“Ubangiji, Ka Koya Mana Yin Addu’a”
“Wani daga cikin almajiransa ya ce masa, Ubangiji, ka koya mana yin addu’a.”—LUKA 11:1.
1. Me ya sa wani cikin almajiran Yesu ya gaya wa Yesu ya koya musu yadda ake addu’a?
WANI lokaci a shekara ta 32 A.Z., wani almajirin Yesu ya gan shi yana addu’a. Bai ji abin da Yesu yake gaya wa Ubansa ba, wataƙila domin yana addu’ar a zuci ne. Duk da haka, sa’ad da Yesu ya gama, almajirin ya ce masa: “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a.” (Luka 11:1) Me ya jawo wannan roƙon? Yahudawa suna addu’a a kai a kai kuma suna hakan a bautarsu. Nassosin Ibrananci na ɗauke da addu’o’i da yawa a littafin Zabura da kuma wasu wurare. Saboda haka, almajirin ba roƙo yake yi a koya masa abin da bai sani ba ko kuma bai taɓa yi ba ne. Babu shakka, yana sane da addu’o’in shugabannin addini na Yahudawa da ke a rubuce. Amma yanzu ya ga Yesu yana addu’a, kuma wataƙila ya ga bambanci ƙwarai tsakanin yadda Yesu ya yi addu’a da addu’o’in shugabannin addini da suke jin sun fi wasu adalci.—Matta 6:5-8.
2. (a) Menene ya nuna cewa Yesu ba ya nufin mu haddace addu’ar misali? (b) Me ya sa muke son mu san yadda ake addu’a?
2 Watanni 18 da suka shige, a Hudubarsa Bisa Dutse, Yesu ya nuna wa almajiransa misalin abubuwa da za su yi addu’a game da su. (Matta 6:9-13) Mai yiwuwa, wannan almajirin ba ya wajen a lokacin, shi ya sa Yesu ya maimaita muhimman darussa na wannan addu’ar misali. Abin da za a lura shi ne, bai maimaita addu’ar da kalmomi da ya yi amfani da su dā, a nuna cewa bai haddace addu’ar ba. (Luka 11:1-4) Kamar wannan almajiri da ba a ambata sunansa ba, ya kamata mu ma a koya mana yadda ake addu’a don addu’o’inmu su jawo mu kusa da Jehovah. Saboda haka, bari mu bincika dukan addu’ar misali, yadda manzo Matta ya rubuta. Ta ƙunshi roƙo bakwai, guda uku game da nufe-nufen Allah ne, huɗu kuma game da bukatunmu na ruhaniya da na zahiri. A wannan talifin za mu bincika guda uku na farko.
Uba Mai Ƙauna
3, 4. Menene yake nufi mu kira Jehovah “Ubanmu”?
3 A somawa, Yesu ya nuna cewa ya kamata addu’armu ta nuna dangantaka ta kurkusa da Jehovah kuma ta ladabi. Domin yana magana musamman don amfanin almajiransa da suka taru kusa da shi a wannan gefen dutsen, Yesu ya gaya musu su kira Jehovah “Ubanmu wanda ke cikin sama.” (Matta 6:9) Wani manazarci ya ce, ko Yesu ya yi maganar yadda ake faɗinsa a Ibrananci ko kuma yaren Aramaic, kalmar da ya yi amfani da ita ga “Uba” kama take da yadda jinjiri zai ce, ‘baba.’ Kiran Jehovah “Ubanmu” yana nuna dangantaka mai daɗaɗa, kuma tabbatacce.
4 Ta cewa “Ubanmu,” mun yarda cewa muna cikin iyali mai girma da ya ƙunshi maza da mata da suka gane Jehovah ne Mai Ba da Rai. (Ishaya 64:8; Ayukan Manzanni 17:24, 28) Kiristoci da aka shafa da ruhu sun zama “ ’ya’yan Allah,” kuma gare shi suna “kira, Abba, Uba.” (Romawa 8:14, 15) Mutane miliyoyi sun zama abokansu masu aminci. Waɗannan sun keɓe kansu ga Jehovah kuma suka nuna alamar keɓe kansu ta yin baftisma cikin ruwa. Dukan “waɗansu tumaki” za su iya yi wa Jehovah addu’a cikin sunan Yesu su kira Shi “Ubanmu.” (Yohanna 10:16; 14:6) Za mu iya yi wa “Ubanmu” na samaniya addu’a a kai a kai mu yabe shi, mu gode masa don dukan nagartarsa a gare mu, mu gaya masa dukan abubuwa da suke damunmu, da gaba gaɗi cewa yana kula da mu.—Filibbiyawa 4:6, 7; 1 Bitrus 5:6, 7.
Ƙaunar Sunan Jehovah
5. Menene roƙo na farko na addu’ar misali, kuma me ya sa wannan ya dace?
5 Roƙon ya soma da abubuwa mafi muhimmanci. Ya ce: “A tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Hakika, tsarkake sunan Jehovah ya kamata ya zama damuwarmu ta farko domin muna ƙaunarsa kuma ba ma son mu ga dukan hanyoyi da yawa da ake zargin sunansa. Tawayen Shaiɗan da kuma sa ma’aurata na farko su yi wa Jehovah Allah rashin biyayya ya ɓata sunan Allah ta sa a riƙa shakka game da hanyar da Allah yake nuna ikon mallakar dukan sararin samaniya. (Farawa 3:1-6) Bugu da ƙari, tun tawaye na farko, ana zargin sunan Jehovah ta wurin ayyuka da ba sa daraja shi da koyarwa na waɗanda suke da’awa suna wakiltansa.
6. Menene ba za mu yi ba idan muna addu’a a tsarkake sunan Jehovah?
6 Addu’armu a tsarkake sunan Jehovah ta nuna wanda muke goyon bayansa a batun ikon mallakar sararin samaniya—muna goyon bayan ikon Jehovah ya yi sarautar sararin samaniya. Jehovah yana son halittu masu basira waɗanda suke son kuma suna farin ciki su yi biyayya da ikon mallakarsa na adalci domin suna ƙaunarsa kuma suna ƙaunar dukan abin da sunansa yake wakilta su yi rayuwa. (1 Labarbaru 29:10-13; Zabura 8:1; 148:13) Ƙaunar sunan Jehovah za ta taimake mu mu ƙi yin kome da zai kawo zargi a kan wannan suna mai tsarki. (Ezekiel 36:20, 21; Romawa 2:21-24) Tun da yake salama ta sararin samaniya da na mazaunanta ta dangana da tsarkake sunan Jehovah da kuma yin biyayya ga ikon mallakarsa, addu’armu “a tsarkake sunanka” tana nuna muna da gaba gaɗi cewa nufin Jehovah zai cika ga yabonsa.—Ezekiel 38:23.
Mulki da Muke Addu’arsa
7, 8. (a) Menene Mulkin da Yesu ya koya mana mu yi addu’arsa? (b) Menene muka koya game da wannan Mulkin a littattafan Daniel da Ru’ya ta Yohanna?
7 Roƙo na biyu cikin addu’ar misali shi ne: “Mulkinka shi zo.” (Matta 6:10) Wannan roƙon yana da nasaba ta kusa da wanda ya gabata. Jehovah yana amfani da Mulkin Almasihu, gwamnatinsa na samaniya ya tsarkake sunansa mai tsarki, wanda Ɗansa, Yesu Kristi ne aka naɗa ya zama Sarki. (Zabura 2:1-9) Annabcin Daniel ya nuna cewa Mulkin Almasihu “dutse” ne da ya fito daga cikin ‘babban tudu.’ (Daniel 2:34, 35, 44, 45) Babban tudun yana wakiltan ikon Jehovah na mallakar sararin samaniya, saboda haka, Mulkin da dutsen yake wakilta sabon nuni ne na sarautar Jehovah a kan sararin samaniya. A cikin annabcin, dutsen ‘ya zama babban tudu; ya cika dukan duniya,’ wannan ya nuna cewa Mulkin Almasihu zai wakilci ikon mallaka na Allah a yin sarautar duniya.
8 Zambar ɗari da zambar arba’in da huɗu da “aka fanshi . . . daga cikin mutane” suna tarayya da Kristi a wannan Mulki, za su yi sarauta na sarakuna da firistoci da shi. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1-4; 20:6) Daniel ya ce waɗannan “tsarkaka na Maɗaukaki” ne, waɗanda tare da Kristi Shugabansu sun karɓi “sarauta da mulki, da girman mulkokin da ke ƙarƙashin sama . . . mulki nas[u] madawwamin mulki ne, dukan mulkoki kuma za su bauta mas[u] su yi biyayya da shi.” (Daniel 7:13, 14, 18, 27) Wannan kwatanci ne da ya dace na gwamnatin samaniya da Kristi ya koya wa mabiyansu su yi addu’a dominsa.
Har Ila Me Ya Sa Muke Addu’a Mulkin Ya Zo?
9. Me ya sa ya dace mu yi addu’a Mulkin Allah ya zo?
9 A cikin addu’arsa ta misali, Kristi ya koya mana mu yi addu’a Mulkin Allah ya zo. Cikar annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an kafa Mulkin Almasihu a sama a shekara ta 1914.a Saboda haka, har ila ya dace ne mu yi addu’a wannan Mulkin ya “zo”? Babu shakka. Domin a cikin annabcin Daniel, Mulkin Almasihu da dutse yake wakilta, yana kan karo da gwamnatin siyasa ta ’yan Adam, da babbar siffa ke wakiltawa. Dutsen zai fāɗa wa siffar, ya buge ta ta zama ƙura. Annabcin Daniel ya ce: “Sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:44.
10. Me ya sa muke son Mulkin Allah ya zo?
10 Muna sauraron Mulkin Allah ya zo ya fāɗa wa mugun zamani na Shaiɗan domin wannan zai sa a tsarkake suna mai tsarki na Jehovah kuma a cire dukan masu hamayya da ikon mallakar Allah. Muna addu’a: “Mulkinka shi zo,” kuma tare da manzo Yohanna mun ce: “Amin: ka zo, ya Ubangiji Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 22:20) Hakika, bari Yesu ya zo ya tsarkake sunan Jehovah kuma ya kunita ikon mallakarsa, don kalmomin mai Zabura ya zama gaskiya: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”—Zabura 83:18.
“Abin da Ka Ke So, a Yi Shi”
11, 12. (a) Menene muke roƙonsa sa’ad da muka yi addu’a a yi nufin Allah “cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama”? (b) Menene addu’armu a yi nufin Jehovah take nufi kuma?
11 Yesu ya ci gaba da koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a: “Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Sararin samaniya ya kasance domin nufin Jehovah. Halittu na samaniya masu iko sun yi ihu: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Jehovah yana da dalilin da ya sa ya halicci “abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.” (Afisawa 1:8-10) Ta yin addu’a cewa a yi nufin Allah, cewa muke Jehovah ya cika nufinsa. Ban da wannan, ta haka muna nuna cewa muna son mu ga an yi nufin Allah a dukan sararin samaniya.
12 Ta wurin wannan addu’a muna nuna muna son rayuwarmu ta yi daidai da nufin Jehovah. Yesu ya ce: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.” (Yohanna 4:34) Kamar Yesu, mu Kiristoci da muka keɓe kanmu, muna farin cikin yin nufin Allah. Ƙaunarmu ga Jehovah da kuma Ɗansa tana motsa mu kada mu yi rayuwa “[m]una bin sha’awoyin mutane, sai dai nufin Allah.” (1 Bitrus 4:1, 2; 2 Korinthiyawa 5:14, 15) Muna ƙoƙari mu guje yin abubuwa da muka sani ba daidai suke da nufin Jehovah ba. (1 Tassalunikawa 4:3-5) Ta wurin sayan lokacin karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nazari, za mu “fahimci ko menene nufin Ubangiji,” wanda ya ƙunshi sa hannu sosai a wa’azin “wannan bishara kuwa ta mulki.”—Afisawa 5:15-17; Matta 24:14.
Nufin Jehovah a Sama
13. Ta yaya ake yin nufin Allah da daɗewa kafin Shaiɗan ya yi tawaye?
13 Ana yin nufin Jehovah a sama da daɗewa kafin ɗaya cikin ’ya’yansa na ruhu ya yi tawaye kuma ya zama Shaiɗan. Littafin Misalai ya kwatanta Ɗan Allah na farko da hikima. Ya nuna cewa shekaru aru aru, Ɗan Allah makaɗaici “kullum [yana] farinciki a gabansa,” yana farin cikin yin nufin Ubansa. Bayan haka, ya zama “gwanin mai-aiki” na Jehovah a halittar dukan abubuwa “cikin sammai da bisa duniya kuma, abubuwa masu-ganuwa da abubuwa marasa-ganuwa.” (Misalai 8:22-31; Kolossiyawa 1:15-17) Jehovah ya yi amfani da Yesu ya zama Kalmarsa, ko kuma Kakaki.—Yohanna 1:1-3.
14. Menene za mu iya koya daga Zabura ta 103 game da yadda mala’iku suke cika nufin Jehovah a sammai?
14 Mai Zabura ya nuna cewa ikon mallakar Jehovah ya fi na dukan halitta kuma cewa mala’iku da yawa suna saurarar kalmominsa da umurninsa. Mu karanta: “Ubangiji ya kafa kursiyinsa a cikin sammai; mulkinsa kuwa yana bisa kowa. Ku albarkaci Ubangiji, ku mala’iku nasa: Ku ƙarfafa masu-iko da ke iyar da saƙonsa, kuna kasa kunne ga muryar maganatasa. Ku albarkaci Ubangiji, ku rundunarsa duka; Ku masu-hidima nasa, waɗanda ke aika yardarsa. Ku albarkaci Ubangiji, ku ayyukansa duka, cikin dukan wuraren mulkinsa [ko kuma, “ikon mallakarsa”].”—Zabura 103:19-22.
15. Ta yaya yadda Yesu ya samu ikon Mulki ya shafi yin nufin Allah a sama?
15 Bayan ya yi tawaye, Shaiɗan yana iya zuwan sama, yadda littafin Ayuba ya nuna. (Ayuba 1:6-12; 2:1-7) Amma, littafin Ru’ya ta Yohanna ya yi annabci cewa lokaci zai zo da za a kore Shaiɗan da aljannunsa daga sama. Lokacin ya zo ba da daɗewa ba bayan Yesu Kristi ya samu ikon Mulki a shekara ta 1914. Tun lokacin, waɗannan ’yan tawaye ba su da wuri a sama. Duniya ce iyakar wajen zamansu. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-11) Ba a yin jayayya a sama, sai muryoyi da suke yabon “ɗan Ragon,” Kristi Yesu, da kuma yabon Jehovah cikin biyayya. (Ru’ya ta Yohanna 4:9-11) Hakika, ana yin nufin Jehovah a sama.
Nufin Jehovah Domin Duniya
16. Ta yaya addu’ar misali ta ƙaryata koyarwar Kiristendam game da begen ’yan Adam?
16 Cocin Kiristendam ba sa ɗaukan duniya tana cikin nufe-nufen Allah, suna da’awa cewa dukan nagargarun mutane za su je sama. Amma, Yesu ya koya mana mu yi addu’a: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Zai yiwu a ce ana nufin Jehovah a yau cikin duniya da ta cika da mugunta, rashin gaskiya, ciwo, da kuma mutuwa? Sam! Saboda haka, ya kamata mu yi addu’a sosai a yi nufin Allah a duniya, daidai da alkawarin da manzo Bitrus ya rubuta: “Bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sababbin sammai [Mulki na gwamnatin Almasihu ta Kristi] da sabuwar duniya [jam’iyyar mutane masu adalci], inda adalci ya ke zaune.”—2 Bitrus 3:13.
17. Menene nufin Jehovah game da duniya?
17 Jehovah yana da dalili da ya sa ya halicce duniya. Ya hure annabi Ishaya ya rubuta: “Hakanan Ubangiji ya faɗi, shi wanda ya halicci sammai; shi ne Allah; mai-sifanta duniya mai-yinta kuma; shi ya kafa ta, ya halicce ta ba wofi ba, ya kamanta ta domin wurin zama; ni ne Ubangiji; babu wani kuma.” (Ishaya 45:18) Allah ya saka ma’aurata na farko cikin lambun aljanna, kuma ya gaya musu: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” (Farawa 1:27, 28; 2:15) A bayyane yake, nufin Mahaliccin ne adalai kamiltattu da suke biyayya da ikon mallakar Jehovah su zauna a duniya har abada cikin Aljanna da Kristi ya yi alkawarinta.—Zabura 37:11, 29; Luka 23:43.
18, 19. (a) Menene dole za a yi kafin a yi nufin Allah sosai a duniya? (b) Waɗanne fannoni game da addu’ar misali na Yesu za a bincika a talifi na gaba?
18 Ba za a taɓa yin nufin Jehovah game da duniya ba yayin da maza da mata da suke rashin biyayya ga ikonsa na mallaka suna zama a duniya. Ta amfani da halittu masu iko a ƙarƙashin sarautar Kristi, Allah zai “halaka waɗanda ke halaka duniya.” Ilahirin mugun zamanin Shaiɗan, da addininta na ƙarya, siyasar lalaci, kasuwanci na haɗama da rashin gaskiya, masu halaka, za a share su har abada. (Ru’ya ta Yohanna 11:18; 18:21; 19:1, 2, 11-18) Za a kunita ikon mallakar Jehovah kuma a tsarkake sunansa. Dukan waɗannan muke addu’arsu sa’ad da muka ce: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Matta 6:9, 10.
19 Amma, a cikin addu’arsa ta misali, Yesu ya nuna cewa za mu iya addu’a game da batutuwa na kanmu ma. Za a bincika wannan fanni na koyarwarsa a kan addu’a a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Ka duba babi na 6 na littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy!, da Shaidun Jehovah suka buga.
A Maimaitawa
• Me ya sa ya dace mu kira Jehovah “Ubanmu”?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu yi addu’a a tsarkake sunan Jehovah?
• Me ya sa muke addu’a Mulkin Allah ya zo?
• Menene muke nufi sa’ad da muka yi addu’a a yi nufin Allah a duniya yadda ake yinsa a sama?
[Hoto a shafi na 15]
Addu’o’in Yesu sun bambanta ƙwarai da addu’o’in Farisawa na nuna adalcin kai
[Hoto a shafi na 16]
Kiristoci suna addu’a Mulkin Allah ya zo, a tsarkake sunansa, kuma a yi nufinsa