Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 6/1 pp. 20-25
  • “Kada Ku Ji Tsoro, Kada Ku Yi Fargaba”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kada Ku Ji Tsoro, Kada Ku Yi Fargaba”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tsaka-Tsaki na Kirista Ya Saɓa da Ta’addanci
  • Kasance da Gaba Gaɗi Duk da Farmaki
  • Ku Tsaya Shuru Ku Ga Ceton Jehovah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ta’addanci Zai Taba Karewa Kuwa?
    Karin Batutuwa
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 6/1 pp. 20-25

“Kada Ku Ji Tsoro, K ada Ku Yi Fargaba”

“Kada ku ji tsoro, kada ku yi fargaba . . . Ubangiji yana tare da ku.” —2 LABARBARU 20:17.

1. Yaya ta’addanci ya shafi mutane, kuma me ya sa za a fahimci dalilin tsoronsu?

TA’ADDANCI! Kalmar kawai tana kawo tsoro, tana sa a ji ba kāriya da kuma rashin taimako. Tana kawo jiye-jiye na fargaba, baƙin ciki, da kuma fushi. Kalma ce da take kwatanta abin da mutane da yawa suke tsoron zai fāɗa wa mutane shekaru da yawa nan gaba. Gaskiya cewa wasu ƙasashe suna ta yaƙi na shekaru yanzu gāba da ta’addanci a dukan fannoninsa amma ba su ci nasara ba tukun ya ba da dalilin irin wannan tsoro.

2. Yaya Shaidun Jehovah suke bi da matsalar ta’addanci, ya ta da waɗanne tambayoyi?

2 Duk da haka, da akwai ƙarfafan dalilin bege. Shaidun Jehovah da suke wa’azi sosai a ƙasashe 234 da yankunan duniya, suna da fatar kirki. Maimakon suna tsoron cewa ba za a taɓa kawar da ta’addanci ba, suna da gaba gaɗin za a iya kawar da shi—kuma ba da jimawa ba. Yana da kyau ne a bi fatarsu ta kirki? Waye zai taɓa iya kawar da wannan bala’i daga duniya, kuma ta yaya zai faru? Tun da yake dukanmu mun shaida wani nuna ƙarfi, zai yi kyau mu bincika dalilin wannan fatar kirki.

3. Waɗanne dalilan jin tsoro muke da su, kuma menene aka annabta game da zamaninmu?

3 A yau, mutane suna tsoro kuma suna fargaba domin dalilai dabam dabam. Ka yi tunanin mutane da yawa da ba sa iya kula da kansu domin tsufa, wasu da suke raunana domin rashin lafiya, da iyalai kuma da suke fama da yanayin tattalin arziki don su iya biyan bukata. Ka yi tunanin tsautsayin rai! Mutuwa ba jiyya ta haɗari ko kuma bala’i, na shirye ya kawo ƙarshen duk kome da muke ƙaunarsa. Irin wannan tsoro da alhini, har da wasu faɗace-faɗace da baƙin ciki, sun sa zamaninmu ya yi daidai da abin da manzo Bulus ya kwatanta: “Sai ka san wannan, cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo. Gama mutane za su zama masu-son kansu, . . . marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta.”—2 Timothawus 3:1-3.

4. Wane gefe mai kyau ke cikin munanan hoto da aka nuna a 2 Timothawus 3:1-3?

4 Ko da yake wannan nassin yana nuna yanayi marar kyau, amma yana ɗauke da bege. Ka lura da cewa miyagun zamanu za su faru a “kwanaki na ƙarshe” na mugun zamanin Shaiɗan. Wannan yana nufin cewa sauƙi ya kusa kuma ba zai daɗe ba za a sake wannan mugun zamani da kamiltaccen Mulkin Allah, da Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a dominsa. (Matta 6:9, 10) Mulkin gwamnati ce ta Allah a samaniya, da “ba za a rushe shi ba daɗai” annabi Daniel ya ce, amma, “za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki [na mutane] ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:44.

Tsaka-Tsaki na Kirista Ya Saɓa da Ta’addanci

5. Yaya al’ummai suke aikatawa game da burgar ta’addanci?

5 Cikin shekaru da yawa, ta’addanci ya ci rayuka dubbai. Duniya tana ƙara tunani game da wannan haɗari bayan fāɗa wa New York City da Washington, D.C., da aka yi a 11 ga Satumba, 2001. Domin yawan ta’addanci a dukan duniya, nan da nan al’umman duniya kewaye suka haɗa kai su yaƙe shi. Alal misali, a 4 ga Disamba, 2001 bisa rahoton ’yan watsa labarai, “ministoci daga ƙasashe 55 na Turai, na Amirka ta Arewa da kuma al’umman Asiya ta Tsakiya sun haɗa kai su tallafa wa wani shiri” da suka yi domin aikata ƙoƙarce-ƙoƙarcensu. Wani ma’aikacin gwamnati mai girma ya yaba wa matakin, cewa suna ba da “sabon iko” don su yaƙe ta’addanci. Farat ɗaya, miliyoyin mutane suka sa hannu cikin abin da jaridar The New York Times Magazine ta kira “somawar yaƙi mai girma.” Ko ƙoƙarce-ƙoƙarcen nan za su yi nasara, sai da shigewar lokaci. Sakamakon yaƙi gāba da ta’adda ya jawo tsoro da kuma alhini ga mutane da yawa, amma ban da waɗanda suke dogara ga Jehovah.

6. (a) Me ya sa yake wa wasu wuya wani lokaci su yarda da tsaka-tsaki na Kirista da Shaidun Jehovah suke yi? (b) Wane misali game da siyasa Yesu ya kafa wa mabiyansa?

6 An san Shaidun Jehovah domin tsaka-tsakinsu a siyasa. Yayin da yawancin mutane za su yi na’am da tsaka-tsakinsu lokacin salama, ba za su yarda da kome ba lokacin da yanayi mai wuya ya taso. Sau da yawa, tsoro da rashin tabbaci da yaƙi ke kawowa yana ta da halin ƙishin ƙasa. Wannan zai iya sa ya zama da wuya ga wasu su fahimci dalilin da zai sa wani zai ƙi ba da goyon baya ga ƙoƙarce-ƙoƙarce na al’ummai. Duk da haka, Kiristoci na gaskiya sun sani cewa dole ne su yi biyayya da dokar Yesu kada su zama “na duniya.” (Yohanna 15:19; 17:14-16; 18:36; Yaƙub 4:4) Wannan ya bukaci su kasance da tsaka-tsaki a batun zaman jama’a da na siyasa. Yesu kansa ya kafa misalin da ya dace. Game da kamiltaccen hikimarsa da iyawa ta musamman, da sai ya ba da goyon baya mai kyau ga harkokin jama’a a zamaninsa. Amma, bai sa hannu ba cikin siyasa. A farkon hidimarsa, ya ƙi da Shaiɗan kai tsaye da yake son ya ba shi sarauta bisa mulkokin duniya. Bayan haka, da gaba gaɗi ya guji matsayin siyasa da ake son a ba shi.—Matta 4:8-10; Yohanna 6:14, 15.

7, 8. (a) Menene tsaka-tsaki na Shaidun Jehovah ba ya nufi, kuma me ya sa? (b) Ta yaya ne Romawa 13:1, 2 ta faɗakar game da yi wa gwamnati ayyukan mugunta?

7 Amma tsaka-tsaki da Shaidun Jehovah suke yi bai kamata a aza cewa suna goyon bayan ayyukan nuna ƙarfi ba. Idan sun yi haka zai ƙaryata gaskiyar cewa su bayin “Allah kuwa na ƙauna da na salama” ne. (2 Korinthiyawa 13:11) Sun koyi yadda Jehovah yake ji game da nuna ƙarfi. Mai Zabura ya rubuta: “Ubangiji yana gwada mai-adalci: amma mai-mugunta da mai-son zalunci ransa yana ƙinsu.” (Zabura 11:5) Sun kuma san abin da Yesu ya gaya wa manzo Bitrus: “Mayar da takobinka gidansa: gama dukan waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi za su lalace.”—Matta 26:52.

8 Ko da yake cikin tarihi a bayyane yake cewa jabun Kiristoci suna ɗaukan “takobi,” wannan ba haka yake ba game da Shaidun Jehovah. Ba sa saka hannu a irin wannan ayyukan. Shaidun cikin aminci suna bin gargaɗin da ke a Romawa 13:1, 2: “Bari kowane mai-rai shi yi zaman biyayya da ikon masu-mulki: gama babu wani iko sai na Allah; ikokin da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah. Wanda ya yi tsayayya da iko fa, yana tsayayya kuwa da umurnin Allah ke nan: masu-tsayayya kuwa za su jawo ma kansu hukunci.”

9. A waɗanne hanyoyi biyu ne Shaidun Jehovah suke yaƙi da ta’addanci?

9 Tun da yake ta’addanci mugunta ce, bai kamata Shaidun Jehovah suna yin wani abu ba ne domin su yaƙe shi? E, ya kamata, kuma suna hakan. Na ɗaya, su kansu ba sa saka hannu cikin irin ayyukan nan. Na biyu, suna koyar da mutane ƙa’idodin Kirista da idan aka bi zai kawar da mugunta a dukan fannoninta.a Shekarar da ta shige, Shaidun sun ba da sa’o’i 1,202,381,302 a taimaka wa mutane su koyi hanyar rayuwa ta Kirista. Wannan ba ɓata lokaci ba kawai, domin an yi wa mutane 265,469 baftisma, ta wannan aikin, suka zama Shaidun Jehovah suna nuna a fili cewa sun ƙi da nuna ƙarfi.

10. Waɗanne zace-zace ake yi game da kawar da mugunta a duniyarmu ta yau?

10 Ban da haka ma, Shaidun Jehovah sun sani cewa su kansu ba za su iya kawar da mugunta daga duniya ba. Abin da ya sa ke nan suka dogara babu ragi ga wanda zai iya—Jehovah Allah. (Zabura 83:18) Duk da yawan ƙoƙarce-ƙoƙarce ta gaske, mutane ba za su iya kawo ƙarshen nuna ƙarfi ba. Hurarren marubucin Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi game da zamaninmu, “kwanaki na ƙarshe,” kuma ya ce: “Miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi, ana ruɗinsu.” (2 Timothawus 3:1, 13) Bisa wannan ra’ayin, zace-zacen mutane na cewa za su ci nasarar mugunta ba zai yiwu ba. A wata sassa, za mu iya dogara ga Jehovah ya kawar da mugunta gabaki ɗayanta kuma dindindin.—Zabura 37:1, 2, 9-11; Misalai 24:19, 20; Ishaya 60:18.

Kasance da Gaba Gaɗi Duk da Farmaki

11. Waɗanne matakai Jehovah ya ɗauka domin ya kawar da mugunta?

11 Da yake Allah na salama ya ƙi mugunta, za mu iya fahimtar dalilin da ya sa ya ɗauki mataki domin ya kawar da tushen mugunta, Shaiɗan Iblis. Hakika, Ya riga ya sa Shaiɗan ya sha kunya a hannun shugaban mala’iku—sabon Sarki da Allah ya naɗa, Kristi Yesu. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi haka: “Aka yi yaƙi cikin sama: Mika’ilu da nasa mala’iku suna fita su yi gāba da dragon; dragon kuma ya yi gāba tare da nasa mala’iku; ba su rinjaya ba, ba a kuwa ƙara tararda matsayinsu cikin sama ba. Aka jefarda babban dragon, tsohon macijin, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan, mai-ruɗin dukan duniya; aka jefarda shi a duniya, aka jefarda mala’ikunsa kuma tare da shi.”—Ru’ya ta Yohanna 12:7-9.

12, 13. (a) Menene muhimmin abu game da shekara ta 1914? (b) Menene annabcin Ezekiel ya faɗi game da waɗanda suke goyon bayan Mulkin Allah?

12 Ƙirgen kwanaki na Littafi Mai Tsarki da aukuwan duniya sun yi daidai a nuni ga shekarar 1914 cewa lokaci ne da yaƙi ya auku a sama. Tun daga lokacin, yanayin duniya ya ci gaba da muni. Ru’ya ta Yohanna 12:12 ta bayyana dalilin da cewa: “Domin wannan fa, ku yi farinciki, ya sammai, da ku mazauna a ciki. Kaiton duniya da teku: domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.”

13 Abin da ya sa ke nan, hasalar Iblis musamman yake bisa kan shafaffu masu bauta wa Allah da kuma abokansu “waɗansu tumaki.” (Yohanna 10:16; Ru’ya ta Yohanna 12:17) Wannan hamayya ba da daɗewa ba za ta kai ƙarshenta lokacin da Iblis zai kai farmaki wa dukan waɗanda suke goyon bayan Mulkin Allah da aka kafa kuma da suka dogara gare shi. Wannan farmaki na duka duka an nuna a Ezekiel sura 38 cewa farmaki ne daga “Gog na ƙasar Magog.”

14. Waɗanne ƙoƙarce-ƙoƙarce na kāriya ne aka yi wa Shaidun Jehovah a lokacin dā, kuma haka zai ci gaba da kasancewa ne?

14 Tun lokacin da aka jefo Shaiɗan daga sama, a wasu lokatai wasu ’yan siyasa sun kāre mutanen Allah daga farmakin Shaiɗan da aka kwatanta a yaren alama ta Ru’ya ta Yohanna 12:15, 16. A saɓawa, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a lokacin farmakin Shaiɗan na ƙarshe, babu ƙungiyar ’yan Adam da za ta taimaka wa waɗanda suka dogara ga Jehovah. Ya kamata ne wannan ya sa Kiristoci su ji tsoro ko kuma su yi fargaba? Babu!

15, 16. (a) Kalmomi na tabbatarwa da Jehovah ya yi wa mutanensa a zamanin Jehoshaphat, wane bege ya ba wa Kiristoci a yau? (b) Wane tafarki Jehoshaphat da mutanensa suka kafa wa bayin Allah a yau?

15 Allah zai yi goyon bayan mutanensa yadda ya goyi bayan al’ummarsa a zamanin Sarki Jehoshaphat. Mu karanta: “Ku kasa kunne, ku Yahuda duka, da ku mazaunan Urushalima, da kuma kai sarki Jehoshaphat: haka Ubangiji ya ce muku, Kada ku ji tsoro, kada ku yi fargaba sabili da wannan babban taro; gama yaƙin ba naku ba ne, amma na Allah ne. . . . Babu bukata ku yi wannan yaƙi: ku yi shiri, ku tsaya shuru, ku ga ceton Ubangiji a wurinku, ya Yahuda da Urushalima; kada ku ji tsoro, kada ku yi fargaba; gobe ku fita garin yaƙi da su, gama Ubangiji yana tare da ku.”—2 Labarbaru 20:15-17.

16 An tabbatar wa mutanen Yahuda cewa ba sa bukatar su yi yaƙi. Haka nan ma, lokacin da Gog na Magog zai yi wa mutanen Allah farmaki, ba za su ɗauka makamai don su yi faɗa ba. Maimako, za su ‘tsaya shuru, su ga ceton Jehovah’ a wurinsu. Hakika, tsayawa cik ba ya nufin zaman dutse ba, yadda ma yake da mutanen Allah a zamanin Jehoshaphat, ba su zauna kawai babu aiki ba. Mu karanta: “Sai Jehoshaphat ya sunkuyadda kansa, fuskatasa a ƙasa: dukan Yahuda da mazaunan Urushalima suka fāɗi a gaban Ubangiji, suna sujjada ga Ubangiji. . . . Sa’anda [Jehoshaphat] ya yi shawara da jama’a, ya sa waɗanda za su yi waƙa ga Ubangiji, su yi yabo cikin jamalin tsarki, lokacinda su ke fitowa a gaban runduna, su ce, Ku yi godiya ga Ubangiji: gama jinƙansa yana tabbata har abada.” (2 Labarbaru 20:18-21) Hakika, har a cikin farmakin abokan gāba ma, mutanen sun ci gaba da yabon Jehovah sosai. Wannan tafarki ne ga Shaidun Jehovah su bi lokacin da Gog ya fāɗa musu.

17, 18. (a) Wane hali na gaba gaɗi ne Shaidun Jehovah suke da shi a yau game da farmakin Gog? (b) Wace tunasarwa aka yi wa matasa Kirista kwanan baya bayan nan?

17 Har sai lokacin—har ma idan farmakin Gog ya fara—Shaidun Jehovah za su ci gaba da goyon bayan Mulkin Allah. Za su ci gaba da samun ƙarfi da kāriya ta wurin yin tarayya da ikilisiyoyi fiye da 94,600 a dukan duniya. (Ishaya 26:20) Lallai lokaci ne da za su yi yabon Jehovah da gaba gaɗi! Hakika, rayuwa da tsammanin farmakin Gog bai sa su noƙe don tsoro ba. Maimako, yana motsa su su ƙara ba da hadayarsu na yabo yadda za su iya.—Zabura 146:2.

18 Matasa dubbai sun nuna irin wannan hali na gaba gaɗi a dukan duniya da suka ɗauki hidima ta cikakken lokaci. Domin a nanata fificin zaɓan yayin rayuwar nan, aka fito da warƙar nan Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku? a taron gunduma na shekara ta 2002. Kiristoci, ƙanana da manya, sun nuna godiya ga wannan tunasarwa a kan kari.—Zabura 119:14, 24, 99, 119, 129, 146.

19, 20. (a) Me ya sa Kiristoci ba su da dalilin jin tsoro ko kuma yin fargaba? (b) Menene talifi na gaba zai yi?

19 Duk da yanayin duniya, Kiristoci ba sa bukatar jin tsoro ko kuma yin fargaba. Sun sani cewa ba da daɗewa ba Mulkin Jehovah zai share mugunta a dukan fannoninsa dindindin. Suna da ta’aziyya kuma na sanin cewa ta tashin matattu waɗanda suka mutu domin mugunta za su sake rayuwa. Tashin matattun zai ba wasu zarafi na farko su koya game da Jehovah, zai sa wasu su ci gaba cikin tafarkin hidimarsu ta keɓe kai gare shi.—Ayukan Manzanni 24:15.

20 Mu Kiristoci na gaskiya, mun fahimta bukatar riƙe tsaka-tsaki na Kirista kuma muna ƙudura yin haka. Muna son mu riƙe zato na iya ‘tsaya shuru, mu ga ceton Ubangiji.’ Talifi na gaba zai ƙarfafa bangaskiyarmu ta wurin sa mu fahimta aukuwa na zamanin nan da ke daɗa ba mu fahimi game da cikar annabcin Littafi Mai Tsarki.

[Hasiya]

a Don ka ga misalan mutane da suka bar halayensu na nuna ƙarfi domin su zama Shaidu, ka duba fitar Awake! na 22 ga Maris, 1990, shafi na 21; 8 ga Agusta, 1991, shafi na 18 (Turanci); da kuma fitar Hasumiyar Tsaro 1 ga Janairu, 1996, shafi na 5; 1 ga Agusta, 1998, shafi na 5 (Turanci).

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Me ya sa mutane da yawa a yau suke rashin bege?

• Me ya sa Shaidun Jehovah suke da bege game da nan gaba?

• Menene Jehovah ya riga ya yi game da tushen dukan nuna ƙarfi?

• Me ya sa babu dalilin mu ji tsoron farmakin Gog?

[Hoto a shafi na 21]

Yesu ya kafa misalin da ya dace na tsaka-tsaki na Kirista

[Hotuna a shafi na 24]

Dubban Shaidu matasa cikin farin ciki sun ɗauki hidima ta cikakken lokaci

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 20]

HOTON UN 186226/M. Grafman

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba