Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 12/1 pp. 9-14
  • Ka Taimaki Wasu Su Karɓi Saƙon Mulki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taimaki Wasu Su Karɓi Saƙon Mulki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Amfani da Fasahar Rinjaya
  • Rinjaya da Take Motsa Zuciya
  • Ka Yi Amfani da Kalmar Allah da Kyau
  • Ka Kasance da Ra’ayin Allah Game da Hidima
  • Ku Zama Masu Hidima Da Ke Cin Gaba Kuma Masu Daidaituwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 12/1 pp. 9-14

Ka Taimaki Wasu Su Karɓi Saƙon Mulki

“Agaribas ya ce ma Bulus, Da ƙanƙanuwar rinjayarwa kana so ka maishe ni [Kirista].”—AYUKAN MANZANNI 26:28.

1, 2. Me ya sa manzo Bulus ya bayyana a gaban Gwamna Fastos da Sarki Hirudus Agaribas na II?

A KAISARIYA a shekara ta 58 A.Z., Sarki Hirudus Agaribas na II da ƙanwarsa Barniki suka ziyarci Gwamnar Roma Borkiyos Fastos. Da yake Gwamna Fastos ne ya gayyace su, suka zo daga Urushalima. Washegari “da rigimar sarauta mai-yawa,” suka “shiga ɗakin saurarawa tare da sarakunan yaƙi, da magabtan birni.” Da Fastos ya ba da umurni, aka kawo Kirista manzo Bulus zuwa gabansu. Ta yaya wannan mabiyin Yesu Kristi ya tsaya a gaban kujerar shari’a na Gwamna Fastos?—Ayukan Manzanni 25:13-23.

2 Abin da Fastos ya gaya wa baƙinsa ya ba da amsar wannan tambaya. Ya ce: “Sarki Agaribas, da ku mutanen da ke nan tare da mu duka, kuna ganin mutumin nan, wanda dukan taron Yahudawa suka yi fadanci a wurina a kansa, a cikin Urushalima duka da nan kuma, suna tada murya, suna cewa. Ba ya kamata ba a ƙara bar shi da rai. Amma na iske ba ya yi wani abu wanda ya isa mutuwa ba: kuma domin shi da kansa ya ɗaukaka roƙonsa wurin Augustus, na yi ƙuduri in aike shi. Ba ni kuwa da wani tabbataccen abu a kansa da zan rubuta ma ubangijina. Domin wannan na kawo shi a gabanku, tun ba wurinka, ya sarki Agaribas, domin, bayan da an yi ƙwanƙwanto, in sami abin da zan rubuta. Gama na ga kamar abin rashin hankali ne, a aike da mutum a ɗaure, ba a kuwa shaida ƙararaki waɗanda aka kawo bisansa ba.”—Ayukan Manzanni 25:24-27.

3. Me ya sa shugabannin addini suka yi wa Bulus tuhuma?

3 Maganar Fastos ta nuna cewa Bulus ya fuskanci tuhumar ƙarya na ta da zaune tsaye—laifin da ke kawo hukuncin kisa. (Ayukan Manzanni 25:11) Amma, Bulus ba shi da laifi. Tuhumar don kishin shugabannin addini a Urushalima ne. Sun yi hamayya da aikin Bulus na mai shelar Mulki kuma suna fushi sosai cewa ya taimake wasu su zama mabiyan Yesu Kristi. Sojojin gadi suka kawo Bulus daga Urushalima zuwa bakin teku inda jirage suke sauka a Kaisariya, inda ya yi wa Kaisar afil.

4. Wane furci na ban mamaki Sarki Agaribas ya yi?

4 Ka yi tunanin Bulus yana fadan gwamna a gaban rukunin da ya haɗa da sarki na muhimmin ɓangare na Daular Roma. Sarki Agaribas ya juya wajen Bulus ya ce: “An yarda maka ka yi magana.” Sa’ad da Bulus yake magana, abin mamaki ya faru. Abin da Bulus ya faɗa ya soma motsa sarkin. Hakika, Sarki Agaribas ya ce: “Da ƙanƙanuwar rinjayarwa kana so ka maishe ni [Kirista].”—Ayukan Manzanni 26:1-28.

5. Me ya sa maganar Bulus ga Agaribas take da iko?

5 Ka yi tunaninsa! Domin Bulus ya ƙware wajen magana, ikon Kalmar Allah da ya ratsa cikinsa ya motsa wani sarki. (Ibraniyawa 4:12) Me ya sa amsar da Bulus ya ba da take da iko haka? Me za mu koya daga Bulus da zai taimake mu a aikinmu na almajirantarwa? Idan mun bincika amsa da ya ba da, abubuwa biyu sun fita sarai: (1) Bulus ya yi amfani da rinjaya. (2) Ya yi amfani da iliminsa na Kalmar Allah sosai, yadda ƙwararren masassaƙi ke amfani da kayan aikinsa da kyau.

Ka Yi Amfani da Fasahar Rinjaya

6, 7. (a) Yadda aka yi amfani da ita cikin Littafi Mai Tsarki, mecece ‘rinjaya’ take nufi? (b) Yaya rinjaya take taimakon wasu su karɓi koyarwar Littafi Mai Tsarki?

6 A littafin Ayukan Manzanni, an yi amfani da kalmomin Helenanci na rinjaya a kai a kai sa’ad da ake kwatanta wa’azin Bulus. Yaya yin amfani da rinjaya zai shafi aikinmu na almajirantarwa?

7 A yaren asali na Nassosin Helenanci na Kiristoci, ‘rinjaya’ na nufin “jawo mutum zuwa gefenmu” ko kuma sa “ya canja ra’ayi ta wurin tabbaci ko kuma yin tunani,” in ji Vine’s Expository Dictionary of New Testament Words. Bincika ma’anarta tana ba da ƙarin fahimi. Tana nufin tabbatarwa. Saboda haka, idan ka rinjayi mutum ya yarda da koyarwar Littafi Mai Tsarki, ka tabbatar da shi ke nan, har ya gaskata da gaskiyar koyarwar. Hakika, bai isa ba ka gaya wa mutum abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa domin ya gaskata kuma ya aikata bisa abin da ya ji. Dole mai sauraronka ya tabbata cewa abin da ka faɗa gaskiya ne, ko yaro ne, maƙwabci, abokin aiki, abokin makaranta, ko kuma dangi.—2 Timothawus 3:14, 15.

8. Menene tabbatar wa mutum gaskiya ta Nassi ta ƙunsa?

8 Ta yaya za ka tabbatar da mutum cewa abin da ka faɗa daga cikin Kalmar Allah gaskiya ce? Ta wurin magana da hujja, tabbaci, da kuma rinjaya ta ƙwarai, Bulus ya yi ƙoƙari ya sa mutane da ya yi wa magana su canja ra’ayinsu. Maimakon kawai ka ce abu gaskiya ne, kana bukatar ka ba da tabbaci mai gamsarwa don ka goyi bayan abin da ka faɗa. Ta yaya za a yi hakan? Ka tabbata cewa abin da kake faɗa yana bisa Kalmar Allah ba naka ra’ayin ba. Ka yi amfani da ƙarin tabbaci don ka goyi bayan furci na Nassi da ka yi daga zuciyarka. (Misalai 16:23) Alal misali, idan ka faɗa cewa mutane masu biyayya za su more rayuwa cikin aljanna a duniya, ka goyi bayan abin da ka faɗa da Nassosi, kamar su Luka 23:43 ko kuma Ishaya 65:21-25. Ta yaya za ka ba da ƙarin tabbaci don ka goyi bayan Nassin? Kana iya amfani da misalai daga labaran mai sauraronka. Kana iya tuna masa kyan farin wata, ƙanshin fure mai daɗi, zaƙin ’ya’yan itace, ko kuma farin cikin kallon tsuntsuwa tana ciyar da ’yarta. Ka taimake shi ya gane cewa abubuwan nan da ake morewa, tabbaci ne cewa Mahalicci yana son mu more rayuwa a duniya.—Mai-Wa’azi 3:11, 12.

9. Ta yaya za mu nuna sanin ya kamata a aikinmu na wa’azi?

9 Sa’ad da kake ƙoƙarin rinjayar mutum ya yarda da wata koyarwa ta Littafi Mai Tsarki, ka mai da hankali kada himmarka ta sa ka zama marar la’akari, ta yin haka ba za ka motsa zuciya da azancin mai sauraronka ba. Littafin nan Ministry School ya ba da wannan gargaɗi: “Yana da wuya a yarda da maganar da ko da gaskiya ce amma da aka yi ta da rashin la’akari a fallasa imanin ƙarya da wani yake bi, ko idan ma an goyi bayanta da jerin Nassosi. Alal misali, idan kawai aka ce wasu bukukuwan hutu ba su da kyau tushensu na arna ne, wannan ba zai iya canja ra’ayin da mutane suke da shi game da su ba. Ba da bayani zai fi amfani.” Me ya sa za mu yi ƙoƙari sosai mu ba da bayanin? Littafin ya ce: “Ba da bayani yana ƙarfafa tattaunawa, yana sa mutane su yi tunani a kan batun daga baya, kuma yana buɗe hanyar tattaunawa a nan gaba. Lallai yana da ikon rinjaya.”—Kolossiyawa 4:6.

Rinjaya da Take Motsa Zuciya

10. Yaya Bulus ya kāre kansa a gaban Agaribas?

10 Bari yanzu mu bincika yadda Bulus ya kāre kansa a Ayukan Manzanni sura ta 26. Ka lura da yadda ya soma maganarsa. Don ya gabatar da batun, Bulus ya samu dalili mai kyau na yaba wa Agaribas, ko da sarkin yana dangantaka na ban kunya da ƙanwarsa Barniki. Bulus ya ce: “Ina ganin kaina mai-arziki ne, sarki Agaribas, da shi ke zan yi kāriyar kaina a gabanka yau a kan dukan abin da Yahudawa suna sarata da su; domin kai masani ne ƙwarai wajen al’adu da matsaloli duka waɗanda su ke wurin Yahudawa: domin wannan fa ina roƙonka ka ji ni da haƙuri.”—Ayukan Manzanni 26:2, 3.

11. Ta yaya kalmomin Bulus ga Agaribas suka nuna daraja, kuma wane amfani wannan ya kawo?

11 Ka lura cewa Bulus ya fahimci matsayin iko na Agaribas ta kiransa da lakabinsa, Sarki? Wannan ya nuna daraja, kuma ta kalmomin da ya yi amfani da su, Bulus ya girmama Agaribas. (1 Bitrus 2:17) Manzon ya ce Agaribas gwani ne a ala’du da dokoki na Yahudawa masu yawa, kuma ya ce yana farin ciki zai kāre kansa a gaban irin wannan sarki da ya koyu. Bulus, Kirista bai aikata kamar ya fi Agaribas ba, wanda ba Kirista ba ne. (Filibbiyawa 2:3) Maimako, Bulus ya roƙi sarkin ya saurare shi da haƙuri. Ta haka, Bulus ya sa Agaribas, da kuma sauran masu sauraronsa, su iya sauraron abin da zai faɗa. Yana nanata abin da dukansu suka yarda da shi, don ya bayyana dalilinsa.

12. A aikin shelar Mulki, ta yaya za mu motsa zuciyar masu sauraronmu?

12 Kamar sa’ad da Bulus yake wa Agaribas magana, daga gabatarwa zuwa kammalawa na saƙon Mulki, bari mu motsa zuciyar masu sauraronmu. Za mu iya yin haka ta daraja mutum da muke wa wa’azi da kuma nuna muna sonsa ko kuma ita, musamman inda ya fito da kuma ra’ayinsa.—1 Korinthiyawa 9:20-23.

Ka Yi Amfani da Kalmar Allah da Kyau

13. Ta yaya za ka motsa masu sauraronka kamar Bulus?

13 Bulus ya so ya motsa masu sauraronsa su aikata bisa bisharar. (1 Tassalunikawa 1:5-7) Saboda haka, ya motsa zuciyarsu, wadda tushen motsawa ce. Idan muka ƙara bincika yadda Bulus ya kāre kansa a gaban Agaribas, za mu lura cewa Bulus ya ‘fassara Kalmar Allah daidai’ ta wajen yin maganar abubuwa da Musa da annabawa suka faɗa.—2 Timothawus 2:15.

14. Ka bayyana yadda Bulus ya yi amfani da rinjaya sa’ad da yake wa Agaribas magana.

14 Bulus ya san cewa Agaribas ba Bayahude ainihi ba ne. Da yake Agaribas ya san Yahudanci, Bulus ya yi bayani cewa a wa’azinsa ba ya “faɗin kome ba sai abin da annabawa da Musa suka ce za ya faru” game da mutuwa da tashin Almasihu daga matattu. (Ayukan Manzanni 26:22, 23) Da yake wa Agaribas magana kai tsaye, Bulus ya yi tambaya: “Sarki Agaribas, kana gaskata annabawa?” Agaribas ya fuskanci yanayi mai wuya. Idan ya ce bai gaskata da annabawa ba, zai ɓata sunansa na Bayahude mai bi. Amma, idan ya yarda da Bulus, zai kasance cikin matsayin da jama’a da suka yarda da manzon suke ciki kuma ba za a kira shi Kirista ba. Da hikima Bulus ya amsa tambayar da ya yi, yana cewa: ‘Na sani kana gaskatawa.’ Yaya zuciyar Agaribas ta motsa shi ya amsa? Ya ce: “Da ƙanƙanuwar rinjayarwa kana so ka maishe ni [Kirista].” (Ayukan Manzanni 26:27, 28) Ko da Agaribas bai zama Kirista ba, babu shakka Bulus ya ɗan motsa zuciyarsa da saƙonsa.—Ibraniyawa 4:12.

15. Ta yaya Bulus ya iya soma ikilisiya a Tassaluniki?

15 Ka lura cewa yadda Bulus ya yi bishara ya haɗa da shela da kuma rinjayarwa? Domin Bulus ya yi hakan yayin da yake ‘fassara kalmar Allah daidai,’ wasu da suka saurare shi sun zama masu bi ba masu ji kawai ba. Hakan ya kasance a Tassaluniki, inda Bulus ya nemo Yahudawa da ’yan Al’umma masu jin tsoron Allah a majami’ar. Labarin Ayukan Manzanni 17:2-4 ya ce: “Bulus kuwa, bisa ga al’adatasa, ya shiga wurinsu, asabarci uku yana mahawara da su daga cikin littattafai, yana buɗewa, yana ƙarfafawa, wajib ne ga Kristi ya sha wahala, ya tashi kuma daga matattu . . . Waɗansu a cikinsu suka rinjayu.” Bulus ya rinjaye mutane. Ya yi bayani, kuma ya ba da tabbaci ta Nassosi cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa da daɗewa. Me ya zama sakamakon? Aka kafa ikilisiyar masu bi.

16. Ta yaya za ka fi jin daɗin shelar Mulki?

16 Za ka ƙara gwaninta a fasahar rinjaya sa’ad da kake bayyana Kalmar Allah? Idan haka ne, za ka fi cim ma abu ka kuma ji daɗin aikinka na wa’azi da koyar da mutane game da Mulkin Allah. Masu shelar bishara da suke yin amfani da shawarar su yi amfani da Littafi Mai Tsarki a aikin wa’azi suna shaida hakan.

17. Domin ka nuna yadda yin amfani da Littafi Mai Tsarki a hidimarmu yake da amfani, ka ba da labarinka ko kuma muhimmancin labari da ke cikin wannan sakin layi.

17 Alal misali, wani mai kula mai ziyara na Shaidun Jehovah ya rubuta: “ ’Yan’uwa da yawa yanzu suna ɗaukan Littafi Mai Tsarki a hannu sa’ad da suke wa’azi gida gida. Wannan yana taimakon masu shela su karanta nassi guda ga mutane da yawa da suke saduwa da su. Yana taimakon mutumin da kuma mai shelar su yi tunanin Littafi Mai Tsarki, ba kawai jaridu da littattafai da muke ba su ba.” Hakika, idan za mu ɗauki Littafi Mai Tsarki a hannu sa’ad da muke aikin wa’azi zai dangana ga abubuwa dabam dabam, har da al’adu ma. Duk da haka, ya kamata a san da mu cewa muna amfani da Kalmar Allah da kyau mu rinjayi wasu su karɓi saƙon Mulki.

Ka Kasance da Ra’ayin Allah Game da Hidima

18, 19. (a) Yaya Allah yake ɗaukan hidimarmu, kuma me ya sa ya kamata mu kasance da ra’ayinsa? (b) Menene zai taimake mu mu yi nasara wajen koma ziyara? (Ka duba akwati mai jigo “Yadda Za Ka Yi Nasara Wajen Koma Ziyara,” a shafi na 12.)

18 Wata hanya ta motsa zuciyar masu sauraronmu ta ƙunshi kasance da ra’ayin Allah game da hidima da kuma yin haƙuri. Nufin Allah shi ne dukan iri-irin mutane “su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:3, 4) Ba haka muke so ba? Jehovah yana haƙuri, kuma haƙurinsa ya ba mutane da yawa zarafi su tuba. (2 Bitrus 3:9) Saboda haka, sa’ad da muka sadu da mutum da yake so ya saurari saƙon Mulki, zai yi kyau mu koma ziyara a kai a kai domin mu koyar da shi. Yana bukatar lokaci da haƙuri mu ga iri na gaskiya yana girma. (1 Korinthiyawa 3:6) Akwati mai jigo “Yadda Za Ka Yi Nasara Wajen Koma Ziyara” ya ba da shawarwari na gina irin wannan so. Ka tuna, rayuwar mutane—matsalolinsu da yanayinsu—suna canjawa koyaushe. Wataƙila za ka yi ta komawa kafin ka same su a gida, amma kwalliya ce da take biyan kuɗin sabulu. Muna son mu ba su zarafi su ji saƙon Allah na ceto. Saboda haka, ka yi wa Jehovah Allah addu’a ka samu hikima ka koyi rinjaya a aikinka na taimakon wasu su karɓi saƙon Mulki.

19 Muddin mun sadu da mutum da yake son ya ƙara jin saƙon Mulki, me za mu sake yi da yake mu Kiristoci ma’aikata ne? Talifinmu na gaba ya ba da shawarwari.

Ka Tuna?

• Me ya sa kāriyar Bulus a gaban Sarki Agaribas take da kyau?

• Ta yaya saƙonmu zai motsa zuciya?

• Me zai taimake mu mu yi amfani da Kalmar Allah da kyau wajen motsa zuciya?

• Ta yaya za mu kasance da ra’ayin Allah game da hidima?

[Box/Hotuna a shafi na 12]

Yadda Za Ka Yi Nasara Wajen Koma Ziyara

• Ka nuna ka damu sosai da mutane.

• Ka zaɓi jigon Littafi Mai Tsarki mai kyau da za ka tattauna.

• Ka shirya ziyara na gaba da za ka yi.

• Ka ci gaba da tunani game da mutumin bayan ka tafi

• Ka koma da sauri, wataƙila bayan kwana ɗaya ko biyu, domin son saƙon ya ci gaba.

• Ka tuna cewa manufarka don ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki na gida ne.

• Ka yi addu’a Jehovah ya sa mutumin ya ci gaba da son nazarin

[Hoto a shafi na 11]

Bulus ya yi amfani da rinjaya sa’ad da yake gaban Gwamna Fastos da Sarki Agaribas

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba