Masu Albarka Ne Waɗanda Suke Ɗaukaka Allah
“Ya Ubangiji, za su zo su yi sujada a gabanka; su darajanta sunanka.”—Zabura 86:9.
1. Me ya sa muna iya ɗaukaka Allah a hanyoyi da suka fi yadda halittu marasa rai sukan ɗaukaka shi?
JEHOVAH ne ya cancanci yabo daga wurin dukan halittunsa. Ko da yake halittunsa marasa rai suna ɗaukaka shi, mu ’yan Adam muna da sanin ya kamata, fahimi, godiya, da son yin sujada. Saboda haka, a gare mu mai Zabura ya ce: “Ku yi sowa ta farinciki ga Allah, ku duniya duka: Ku rera, ku furta darajar sunansa: Ku darajanta yabonsa.”—Zabura 66:1, 2.
2. Su wanene suka bi umurnin nan su ɗaukaka sunan Allah, kuma me ya sa?
2 Yawancin mutane sun ƙi su san Allah ko su ɗaukaka shi. Amma a ƙasashe 235, Shaidun Jehovah fiye da miliyan shida suna nuna cewa sun ga “al’amura da ba su ganuwa” na Allah da ya yi kuma sun “ji” shaidar halittu marasa murya. (Romawa 1:20; Zabura 19:2, 3) Ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki, mun san Jehovah kuma muna ƙaunarsa. Zabura 86:9, 10 ta annabta: “Ya Ubangiji, dukan al’ummai waɗanda ka yi su za su zo su yi sujada a gabanka; su darajanta sunanka. Gama mai-girma ne kai, mai-aikata al’ajabai: kai kaɗai ne Allah.”
3. Ta yaya “taro mai-girma” suke bauta “dare da rana”?
3 Haka ma Ru’ya ta Yohanna 7:9, 15 ta kwatanta “taro mai-girma” na masu sujada “suna yi ma [Allah] bauta kuma dare da rana cikin haikalinsa.” Allah ba ya bukatar yabo kowace daƙiƙa daga bayinsa, amma masu bauta masa ƙungiya ce ta dukan duniya. Saboda haka, sa’ad da ake dare a wasu ƙasashe, bayin Allah a wani ɓangaren duniya suna shagala a yin wa’azi. Ta haka ne za a iya cewa rana ba ta faɗuwa a kan waɗanda suke ɗaukaka Jehovah. Ba da daɗewa ba “duka abin da yake da numfashi” zai ɗaga muryarsa a yabo ga Jehovah. (Zabura 150:6) Amma kafin nan, menene kowannenmu zai iya yi domin ɗaukaka Allah? Waɗanne ƙalubalai ne za mu fuskanta? Kuma wace albarka ce ke jiran waɗanda suke ɗaukaka Allah? Domin amsar, bari mu yi la’akari da wani labarin Littafi Mai Tsarki game da ƙabilar Gad na Isra’ila.
Wani Ƙalubale na Dā
4. Wane ƙalubale ne ƙabilar Gad ta fuskanta?
4 Kafin su shiga Ƙasar Alkawari, ’ya’yan ƙabilar Gad na Isra’ila sun roƙa a yarda su zauna a ƙasa mai kyaun kiwon dabbobi da ke gabacin Urdun. (Littafin Lissafi 32:1-5) Zama a wurin zai bukaci jimrewa da ƙalubalai masu tsanani. Ƙabilai da ke zama ta yamma za su sami kāriyar Kwarin Urdun—wanda yake ba da kāriya na hari. (Joshua 3:13-17) The Historical Geography of the Holy Land, na George Adam Smith ya faɗi game da ƙasashen da suke gabacin Urdun, ya ce: “Duka ƙasashen suna da faɗi, kusan babu wani abin hani, a kan tudun Arabiya. Kullum makiyaya suna kiwo a wajen, wasu rukuninsu suna ruga wajen kowacce shekara domin kiwo.”
5. Ta yaya ne Yakubu ya ƙarfafa ‘yan Gad su yi sa’ad da aka kawo musu hari?
5 Ta yaya ƙabilar Gad za ta jure da irin wannan matsi na kullum? Ƙarnuka da farko, kakansu Yakubu a kan gadon mutuwarsa ya annabta cewa: “Gad fa, mahara za su matsa shi: amma shi za ya matsa duddugensu.” (Farawa 49:19) Da farko waɗannan kalmomin kamar na masifa ne. Amma a kashin gaskiya, umurni ne ga ’yan Gad su yi ramako. Yakubu ya ba su tabbacin cewa idan sun yi haka nan, masu kawo harin za su koma da gudu, ’yan Gad kuwa su bi su.
Ƙalubalai ga Bautarmu a Yau
6, 7. Yaya yanayin Kiristoci a yau ya yi daidai da na ƙabilar Gad?
6 Kiristoci a yau, kamar ƙabilar Gad suna shan matsi da wahalar tsarin Shaiɗan; babu wata kāriya ta mu’ujiza da za ta hana mu kokawa. (Ayuba 1:10-12) Yawancinmu muna jimrewa da matsin zuwan makaranta, yin tattalin rayuwa, da kuma renon yara. Akwai kuma matsaloli na kanmu ko kuma na cikin jiki. Wasu dole ne su jimre da “masuki cikin jiki,” wataƙila naƙasa ko kuma ciwo mai tsanani. (2 Korinthiyawa 12:7-10) Wasu suna wahalar jin cewa ba su cancanta ba. “Miyagun kwanaki” na tsufa zai iya hana Kiristoci tsofaffi su bauta wa Jehovah da kuzari yadda suka yi a dā.—Mai Wa’azi 12:1.
7 Manzo Bulus ya tunasar mana cewa “kokawarmu . . . da rundunai masu-ruhaniya na mugunta [ne] cikin sammai.” (Afisawa 6:12) Kullum muna fuskantar “ruhun duniya,” ruhun tawaye da ɓatancin ɗabi’a wadda Shaiɗan da aljanunsa ke gabatarwa. (1 Korinthiyawa 2:12; Afisawa 2:2, 3) Kamar Lutu mai tsoron Allah, mu a yau muna iya baƙin ciki domin lalata da mutane gewaye da mu suke taɗinsa ko kuma suke yi. (2 Bitrus 2:7) Muna fuskantar farmaki na kai tsaye ma daga Shaiɗan. Shaiɗan yana yaƙi da raguwar shafaffu, “waɗanda ke kiyaye da dokokin Allah, suna riƙe da shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:17) “Waɗansu tumaki” na Yesu ma suna shan farmaki na Shaiɗan ta wurin hani da kuma tsanantawa.—Yohanna 10:16.
Mu Ba da Kanmu Ko Mu Yi Ramako Ne?
8. Yaya ya kamata mu yi da farmakin Shaiɗan, kuma me ya sa?
8 Menene ya kamata mu yi game da farmakin Shaiɗan? Kamar ƙabilar Gad na dā, dole mu yi ƙarfi a ruhaniya kuma mu yi ramako daidai da ja-gorar Allah. Abin baƙin ciki, wasu sun soma kasala domin matsalolin rayuwa, suna banza da hakkinsu na ruhaniya. (Matta 13:20-22) Wani Mashaidi ya faɗi dalili da ya sa adadin da suke halartar taro a ikilisiyarsa ya ragu: “ ’Yan’uwa dai sun soma gajiya. Dukansu sun wahala.” Hakika, mutane da yawa a yau suna da dalilan gajiya. Saboda haka, yana da sauƙi mu ɗauki bautar Allah cewa wani matsi ne, hakki mai nauyi. Amma wannan ra’ayi mai kyau ne—ko a ce ya dace?
9. Ta yaya ɗaukan karkiya na Kristi ke kawo hutu?
9 Ka yi la’akari da abin da Yesu ya faɗa wa jama’a na kwanansa waɗanda suka nauyaya domin matsalolin rayuwa: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa.” Abin da Yesu ya faɗi yana nufin cewa mutum zai sami hutu idan ya daina hidimarsa ga Allah ne? Ba haka ba, Yesu ya ce: “Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya; za ku sami hutawa ga rayukanku.” Karkiya sandar ƙarfe ne ko na katako da ke sa mutum ko dabba ya ɗauki kaya mai nauyi. Me ya sa wani zai so ya ɗauka irin wannan karkiya? Ba mu da “nauyin kaya” ne? Muna da shi, amma ga yadda matanin Helenanci ya ce: “Ku shiga ƙarƙashin karkiyata da ni.” Ka yi tunanin wannan: Yesu ya yarda ya taimake mu ɗaukan kayanmu! Ba ma bukatar mu yi shi da ƙarfinmu kaɗai ba.—Matta 9:36; 11:28, 29, hasiya na NW; 2 Korinthiyawa 4:7.
10. Menene sakamakon ƙoƙarinmu na ɗaukaka Allah?
10 Sa’ad da muka ɗauka karkiyar almajirantarwa, muna yaƙi ne da Shaiɗan. Yaƙub 4:7 ta yi alkawari: “Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.” Wannan ba ya nufin cewa yin haka yana da sauƙi ba. Bauta wa Allah yana bukatar ƙoƙari mai yawa. (Luka 13:24) Amma Littafi Mai Tsarki ya yi wannan alkawari a Zabura 126:5: “Masu-shuka da hawaye za su yi girbi da murna.” Hakika, ba ma bauta wa Allah mai butulci. Shi “mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa,” kuma yana albarkar waɗanda suke ɗaukaka shi.—Ibraniyawa 11:6.
Mu Ɗaukaka Allah Mu Masu Wa’azin Mulki
11. Ta yaya hidimar fage ke zama kāriya daga farmakin Shaiɗan?
11 Yesu ya umurce mu: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai.” Aikin wa’azi shi ne hanya ta farko na miƙa “hadaya ta yabo” ga Allah. (Matta 28:19; Ibraniyawa 13:15) ‘Ɗaura wa sawayenmu shirin bishara ta salama’ “dukan makamai” da wajibi ne—wato kāriyarmu daga farmakin Shaiɗan. (Afisawa 6:11-15) Yin yabo ga Allah a hidimar fage hanya ce mai kyau na gina bangaskiyarmu. (2 Korinthiyawa 4:13) Zai taimake mu mu bar mummunan tunani. (Filibbiyawa 4:8) Shagala a hidimar fage tana sa mu yi tarayya mai kyau da ’yan’uwa masu bi.
12, 13. Ta yaya shagalawa cikin hidimar fage a kai a kai zai amfane iyalai? Ka ba da misali.
12 Aikin wa’azi yana iya zama aiki mai kyau domin iyali. Hakika, matasa suna bukatar hutu da ta dace. Duk da haka, ba zai dace ba lokaci da iyali za su ɓatar tare a hidimar fage ya zama na gajiya. Iyaye za su iya sa ya zama da daɗi ta wurin yin renon yaransu su inganta a yi wa mutane magana a hidima. Matasa ba sa jin daɗin abin da suka yi da kyau ba ne? Iyaye za su iya taimakon yara su yi farin ciki a hidima ta daidaitawa, ba ta wurin matsa musu ba.—Farawa 33:13, 14.
13 Bugu da ƙari, iyali da ke yabon Allah tare suna gina dangantaka na kud da kud. Ka yi la’akari da wata ’yar’uwa da mijinta marar bi ya bar ta da yara biyar. Ta fuskanci ƙalubalen samun aiki don ta yi wa yaranta tanadin abubuwan mallaka. Gajiya ta sha kanta ne kuma ta yi watsi da ruhaniyar yaranta? Ta tuna cewa: “Na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Littattafan Littafi Mai Tsarki sosai kuma na yi ƙoƙarin yin amfani da abin da na karanta. Na kan kai yaran taro da hidimar ƙofa ƙofa a kai a kai. Menene sakamakon ƙoƙarina? Dukan yaran biyar sun yi baftisma.” Shagalawa cikin hidimar fage zai iya taimake ka a ƙoƙarinka ka yi renon yaranka “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.”—Afisawa 6:4.
14. (a) Ta yaya matasa za su ɗaukaka Allah a makaranta? (b) Menene zai taimake matasa kada ‘bishara ta zama abin kunya’ gare su?
14 Matasa, idan kuna zama a ƙasa da dokarsu ta yarda, kuna ɗaukaka Allah ta wurin yin wa’azi a makaranta, ko kuma kuna yarda wa tsoron mutum ya hana ku? (Misalai 29:25) Wata Mashaidiya mai shekaru 13 a Puerto Rico ta rubuta: “Ban taɓa jin tsoron yin wa’azi a makaranta ba domin na san wannan ne gaskiya. Kullum ina ɗaga hannu a aji in faɗi abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki. Idan na sami lokaci, sai na je laburare kuma na karanta littafin nan Young People Ask.”a Jehovah ya albarkaci ƙoƙarinta kuwa? Ta ce: “Wasu lokatai ’yan ajina sukan yi mini tambayoyi har kuma su ce na ba su nasu littafin.” Idan dā kana ja da baya, ƙila kana bukatar ka gwada wa kanka “ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke” ta wurin himmantuwa cikin nazari na kanka. (Romawa 12:2) Sa’ad da ka tabbata cewa abin da ka koya gaskiya ne, ‘bishara ba za ta zama abin kunya’ gare ka ba.—Romawa 1:16.
‘Ƙofa Mai Faɗi’ na Hidima
15, 16. Wace “ƙofa mai-faɗi, mai-yalwar aiki” wasu Kiristoci suka shiga, kuma wane sakamako suka samu?
15 Manzo Bulus ya rubuto cewa “ƙofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” tana buɗe dominsa. (1 Korinthiyawa 16:9) Yanayinka zai yarda maka ka shiga hidima? Sa hannu a aikin hidimar majagaba na kullum ko na ɗan lokaci, ya ƙunshi ɓatar da awoyi 70 ko 50 a wata a yin wa’azi. Hakika, ’yan’uwa Kiristoci suna daraja majagaba domin hidimarsu ta aminci. Amma domin suna ɓatar da lokaci mai yawa a hidima ba sa nuna sun fi ’yan’uwansu maza da mata ba. Maimakon haka, suna nuna irin hali da Yesu ya ƙarfafa: “Mu bayi marasa-amfani ne; mun yi abin da ya wajaba garemu.”—Luka 17:10.
16 Yin aikin majagaba yana bukatar mutum ya hori kansa, ya zama mai tsari, kuma mai sadaukar da kai. Kwalliya tana biyan kuɗin sabulu a samun albarkar. “Iya rarraba Kalmar gaskiya na Allah albarka ce ƙwarai,” in ji wani matashi majagaba mai suna Tamika. “Idan kana aikin majagaba, za ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki sosai. Yanzu idan ina wa’azi ƙofa ƙofa, ina iya tuna nassosi da sun dace da duk wanda na same shi.” (2 Timothawus 2:15) Wata majagaba mai suna Mica ta ce: “Ganin yadda gaskiyar take shafan mutane albarka ce mai girma.” Haka ma wani matashi mai suna Matthew ya yi magana game da farin cikin “ganin wani ya zo cikin gaskiyar. Babu wata farin ciki da ta kai wannan.”
17. Ta yaya wata Kirista ta sha kan mugun tunani game da majagaba?
17 Za ka iya tunanin shigar ƙofar aikin majagaba? Wataƙila za ka so ka yi haka amma kana jin ba ka inganta ba. “Dā ba na son aikin majagaba,” in ji wata ’yar’uwa matashiya da sunanta Kenyatte. “Ina jin ba zan iya ba. Ban san yadda zan shirya gabatarwa ko kuma na yi nazari daga cikin Nassosi ba.” Duk da haka, dattawa sun sa wata ’yar’uwa majagaba da ta manyanta ta yi aiki tare da ni. Kenyatte ta tuna cewa “na ji daɗin yin aiki da ita. Wannan ya sa na so aikin majagaba.” Tare da ɗan ƙarfafa da koyarwa, kai ma ƙila za ka so ka yi aikin majagaba.
18. Waɗanne albarka waɗanda suke hidima a wata ƙasa suke samu?
18 Aikin majagaba yakan buɗe zarafi zuwa wasu gatar hidima. Alal misali, wasu ma’aurata sun inganta su koyi aikin masu wa’azi a ƙasashen waje domin a aike su zuwa wata ƙasa su yi wa’azi. Dole ne masu aikin wa’azi na ƙasashen waje su yi gyara a rayuwarsu bisa sabuwar ƙasar, wataƙila sabon yare, sabon al’ada, da sababbin irin abinci. Amma albarkar sukan sha kan matsalolin. Mildred, wata da ta daɗe a aikin wa’azi na ƙasashen waje a Mexico, ta ce: “Ban taɓa nadama da shawarata na zama mai wa’azi na ƙasan waje ba. Sha’awata ce tun lokacin da nake ƙaramar yarinya.” Waɗanne albarka ta samu? “A can garinmu, samun wani da za a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi yana da wuya. A nan, na sami ɗalibai huɗu a lokaci ɗaya da na fita hidimar fage!”
19, 20. Ta yaya mutane da yawa suka sami albarka a hidima a Bethel, na ƙasashen waje, da na Makarantar Koyar da Masu Hidima?
19 Waɗanda suke hidima a Bethel a rassa na Shaidun Jehovah ma suna samun albarka. Sven, wani ɗan’uwa matashi da ke hidima a Jamus, ya ce game da aiki a Bethel: “Ina jin cewa ina wani aiki da ke da madawwamiyar daraja. Da na yi amfani da gwaninta a cikin duniya. Amma da zai zama kamar ina ajiyar kuɗi ne a bankin da arzikinsa ya karye.” Gaskiya kam, yin aiki babu albashi na wanda ya ba da kansa yana bukatar sadaukar da kai. Amma Sven ya ce: “Sa’ad da mutum ya koma gida, zai san cewa dukan abin da ya yi ranar domin Jehovah ne. Wannan yana sa mutum ya ‘burge’ sosai.”
20 Wasu ’yan’uwa sun mori albarkar hidima ta ƙasan waje, aikin gine-ginen rassa a ƙasashen waje. Wani mutum da matarsa da sun yi hidima na shekaru takwas a aikin ƙasan waje sun rubuta: “ ’Yan’uwa a nan suna da kirki. Abin baƙin ciki ne mu bar wannan wuri—sau takwas ke nan da muke ‘ɓacin rai.’ Mun ji daɗi ƙwarai!” Akwai kuma Makarantar Koyar da Masu Hidima. Tana koyarwa ta ruhaniya wa ‘yan’uwa maza marasa aure da suka inganta. Wani wanda ya sauke karatu ya ce: “Na riƙice da nake neman yadda zan gode muku domin wannan makaranta ta ban al’ajabi. Wace ƙungiya ce za ta yi yawan ƙoƙarin nan domin koyarwa?”
21. Wane ƙalubale dukan Kiristoci suke fuskanta cikin hidimarsu ga Allah?
21 Hakika, ƙofar aiki da yawa suna buɗe. Gaskiya ne cewa yawancinmu ba za mu iya hidima a Bethel ko kuma ƙasan waje ba. Yesu Kristi kansa ya sani cewa Kiristoci za su bambanta a ba da “ ’ya’ya” masu yawa domin yanayinsu ya bambanta. (Matta 13:23) Saboda haka, ƙalubalen mu na Kiristoci shi ne yin amfani da yanayinmu da kyau—mu shagala a hidimar Jehovah yadda yanayinmu ya ƙyale. Idan mun yi haka, muna ɗaukaka Jehovah, kuma muna da tabbacin cewa yana murna ƙwarai. Ka yi la’akari da Ethel, ’yar’uwa tsohuwa a wani gidan kulawa. Kullum tana wa’azi wa abokan zamanta kuma tana yin wa’azi a tarho. Duk da kasawarta, tana hidima da dukan zuciyarta.—Matta 22:37.
22. (a) A waɗanne hanyoyi kuma za mu ɗaukaka Allah? (b) Wane lokaci na ban al’ajabi ke jiranmu?
22 Ka tuna fa, cewa aikin wa’azi hanya ɗaya ce kawai da muke ɗaukaka Jehovah. Ta wurin kasance da misalin kirki a ɗabi’armu da adonmu lokacin da muke a wajen aiki, a makaranta, da kuma a gida, muna faranta wa Jehovah zuciya. (Misalai 27:11) Misalai 28:20 ta yi alkawari: “Amintaccen mutum za ya cika da albarka.” Saboda haka, ya kamata mu ‘shuka da yalwa’ a hidimarmu ga Allah, da sanin cewa za mu sami albarka masu yawa. (2 Korinthiyawa 9:6) Ta yin haka, gata ce idan muna da rai a lokaci na ban al’ajabi da “abin da yake da numfashi duka” za su ɗaukaka Jehovah yadda ya dace!—Zabura 150:6.
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga littafin nan, Questions young People Ask—Answers That Work.
Ka Tuna?
• Ta yaya mutanen Allah suke bauta masa “dare da rana?”
• Wane ƙalubale ne ƙabilar Gad ta fuskanta, kuma menene wannan ya koya wa Kiristoci a yau?
• Ƙaƙa hidimar fage ke kāriya daga farmakin Shaiɗan?
• Wane “ƙofa mai-faɗi” ne wasu sun shiga, kuma waɗanne albarka suka samu?
[Hoto a shafi na 23]
Kamar yadda ’yan Gad suka yaƙi mahara, dole Kiristoci su yaƙi farmakin Shaiɗan
[Hoto a shafi na 25]
Muna moran tarayya mai kyau a hidimar fage
[Hotuna a shafi na 26]
Aikin Majagaba yana kawo gata da sun ƙunshi:
1. Hidima a wata ƙasa
2. Hidima a Bethel
3. Aikin wa’azi na ƙasan waje