Ka Riƙe Tsabtar Ɗabi’a Ta Wurin Tsare Zuciyarka
“Ka kiyaye zuciyarka, gaba da dukan abin da kake kiyayewa, gama daga cikinta mafitan rai suke.”—MISALAI 4:23.
1-3. (a) Ta yaya mutane suke nuna cewa ba sa daraja tsabtarsu ta ɗabi’a? Ka ba da misali. (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu yi la’akari da tsabtar ɗabi’a?
AWASU ƙasashe ana ɗaukan zane da tamani. A ce zane da ke gidanka ya zama kamar tsohon yayi. Ko yaya yake, mai shi ba ya son ya ajiye kuma. Hoton sai ya zama gwanjo a kan farashin dalla 29. Bayan ’yan shekaru, hoton ya kai kusan dalla miliyan! Hakika, ya zama hoto ne mai kyau ƙwarai. Ka tsammance yadda mai shi na dā zai ji saboda ya ƙasƙanta darajar wannan mallakar!
2 Abubuwa kamar haka sukan faru da tsabtar ɗabi’a, ko kuma tsarki. Yawancin mutane a yau sun rage darajar tsabtar ɗabi’arsu. Waɗansu suna ɗaukansa tsohon yayi, wanda bai dace ba da rayuwan zamani. Ta haka, suna ɓata ɗabi’arsu domin ’yar lada. Waɗansu sun ɓata tsabtar ɗabi’arsu don jin daɗin jima’i na ɗan lokaci. Waɗansu sun sadaukar da shi suna sa rai cewa za su samu tagomashi a gaban tsaransu ko kuma kishiyar jinsi.—Misalai 13:20.
3 Mutane da yawa sun makara a sanin tamanin tsabtar ɗabi’arsu. Hasararsu yana da ban tausayi. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, sakamakon lalata kama yake da guba, mai “daci ne kamar tafashiya.” (Misalai 5:3, 4) Saboda wannan lalataccen yanayin ɗabi’a a yau, yaya za ka iya tsare kuma ka riƙe tsabtarka ta ɗabi’a? Za mu yi la’akari da matakai uku da za mu bi.
Ka Kiyaye Zuciyarka
4. Mecece zuciyarka ta alama, kuma me ya sa za mu kiyaye ta?
4 Mataki na riƙe tsabtar ɗabi’a shi ne mu kiyaye zuciyarmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa: Gama daga cikinta mafitan rai su ke.” (Misalai 4:23) Mecece “zuciyarka” da ake nufi a nan? Ba zuciya ta zahiri ba ce. Wannan zuciya ce ta alama. Yana nufin mutum da kake a ciki, da tunaninka, yadda kake ji, tsotsuwar zuciyarka da kuma ra’ayinka. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Za ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka.’ (Kubawar Shari’a 6:5) Yesu ya yi nuni ga wannan dokar cewa ta fi kowacce muhimmanci. (Markus 12:29, 30) Babu shakka, zuciyarmu tana da tamani mai girma. Ta isa a kiyaye ta.
5. Ta yaya zuciya za ta kasance abu mai tamani kuma abin haɗari?
5 Ko yaya, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya ta fi kome rikici, cuta gareta ƙwarai.” (Irmiya 17:9) Ta yaya zuciya ke da rikici—kuma da haɗari gare mu? Alal misali, ko da yake, mota, kayan aiki ne mai daraja, ana amfani da ita a ceci rai lokacin gaggawa. Amma idan direba bai bi da motar a hanyar da ta dace ba, wannan motar tana iya zama makamin kisa. Haka ma, sai ka kiyaye zuciyarka, idan ba haka ba sha’awarka da tsotsuwar zuciya za su sa rayuwarka cikin bala’i. Kalmar Allah ta ce: “Wanda ya dogara ga zuciyar kansa wawa ne: Amma wanda ya taka a hankali za a cece shi.” (Misalai 28:26) Hakika, za ka iya tafiya cikin hikima ka kuma tsira daga bala’i idan Kalmar Allah ta tsare ka, yadda za ka yi amfani da taswira kafin ka fara wata tafiya.—Zabura 119:105.
6, 7. (a) Menene tsarki, kuma me ya sa yake da muhimmanci ga bayin Jehovah? (b) Ta yaya muka sani cewa mutane ajizai za su iya nuna tsarkaka ta Jehovah?
6 Zuciyarmu ba za ta kasance da tsabtar ɗabi’a da kanta ba. Sai mun sa ta ta kasance haka. Hanya ɗaya da za mu iya yin haka ita ce mu yi tunanin darajar tsabtarmu ta ɗabi’a. Wannan halin yana da nasaba da tsarki, wanda yake nufin tsabta, da kuma barin zunubi. Tsarkaka tana da tamani, halin Jehovah Allah ne na musamman. Ɗarurruwan ayoyin Littafi Mai Tsarki suna haɗa wannan hali da Jehovah. Gaskiya kam, Littafi Mai Tsarki ya ce, “Mai-Tsarki ne Ubangiji.” (Fitowa 28:36) Amma, wace nasaba wannan hali mai girma take da shi da mutane ajizai?
7 A cikin Kalmarsa, Jehovah ya gaya mana: “Ku za ku zama masu tsarki; gama ni mai-tsarki ne.” (1 Bitrus 1:16) Hakika, muna iya kwaikwayon tsarkaka na Jehovah; za mu iya zama masu tsabta a gabansa, idan mun riƙe tsabtarmu ta ɗabi’a. Idan mun ƙi ayyuka marasa tsabta, ayyuka na ƙazanta, za mu iya samun bege da gata mai girma—na kasance da hali mai kyau na Allah Mai Girma Duka! (Afisawa 5:1) Kada mu yi zaton cewa ba zai yiwu ba, domin Jehovah mai hikima ne kuma Ubangiji da yake da sanin ya kamata wanda ba ya bukatan abin da ya fi ƙarfinmu. (Zabura 103:13, 14; Yaƙub 3:17) Gaskiya ne, kasancewa da tsabtar ruhaniya da ta ɗabi’a yana bukatar ƙoƙari. Manzo Bulus ya nuna ‘sahihanci da tsabta da ke wajen Kristi.’ (2 Korinthiyawa 11:3) Domin albarkacin Kristi da na Ubansa ba ya kamata ba ne mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu kasance da tsabtar ɗabi’a? Ballantana ma, sun nuna mana ƙauna da ba za mu iya biyansu ba. (Yohanna 3:16; 15:13) Ya dace mu nuna godiyar zuciyarmu ta yin rayuwa mai tsabta, ta ɗabi’a. Idan mun yi tunanin tsabtar ɗabi’armu a wannan hanya, za mu daraja ta, mu kuma kiyaye zuciyarmu.
8. (a) Ta yaya za mu kiyaye zuciyarmu ta alama? (b) Menene taɗinmu yake nunawa game da mu?
8 Muna iya kiyaye zuciyarmu ta hanyar da muke ciyar da kanmu. Muna bukatar kiyaye hankalinmu da kuma zuciyarmu ta cin abinci mai kyau ta ruhaniya, muna mai da hankali da bisharar Mulkin Allah. (Kolossiyawa 3:2) Har a taɗinmu mu nuna muna mai da hankali. Idan muna yawan taɗin sha’awar jiki ne, na lalata, muna nuna wani abu ke nan game da yanayin zuciyarmu. (Luka 6:45) Bari a san mu da taɗi na ruhaniya mai ƙarfafawa. (Afisawa 5:3) Don mu kiyaye zuciyarmu, akwai wasu haɗari masu tsanani da dole mu guje musu. Bari mu tattauna guda biyu cikinsu.
Ka Guje wa Fasikanci
9-11. (a) Me ya sa yake da sauƙi ga waɗanda suka yi banza da gargaɗin 1 Korinthiyawa 6:18 su soma muguwar lalata? Ka ba da misali. (b) Idan za mu gudu daga fasikanci, me za mu guje wa? (c) Wane misali mai kyau ne amini Ayuba ya bar mana?
9 Jehovah ya hure manzo Bulus ya rubuta wasu gargaɗi da ya taimaki mutane da yawa su tsare zuciyarsu kuma su riƙe tsabtar ɗabi’a. Bulus ya ce: “Ku guje ma fasikanci.” (1 Korinthiyawa 6:18) Ka lura, ba kawai ya ce, “Ka kauce daga fasikanci” ba. Ya kamata Kiristoci su ƙara yin wani abu. Suna bukatar su guji kowanne irin ayyukan lalata, daidai da yadda za su guji wani haɗari. Idan muka yi banza da wannan gargaɗi, zai kasance da sauƙi mu soma lalata kuma mu yi rashin tagomashin Allah.
10 Ga misali: Wata uwa ta yi wa ɗanta wanka ta yi masa ado na zuwa wata muhimmiyar liyafa. Ya gaya mata yana son ya fita wasa kafin sauran iyalin su shirya, ta yarda—amma dangane da abu ɗaya. Ta ce: “Kada ka je kusa da ruwan taɓo. Idan ka shiga taɓo, zan yi maka horo.” Amma, a ’yan mintoci, ta ga yaron yana wasa ya kai kusa da taɓon. Bai shiga taɓo ba tukuna. Duk da haka, ai ya yi banza da gargaɗinta cewa kada ya je kusa da taɓon, ga shi kuwa ya kusan shiga taɓo. (Misalai 22:15) Manya da matasa da yawa ma ya kamata su lura kada su yi irin wannan kuskuren. Ta yaya?
11 A cikin wannan zamani da mutane da yawa sun “ƙuna cikin sha’awarsu,” an soma sabon kasuwanci na gabatar da mugun jima’i. (Romawa 1:26, 27) Hotunan tsirarun mutane sun cika jaridu, littattafai, bidiyo, da kuma Intane. Waɗanda suka zaɓi su kalli irin hotunan nan ba sa gudu daga fasikanci ba. Suna wasa da shi, suna wasa kusa da shi, suna banza da gargaɗin Littafi Mai Tsarki. Maimakon su tsare zuciya, suna sa mata guba ta wurin kallon munanan hotuna da zai daɗe kafin su daina tunaninsu. (Misalai 6:27) Bari mu koya daga Ayuba mai aminci, wanda ya yi alkawari—wato, yarjejeniya—da idanunsa, domin kada ya kalli abin da zai jarabce shi ga yin mugunta. (Ayuba 31:1) To, wannan misali ne da za mu bi!
12. Ta yaya Kiristoci za su “guje ma fasikanci” a lokacin zawarci?
12 Yana da muhimmanci a “guje ma fasikanci” musamman ma a lokacin zawarci. Ya kamata lokacin ya zama na farin ciki da bege mai kyau, amma wasu da suke zawarci sun ɓata shi ta yin wasa da lalata. Ta haka, sun hana kansu samun tushe mai kyau na aure—dangantaka da ke bisa ƙauna ta gaske, kamewa, da kuma biyayya ga Jehovah Allah. Wasu aurarru Kiristoci sun yi lalata a lokacin da suke zawarci. Bayan da suka yi aure, matar ta ce lamirinta yana mata azaba, har ya ɓata farin cikin ranar aurensu. Ta ce: “Na biɗi gafarar Jehovah sau da sau, amma ko da shekaru bakwai sun shige, lamirina ya ci gaba da tuhumata.” Muhimmin abu ne waɗanda suka yi irin zunubin nan su biɗi taimako daga Kiristoci dattawa. (Yaƙub 5:14, 15) Amma, wasu aurarru Kiristoci suna aikata da hikima su guje wa waɗannan haɗari a lokacin zawarci. (Misalai 22:3) Suna rage yadda suke nuna soyayyarsu. Suna yarda abokansu su kasance tare da su kuma suna mai da hankali kada su kasance a wurin da babu kowa.
13. Me ya sa bai kamata Kiristoci su yi zawarci da wadda ba ta bauta wa Jehovah ba?
13 Kiristoci da suke zawarci da waɗanda ba sa bauta wa Jehovah suna iya fuskantar ƙarin matsaloli. Alal misali, ta yaya za ka haɗa kanka da wadda ba ta ƙaunar Jehovah Allah? Waɗanda suke ƙaunar Jehovah kuma suke biyayya da mizanansa na tsabtar ɗabi’a ne kaɗai ya kamata Kiristoci su yi abokantaka da su. Kalmar Allah ta gaya mana haka: “Kada ku yi karkiya marar-dacewa tare da marasa-bangaskiya: gama wace zumunta ke tsakanin adalci da zunubi? ko kuwa wace tarayya haske ya ke da duhu?”—2 Korinthiyawa 6:14.
14, 15. (a) Wane irin mugun ra’ayi ne wasu suke da shi game da ma’anar “fasikanci”? (b) “Fasikanci” ta haɗa da waɗanne irin ayyuka ne, kuma ta yaya Kiristoci za su iya guje wa “fasikanci”?
14 Sani yana da muhimmanci. Ba za mu iya guje wa fasikanci yadda ya dace ba idan ba mu san shi ba. Wasu a duniya ta yau ba su san ainihin ma’anar “fasikanci” ba. Suna tsammanin cewa za su iya gamsar da sha’awarsu ta jima’i ba tare da aure ba idan ba su yi ainihin jima’in ba. Saboda haka, mutane da yawa suna jin za su iya gamsar da sha’awarsu ta jima’i ba tare da yin aure ba, har ila kuma cewa suna guje wa zunubin fasikanci. Har wasu asibitoci ma suna neman yadda za su rage ɗaukan ciki da yara masu shekara goma-sha suke yi, suna ƙarfafa matasa su yi mugun jima’i da ba za su ɗauki ciki ba. Abin baƙin ciki ne, domin irin shawarar nan muguwa ce. Guje wa ɗaukan ciki ba tare da aure ba ba ɗaya ba ne da riƙe tsabtar ɗabi’a, kuma ba iyakar ainihin ma’anar “fasikanci” ba ke nan.
15 Kalmar Helenancin nan por·neiʹa, da aka fassara ta “fasikanci,” ma’anarta tana da faɗi. Tana nufin jima’i tsakanin mutanen da ba su yi aure ba kuma tana zance ma game da ɓata amfanin azzakari ko farji. Por·neiʹa ta haɗa da tsotsar al’aura, luwaɗi, da kuma tsarancewa—ayyukan da aka san su cewa daga gidajen karuwai ne. Waɗanda suke jin cewa waɗannan ayyuka ba “fasikanci” ba ne suna cucin kansu ne kuma sun kamu ke nan cikin wani tarkon Shaiɗan. (2 Timothawus 2:26) Ban da haka, riƙe tsabtar ɗabi’a ba ƙin yin wasu ayyuka ne kawai da ke na fasikanci ba. Don mu “guje ma fasikanci,” dole ne mu kauce wa dukan irin ƙazanta ta jima’i da kuma lalata wadda za ta iya kai mu cikin mugun zunubi na por·neiʹa. (Afisawa 4:19) Ta haka ne muke riƙe tsabtar ɗabi’a.
Ka Kauce wa Haɗarin Kwarkwasa
16. A wane yanayi ne nuna soyayya ta dace, wane misali ne cikin Nassosi ya nuna wannan?
16 Idan za mu riƙe tsabtar ɗabi’a, wani haɗari da za mu lura da shi shi ne kwarkwasa. Wasu suna iya nace cewa kwarkwasa ba laifi ba ne, marar lahani ne tsakanin waɗanda suke kishiyar jinsi. Gaskiya kam, da akwai lokaci da kuma wurin da ake iya nuna soyayya. An ga Ishaƙu da Rifkatu suna “wasa” tare, ya kasance a bayyane ga waɗanda suke gani cewa su ba ya da ƙanwa ba ne ko kuma abokai ba kawai. (Farawa 26:7-9) Amma, mata da miji ne. Ya dace su nuna soyayya ga junansu. Kwarkwasa dabam take.
17. Mecece kwarkwasa, kuma ta yaya za a iya sarrafa matsalar?
17 An ba da ma’anar kwarkwasa haka: nuna soyayya ga wani ba tare da niyyar aurensa ba. Mutane sun bambanta, saboda haka, da akwai hanyoyi da yawa na yin kwarkwasa, wasu hanyoyin, da wuyan ganewa. (Misalai 30:18, 19) Saboda haka, doka ba za ta iya sarrafa al’amarin ba. Maimako, ana bukatar wani abu mai muhimmanci—bincika kanmu da kuma ƙoƙari ƙwarai mu yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.
18. Me ke sa wasu yin kwarkwasa, kuma me ya sa kwarkwasa take da lahani?
18 Hakika, sau da yawa idan wani kishiyar jinsi yana nuna mana soyayya, kamar shafa mana mai ne a leɓa. Wannan haka yake. Amma domin kawai muna so a nuna mana soyayya za mu yi kwarkwasa ne ko mu sa wata ta yi irin wannan tunani? Idan haka ne, muna tunanin irin azaba da muke ganawa kuwa? Alal misali, Misalai 13:12 ta ce: “Muradin da ba a biya ba ya kan sa zuciya ta yi ciwo.” Idan muka yi wa wani kwarkwasa, mai yiwuwa ne ba mu san yadda mutumin yake ji game da haka ba. Wataƙila za ta ko za ya yi tsammanin zawarci har ma aure. Idan hakan bai yiwu ba, abin ɓacin rai ne ƙwarai. (Misalai 18:14) Yin wasa da tsotsuwar zuciyar wasu mugunta ce.
19. Ta yaya kwarkwasa za ta iya lalace auren Kiristoci?
19 Muhimmin abu ne ga aurarru musamman su tsare kansu daga kwarkwasa. Nuna soyayya ga wata da ta yi aure—ko wadda ta yi aure ta nuna soyayya ga wani da ba mijinta ba—bai da kyau. Abin baƙin ciki ne, wasu Kiristoci suna da mugun ra’ayin nan cewa ya dace a nuna soyayya wa waɗanda suke kishiyar jinsi da ba matarsa ko mijinta ba. Sai wasu ma su nuna niyyarsu ta cewa “aboki” ne har suna gaya masa asiri da ba za su iya gaya wa mijinsu ba. Saboda wannan, soyayya ta kai tsotsuwar zuciya da ke jawo dangantaka da take lalace aure. Yana da kyau aurarru Kiristoci su tuna da gargaɗin Yesu game da zina—cewa tana somawa daga zuciya ce. (Matta 5:28) Saboda haka, bari mu tsare zuciyarmu kuma mu guje wa yanayi da zai kai mu ga mugun sakamako.
20. Yaya ya kamata ra’ayinmu ya kasance game da tsabtar ɗabi’a?
20 Hakika, bai da sauƙi a kasance da tsabtar ɗabi’a a duniyar yau ta lalata. Amma, ka tuna cewa ya fi sauƙi ka riƙe tsabtarka ta ɗabi’a maimakon ka maido da ita bayan ta lalace. Babu shakka, Jehovah yana “gafara a yalwace” kuma yana iya tsabtace waɗanda suke tuba daga zunubansu. (Ishaya 55:7) Amma, Jehovah ba ya tsare waɗanda suke lalata daga sakamakon ayyukansu ba. Sakamakon zai kasance na shekaru da yawa, har ma a duk rayuwa. (2 Samu’ila 12:9-12) Ko yaya dai, ka riƙe tsabtarka ta ɗabi’a ta wurin tsare zuciyarka. Ka daraja tsayawarka da tsabtar ɗabi’a a gaban Jehovah Allah—kuma kada ka ƙyale!
Yaya Za Ka Amsa?
• Mecece tsabtar ɗabi’a, kuma me ya sa take da muhimmanci?
• Ta yaya za mu tsare zuciyarmu?
• Menene guje wa fasikanci ta ƙunsa?
• Me ya sa ya kamata mu guje wa kwarkwasa?
[Hoto a shafi na 9]
Idan ba a sarrafa mota da kyau ba za ta iya zama da haɗari
[Hotuna a shafi na 10]
Me zai iya faruwa idan muka yi banza da gargaɗi?
[Hoto a shafi na 11]
Zawarci mai tsabta abin farin ciki ne kuma yana daraja Allah