Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 10/1 pp. 24-29
  • Jimre Wa Gwaji Yana Kawo Wa Jehovah Yabo

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jimre Wa Gwaji Yana Kawo Wa Jehovah Yabo
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kasance da Aminci Ƙarƙashin Gwaji
  • “Kada Ku Saka ma Kowanne Mutum Mugunta da Mugunta”
  • Farin Cikin Tsarkake Sunan Jehovah
  • Shan Tsanani Domin Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Za Ka Iya Jimre Tsanantawa
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Mu Rika Farin Ciki Sa’ad da Muke Jimre Jarrabawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 10/1 pp. 24-29

Jimre Wa Gwaji Yana Kawo Wa Jehovah Yabo

“Idan, sa’anda ku ke yin nagarta, kuna shan wuya dominta kuwa, kuka yi haƙuri, wannan abin karɓa ne wurin Allah.”—1 BITRUS 2:20.

1. Tun da yake Kiristoci na gaskiya suna damuwa game da keɓewar kansu, wace tambaya ce za a bincika?

KIRISTOCI sun keɓe kansu ga Jehovah kuma suna son su yi nufinsa. Domin su cika wannan keɓewar kai, sun yi iyakacin ƙoƙarinsu su bi sawun Gurbinsu, Yesu Kristi, kuma su ba da shaida ga gaskiya. (Matta 16:24; Yohanna 18:37; 1 Bitrus 2:21) Amma Yesu da wasu masu aminci sun ba da ransu suka mutu domin imaninsu. Wannan yana nufin cewa dukan Kiristoci za su yi zaton su mutu domin imaninsu ne?

2. Yaya Kiristoci suke ɗaukan gwaji da kuma tsanani?

2 Mu Kiristoci, an gargaɗe mu mu kasance da aminci har mutuwa, ba sai mun mutu domin imaninmu ba. (2 Timothawus 4:7; Ru’ya ta Yohanna 2:10) Wannan yana nufin cewa a shirye muke mu sha wahala—har ma idan ya wajaba mu mutu—domin imaninmu, ba ma sha’awar yin haka. Ba ma murna mu sha wahala ba kuma ba ma jin daɗin azaba ko kuma shan kunya ba. Tun da yake muna tsammanin gwaji da tsanani, muna bukatar mu mai da hankali mu lura da yadda za mu aikata sa’ad da hakan ya faru mana.

Kasance da Aminci Ƙarƙashin Gwaji

3. Waɗanne misalai na Littafi Mai Tsarki na yadda ake bi da tsanantawa za ka iya ba da? (Duba akwati “Yadda Suka Bi da Tsanantawa,” a shafi na gaba.)

3 A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai labarai da yawa da sun nuna yadda bayin Allah a dā suka aikata sa’ad da suka fuskanci yanayi na razanar da rai. Yadda suka aikata ya zama wa Kiristoci a yau ja-gora idan suka fuskanci irin waɗannan gwaji. Yi la’akari da labarai na cikin akwatin nan “Yadda Suka Bi da Tsanantawa,” ka ga abin da za ka koya daga ciki.

4. Me za a ce game da yadda Yesu da wasu bayi masu aminci suka aikata sa’ad da suke fuskantar gwaji?

4 Ko da yake Yesu da wasu bayin Allah masu aminci sun aikata dabam dabam ga tsanantawa dangane da yanayin, a bayyane yake cewa ba su saka ransu cikin haɗari ba. Sa’ad da suke cikin yanayi na haɗari, sun yi gaba gaɗi amma da wayo. (Matta 10:16, 23) Manufarsu su ci gaba da wa’azin ne kuma su riƙe amincinsu ga Jehovah. Yadda suka aikata a yanayi dabam dabam ya zama misali ga Kiristoci waɗanda a yau suke fuskantar gwaji da tsanantawa.

5. Wace irin tsanantawa ce ta taso a Malawi a shekarun 1960, yaya Shaidun suka yi?

5 A zamanin yau, mutanen Jehovah suna iske kansu cikin yanayi na wahala ƙwarai kuma da takunkumi saboda yaƙi, hani, ko kuma tsanantawa kai tsaye. Alal misali, a shekarun 1960, an tsananta wa Shaidun Jehovah a Malawi ƙwarai. An halaka Majami’un Mulkinsu, gidaje, abinci, da kuma kasuwancinsu—kusan kome da suke da shi. An yi musu dūka kuma an gana musu azaba. Yaya ’yan’uwan suka aikata? Dubbansu sun gudu sun bar ƙauyukansu. Wasu da yawa sun yi mafaka cikin daji, sa’in nan kuma wasu sun yi gudun hijira na ɗan lokaci zuwa Mozambique. Ko da yake mutane masu aminci da yawa sun mutu, wasu sun gudu daga wurin haɗarin, mataki ne da ya dace a cikin irin yanayin nan. A yin haka, ’yan’uwan sun bi tafarkin Yesu da Bulus.

6. Menene Shaidu na Malawi ba su daina yi ba duk da yawan tsanantawa?

6 Ko da ’yan’uwa na Malawi sun ƙaura ko kuma ɓoye, sun nemi kuma bi ja-gora na tsarin Allah, kuma sun ci gaba da aikin Kirista a ɓoye iyakacin ƙoƙarinsu. Menene sakamakon haka? An samu ƙolin masu shelar Mulki 18,519 kafin a yi musu hani a shekara ta 1967. Ko da ana kan hani kuma mutane sun gudu zuwa Mozambique, an samu rahoton sabon ƙoli na masu shela 23,398 a shekara ta 1972. Suna samun avirejin fiye da awa 16 kowanne wata a hidima. Babu shakka ayyukan ya kawo wa Jehovah yabo, kuma waɗannan ’yan’uwa masu aminci sun sami albarkar Jehovah a lokacin nan mafi wuya.a

7, 8. Saboda waɗanne dalilai ne wasu suka zaɓi ba za su gudu ba, ko da hamayya tana kawo wasu matsaloli?

7 A wata sassa, a ƙasashe inda hamayya take kawo matsaloli, wasu ’yan’uwa suna iya shawara ba za su ƙaura ba ko da za su iya yin haka. Ƙaura na iya kawar da wasu matsaloli, amma tana iya kawo wasu matsaloli. Alal misali, za su iya sadawa da ’yan’uwanci na Kirista ba tare da ware kansu a ruhaniya ba? Za su iya ci gaba ne da tsarin ruhaniya yayin da suke fama su sami zama, ƙila a ƙasashe masu arziki ko kuma da zai ba su zarafin samun abin duniya?—1 Timothawus 6:9.

8 Wasu sun zaɓi ba za su ƙaura ba domin sun damu da lafiyar ruhaniya na ’yan’uwansu. Sun zaɓi su zauna kuma su fuskanci yanayin domin ci gaba da wa’azi a garinsu kuma su zama abin ƙarfafa ga ’yan’uwa masu bauta. (Filibbiyawa 1:14) Ta yin irin zaɓen nan, wasu sun taimaka a samun nasara ta doka a ƙasarsu.b

9. Waɗanne abubuwa dole mutum ya bincika sa’ad da ake shawarar za a ƙaura ko ba za a ƙaura ba saboda tsanantawa?

9 A zauna ko a ƙaura—hakika zaɓenka ne. Ya kamata a yi irin shawarar nan bayan an yi addu’a ta neman ja-gora daga Jehovah. Kowanne tafarki muka zaɓa, dole mu tuna da kalmomin manzo Bulus: “Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Romawa 14:12) Yadda muka lura da farko, abin da Jehovah yake bukata shi ne cewa kowanne cikin bayinsa su kasance da aminci a dukan yanayi. Wasu cikin bayinsa suna fuskantar gwaji da tsanantawa a yau; wasu kuma yana nan gaba. Kowa zai sami nasa gwajin, kar wani ya ce ba zai fuskanci gwaji ba. (Yohanna 15:19, 20) Da yake mu bayin Jehovah ne da suka keɓe kai, ba za mu iya guje wa batun nan na dukan halitta da ya shafi tsarkake sunan Jehovah da kuma kunita ikon mallakarsa ba.—Ezekiel 38:23; Matta 6:9, 10.

“Kada Ku Saka ma Kowanne Mutum Mugunta da Mugunta”

10. Wane muhimmin misali Yesu da manzanni suka bar mana a yadda za mu bi da matsi da kuma hamayya?

10 Wata muhimmiyar ƙa’ida kuma da za mu koya daga yadda Yesu da manzanninsa suka aikata a lokacin matsi ita ce, kada mu rama wa waɗanda suke tsananta mana. Babu wani waje a Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa Yesu ko kuma mabiyansa sun shirya su yi wata zanga-zanga ko kuma yi faɗā da waɗanda suka tsananta musu ba. Maimako, Bulus ya gargaɗi Kiristoci kada su “saka wa kowanne mutum mugunta da mugunta. . . . Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” Ban da haka, “kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.”—Romawa 12:17-21; Zabura 37:1-4; Misalai 20:22.

11. Menene wani ɗan tarihi ya ce game da halin Kiristoci na farko wajen Gwamnati?

11 Kiristoci na farko sun yi amfani da gargaɗin. A cikin littafinsa The Early Church and the World, ɗan tarihi Cecil J. Cadoux ya kwatanta halin Kiristoci wajen Gwamnati a shekaru na 30 zuwa 70 A.Z. Ya rubuta: “Ba mu da tabbaci cewa Kiristoci na lokacin sun taɓa ƙoƙarin hana tsanantawa ƙarfi da yaji ba. Abin da suke iya yi shi ne su hukunta masarautar ta wurin tsayawarsu tsayin daka ko kuma masarautar su yi mamakin yadda suke kuɓucewa. Yadda Kirista ke bi da tsanantawa bai wuci ya ƙi yin biyayya ga dokokin gwamnati da sun saɓa da na Kristi ba kuma ya dage yin haka cikin ladabi.”

12. Me ya sa ya fi kyau a jimre da wahala maimakon a rama?

12 Irin wannan da’awar yin biyayya tafarkin hikima ce? Waɗanda suke yin haka ba zai zama da sauƙi ba ne masu son su kawar da su su yi haka ba? Ba zai kasance abin hikima ce mutum ya kāre kansa ba? Bisa ra’ayin ’yan Adam, hakan gaskiya ne. Amma mu bayin Jehovah muna da tabbacin cewa bin ja-gorar Jehovah a dukan al’amura shi ne tafarki mai kyau. Muna tuna da kalmomin Bitrus: “Idan, sa’anda ku ke yin nagarta, kuna shan wuya dominta kuwa, kuka yi haƙuri, wannan abin karɓa ne wurin Allah.” (1 Bitrus 2:20) Mun tabbata cewa Jehovah ya san yanayin sarai kuma ba zai ƙyale al’amura su ci gaba haka ba. Yaya za mu tabbata da haka? Jehovah ya sanar da haka game da mutanensa da suke bauta a Babila: “Shi wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar ido[na].” (Zechariah 2:8) Har yaushe wani zai yarda a dinga taɓa ƙwayar idonsa? Jehovah zai kawo sauƙi a lokacin da ya dace. Babu shakkar wannan.—2 Tassalunikawa 1:5-8.

13. Me ya sa Yesu ya ƙyale magabtansa su kama shi?

13 Game da wannan, za mu yi koyi da misalin Yesu gurbinmu. Sa’ad da ya ƙyale magabtansa su kama shi a lambun Jathsaimani, ba domin ba zai iya tsare kansa ba ne. Hakika, ya gaya wa almajiransa: “Ko kuwa kuna tsammani ba ni da iko in roƙi Ubana, ko yanzu ma shi aiko mini rundunan mala’iku ya fi goma sha biyu? Ƙaƙa fa littattafai za su cika da sun ce dole ya zama haka?” (Matta 26:53, 54) Cika nufin Jehovah shi ya fi wa Yesu muhimmanci, ko idan ma zai sha wahala. Yana da cikakken tabbaci na kalmomin annabci na mai Zabura Dauda: “Ba za ka bar raina ga Lahira ba; ba kuwa za ka bar mai-tsarkinka shi ga ruɓa ba.” (Zabura 16:10) Shekaru bayan haka manzo Bulus ya ce game da Yesu: “Ya jimre da [gungumen azaba] domin farinzuciya da aka sa gabansa, yana rena kunya, ya kuwa zauna ga hannun dama na al’arshen Allah.”—Ibraniyawa 12:2.

Farin Cikin Tsarkake Sunan Jehovah

14. Wane farin ciki ne ya taimaki Yesu a dukan gwajinsa?

14 Wane farin ciki ne ya taimaki Yesu cikin gwaji mafi tsanani? A cikin dukan bayin Jehovah, Yesu, Ɗan Allah ƙaunatacce ne Shaiɗan ya fi fakonsa. Saboda haka, yadda Yesu ya riƙe amincinsa cikin gwaji ne cikakkiyar amsa wa zolayar Shaiɗan ga Jehovah. (Misalai 27:11) Za ka iya tunanin farin ciki da gamsuwa da Yesu ya yi bayan da aka ta da shi? Lallai ya yi farin ciki da sanin cewa ya cika aikin da zai yi na mutum kamili a kunita ikon mallakar Jehovah da tsarkake sunansa! Ban da haka, zama a ‘hannun dama na kursiyin Allah’ daraja ce ƙwarai kuma dalili mai girma na farin ciki ne wa Yesu.—Zabura 110:1, 2; 1 Timothawus 6:15, 16.

15, 16. Wace mugun tsanantawa Shaidu a Sachsenhausen suka jimre wa, kuma menene ya ba su ƙarfin yin haka?

15 Ga Kiristoci ma, abin farin ciki ne, mu sa hannu a tsarkake sunan Jehovah ta jimre wa gwaji da tsanantawa, muna bin misalin Yesu. Wani labari da ya dace shi ne Shaidu da suka sha wahala a sansanin fursuna na Sachsenhausen kuma suka tsira daga tafiyar mutuwa a ƙarshen Yaƙin Duniya na II. A lokacin tafiyar, dubban fursunoni sun mutu, domin babu kulawa, domin cuta, ko kuma yunwa ko ’yan gadin Hitler su kakkashe su a kan hanya. Shaidun, dukansu 230 sun tsira ta wurin kasance kusa da juna suna taimakon juna ko da suna saka ransu ne cikin haɗari.

16 Me ya ba waɗannan Shaidu ƙarfi su jimre irin wannan mugun tsanantawa? Da zarar sun isa, suka furta godiyarsu da farin cikinsu ga Jehovah a cikin wata takarda mai jigo “Zartarwa na Shaidun Jehovah 230 daga ƙasashe shida, da suka taru a kurmi kusa da Schwerin a Mecklenburg.” A ciki suka furta cewa: “Gwaji mai tsanani na dogon lokaci ya wuce, kuma waɗanda aka cece su, a ce an ƙwace su daga tanderun wuta, da ba sa warin wuta ma. (Duba Daniel 3:27.) Suka kasance da ƙarfi da iko daga wurin Jehovah kuma suna jiran sababbin dokoki daga Sarkin su ɗaukaka abubuwa na tsarin Allah.”c

17. Waɗanne irin gwaji mutanen Allah suke fuskanta a yanzu?

17 Kamar waɗannan masu aminci 230, mu ma za a iya gwada bangaskiyarmu ko da ma ba mu “tsayayya ba tukuna har jini.” (Ibraniyawa 12:4) Gwaji na iya zuwa a hanyoyi dabam dabam. Zai iya zama ba’a daga ’yan ajinka, ko kuma matsi na tsara cewa ka yi lalata da kuma wasu laifi. Ƙari ga haka, tsai da shawarar ƙin ƙarin jini, yin aure sai cikin Ubangiji, ko kuma reno na imani a iyalin da ke a rabe wasu lokatai, na kawo matsi da kuma gwaji ƙwarai.—Ayukan Manzanni 15:29; 1 Korinthiyawa 7:39; Afisawa 6:4; 1 Bitrus 3:1, 2.

18. Wane tabbaci muke da shi na cewa za mu iya jimre da gwaji mafi tsanani?

18 Kowanne gwaji da za mu fuskanta, mun san muna wahala saboda mun sa Jehovah farko ne da Mulkinsa, kuma muna ɗaukansa gata ta musamman kuma abin farin ciki ne. Muna samun ƙarfafa daga kalmomin tabbaci na Bitrus: “Idan kuna shan zargi sabili da sunan Kristi masu-albarka ne ku; domin Ruhu na daraja da Ruhu na Allah yana zaune a kanku.” (1 Bitrus 4:14) Da ikon ruhun Jehovah, muna samun ƙarfi mu jimre gwaji mafi wuya, zuwa ɗaukaka da yabonsa.—2 Korinthiyawa 4:7; Afisawa 3:16; Filibbiyawa 4:13.

[Hasiya]

a Aukuwa na shekarun 1960 somawa ne kawai na mugun tsanantawa da Shaidu a Malawi suka jimre na kusan shekara talatin. Don ka sami cikakken labari, duba 1999 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafofi na 171-212.

b Dubi talifin nan “High Court Upholds True Worship in ‘the Land of Ararat,’ ” a cikin fitar Hasumiyar Tsaro ta (Turanci) 1 ga Afrilu, 2003, shafofi 11-14.

c Don a sami cikakken zartarwar, duba 1974 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafofi 208-209. Ana iya samun labarin wani da ya tsira daga tafiyar mutuwa a cikin fitar Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 1998, shafofi 25-29.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Yaya Kiristoci suke ɗaukan wahala da tsanantawa?

• Me za mu iya koya daga yadda Yesu da wasu masu aminci suka aikata cikin gwaji?

• Me ya sa ba hikima ba ce mu rama sa’ad da ake tsananta mana?

• Wane farin ciki ne ya taimake Yesu cikin gwajinsa, kuma me za mu koya daga wannan?

[Box/Hotuna a shafi na 25]

Yadda Suka Bi da Tsanantawa

• Kafin sojojin Hirudus su isa Baitalahmi su kakkashe jarirai maza masu shekara biyu zuwa kasa, mala’ika ya gaya wa Yusufu da Maryamu su ɗauki jariri Yesu su gudu zuwa Masar.—Matta 2:13-16.

• A lokatai da yawa a hidimar Yesu, magabtansa sun nemi su kashe shi saboda ƙarfafar shaida da ya bayar. A kowanne cikin lokacin nan Yesu ya kuɓuce ya bar su.—Matta 21:45, 46; Luka 4:28-30; Yohanna 8:57-59.

• Lokacin da sojoji da wakilai suka zo lambun Jathsaimani su kama Yesu, ya nuna kansa sau biyu yana gaya musu “Ni ne.” Ya hana mabiyansa ma daga yin faɗā da taron, su ƙyale a tafi da shi.—Yohanna 18: 3-12.

• A Urushalima, an kama Bitrus da wasu, aka yi musu dūka, aka dokace su su daina magana game da Yesu. Duk da haka, sa’ad da aka sake su “suka fita . . . , kowacce rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fasa koyarwa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne” ba.—Ayukan Manzanni 5: 40-42.

• Sa’ad da Shawulu, wanda daga baya ya zama manzo Bulus, ya ji Yahudawa a Dimashka suna ƙulli su kashe shi, ’yan’uwa suka saka shi cikin kwando suka sauƙe ta bayan gari daddare, kuma ya tsira.—Ayukan Manzanni 9:22-25.

• Shekaru daga baya, Bulus ya zaɓi ya ɗaukaka roƙo zuwa wurin Kaisar, ko da Gwamna Fastos da Sarki Agaribas ba su gan shi da wani laifi ba “abin da ya isa mutuwa ko sarƙa” ba.—Ayukan Manzanni 25:10-12, 24-27; 26:30-32.

[Hotuna a shafuffuka na 26, 27]

Ko da mugun tsanantawa ya sa su gudu, dubban Shaidu masu aminci na Malawi sun ci gaba da hidimar Mulki da farin ciki

[Hotuna a shafi na 27]

Farin cikin tsarkake sunan Jehovah ya taimaki waɗannan masu aminci cikin tafiyar mutuwa na ’yan gadin Hitler da kuma sansanin fursuna

[Inda aka Dauko]

Death march: KZ-Gedenkstätte Dachau, courtesy of the USHMM Photo Archives

[Hotuna a shafi na 28]

Gwaji da matsi na iya zuwa a hanyoyi dabam dabam

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba