mizanan Jehovah ba su da wuya ainu a bi?

13 Kalmomin Bulus ya nuna cewa ya kamata Kiristoci su “yafa tufafi na ladabi.” Bai kamata su kasance buzu-buzu ba, da datti a adonsu. Kusan kowa, har da matalauta, za su iya bin mizanai na sa tufafinsu su zama da tsabta, da kyan gani. Alal misali, kowacce shekara Shaidu a Amirka ta Kudu suna yin tafiya na mil da yawa cikin kurmi da kuma cikin kwalekwale na awoyi da yawa don su halarci taron gunduma. Yana da sauƙi wani ya faɗā cikin kogin ko kuma ƙaya ta kama rigarsa yayin da suke cikin tafiya. Saboda haka, yayin da masu hallarar suka isa wajen taron, sai a gansu buzu-buzu. Domin wannan, sai suka fara ɗinka maɓallai, zik, kuma su wanke, su yi gugar rigunansu da za su yafa a taron. Suna nuna godiya ga gayyatar da aka yi musu su ci daga teburin Jehovah, kuma suna so su yi adon da ya dace.

14. (a) Menene ake nufi a sa tufafi da “ladabi tare da tsantsani da hankali”? (b) Me ya ƙunsa mu sa tufafi irin ‘na mutane da suke tsoron Allah’?

14 Bulus ya sake nuna cewa ya kamata mu yi ado da “ladabi tare da tsantsani da hankali.” Wannan yana nufin cewa bai kamata mu kasance da tufafi da ba su da fasali ba, na ta da bori, na nuna asiri, ko kuma na salon yayi. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi ado a hanyar da zai ‘nuna tsoron Allah.’ Wannan ba abin da za a yi tunani a kai ba ne? Ba batun kawai mu yi ado da kyau yayin da muke halartan taron ikilisiya ba sai kuma mu yi banza da hakan a wasu lokatai. Ya kamata yadda muke ado ya nuna tsoronmu na Allah ko da yaushe, hali mai daraja domin mu Kiristoci ne kuma masu hidima a dukan lokatai. Daidai ne tufafinmu na aiki da na makaranta su dace da yanayin. Amma, ya kamata mu yi ado da tsantsani da daraja kuma. Idan tufafinmu koyaushe na nuna imaninmu wajen Allah, ba za mu ji kunya ko ja da baya a yin wa’azi babu shiri ba.—1 Bitrus 3:15.

‘Kada Ka Yi Ƙaunar Duniya’

15, 16. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu guji yin koyi da duniya a batun yin ado da sa tufafi? (1 Yohanna 5:19) (b) Don wane dalili mai kyau ne za mu guji salo a yin ado da sa tufafi?

15 Gargaɗin da ke rubuce a 1 Yohanna 2:15, 16 ma ya yi tanadin ja-gora a zaɓenmu na ado da sa tufafi. Mun karanta: “Kada ku yi ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. Gama dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.”

16 Wannan gargaɗin lallai ya zo a kan lokaci! Cikin wannan tsara da matsi na tsara babu na biyunta, kada mu yarda wa duniya ta zaɓa mana tufafin da za mu yafa. Salon sa tufafi da yin ado ya yi muni a shekarun bayan nan. Har ma tsarin tufafi na kasuwanci da na mutane masu sana’a ba koyaushe ba yake bisa mizanai masu kyau na abin da ya dace wa Kirista. Wannan ƙarin dalili ne da ya sa muke bukatar kada mu “kamantu bisa ga kamar wannan zamani” idan za mu yi rayuwa bisa mizanan Allah da haka za mu yi “ado ga koyarwa ta Allah Mai-cetonmu cikin dukan abu.”—Romawa 12:2; Titus 2:10.

17. (a) Waɗanne tambayoyi ya kamata mu bincika sa’ad da muke sayen kayan ko kuma zaɓan wani salo? (b) Me ya sa magidanta za su maida hankali ga yadda waɗanda suke cikin iyalin suke ado?

17 Kafin ki yanke shawarar sayan wata tufa, yana da kyau ki tambayi kanki: ‘Me ya sa nake son wannan salon? Wata shahararriya ce aka san ta da ita—wata da nake so? ’Yan iska suna amfani da ita ko kuma wasu rukunin neman ’yancin kai, ko ’yan tawaye ne suke amfani da ita? Ya kamata kuma mu bincika tufar sosai. Idan riga ce ko kuma siket, yaya tsawonta? Tsawon inda aka tsaga ta fa? Taguwar mai kyau ce, wadda ta dace, mai daraja, ko kuma matsatsiya ce, tana ta da bori, ko kuma marar fasali ce? Ki tambayi kanki, ‘Idan na yafa tufafin nan zai sa wasu tuntuɓe ne?’ (2 Korinthiyawa 6:3, 4) Me ya sa ya kamata mu damu da wannan? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kristi kuma ba ya yi son kai ba.” (Romawa 15:3) Ya kamata shugabannin iyalai su kula sosai da adon iyalinsu. Domin girmama Allah mai daraja da suke bauta wa, shugabannan iyalai ya kamata su ba da gargaɗi mai ƙarfi, na ƙauna yayin da ake bukatar haka.—Yaƙub 3:13.

18. Me ke motsa ka ka mai da hankali ga adonka da sa tufafi?

18 Saƙon da muke ɗauke da shi ya fito ne daga wurin Jehovah, wanda shi ne tushen daraja da tsarki. (Ishaya 6:3) Littafi Mai Tsarki ya aririce mu mu yi koyi da shi “kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” (Afisawa 5:1) Adonmu da tufafi yana iya kawo yabo ko kuma ya kawo zargi ga Ubanmu na samaniya. Hakika muna son mu faranta zuciyarsa!—Misalai 27:11.

19. Wane amfani ke zuwa daga sanar da “ayyuka masu-girma na Allah” ga wasu?

19 Yaya kake ji game da “ayyuka masu-girma na Allah” da ka koya? Hakika, gata ce mai girma gare mu da muka koyi gaskiyar nan! Domin mun ba da gaskiya cikin jinin Yesu Kristi da ya zubar, an gafarta mana zunubanmu. (Ayukan Manzanni 2:38) Domin haka muna da ’yancin magana a gaban Allah. Ba ma tsoron mutuwa kamar waɗanda ba su da bege. Maimako, muna da tabbaci daga Yesu cewa wata rana “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.” (Yohanna 5:28, 29) Jehovah yana da alheri da ya bayyana mana dukan waɗannan abubuwa. Ƙari ga haka, ya zubo mana ruhunsa. Saboda haka, nuna godiya ga dukan waɗannan kyauta masu kyau, ya kamata mu motsa mu mu yi ladabi ga mizanansa masu girma kuma mu yaba masa da himma, muna faɗa wa wasu “ayyuka masu-girma.”

[Hasiya]

a Yayin da Jehovah ya naɗa Musa da Haruna su yi magana da Fir’auna a madadin mutanensa, Ya gaya wa Musa: “Na sanya ka wani allah ga Fir’auna: ɗan’uwanka kuwa Haruna za ya zama annabinka.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Fitowa 7:1) Haruna ya yi hidima na annabi, ba a azancin faɗin abubuwa da za su auku a nan gaba ba, amma ta wajen kasancewa kakakin Musa.

b Cikin taro mai yawa da suka hallara a bikin Jibin Maraice na Ubangiji da aka yi a ranar 28 ga Maris, 2002, har ila miliyoyinsu ba sa bauta wa Jehovah. Addu’armu ce zukata da yawa cikin waɗannan da suke son saƙon, ba da jimawa ba su motsa su kai gatar zama masu shelar bisharar.

c Ko da yake kalmomin Bulus domin mata Kirista ne, ƙa’ida ɗaya ce ga maza Kirista da kuma matasa.

Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne “ayyuka masu-girma” ne mutane suka ji a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., kuma me suka yi?

• Ta yaya mutum yake zama almajirin Yesu Kristi, kuma me almajiranci ya ƙunsa?

• Me ya sa yake da muhimmanci mu mai da hankali ga ado da kuma tufafinmu?

• Menene ya kamata a bincika yayin da ake duba ko salon taguwa ta dace?

[Hoto a shafi na 27]

Bitrus ya sanar da cewa an tashi Yesu daga matattu

[Hotuna a shafi na 29]

Adonka yana yaba wa Allah da kake bauta wa?

[Hotuna a shafi na 30]

Iyaye Kirista dole ne su kula da adon iyalinsu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba