Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 1/1 pp. 3-5
  • Ƙarshen Yaƙi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙarshen Yaƙi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sun Koyi Yadda Ake Kisa
  • Koyon Salama Maimakon Yaƙi
  • Tabbacin Samun Salama ta Duniya
  • Salama a Duniya​—Ta Yaya Za a Same Ta?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 1/1 pp. 3-5

Ƙarshen Yaƙi

‘Mu yara ’yan shekara 12 ne. Ba mu da iko a kan siyasa da yaƙi, amma muna son mu rayu! Muna jiran salama. Za ta kasance sa’ad da muke da rai kuwa?’—Yaran makaranta ’yan aji biyar.

‘Muna son mu je makaranta, mu ziyarci abokanmu da iyalanmu ba tare da tsoron za a sace mu ba. Ina fatan gwamnati za ta saurare mu. Muna son rayuwa da ta fi kyau. Muna son salama.’ ’—Alhaji, ɗan shekara 14

WAƊANNAN kalmomi masu ban tausayi suna nuna fatar matasa da suka wahala na shekaru domin tarzoma na ƙare dangi. Sha’awarsu kawai su yi rayuwar yau da kullum ne. Bai da sauƙi a sa abubuwa da ake fatarsu su kasance gaskiya ba. Za mu rayu mu ga duniya da babu yaƙi kuwa?

A shekarun baya bayan nan, an yi ƙoƙari a magance wasu yaƙe-yaƙen basasa a dukan duniya ta wajen matsa wa abokan gaba su sa hannu a yarjejeniya ta salama. Wasu ƙasashe sun aika da rundunar kawo zaman lafiya domin a yi irin wannan yarjejeniya. Manisantar ƙasashe da suke ƙiyayya da daɗewa kuma suna tuhumar juna sun sa taimakon al’ummai kalilan da suke da kuɗi ko niyyar taimakawa ya kasance da wuya. Sau da yawa, yaƙin yana somawa makonni kaɗan ko kuma watanni bayan an yarda za a daina harbi. Yadda rahoto da wata ƙungiyar bincike a Stockholm game da samun salama da ake kira SIPRI ya nuna, “yana da wuya a yi salama sa’ad da masu faɗān suna so a ci gaba da yaƙin kuma suna da iyawa.”

Amma kuma, waɗannan fāɗāce-fāɗāce da ba a magancewa da ke damun ɓangarorin duniya da yawa na tuna wa Kiristoci annabci na Littafi Mai Tsarki. Littafin Ru’ya ta Yohanna ya yi maganar miyagun zamanu cikin tarihi sa’ad da mahayi na alama zai “amshi salama daga duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 6:4) Wannan kwatancin yaƙi da zai ci gaba yana cikin haɗaɗɗiyar alama da take nuna cewa yanzu muna zama cikin lokacin da aka kwatanta cikin Littafi Mai Tsarki, “kwanaki na ƙarshe.”a (2 Timothawus 3:1) Amma, Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa, waɗannan kwanaki na ƙarshe za su kai ga samun salama.

Littafi Mai Tsarki ya yi bayani a Zabura 46:9 cewa don a samu salama ta gaske ana bukatar a daina yaƙi, ba kawai a jiha ɗaya ta duniya ba, amma a dukan duniya. Ƙari ga haka, wannan zabura ta ambata musamman cewa za a halaka makamai na lokatan da aka soma rubuta Littafi Mai Tsarki—baka, da kuma māshi. Dole a halaka makamai da suke ƙaruwa kwanan nan idan ’yan Adam za su yi zaman lafiya.

Amma, ƙiyayya ce da haɗama suke sa yaƙi ya ci gaba maimakon harsashi da bindigogi. Ƙyashi, ko kuma haɗama ce musamman ke jawo yaƙi, kuma ƙiyayya sau da yawa tana jawo mugunta. Domin a cire waɗannan mugun tunani, mutane suna bukatar su canja yadda suke tunani. Suna bukatar a koya musu yadda ake zaman lafiya. Shi ya sa, annabi na dā, Ishaya ya ce za a daina yaƙi sa’ad da mutane ba za su “ƙara koya yaƙi nan gaba ba.”—Ishaya 2:4.

Amma, a yanzu muna zama a duniya da ke koya wa manya da yara, darajar yaƙi ba darajar salama ba. Abin baƙin ciki, har ana koya wa yara su yi kisa.

Sun Koyi Yadda Ake Kisa

Sa’ad da yake ɗan shekara 14, Alhaji ya riga ya daina aikin soja. Shekararsa goma sa’ad da rukunin ’yan tawaye suka kama shi kuma suka koya masa yadda ake faɗā da bindiga da ake kira AK-47. Bayan an tilasta masa ya zama soja, yana satan abinci ya kuma ƙone gidaje. Ya kashe kuma naƙasa mutane. Yau, Alhaji yana iske shi da wuya ya manta da yaƙi kuma ya yi rayuwa yadda mutane suke yi. Abraham, wani yaro soja, ya koyi yadda ake kisa kuma ba ya son ya bar makaminsa. Ya ce: “Idan sun gaya mini na tafi ba tare da bindiga ta ba, me zan yi, kuma yaya zan samu abin ci.”

Yara sojoji fiye da 300,000—maza da mata—har ila suna faɗā kuma suna mutuwa a yaƙe-yaƙen basasa da ba sa ƙarewa a duniyarmu. Wani shugaban ’yan tawaye ya ce: “Suna bin umurni; ba sa damuwa game da komawa su sami matansu ko kuma iyali; kuma ba sa jin tsoro.” Duk da haka, waɗannan yara suna son kuma sun cancanci rayuwa da ta fi kyau.

A ƙasashe da suka bunƙasa, yanayi na ban tsoro na yaro soja zai yi wuya a san yadda yake. Duk da haka, yara da yawa a ƙasashe da suka bunƙasa suna koyon yaƙi a gidajensu. Ta yaya?

Ga misalin José daga kudu maso gabashin Spain. Yaro ne da yake jin daɗin koyon dambe. Ya fi son dogon takobi na ’yan Japan da babansa ya sayo masa kyautar Kirsimati. Kuma yana son wasan bidiyo, musamman na mugunta. A ranar 1 ga Afrilu, 2000, ya yi koyi da faɗān jaruminsa na wasan bidiyo. A ayyukansa na mugunta, ya kashe babansa, mamarsa, da ƙanwarsa da takobin nan da babansa ya ba shi. Ya bayyana wa ’yan sanda cewa: “Ina son ni kaɗai na kasance a duniya; ba na son iyayena suna nema na.”

Da yake magana a kan sakamakon nishaɗi da ba shi da kyau, mawallafi da kuma shugaban sojoji, Dave Grossman ya ce: “Muna kai wa lokacin nan da azabtar da mutane da sa su wahala zai zama abin nishaɗi: suna more waɗannan ayyukan maimako su ƙi su. Muna koyon mu yi kisa, kuma muna koyon mu ji daɗinsa.”

Alhaji da José sun koyi yadda ake kisa. Ba su da nufin su zama masu kisa, amma irin wannan koyo ya ɓata tunaninsu. Irin wannan koyon—ga yara ko manya—yana shuka mugunta da yaƙi.

Koyon Salama Maimakon Yaƙi

Ba za a taɓa samun salama ta dindindin ba yayin da mutane suke koyon kisa. Ƙarnuka da yawa da suka shige, annabi Ishaya ya rubuta: “Da ma ka yi sauraro ga dokokin [Allah]! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi.” (Ishaya 48:17, 18) Sa’ad da mutane suka samu cikakken sani game da Kalmar Allah kuma suka koya su ƙaunaci dokar Allah, za su ƙi mugunta da yaƙi. Iyaye yanzu ma za su iya tabbata cewa wasan da yaransu suke yi ba ya ƙarfafa mugunta. Manya kuma za su iya koya su sha kan ƙiyayya da haɗama. Shaidun Jehovah sun gano ta misalai da yawa cewa Kalmar Allah tana da ikon canja mutum.—Ibraniyawa 4:12.

Ka yi la’akari da misalin Hortêncio. Matashi ne sa’ad da aka tilasta masa ya zama soja. Ya ce, an shirya aikin soja “ya sa mu so kashe mutane kuma kada mu ji tsoron kisa.” Ya yi faɗā na dogon lokaci a yaƙin basasa da aka yi a Afirka. “Yaƙi ya shafi halina,” in ji shi. “Har wa yau ina tuna da kome da na yi. Ina baƙin cikin abin da aka tilasta mini na yi.”

Sa’ad da wani soja ya yi wa Hortêncio magana game da Littafi Mai Tsarki, ya motsa zuciyarsa. Alkawari da Allah ya yi a Zabura 46:9 cewa zai kawo ƙarshen dukan yaƙe-yaƙe ya burge shi. Da ya ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki bai so ya yi faɗā ba kuma. Ba da daɗewa ba, aka kore shi da abokinsa daga aikin soja, kuma suka keɓe kansu ga Jehovah Allah. “Gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya taimake ni na ƙaunaci magabtana,” in ji Hortêncio. “Na fahimci cewa sa hannu a yaƙi, ina yi wa Jehovah zunubi ne, domin Allah ya ce kada mu kashe magabtanmu. Don na yi irin wannan ƙauna, ya kamata na canja yadda nake tunani kuma ba zan na ɗaukan mutane cewa su magabta ne.”

Irin wannan labarin rayuwa ya nuna cewa koyarwar Littafi Mai Tsarki tana kawo salama. Wannan ba abin mamaki ba ne. Annabi Ishaya ya ce akwai nasaba tsakanin koyarwa ta Allah da salama. Ya annabta: ‘Dukan ’ya’yanki kuma za su zama masu-koyi na Ubangiji: salamar ’ya’yanki kuma mai-girma ce.’ (Ishaya 54:13) Annabin ya hangi sa’ad da mutane na dukan al’ummai za su ruga zuwa bauta mai tsarki ta Jehovah Allah su koyi hanyoyinsa. Da wane sakamako? ‘Za su kuma bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna: al’umma ba za ta zāre ma al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koya yaƙi nan gaba ba.’—Ishaya 2:2-4.

Daidai da wannan annabci, Shaidun Jehovah suna aikin ilimantarwa a dukan duniya, da ya riga ya taimaki miliyoyi su sha kan ƙiyayya da ke jawo yaƙi na ’yan Adam.

Tabbacin Samun Salama ta Duniya

Ban da koyarwa, Allah ya kafa gwamnati, ko “mulki,” da zai iya kawo salama a dukan duniya. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Sarkin da Allah ya zaɓa, Yesu Kristi, shi ne “Sarkin Salama.” Ya kuma tabbatar mana cewa “ƙaruwar mulkinsa da salama ba ta da iyaka.”—Ishaya 9:6, 7.

Wane tabbaci muke da shi cewa mulkin Kristi zai kawar da kowane irin yaƙi? Annabi Ishaya ya daɗa: “Himmar Ubangiji mai-runduna za ya aikata wannan.” (Ishaya 9:7) Allah yana son kuma yana da iyawar adana salama na dindindin. Yesu ya tabbata da wannan alkawarin ƙwarai. Shi ya sa ya koya wa mabiyansa su yi addu’a Mulkin Allah ya zo kuma a yi nufin Allah a duniya. (Matta 6:9, 10) Sa’ad da aka amsa wannan roƙo, yaƙi ba zai sake baƙanta duniya ba.

[Hasiya]

a Don ka bincika tabbacin cewa muna zama a kwanaki na ƙarshe, ka duba babi na 11 na littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, Shaidun Jehovah ne suka buga.

[Hoto a shafi na 5]

Koyarwa ta Littafi Mai Tsarki tana ɗaukaka salama ta gaske

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba