Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 1/1 pp. 18-27
  • Ka Kasance A Faɗake Fiye Da Dā!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance A Faɗake Fiye Da Dā!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙarshen Zamanin Yahudawa
  • Gargaɗi a Kan Lokaci Daga Manzanni
  • Miliyoyi Sun Kasance a Faɗake
  • Darasi Daga Lutu
  • “Ku Yi Tsaro”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • “Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 1/1 pp. 18-27

Ka Kasance A Faɗake Fiye Da Dā!

“Kada fa mu yi barci, kamar sauran mutane, amma mu yi zamanmu ba barci ba maye.”—1 TASSALUNIKAWA 5:6.

1, 2. (a) Waɗanne irin birane ne Pompeii da kuma Herculaneum? (b) Wane gargaɗi ne mazauna da yawa a Pompeii da kuma Herculaneum suka yi banza da shi, kuma menene sakamakon haka?

A ƘARNI na farko na Zamaninmu, Pompeii da Herculaneum sanannun biranen Romawa ne da ke kusa da Dutsen Basubiyus. Wuri ne da Romawa mawadata suke zuwa shaƙatawa. Babban ɗakin wasansu yana iya ɗaukan mutane fiye da dubu, a Pompeii kuma suna da babban ɗakin wasa da zai iya ɗaukan dukan mutanen birnin. Masu tonan ƙasa a Pompeii sun ƙirga wuraren shaƙatawa 118, da an yi amfani da wasunsu domin caca da kuma karuwanci. Yadda hotuna da kuma zane-zane na jikin bango suka nuna, lalata da son abin duniya ruwan dare ne.

2 A ranar 24 ga Agusta, 79 A.Z., Dutsen Basubiyus ya yi gobara. Masana gobarar dutse sun gaskata cewa gobarar ta farko, ta zubo wuta da toka a kan biranen biyu, amma ƙila bai hana mazaunan tsira ba. Hakika, wasu da yawa sun yi hakan. Amma wasu da ba su ga haɗari ba ko kuma sun yi banza da alamun faɗakarwa suka yi zamansu. Sai da tsakar dare, iskar gas, wuta, da kuma duwatsu suka malalo zuwa Herculaneum, suka halaka dukan mazauna da ke cikin birnin. Washegari, makamancinsa ya halaka kowa a Pompeii. Lallai kuwa mummunar sakamakon rashin lura da alamun haɗari!

Ƙarshen Zamanin Yahudawa

3. Wane kamani yake tsakanin halakar Urushalima da na Pompeii da kuma Herculaneum?

3 Bala’i na halakar Urushalima shekaru tara da farko ya wuce a kamanta shi da mummunar halaka ta Pompeii da Herculaneum, ko da halakar daga mutane ne. An kwatanta ta da cewa “ɗaya ce cikin bala’i mafi muni a dukan tarihi,” an ce ta jawo mutuwar Yahudawa fiye da miliyan. Amma, kamar bala’in da ya shafi Pompeii da Herculaneum, halakar Urushalima ba ta zo babu gargaɗi ba.

4. Wace alama ce ta annabci Yesu ya bayar ya yi wa mabiyansa gargaɗi cewa ƙarshen zamanin ya kusa, kuma yaya cikarsa ta farko ta kasance a ƙarni na farko?

4 Yesu Kristi ya annabta halakar birnin, kuma ya faɗi aukuwa da za su zo kafin haka—irinsu yaƙe-yaƙe masu yawa, karancin abinci, girgizar ƙasa, da kuma taka doka. Annabawan ƙarya za su yi yawa, amma za a yi wa’azin bisharar Mulkin Allah a dukan duniya. (Matta 24:4-7, 11-14) Ko da yake kalmomin Yesu suna cika sosai a yau, sun cika a ƙaramar hanya a can dā. Tarihi ya yi magana game da yunwa mai tsanani a Yahudiya. (Ayukan Manzanni 11:28) Ɗan tarihi Bayahude Josephus ya faɗi game da girgizar ƙasa da ta auku ba da daɗewa ba kafin a halaka birnin. Yayin da ƙarshen Urushalima ya zo kusa, an shaida hayaniya, faɗace-faɗace tsakanin fannonin siyasa na Yahudawa, da kuma kashe kashe a birane da yawa da Yahudawa suka gauraya da mutanen Al’ummai. Duk da haka, an yi wa’azin bisharar Mulkin ga “dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.”—Kolossiyawa 1:23.

5, 6. (a) Waɗanne kalmomin annabci na Yesu ne suka cika a shekara ta 66 A.Z.? (b) Me ya sa waɗanda suka mutu suke da yawa yayin da Urushalima ta halaka a shekara ta 70 A.Z.?

5 A ƙarshe, a shekara ta 66 A.Z., Yahudawa suka yi wa Roma tawaye. Lokacin da Cestius Gallus ya ja-goranci rundunarsa suka kewaye Urushalima, mabiyan Yesu sun tuna kalmomin Yesu: “Sa’anda kun ga Urushalima tana kewaye da dāgar yaƙi, sa’annan ku sani ribɗewarta ta kusa. Sa’annan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu; waɗanda suna cikin tsakiyarta su fita waje; waɗanda ke cikin ƙauyuka kada su shigo ciki.” (Luka 21:20, 21) Lokaci ya yi da za a guji Urushalima—amma ta yaya? Babu dalili, Gallus ya janye rundunarsa ya ba da zarafi ga Kiristoci cikin Urushalima da Yahudiya su yi biyayya ga kalmomin Yesu su gudu zuwa kan duwatsu.—Matta 24:15, 16.

6 Shekara huɗu bayan haka, kusan lokacin Faska, rundunar Romawa ƙarƙashin ja-gorar Janar Titus suka dawo, da niyyar su murtsuke tawayen Yahudawa. Rundunarsa suka kewaye Urushalima suka gina “ganuwa, su sa [su] a tsaka,” yadda ba za su iya tsira ba. (Luka 19:43, 44) Duk da burgar yaƙi, Yahudawa a dukan Daular Roma sun je Urushalima domin Faskar. Sai aka tsare su ciki. In ji Josephus, waɗannan baƙi da ba su da sa’a ne yawancin waɗanda aka yi musu rauni a kewayar da Romawa da suka yi.a A ƙarshe da aka halaka Urushalima, kusan kashi bakwai bisa goma na Yahudawa da suke Daular Roma suka halaka. Halakar Urushalima da haikalinta tana nufin ƙarshen yanayin Yahudawa da kuma tsarin addininsu da ke daga Dokar Musa.b—Markus 13:1, 2.

7. Me ya sa Kiristoci masu aminci suka tsira daga halakar Urushalima?

7 A shekara ta 70 A.Z., da an halakar ko kuma kai Kiristoci Yahudawa bauta tare da sauran mutanen a Urushalima. Amma, yadda tarihi ya nuna, sun yi biyayya da gargaɗin Yesu da ya bayar shekara 37 da suka shige. Sun bar birnin kuma ba su koma ba.

Gargaɗi a Kan Lokaci Daga Manzanni

8. Wace bukata Bitrus ya lura da ita, kuma waɗanne kalmomin Yesu ne mai yiwuwa ya tuna?

8 A yau, da akwai halaka mafi girma da ke kan hanya, wadda za ta kawo ƙarshen dukan wannan zamani. Shekara shida kafin halakar Urushalima, manzo Bitrus ya ba da gargaɗi na gaggawa kuma a kan lokaci domin Kiristoci musamman na zamaninmu: Ku kasance a faɗake! Bitrus ya ga bukatar Kiristoci su mai da ‘hankali’ domin kada su yi banza da “umurnin Ubangiji,” Yesu Kristi. (2 Bitrus 3:1, 2) A gaya wa Kiristoci su kasance a faɗake, mai yiwuwa ne Bitrus ya tuna da abin da ya ji Yesu ya gaya wa manzanninsa kwanaki kalilan kafin mutuwarsa: “Ku yi lura, ku yi tsaro, . . . gama ba ku san lokacinda sa’a ta ke ba.”—Markus 13:33.

9. (a) Wane hali mai haɗari ne wasu za su iya kasancewa da shi? (b) Me ya sa halin shakka yake da haɗari?

9 A yau, wasu suna yin tambaya cikin ba’a: “Ina alkawarin tahowarsa?” (2 Bitrus 3:3, 4) Hakika, irin waɗannan mutane ba sa jin abubuwa sun canja, amma wai sun ci gaba kamar yadda suke daga farkon duniya. Irin halin shakkar nan yana da haɗari. Shakka takan raunana yadda muke ji game da gaggawa, tana sa mu shiga damuwa da sha’awoyinmu. (Luka 21:34) Ban da haka, kamar yadda Bitrus ya nuna, waɗannan masu ba’a sun manta da Rigyawar zamanin Nuhu, da ta halaka dukan zamanin. Lallai yanayi ya canja a lokacin!—Farawa 6:13, 17; 2 Bitrus 3:5, 6.

10. Da waɗanne kalmomi Bitrus ya ƙarfafa waɗanda ƙila ba sa son su yi haƙuri?

10 Bitrus ya taimaki masu karatunsa su kasance da haƙuri ta wurin tuna musu kullum dalilin da ya sa Allah sau da yawa ba ya aikata abin da yake so nan da nan. Da farko, Bitrus ya ce: “Rana ɗaya a wurin Ubangiji kamar shekara dubu ce, shekara dubu kuma kamar rana ɗaya ne.” (2 Bitrus 3:8) Tun da yake Jehovah yana rayuwa har abada, zai lura da dukan fasaloli kuma ya zaɓi lokaci mafi kyau domin ya aikata abin da yake so. Sai kuma Bitrus ya yi nuni ga sha’awar da Jehovah yake da ita na cewa mutane daga ko’ina su tuba. Haƙurin Allah ceto ne ga mutane da yawa da za su halaka idan ya aikata da hanzari. (1 Timothawus 2:3, 4; 2 Bitrus 3:9) Amma, haƙurin Jehovah ba ya nufin cewa ba zai aikata abin da yake so ba. Bitrus ya ce: “Ranar Ubangiji kamar ɓarawo za ta zo.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; 2 Bitrus 3:10.

11. Menene zai taimake mu mu kasance a faɗake a ruhaniya, kuma yaya wannan zai ‘hanzarta,’ ranar Jehovah?

11 Kwatancin Bitrus abu ne da ya kamata a lura da shi. Ba shi da sauƙi a kama ɓarawo, amma mai gadi da yake a faɗake duk dare zai iya ganin ɓarawo fiye da wanda yake gyangyaɗi da barci. Ta yaya ne mai gadi zai iya kasancewa a faɗake? Zagayawa ya fi sa mutum ya kasance a faɗake fiye da zama wuri ɗaya dukan dare. Haka nan ma, kasancewa da ƙwazo a ruhaniya zai taimaki Kiristoci su kasance a faɗake. Saboda haka, Bitrus ya aririce mu mu shagala cikin “tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma.” (2 Bitrus 3:11) Irin waɗannan ayyukan za su taimake mu mu ‘saurari ranar Jehovah.’ Kalmar Helenanci da aka fassara ‘saurari’ ana iya fassara ta a zahiri “daɗa masa hanzari.” (2 Bitrus 3:12; hasiya na NW ) Hakika, ba za mu iya canja ma’ajin lokaci na Jehovah ba. Ranarsa za ta zo a sa’ar da ya ayana. Amma daga yanzu har ranar, lokaci zai hanzarta idan mun shagala cikin hidimarsa.—1 Korinthiyawa 15:58.

12. Ta yaya kowannenmu zai yi amfani da lokaci na haƙurin Jehovah?

12 Saboda haka, duk waɗanda suke jin ranar Jehovah tana jinkiri ana ƙarfafa su su bi gargaɗin Bitrus, su jira lokacin da Jehovah ya ayana cikin haƙuri. Hakika, za mu iya amfani da kyau da lokaci da haƙurin Allah ya bayar. Alal misali, za mu iya ci gaba da koyon muhimman halayen Kirista kuma mu ƙara sa hannu a yaɗa bisharar ga wasu da yawa da ba zai yiwu ba dā. Idan muka kasance a faɗake, Jehovah zai iske mu “cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi” a ƙarshen wannan zamani. (2 Bitrus 3:14, 15) Lallai wannan zai kasance lada kuwa!

13. Waɗanne kalmomin Bulus ne ga Kiristoci Tassalunikawa musamman suka dace a yau?

13 A cikin wasiƙarsa ta farko zuwa ga Kiristoci na Tassalunika, Bulus kuma ya yi magana game da kasancewa a faɗake. Ya yi gargaɗi: “Kada fa mu yi barci, kamar sauran mutane, amma mu yi zamanmu ba barci ba maye.” (1 Tassalunikawa 5:2, 6) A yau, da halakar wannan zamanin ke zuwa kusa, wannan lallai ya dace! Masu bauta wa Jehovah suna zama cikin duniya da ke cike da rashin son abubuwa na ruhaniya, kuma wannan zai iya shafansu. Saboda haka, Bulus ya yi gargaɗi: “Mu yi natsuwa, muna yafe da sulke na bangaskiya da ƙauna; kuma da bege na ceto, kwalkwali ke nan.” (1 Tassalunikawa 5:8) Yin nazarin Kalmar Allah kullum da kuma tarayya da ’yan’uwanmu a taro zai taimaka mana mu bi gargaɗin Bulus kuma mu natsu domin gaggawar lokaci.—Matta 16:1-3.

Miliyoyi Sun Kasance a Faɗake

14. Wane adadi ya nuna cewa mutane da yawa a yau suna bin gargaɗin Bitrus su kasance a faɗake?

14 Da akwai mutane da yawa ne a yau da suke bin huraren ƙarfafa na kasancewa a faɗake? E. A shekarar hidima ta 2002, ƙolin masu shela 6,304,645—ƙarin kashi 3.1 bisa ɗari a kan shekara ta 2001—ya ba da tabbacin kasancewa a faɗake a ruhaniya ta wurin ba da sa’o’i 1,202,381,302 a yin magana da wasu game da Mulkin Allah. Ga waɗannan, aikin nan ba marar amfani ba ne. Dalilin rayuwarsu ce. Halin mutane da yawa cikinsu mun gani a misalin Eduardo da kuma Noemi a ƙasar El Salvador.

15. Wane labari ne daga El Salvador ya nuna cewa mutane da yawa suna kasancewa a faɗake?

15 Shekarun baya, Eduardo da Noemi suka mai da hankali ga kalmomin Bitrus: “Ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa.” (1 Korinthiyawa 7:31) Suka sauƙaƙa rayuwarsu suka shiga hidimar majagaba na cikakken lokaci. Da shigewar lokaci, sun sami albarka da yawa har ma sun yi aikin ziyarar da’ira da kuma na gunduma. Duk da fuskantar matsalolin masu tsanani, Eduardo da Noemi sun tabbata cewa sun zaɓi abin da ya dace yayin da suka sadaukar da more abin duniya domin hidima ta cikakken lokaci. Da yawa cikin masu shela 29,269—haɗe da majagaba 2,454 —a El Salvador sun nuna irin wannan hali na sadaukar da kai, wanda dalili ɗaya ne da ya sa ƙasar ta samu ƙarin kashi 2 bisa ɗari a yawan masu shela a shekarar da ta shige.

16. Wane hali ne wani matashi a Côte d’Ivoire ya nuna?

16 A Côte d’Ivoire, wani matashi Kirista ya nuna irin wannan hali sa’ad da ya rubuta zuwa ga ofishin reshen: “Ni bawa mai hidima ne. Amma ba zan iya gaya wa ’yan’uwa su shiga aikin majagaba ba tun da ni kaina ba majagaba ba ne. Domin haka, na bar aiki da nake samun kuɗi sosai, yanzu ina aikin kaina da ke ba ni zarafi domin hidima.” Wannan matashin yana cikin majagaba 983 da suke hidima a Côte d’Ivoire, da masu shela 6,701 da suka ba da rahoton aiki a shekarar da ta shige, ƙarin kashi 5 bisa ɗari.

17. Ta yaya ne wata Mashaidiya matashiya a Belgium ta nuna cewa ba ta razana ba domin son kai?

17 Rashin jituwa, son kai, da kuma wariya suna ci gaba da kasancewa matsaloli ga masu shelar Mulki 24,961 a Belgium. Duk da haka, sun ci gaba da ƙwazo ba su razana ba. Lokacin da wata yarinya ’yar shekara 16 ta ji ana kwatanta Shaidun Jehovah da rukunin asiri a lokacin koyar da wani darasi a makaranta, ta karɓi izini ta bayyana ra’ayin Shaidu. Ta wurin amfani da bidiyon nan Jehovah’s Witnesses—The Organization Behind the Name da kuma mujallar nan Shaidun Jehovah—Su Wanene ne Su?, ta yi bayani game da Shaidu. Bayanin da ta yi an so shi sosai, kuma a mako na biyu an ba wa ɗaliban jarrabawa wadda dukan tambayoyin game da addinin Kirista ne, Shaidun Jehovah.

18. Wane tabbaci ne ke akwai cewa masu shela a Argentina da kuma Mozambique hankalinsu bai rabu ba daga bauta wa Jehovah domin matsalolin tattalin arziki?

18 Yawancin Kiristoci za su fuskanci matsaloli masu tsanani cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe. Duk da haka, ba su yarda hankalinsu ya rabu ba. Duk da matsalar tattalin arziki da ke ko’ina, Argentina ta ba da rahoton sabon ƙoli na Shaidu 126,709 a shekarar da ta shige. Har ila, da akwai talauci a Mozambique. Amma, mutane 37,563 suka ba da rahoton sa hannu cikin aikin wa’azi, ƙarin kashi 4 bisa ɗari. Rayuwa tana da wuya ga mutane da yawa a Albania, duk da haka wannan ƙasar ta ba da rahoto na ƙari kashi 12 bisa ɗari, da suka kai masu shela 2,708 . A bayyane yake cewa babu yanayi mai wuya da yake hana ruhun Jehovah idan bayinsa sun saka abubuwa na Mulkin da farko.—Matta 6:33.

19. (a) Menene ya nuna cewa har ila da akwai mutane masu kama da tumaki da suke da yunwa ta gaskiyar Littafi Mai Tsarki? (b) Waɗanne wasu cikakken rahoto na shekara ne suka nuna cewa bayin Jehovah suna kasancewa a faɗake a ruhaniya? (Dubi taswira a shafofi na 22-25.)

19 Avirejin 5,309,289 waɗanda aka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kowanne wata da su a duk duniya a shekarar da ta shige ya nuna cewa har ila akwai mutane masu kama da tumaki da suke da yunwa ta gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Game da sabon ƙolin 15,597,746 da suka halarci Bikin Tuna Mutuwar Yesu, yawanci ba masu bauta wa Jehovah ba ne tukuna. Bari su ci gaba da ƙaruwa a sani da Jehovah da kuma ƙaunarsa da ƙaunar ’yan’uwanci. Abin farin ciki ne mu ga cewa “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” sun ci gaba da ba da ’ya’ya yayin da suke bauta wa Mahalicci “dare da rana cikin haikalinsa” tare da ’yan’uwansu shafaffu daga ruhu.—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 15; Yohanna 10:16.

Darasi Daga Lutu

20. Menene muka koya daga misalin Lutu da matarsa?

20 Hakika, bayin Allah masu aminci ma a wani lokaci sukan yi rashin azanci na gaggawa. Ka yi tunanin Lutu ɗan wan Ibrahim. Mala’iku biyu baƙi da suka zo gidansa suka gaya masa cewa Allah zai halaka Saduma da Gwamrata. Labarin bai ba Lutu mamaki ba, wanda “ransa ya ɓaci ƙwarai domin zaƙuwa ta masu-mugunta.” (2 Bitrus 2:7) Duk da haka, lokacin da mala’ikun biyu suka zo su fitar da shi daga Saduma, ya ‘yi jinkiri.’ Sai da mala’ikun ma suka jawo shi ne da iyalin daga cikin birnin. Daga baya, matar Lutu ta yi banza da gargaɗin mala’ikun kuma ta juya baya. Halinta na rashin lura ya kasance ajalinta. (Farawa 19:14-17, 26) Yesu ya yi gargaɗi: “Ku tuna da matar Lutu.”—Luka 17:32.

21. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance a faɗake yanzu fiye da dā?

21 Bala’in da ya sami Pompeii da Herculaneum da abubuwa da suke tattare da halakar Urushalima, har da misalan Rigyawan zamanin Nuhu da kuma Lutu, sun nuna muhimmancin saurarawa da kyau ga gargaɗi. Mu bayin Jehovah muna lura da alama ta zamani na ƙarshe. (Matta 24:3) Mun ware kanmu daga addinin ƙarya. (Ru’ya ta Yohanna 18:4) Kamar Kiristoci na ƙarni na farko, muna bukatar mu ‘tuna da ranar Jehovah.’ (2 Bitrus 3:12) Hakika, dole ne mu kasance a faɗake fiye da dā! Waɗanne matakai za mu iya ɗauka, kuma waɗanne halaye ya kamata mu kasance da su don mu kasance a faɗake? Talifi na biye zai bincika waɗannan al’amura.

[Hasiya]

a Zai yi wuya idan mazauna Urushalima na ƙarni na farko sun fi 120,000. Eusebius ya ƙirga mazauna 300,000 daga yankin Yahudiya da suka je Urushalima domin bikin Faska ta shekara ta 70 A.Z. Wasu da suka mutu kuma sun fito ne daga wasu ɓangarorin daular.

b Hakika, a ra’ayin Jehovah, an sake Dokar Musa da sabon alkawari a shekara ta 33 A.Z.—Afisawa 2:15.

Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne aukuwa ne suka sa Kiristoci Yahudawa su tsira daga halakar Urushalima?

• Yaya gargaɗin da ke cikin rubuce-rubuce na manzanni Bitrus da Bulus ke taimakon mu mu kasance a faɗake?

• Su waye a yau suke tabbatar da cewa suna faɗake sosai?

• Waɗanne darasi muke koya daga labarin Lutu da matarsa?

[Taswira a shafi nas 22-25]

RAHOTO NA HIDIMAR SHEKARA TA 2002 NA SHAIDUN JEHOVAH A DUKAN DUNIYA

(See bound volume)

[Hoto a shafi na 19]

A shekara ta 66 A.Z., Kiristoci da suke Urushalima sun saurari gargaɗin Yesu

[Hotuna a shafi na 20]

Kasancewa da ƙwazo na taimakon Kiristoci su kasance a faɗake

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba