Yaya Ya Kamata Mu Ɗauki Mutane Yayin Da Ranar Jehovah Take Kusa?
“Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zancen alkawarinsa . . . amma mai-haƙuri ne zuwa gareku, ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.”—2 BITRUS 3:9.
1, 2. (a) Yaya Jehovah yake ɗaukan mutane a yau? (b) Waɗanne tambayoyi za mu yi wa kanmu?
BAYIN Jehovah suna da aiki na “almajirtadda dukan al’ummai.” (Matta 28:19) Yayin da muke cika wannan aikin kuma jiran “ranar Ubangiji,” muna bukatar mu ɗauki mutane yadda yake ɗaukansu. (Zephaniah 1:14) Yaya Jehovah yake ɗaukan mutane? Manzo Bitrus ya ce: “Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zancen alkawarinsa, yadda waɗansu mutane su ke aza jinkiri; amma mai-haƙuri ne zuwa gareku, ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.” (2 Bitrus 3:9) Allah yana ɗaukan mutane da cewa waɗanda za su tuba ne. Nufinsa ne “[ire-iren] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:4) Jehovah yana farin ciki ma sa’ad da “mugun [ya] juyo ga barin hanyarsa shi yi rai”!—Ezekiel 33:11.
2 Muna ɗaukan mutane yadda Jehovah yake ɗaukansu? Kamarsa, muna ɗaukan mutane na kowacce ƙabila da al’umma waɗanda za su zama “tumakin makiyayatasa” ne? (Zabura 100:3; Ayukan Manzanni 10:34, 35) Bari mu bincika misalai biyu da suka nuna muhimmancin kasance da ra’ayin Allah. A dukan yanayin, halaka ta kai kuma an gaya wa bayin Jehovah wannan tun da wuri. Waɗannan misalai suna da muhimmanci yayin da muke jiran babbar rana na Jehovah.
Ibrahim Yana da Ra’ayin Jehovah
3. Menene ra’ayin Jehovah game da mazaunan Saduma da Gwamrata?
3 Misali na farko ya ƙunshi Ibrahim uban iyali mai aminci da miyagun biranen Saduma da Gwamrata. Sa’ad da Jehovah ya ji “ƙarar [Saduma] da [Gwamrata]” bai halaka waɗannan biranen da dukan mazaunansu nan da nan ba. Da farko ya yi bincike. (Farawa 18:20, 21) An aiki mala’iku biyu zuwa Saduma, inda suka zauna a gidan Lutu mutum mai adalci. Daddare da mala’ikun suka isa, “mutanen birni . . . suka kewaye gida, da samari da tsofaffi, dukan mutane daga kowacce unguwa,” suna son su yi jima’i da mala’ikun. A bayyane, mugun yanayi na mazaunan birnin ya nuna cewa ya cancanci a halaka shi. Duk da haka, mala’ikun suka gaya wa Lutu: “Kana da waɗansu kuma daga nan? ko suruki, da ’ya’yanka, maza da mata, wanda ka ke da shi duka cikin birni kuma; ka fitarda su daga wurin nan.” Jehovah ya buɗe hanyar ceton wasu mazaunan birnin, amma a ƙarshe, Lutu ne kaɗai da ’ya’yansa mata biyu suka tsira wa halakar.—Farawa 19:4, 5, 12, 16, 23-26.
4, 5. Me ya sa Ibrahim ya yi roƙo domin mazaunan Saduma, ra’ayinsa game da mutane ya yi daidai da na Jehovah ne?
4 To, bari mu koma zuwa lokacin da Jehovah ya bayyana nufinsa ya bincika biranen Saduma da Gwamrata. Lokacin ne Ibrahim ya yi roƙo: “Wataƙila ko da akwai masu-adalci guda hamsin a cikin birni: za ka halaka wurin, ka ƙi keɓewa sabili da masu-adalci hamsin da ke ciki? Wannan ya yi nisa da kai ka yi irin wannan, a kashe masu-adalci tare da miyagu, har kuma masu-adalci za su zama ɗaya da miyagu; wannan ya yi nisa da kai: Mai-shari’an dukan duniya ba za ya yi daidai ba?” Ibrahim ya yi amfani da furcin nan “wannan ya yi nisa da kai” sau biyu. Daga abin da ya faru, Ibrahim ya sani cewa Jehovah ba zai halaka masu adalci tare da miyagu ba. Sa’ad da Jehovah ya ce ba zai halaka Saduma ba idan akwai “masu-adalci guda hamsin a cikin birni,” Ibrahim ya ci gaba da rage adadin har ya kai goma kaɗai.—Farawa 18:22-33.
5 Da Jehovah zai saurari roƙon Ibrahim ne idan ba su yi daidai da nasa ra’ayin ba? Sam. Da yake shi “abokin Allah ne” babu shakka cewa Ibrahim ya san kuma yana da ra’ayinsa. (Yaƙub 2:23) Sa’ad da Jehovah ya mai da hankalinsa zuwa Saduma da Gwamrata, ya nuna yardan rai a yin la’akari da roƙon Ibrahim. Me ya sa? Domin Ubanmu na samaniya “ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.”
Yadda Yunana Yake Ɗaukan Mutane—Ya Yi Dabam Sosai
6. Yaya mutanen Nineba suka aikata ga sanarwar Yunana?
6 Yanzu ka yi la’akari da misali na biyu—Yunana ne. A wannan misalin birni da ake son a halaka Nineba ne. An gaya wa annabi Yunana ya sanar cewa muguntar birnin ‘ta hau gaban Jehovah.’ (Yunana 1:2) Har da unguwar waje, Nineba babban birni ce, “na tafiyar yini uku.” Sa’ad da a ƙarshe Yunana ya yi biyayya kuma shiga Nineba, ya ci gaba da sanarwa: “Da sauran kwana arba’in tukuna, kāna a kaɓantadda Nineveh.” Da haka, “mutanen Nineveh suka gaskata Allah; suka yi shelar azumi, suka sa tsummoki.” Har ma sarkin Nineba ya tuba.—Yunana 3:1-6.
7. Yaya Jehovah ya ɗauki halin tuba na mutanen Nineba?
7 Wannan dabam yake da yadda Saduma ta aikata! Yaya Jehovah ya ɗauki mutanen Nineba da suka tuba? Yunana 3:10 ta ce: “Allah kuwa ya tuba ga barin masifar da ya ce za ya yi musu.” Jehovah “ya tuba” yana nufin cewa ya canja ra’ayinsa game da mutanen Nineba domin sun canja hanyoyinsu. Mizanan Allah bai canja ba, amma Jehovah ya canja shawararsa da ya ga cewa mutanen Nineba sun tuba.—Malachi 3:6.
8. Me ya sa Yunana ya yi baƙin ciki?
8 Sa’ad da Yunana ya gano cewa ba za a halaka Nineba ba, ya ɗauki abubuwa ne bisa ra’ayin Jehovah? A’a, domin an gaya mana: “Amma abin ya ɓata zuciyar Yunana ƙwarai, har ya yi fushi.” Menene kuma Yunana ya yi? Labarin ya ce: “Ya yi addu’a ga Ubangiji, ya ce, Ina roƙonka, ya Ubangiji, ko ba abin da na ce ke nan ba, tun ina can garina tukuna? Domin wannan na gaggauta in yi gudu zuwa Tarshish; gama na sani kai Allah mai-nasiha ne, cike da juyayi, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai, kana kuwa tuba ga barin masifan.” (Yunana 4:1, 2) Yunana ya san game da halayen Jehovah. Amma a lokacin, annabin ya yi baƙin ciki kuma bai kasance da ra’ayin Allah ba game da mazaunan Nineba da suka tuba.
9, 10. (a) Wane darasi ne Jehovah ya koya wa Yunana? (b) Me ya sa za mu yi tsammani cewa Yunana daga baya ya ɗauki ra’ayin Jehovah game da mutanen Nineba?
9 Yunana ya fita daga Nineba, ya gina rumfa kuma zauna a inuwanta “har shi ga abin da za ya faru ga birnin.” Jehovah ya sa zurma ta tsiro don ya kawo wa Yunana inuwa. Washegari, tsiron ya yi yaushi. Sa’ad da Yunana ya ji haushi game da wannan, Jehovah ya ce: “Ka ji juyayin zurman, . . . ni kuwa ba zan ji tausayin Nineveh, babban birnin nan ba, wadda mutum da ke cikinta sun fi zambar ɗari da ashirin waɗanda ba su iya rarrabe hannun damansu da hagu ba; da kuwa dabbobi dayawa?” (Yunana 4:5-11) Lallai Yunana ya koyi darasi game da yadda Jehovah yake ɗaukan mutane!
10 Ba a rubuta amsar da Yunana ya bayar ba game da abin da Allah ya ce game da jin tausayin mutanen Nineba. Duk da haka, a bayyane yake cewa annabin ya gyara ra’ayinsa game da mutanen Nineba da suka tuba. Za mu iya kammala haka domin yadda Jehovah ya yi amfani da shi ya rubuta wannan hurarren labarin.
Wane Hali Kake da Shi?
11. Da yaya Ibrahim zai ɗauki mutane da suke a yau?
11 A yau, muna jiran wata halaka—na wannan mugun zamani a babbar rana ta Jehovah. (Luka 17:26-30; Galatiyawa 1:4; 2 Bitrus 3:1) Da yaya Ibrahim zai ɗauki mutane da suke zama cikin wannan duniya da ba da daɗewa ba za a halaka? Lallai zai damu game da waɗanda har ila ba su ji “bishara kuwa ta mulki” ba. (Matta 24:14) Ibrahim a kai a kai ya roƙi Allah game da masu adalci a Saduma. Muna damuwa game da mutane da za su ƙi da hanyoyin wannan duniya da Shaiɗan ke mallakarta idan an ba su zarafi su tuba su bauta wa Allah?—1 Yohanna 5:19; Ru’ya ta Yohanna 18:2-4.
12. Me ya sa yake da sauƙi mu koya hali kamar na Yunana game da mutane da muke saduwa da su a hidimarmu, menene za mu iya yi game da wannan?
12 Ya dace mu so ganin ƙarshen mugunta. (Habakkuk 1:2, 3) Duk da haka, yana da sauƙi mu koya hali kamar na Yunana, ba za mu damu da zaman lafiyar mutane da ƙila za su tuba ba. Wannan haka yake idan mun ci gaba da saduwa da mutane da ba sa so, suna hamayya, ko kuma masu faɗa sa’ad da muka je gidajensu da saƙon Mulki. Za mu iya manta da waɗanda har ila Jehovah zai tara su daga cikin wannan mugun zamani. (Romawa 2:4) Idan bayan mun bincika kanmu sosai muka ga cewa muna da ɗan halin Yunana game da mutanen Nineba, za mu iya addu’a mu daidaita ra’ayinmu da na Jehovah.
13. Me ya sa za mu ce Jehovah yana damuwa game da mutane a yau?
13 Jehovah yana damuwa da waɗanda ba su soma bauta masa ba tukuna, kuma yana sauraron roƙon mutanensa da suka keɓe kansu. (Matta 10:11) Alal misali, “za ya rama musu” wajen amsa addu’o’insu. (Luka 18:7, 8) Ƙari ga haka, Jehovah zai cika alkawura da nufe-nufensa a nasa lokacin. (Habakkuk 2:3) Wannan zai haɗa da kawar da dukan mugunta daga duniya, yadda ya halaka Nineba bayan mazaunan suka sake faɗuwa cikin mugunta.—Nahum 3:5-7.
14. Me ya kamata muna yi yayin da muke jiran babbar rana ta Jehovah?
14 Za mu ci gaba da jira da haƙuri har sai an cire wannan mugun zamani a babbar rana ta Jehovah, muna shagala a yin nufinsa? Ba mu san dalla-dalla game da yawan yadda za a yi aikin wa’azi kafin ranar Jehovah ta zo ba, amma mun sani cewa za a yi wa’azin bisharar Mulki a dukan duniya har Allah ya gamsu kafin ƙarshen ya zo. Kuma babu shakka ya kamata mu damu game da “muradin” da har ila za a shigo da su yayin da Jehovah ya ci gaba da cika gidansa da ɗaukaka.—Haggai 2:7.
Ana Ganin Ra’ayinmu ta Ayyukanmu
15. Menene zai ƙara godiyarmu ga aikin wa’azi?
15 Wataƙila muna zama a yankin da ba a son aikin wa’azi, kuma yanayinmu bai ƙyale mu mu ƙaura ba zuwa inda akwai bukata matuƙa na masu shelar Mulki. A ce za a samu goma a yankinmu kafin ƙarshen ya zo. Muna jin waɗannan goma sun cancanci a neme su? Yesu ya “yi juyayin” taron “domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Matta 9:36) Ta nazarin Littafi Mai Tsarki da karatun talifofin Hasumiyar Tsaro da Awake!, za mu samu fahimi sosai game da yanayin duniya. Wannan zai ƙara godiyarmu don bukatar wa’azin bishara. Ƙari ga haka, yin amfani da littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ke tanadinsa za su daɗa rinjayarmu a yankin da ake aiki a kai a kai.—Matta 24:45-47; 2 Timothawus 3:14-17.
16. Ta yaya za mu ƙara kyautata hidimarmu?
16 Damuwarmu game da waɗanda nan gaba wataƙila za su saurari saƙon Littafi Mai Tsarki mai ba da rai za ta sa mu yi la’akari da lokatai da muke wa’azi da hanyoyi da muke soma magana da mutane a hidimarmu. Muna iske cewa mutane da yawa ba sa gida lokacin da muke ziyara? Idan haka ne, za mu iya ƙara kyautata hidimarmu ta canja lokatai da wuraren aikinmu na wa’azi. Masunta suna zuwan kama kifi lokacin da za su iya samu. Za mu iya yin haka nan a aikinmu na kama kifi na ruhaniya? (Markus 1:16-18) Me ya sa ba za ka gwada yin wa’azi da yamma da kuma yin wa’azi ta tarho, inda ake amfani da waɗannan ba? Wasu sun iske cewa wuraren da ake ajiye motoci, inda manyan motoci na kaya suke tsayawa, tashan shan mai, da kantuna ‘wuraren kamun kifi’ ne masu ba da amfani. Zai zama a bayyane idan muna da hali kamar na Ibrahim game da mutane sa’ad da muka yi amfani da zarafi mu yi wa’azi na zarafi.
17. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya ƙarfafa masu wa’azi na ƙasashen waje da wasu da suke hidima a wasu ƙasashe?
17 Mutane da yawa har ila ba su ji saƙon Mulki ba. Ƙari ga wa’azinmu, za mu nuna muna damuwa da mutane ko daga cikin gidanmu ma? To, mun san masu wa’azi na ƙasashen waje ko masu hidima na cikakken lokaci da suke hidima a wata ƙasa? Idan haka ne, zai yi kyau mu rubuta musu wasiƙa mu nuna muna godiya da aikinsu. Yaya wannan zai nuna damuwa da mutane? Wasiƙunmu na ƙarfafa da yabo zai iya ƙarfafa masu wa’azi na ƙasashen waje su ci gaba da aikinsu, da haka su ƙara taimakon mutane su zo ga sanin gaskiya. (Alƙalawa 11:40) Za mu iya yi wa masu wa’azi na ƙasashen waje addu’a da kuma waɗanda suke yunwar gaskiya a wasu ƙasashe. (Afisawa 6:18-20) Wata hanya da za mu nuna muna damuwa ita ce ta ba da kyautar kuɗi ga aikin da Shaidun Jehovah suke yi a dukan ƙasashe.—2 Korinthiyawa 8:13, 14; 9:6, 7.
Za Ka Iya Ƙaura?
18. Menene wasu Kiristoci suka yi don su ɗaukaka abubuwa na Mulki a ƙasar da suke da zama?
18 Waɗanda suka ƙaura zuwa wurare da akwai matuƙar bukata na masu shelar Mulki sun samu albarka don sadaukar da kansu. Yayin da suke ƙasarsu wasu Shaidun Jehovah sun koyi wani yare don su taimaki waɗanda suka bar ƙasarsu a ruhaniya. An albarkace irin wannan ƙoƙarin. Alal misali, Shaidu bakwai da suke taimakon mutanen Sin a birnin Texas, a Amirka sun yi wa mutane 114 maraba a bikin Jibin Maraice na Ubangiji a shekara ta 2001. Waɗanda suke taimakon irin waɗannan rukunin sun iske cewa filayensu sun kai a yi girbi.—Matta 9:37, 38.
19. Menene zai fi kyau ka yi idan kana tunanin ƙaura zuwa wata ƙasa don ka faɗaɗa aikin wa’azi na Mulki a wurin?
19 Wataƙila da kai da iyalinka kuna jin kuna matsayin ƙaura zuwa wurin da akwai matuƙar bukata na masu wa’azin Mulki. Amma, da farko, ya fi kyau ka “fara zaunawa tukuna, [k]a yi lissafin tamanin.” (Luka 14:28) Wannan gaskiya ne sa’ad da mutum yake tunanin ƙaura zuwa wata ƙasa. Zai yi kyau kowa da yake tunanin wannan ya yi wa kansa irin waɗannan tambayoyi: ‘Zan iya biya wa iyalina bukatar kuɗi? Zan iya samun takardar tafiya da ya dace? Na iya yaren ƙasar, ko zan yarda in koya? Na yi tunanin yanayin da kuma al’adar? Zan kasance mai yin “ta’aziyya” ba kaya ba ga ’yan’uwa masu bi a ƙasar?’ (Kolossiyawa 4:10, 11) Don ka san bukatar da take ƙasar da kake tunanin zuwa, ya dace ka rubuta wa ofishin reshe na Shaidun Jehovah da suke kula da aikin wa’azi a wurin.a
20. Yaya wani matashi Kirista ya ba da kansa don amfanin ’yan’uwa masu bi da kuma wasu a wata ƙasa?
20 Wani Kirista da yake cikin aikin gina Majami’un Mulki a Japan ya ji cewa ana bukatar gwanaye da za su gina wajen bauta a Paraguay. Da yake bai yi aure ba kuma yana da ƙarfi na matashi, ya ƙaura zuwa wannan ƙasar kuma ya yi aiki na watanni takwas shi kaɗai ne mai aikin gini na cikakken lokaci. Lokacin da yake wurin, ya koyi Spanisanci kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida. Ya ga ana bukatar masu shelar Mulki a ƙasar. Ko da ya koma Japan, ba da daɗewa ba ya koma Paraguay kuma ya taimaka a tara mutane zuwa wannan Majami’ar Mulki.
21. Me ya kamata ya zama damuwarmu ta musamman da kuma ra’ayinmu yayin da muke jiran babbar rana ta Jehovah?
21 Allah zai tabbata cewa an yi aikin wa’azin sosai, cikin jituwa da nufinsa. A yau, yana hanzarta girbi na ruhaniya na ƙarshe. (Ishaya 60:22) Yayin da muke jiran ranar Jehovah, bari mu sa hannu cikin aikin girbi da himma kuma mu ɗauki mutane yadda Allahnmu mai ƙauna yake ɗaukansu.
[Hasiya]
a Ba koyaushe yake da kyau ka ƙaura kawai zuwa wata ƙasa inda aka hana aikin wa’azi ba tambaya ba. Yin haka zai ma jawo wahala ga masu shelar Mulki da suke aiki cikin hikima a irin wannan yanayi.
Ka Tuna?
• Yayin da muke jira ranar Jehovah, yaya ya kamata mu ɗauki mutane?
• Menene ra’ayin Ibrahim game da masu adalci da ƙila suke zama a Saduma?
• Yaya Yunana ya ɗauki mutanen Nineba da suka tuba?
• Ta yaya za mu nuna muna da ra’ayin Jehovah game da mutane da ba su ji bisharar ba tukuna?
[Hoto a shafi na 14]
Ibrahim ya ɗauki mutane yadda Jehovah yake ɗaukansu
[Hoto a shafi na 15]
Daga baya Yunana ya ɗauki ra’ayin Jehovah game da mutanen Nineba da suka tuba
[Hotuna a shafi na 16]
Damuwa da mutane na motsa mu mu yi la’akari da lokatai da hanyoyin wa’azin bishara