Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 11/1 pp. 14-18
  • Ka Nuna Kamewa Domin Ka Sami Lada!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Nuna Kamewa Domin Ka Sami Lada!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ana Bukatar Kamewa don a Yi Nagarta
  • “Cikin Dukan Abu”?
  • Ka Ƙware ta Wurin Kamewa
  • Koyon Kamewa
  • Ka Ƙara Wa Saninka Kamewa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Rika Kame Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Kamewa​—Halin da Ke Faranta Ran Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Mu Rika Kame Kanmu
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 11/1 pp. 14-18

Ka Nuna Kamewa Domin Ka Sami Lada!

“Dukan wanda ya ke ƙoƙari wurin wasa yana daurewa cikin dukan abu.”—1 Korinthiyawa 9:25.

1. Daidai da Afisawa 4:22-24, ta yaya miliyoyi suka amince da Jehovah?

IDAN an yi maka baftisma na zama Mashaidin Jehovah, ka sanar wa jama’a a fili ke nan cewa ka shiga gasa da take da ladar rai madawwami. Ka yi na’am da yin nufin Jehovah. Kafin mu keɓe kai ga Jehovah, wasunmu da yawa sun yi canje-canje don keɓe kanmu ya zama tabbatacce da Allah zai amince da shi. Mun bi gargaɗin manzo Bulus ga Kiristoci: “Ku tuɓe, ga zancen irin zamanku na dā, tsohon mutum, wanda yana ƙara lalacewa bisa ga sha’awoyin yaudara; . . . ku yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afisawa 4:22-24) Wato, kafin mu keɓe kanmu ga Allah, za mu ƙi da hanyar rayuwa ta dā da ba ta da kyau.

2, 3. Ta yaya 1 Korinthiyawa 6:9-12 ta nuna cewa dole a yi canje-canje iri biyu don a sami amincewar Allah?

2 Kalmar Allah ta haramta wasu fasalolin tsohon hali da waɗanda suke son su zama Shaidun Jehovah dole su daina. Bulus ya lissafa wasu cikin wasiƙarsa zuwa ga Korantiyawa, yana cewa: “Masu-fasikanci, da masu-bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da masu-kwana da maza, da ɓarayi, da masu-ƙyashi, da masu-maye, da masu-alfasha, da masu-ƙwace, ba za su gāji mulkin Allah ba.” Sai ya nuna cewa Kiristoci na ƙarni na farko sun yi canji a halayensu, ya daɗa: “Waɗansu ma a cikinku dā haka ku ke.” Ka lura da cewa dā ne ba yanzu ba.—1 Korinthiyawa 6:9-11.

3 Bulus ya nuna cewa za a bukaci ƙarin canje-canje, domin ya ci gaba: “Dukan abu halal ne a gareni; amma ba dukan abu ya dace ba.” (1 Korinthiyawa 6:12) Saboda haka, mutane da yawa a yau da suke son su zama Shaidun Jehovah sun ga suna bukatar su ce a’a ga abubuwa da halal ne amma ba su da amfani ko kuma muhimmancinsu kaɗan ne. Ƙila waɗannan abubuwa suna cin lokaci da za su iya raba hankalinsu daga biɗan abubuwa mafi muhimmanci.

4. A kan menene Kiristoci da suka keɓe kai suka yarda da Bulus?

4 Ana keɓe kai ga Allah da son rai, ba dole ba ne, sai ka ce tana bukatar sadaukarwa mai girma. Kiristoci da suka keɓe kai sun yarda da Bulus, wanda bayan ya zama mabiyin Kristi ya ce: “[Yesu] wanda na sha hasarar dukan abu sabili da shi, kamar najasa kuwa ni ke maishe su, domin in ribato Kristi.” (Filibbiyawa 3:8) Bulus da farin ciki ya ce a’a ga abubuwa da ba su da muhimmanci domin ya ci gaba da amince da Allah.

5. A wane irin tsere Bulus ya yi nasara, kuma yaya za mu iya yin haka?

5 Bulus ya nuna kamewa a tserensa na ruhaniya da a ƙarshe ya iya faɗa: “Na yi yaƙi mai-kyau, na kure fagen, na kiyaye imani: saura, an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, adalin mai-shari’a, za ya ba ni a wannan rana: ba kuwa ni kaɗai ba, amma dukan waɗanda sun ƙaunaci bayyanuwassa.” (2 Timothawus 4:7, 8) Wata rana za mu iya yin irin wannan furcin kuwa? Za mu iya, idan mun nuna kamewa da bangaskiya sa’ad da muke tserenmu na Kirista babu kasawa har zuwa ƙarshe.

Ana Bukatar Kamewa don a Yi Nagarta

6. Mecece kamewa, a waɗanne hanyoyi biyu ne dole mu nuna ta?

6 Kalmomin Ibrananci da Helenanci da aka fassara “kamewa” cikin Littafi Mai Tsarki a zahiri yana nufin cewa mutum yana da iko ko kuma ya iya riƙe kansa. Yawancin lokaci yana nufin mutum ya riƙe kansa daga yin mugunta. Amma a bayyane yake cewa ana bukatar kamewa ma idan za mu yi amfani da jikunanmu a yin nagargarun ayyuka. Mutane ajizai suna da halin yin mugunta, saboda haka muna da kokawa iri biyu. (Mai-Wa’azi 7:29; 8:11) Yayin da muke ƙin yin mugunta, dole mu nace wa kanmu mu yi nagarta. Hakika, nace wa jikinmu mu yi nagarta ɗaya ne cikin hanyoyi mafi kyau na guje yin mugunta.

7. (a) Game da menene ya kamata mu yi addu’a, yadda Dauda ya yi? (b) Bimbini a kan menene zai taimake mu mu nuna kamewa?

7 A bayyane yake, kamewa tana da muhimmanci idan za mu cika keɓe kanmu ga Allah. Muna bukatar mu yi addu’a yadda Dauda ya yi: “Daga cikina ka halitta zuciya mai-tsabta, ya Allah; ka sabonta daidaitacen ruhu daga cikina.” (Zabura 51:10) Za mu iya bimbini a kan amfanin guje wa abubuwa da ba su da kyau ko kuma na raunana jiki. Ka yi tunanin lahani da yake cikin ƙin guje wa waɗannan abubuwa: matsalar rashin lafiya, dangantaka da ta ɓace, har ma mutuwar kadangatse. A wata sassa kuma ka yi tunanin fa’idodi da yawa na yin rayuwa da Jehovah ya tsara. Amma, kada mu manta cewa zuciyarmu rikici gare ta. (Irmiya 17:9) Dole mu ƙudura mu ƙi sarai da wani ƙoƙarin rage darajar ɗaukaka mizanan Jehovah.

8. Idan abu ya faru me yake koya mana? Ka ba da misali.

8 Yawancinmu mun sani daga abin da ya faru mana yadda rashin niyya ke ƙoƙarin kawar da himmar son yin abu. Alal misali, wa’azin Mulki. Jehovah yana farin ciki da ’yan Adam da suke da niyyar wannan aiki mai ba da rai. (Zabura 110:3; Matta 24:14) Koyon yin wa’azi a fili ga yawancinmu bai kasance da sauƙi ba. Wataƙila ya bukaci—kuma har ila yana bukatar—mu riƙe jikinmu mu “dandaƙi” shi kuma “kai shi cikin bauta,” maimakon mu ƙyale shi ya hana mu wa’azi.—1 Korinthiyawa 9:16, 27; 1 Tassalunikawa 2:2.

“Cikin Dukan Abu”?

9, 10. Menene nuna kamewa “cikin dukan abu” ya ƙunsa?

9 Gargaɗin Littafi Mai Tsarki na mu nuna kamewa “cikin dukan abu” yana nuna cewa akwai ƙarin abin da za mu yi ban da riƙe fushinmu da kuma ƙin lalata. Za mu iya jin cewa muna kamewa a waɗannan wurare, kuma idan haka ne abin farin ciki ne. Amma wasu wurare a rayuwa da muke bukatar kamewa fa? Alal misali, a ce muna zama a ƙasar da take da ɗan arziki da yayin rayuwa mai tsada. Ba zai yi kyau ba mu ce a’a ga yawan kashe kuɗi? Yana da kyau iyaye su koya wa yaransu kada su dinga sayan kome da suka gani domin akwai shi ba, cewa abin yana da kyau, ko kuma suna da kuɗin sayan sa ba. Hakika, domin irin koyarwa nan ta kasance da amfani dole iyaye su kafa misali da ya dace.—Luka 10:38-42.

10 Koyon mu yi amfani da ɗan abin da muke da shi zai iya ƙarfafa niyyarmu. Yana kuma iya sa mu daɗa godiya ga abin mallaka da muke da shi kuma yana sa mu daɗa tausayin waɗanda ba su da wasu abubuwa, ba da son su ba amma domin ya zama dole ne. Hakika, yayin rayuwa mai kyau ya saɓa da ra’ayin da mutane suke da shi na cewa “ka more rayuwarka” ko kuma “kana bukatar abu mafi kyau.” Duniyarmu ta talla tana ƙarfafa sha’awar morewa nan da nan, amma tana yin haka domin nata riba ce. Wannan yanayi zai iya rage ƙoƙarinmu na nuna kamewa. Wata jarida daga wata ƙasar Turai mai arziki a kwanan baya nan ta lura: “Idan waɗanda suke zama cikin yanayi na mugun talauci suna bukatar kokawa don su kawar da muguwar sha’awa, haka wannan yake musamman ga waɗanda suke zama a ƙasashe masu arziki a yau!”

11. Me ya sa koyon yin amfani da ɗan abin da muke da shi yake da kyau, amma me ya sa wannan yake wuya?

11 Idan muna iske shi da wuya mu bambanta tsakanin abin da muke so da abin da muke bukata da gaske, zai yi kyau mu ɗauki matakai mu tabbata cewa ba mu yi wauta ba. Alal misali, idan muna so mu rage yadda muke kashe kuɗi babu gaira, za mu so mu tsai da mu je kasuwa da ɗan kuɗi, kada mu ci bashi a cefane. Ka tuna Bulus ya ce “ibada tare da wadar zuci riba ce mai-girma.” Ya ce: “Ba mu shigo da kome cikin duniya ba, ba kuwa za mu iya fita cikinta da kome ba; amma da shi ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.” (1 Timothawus 6:6-8) Haka muke? Koyon yin rayuwa mai sauƙi ba tare da tattara abubuwa da ba su da amfani ba ko da menene, yana bukatar niyya da kuma kamewa. Abin da ya kamata mu koya ne.

12, 13. (a) A waɗanne hanyoyi taron Kirista ya bukaci kamewa? (b) A waɗanne fannoni muke bukatar mu koya kamewa?

12 Halarta taron Kirista, babban taro da kuma na gunduma ya ƙunshi nuna kamewa. Alal misali, ana bukatar halin nan domin kada hankalinmu ya rabu lokacin taro. (Misalai 1:5) Zai bukaci kamewa kada mu dami wasu ta raɗa musu magana maimakon mu mai da hankalinmu ga mai ba da jawabi. Yin gyara a tsarinmu don mu isa wurin taro da wuri na bukatar kamewa. Ƙari ga haka, ana bukatar kamewa a keɓe lokaci don shirya taro kuma a yi kalami.

13 Nuna kamewa a ƙananan abubuwa na ƙarfafa mu mu yi haka a manyan batu. (Luka 16:10) Saboda haka, yana da kyau mu hori kanmu mu yi karatun Kalmar Allah da littattafan Littafi Mai Tsarki a kai a kai muna nazarinsu kuma mu yi bimbini a kan abin da muka koya! Yana da kyau mu hori kanmu game da aiki, abokantaka, halaye, da ba su dace ko kuma mu hori kanmu mu ƙi ayyuka da za su ci lokacinmu mai tamani don hidimar Allah! Yin aiki sosai cikin hidimar Jehovah lallai kāriya ce mai kyau daga abubuwa da za su iya janye mu daga aljanna ta ruhaniya na ikilisiyar Jehovah ta dukan duniya.

Ka Ƙware ta Wurin Kamewa

14. (a) Yaya ya kamata yara su koya kamewa? (b) Waɗanne fa’idodi ake samu idan yara sun soma koyon kamewa tun da wuri?

14 Jariri ba ya kamewa. Wata takarda da gwanaye suka rubuta game da halin yaro ta yi bayani: “Ba a kamewa farat ɗaya. Jarirai suna bukatar ja-gora da goyon bayan iyaye su soma koyon kamewa. . . . Ta ja-gorar iyaye, suna daɗa kamewa lokacin da suke makaranta.” Wani bincike a kan yara ’yan shekara huɗu ya nuna cewa waɗanda sun koyi ɗan kamewa “galiba yana musu sauƙi su yi gyara in sun yi girma, an fi san da su, suna ƙarfin zuciya, gaba gaɗi, yara da za a tabbata da su.” Waɗanda ba su soma koyon wannan halin ba “za su fi kaɗaitawa, su fi baƙin ciki da kuma taurin kai. Suna fāɗa wa matsi da kuma guje wa kaluɓale.” Babu shakka, dole yaro ya koyi kamewa don ya zama mutum da ya ƙware.

15. Menene rashin kamewa yake nunawa, ya saɓa da wane makasudi da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

15 Hakanan ma, idan za mu zama Kiristoci da suka ƙware, dole mu koya nuna kamewa. Rashinta yana nuna cewa mu jarirai ne a ruhaniya har ila. Littafi Mai Tsarki ya yi mana kashedi “ga azanci kuwa ku zama cikakkun mutane.” (1 Korinthiyawa 14:20) Makasudinmu shi ne “mu kai zuwa ɗayantuwar imani da sanin Ɗan Allah, zuwa cikakken mutum, zuwa misalin tsawon cikar Kristi.” Me ya sa? Domin “kada nan gaba mu zama yara, waɗanda ana wofadda su suna shillo ga kowace iskan sanarwa, ta wurin wawa-idon mutane masu-gwaninta zuwa makidar saɓo.” (Afisawa 4:13, 14) A bayyane yake, koyon kamewa yana da muhimmanci a ruhaniyarmu.

Koyon Kamewa

16. Yaya Jehovah yake ba da taimako?

16 Domin mu koya kamewa, muna bukatar taimakon Allah, kuma za mu samu. Kalmar Allah kamar madubi ce, tana nuna mana inda muke bukatar gyara, kuma tana ba da gargaɗi a yadda za a yi haka. (Yaƙub 1:22-25) ’Yan’uwanci da ke ƙauna suna shirye su ba da taimako su ma. Dattawa Kirista sun nuna fahimi a ba da taimako. Jehovah yana ba da ruhunsa mai tsarki a sake idan muka roƙa ta wurin addu’a. (Luka 11:13; Romawa 8:26) Saboda haka, bari mu yi amfani da waɗannan tanadi da farin ciki. Shawarwari da ke shafi na 17 za su iya taimakawa.

17. Wace ƙarfafa muka samu a misalai 24:16?

17 Abar ƙarfafa ce mu sani cewa Jehovah yana daraja ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu sa’ad da muke ƙoƙarin faranta masa rai! Ya kamata wannan ya motsa mu mu ci gaba da ƙoƙarin ƙara kamewa. Ko da sau nawa muka yi tuntuɓe, ba za mu kasala ba a ƙoƙarin da muke yi. “Mai-adalci ya kan fāɗi so bakwai, ya sake tashi kuma.” (Misalai 24:16) Duk lokacin da muka ci nasara muna da dalilin yin farin ciki. Za mu kuma tabbata cewa Jehovah yana farin ciki da mu. Wani Mashaidi ya ce kafin ya keɓe kansa ga Jehovah, duk lokacin da ya yi nasara bai sha taba ba a mako, yana sāka wa kansa ta wajen sayan wani abu mai amfani da kuɗin da ya samu ta wurin kame kansa.

18. (a) Menene yaƙinmu game da kamewa ya ƙunsa? (b) Wane tabbaci Jehovah ya ba da?

18 Fiye da kome, ya kamata mu tuna cewa kamewa tana shafan zuciya da tsotsuwar rai. Za mu ga wannan daga kalmomin Yesu: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Matta 5:28; Yaƙub 1:14, 15) Wanda ya koyi ya kame zuciyarsa da tsotsuwar ransa zai iske shi da sauƙi ya kame dukan jikinsa. Saboda haka, bari mu ƙarfafa ƙudurinmu ba na guje yin mugunta kawai ba amma da guje yin tunaninsa ma. Idan mugun tunani ya taso, mu ƙi da su nan da nan. Za mu iya guje wa jaraba ta wurin kira bisa ga Yesu. (1 Timothawus 6:11; 2 Timothawus 2:22; Ibraniyawa 4:15, 16) Yayin da muke iyakacin ƙoƙarinmu, muna bin gargaɗin Zabura 55:22: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya agaje ka: Ba za ya yarda a jijjige masu-adalci ba daɗai.”

Ka Tuna?

• A waɗanne hanyoyi biyu ne dole mu nuna kamewa?

• Menene yake nufi a nuna kamewa “cikin dukan abu”?

• Waɗanne shawarwari masu kyau na koyon kamewa ka lura da su musamman a nazarinmu?

• Ina aka soma kamewa?

[Box/Hotuna a shafi na 17]

Yadda Za Ka Ƙarfafa Kamewa

• Ka koye ta har cikin ƙananan abubuwa

• Ka yi bimbini a kan amfaninta na yanzu da nan gaba

• Ka sake abubuwa da Allah ba ya so da waɗanda ya ce a yi

• Ka ƙi da ra’ayoyi da ba su dace ba nan da nan

• Ka cika zuciyarka da abubuwa na ruhaniya masu ƙarfafawa

• Ka amince da taimakon ’yan’uwa Kiristoci da suka ƙware

• Ka guje wa yanayi da zai sa ka cikin jaraba

• Ka yi addu’a don taimakon Allah lokacin jaraba

[Hotuna a shafuffuka na 14, 15]

Kamewa na sa mu yi nagarta

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba