Mulkin Allah Ya Kasance A yau
“Ta yaya ne ƙasashe masu yawa da suke da al’adu da suka bambanta da kuma ci gaba dabam dabam za su kasance da haɗin kai? An ce farmaki daga wata duniya kaɗai ce za ta haɗa kan ’yan Adam.”—Jaridar The Age, na Australia.
FARMAKI daga wata duniya? Ko da yake ba mu sani ba ko farmakin za ta haɗa kan dukan al’ummai ta duniya ko ba za ta haɗa ba, amma annabci na Littafi Mai Tsarki ya faɗi wani hargitsi wanda zai haɗa al’umman duniya. Kuma iko na samaniya ne za su jawo wannan hargitsi.
Cikin annabci sarkin Isra’ila na dā, Dauda ya yi magana game da yanayin wannan duniyar. Allah ya hure shi ya rubuta: “Sarakunan duniya sun yi tayarwa, masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare, gabā da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa. Suna cewa, ‘Bari mu ’yantar da kanmu daga mulkinsu, bari mu fice daga ƙarƙashinsu!’ ” (Zabura 2:2, 3; Ayyukan Manzanni 4:25, 26) Ka lura cewa sarakunan duniyar nan za su haɗa kansu don su tayar wa Jehovah mahaliccin sararin samaniya, da zaɓaɓɓensa, ko kuwa sarkin da ya naɗa, Yesu Kristi. Ta yaya hakan za ta faru?
In ji ƙirgen kwanaki na lokacin Littafi Mai Tsarki da kuma annabce-annabce da suka cika sun nuna cewa a shekarar 1914 ne, Allah ya kafa Mulkinsa a sama da Sarkinsa Yesu Kristi.a A wannan lokacin dukan al’umman duniya suna da nufi ɗaya. Maimakon su yi biyayya ga ikon mallaka na sabon Mulkin Allah, sun cuɗe a neman iko—Babban Yaƙi, ko Yaƙin Duniya na 1.
Ta yaya ne Jehovah Allah ya ɗauki matakin da masu mulkin suka ɗauka? “Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama, ya mai da su abin dariya. Ya yi musu magana da fushi, ya razanar da su da hasalarsa.” Sa’an nan Jehovah zai gaya wa Ɗansa, zaɓaɓɓen Sarkin Mulkin: “Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai, dukan duniya kuma za ta zama taka. Za ka mallake su da sandar ƙarfe, za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.”—Zabura 2:4, 5, 8, 9.
Farfashewar al’ummai ’yan adawa da sandar ƙarfe za ta faru ne a Armageddon ko Har-Magedon. Littafin ƙarshe na Littafi Mai Tsarki, Wahayin Yahaya, ya kwatanta wannan aukuwa na ƙarshe cewa “yaƙi a babbar ranan nan ta Allah Maɗaukaki” ne inda aka tattara “sarakunan duniya duka.” (Wahayin Yahaya 16:14, 16) Da ikon aljanu, al’ummai na dukan duniya za su haɗa kai da nufi ɗaya—su yaƙi Allah Maɗaukaki.
Lokaci ya kusato da mutane za su haɗa kai domin su yaƙi ikon mallaka na Allah. Akasarin haka, “haɗin kansu” ba zai yi musu amfani ba. Maimako, matakinsu zai kai ga salama da ake jira tuni ga dukan mutane. Ta yaya? A wannan yaƙi na ƙarshe, Mulkin Allah “zai ragargaje dukan waɗannan mulkokin [na duniya] ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.” (Daniyel 2:44) Mulkin Allah kaɗai ne gwamnatin da za ta cika sha’awar mutane na samun salama a duk duniya ba wata ƙungiya ta mutane ba.
Shugaban Mulkin
Mulkin Allah shi ne Mulkin da sahihan mutane da yawa suke addu’a cewa: “Mulkinka yā zo, a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.” (Matiyu 6:10) Maimakon a ɗauka cewa yanayin zuciya ne, Mulkin Allah gwamnati ce ta gaske wadda ta riga ta cim ma abubuwa masu ban sha’awa tun lokacin da aka kafa ta a sama a shekara ta 1914. Bari mu duba wasu muhimman fasaloli da suka nuna cewa Mulkin Allah yana aiki a yau.
Na farko, yana da majalisa da take aiki da kyau, wanda Sarkin da ke a kan kursiyi Yesu Kristi ke shugabancinta. A shekara ta 33 A.Z., Jehovah Allah ya naɗa Yesu Kristi Shugaban ikilisiya ta Kirista. (Afisawa 1:22) Tun lokacin, Yesu yana shugabancinsa, ta haka yana nuna ingancinsa na iya sarauta. Alal misali, sa’ad da aka yi wata babbar yunwa a Yahudiya a ƙarni na farko, nan da nan ikilisiyar Kirista ta ba da taimako ga ’yan’uwa. Aka shirya kayan agaji, sai aka aika Barnaba da Shawulu daga Antakiya su kai gudummawar.—Ayyukan Manzanni 11:27-30.
Za mu iya tsammanci fiye da haka daga wurin Yesu Kristi a yau, domin Mulkin da aka kafa yana aiki. A lokacin da masifu—girgizar ƙasa, yunwa, ambaliya, guguwa, hadari, ko tafasawar manyan duwatsu da ke cikin ƙasa—suka auku, ikilisiyar Kiristoci na Shaidun Jehovah tana ba da taimako na gaggawa ga ’yan’uwa masu bi da kuma wasu da abin ya shafa a yankin. Alal misali, sa’ad da girgizar ƙasa mai ɓarna ta auku a El Savador a Janairu da Fabrairu a shekara ta 2001, an shirya kayan agaji a duka ƙasar, kuma rukunin Shaidun Jehovah daga Amirka, Guatemala, da Kanada sun ba da taimako. Wurarensu na yin bauta guda uku da kuma fiye da gidaje 500 ne aka sake ginawa a ƙanƙanin lokaci.
Talakawan Mulkin Allah
Tun lokacin da aka kafa shi a shekara ta 1914, Mulkin Allah na samaniya yana tattara kuma yana tsara talakawansa daga mutane a gewayen duniya. Wannan ya cika annabci mai girma da Ishaya ya rubuta: “A kwanaki masu zuwa, dutse inda aka gina Haikali [ibadarsa ta gaskiya mai ɗaukaka] zai zama mafi tsayi duka. Al’ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi.” Wannan annabcin ya nuna cewa “al’ummai da yawa” za su hau wannan dutsen kuma su karɓi umurni da dokokin Jehovah.—Ishaya 2:2, 3.
Wannan aikin ya sami ci gaba na musamman a zamanin nan—’yan’uwanci na dukan ƙasashe na Kiristoci fiye da 6,000,000 a ƙasashe sama da 230. A lokacin taron dukan ƙasashe na Shaidun Jehovah, masu lura sun yi mamakin ganin irin ƙauna, salama, da haɗin kai da ke tsakanin mutane masu yawa, babu bambancin ƙasashe, al’adu, da kuma yare. (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Amma ba za ka yarda ba cewa idan gwamnati tana son ta haɗa kan ɗarurukan mutane na yare dabam dabam cikin salama da jituwa, dole ne ta kasance mai amfani wadda ta kahu—ta gaske ba?
Mulkin Allah da Ilimantarwa
Kowace gwamnati tana da ƙa’idodin da take bukatar kowane ɗan ƙasar ya bi, kuma duk wanda yake son ya kasance ƙarƙashin wannan gwamnatin dole ne ya bi waɗannan ƙa’idodin. Haka nan ma, Mulkin Allah yana da ƙa’idodin da duk wanda yake son ya zama talikinsa zai bi. Amma, babu shakka babban aiki ne mutane da yawa da suka zo daga wurare dabam dabam su amince kuma su bi ƙa’idodi ɗaya. Ga kuma wani abu da ya tabbatar da hakikancewar Mulkin Allah—tsarin koyarwarsa mai amfani ba kawai yana canja tunaninmu ba amma kuma yana motsa zuciyarmu.
Ta yaya ne Mulkin ya cim ma wannan aiki mai wuya? Ta yin amfani da tsarin manzanni na yin wa’azi a “gida gida” da kuma koyar da Kalmar Allah ga mutane ɗai ɗai. (Ayyukan Manzanni 5:42; 20:20) Me ya sa wannan tsarin ilimin yake da amfani? Jacques Johnson, wani firist na Katolika, ya rubuta a cikin jarida ta kowane mako na Kanada game da ƙoƙarin da ya yi ya hana wata mata yin nazari da Shaidun Jehovah. Ya ce, “na yi mamaki matuƙa kuma na gane cewa na sa hannu a yaƙin da ba zan yi nasara ba, sai na gano cewa a cikin waɗannan watanni masu yawa wannan mata Mashaidiyar Jehovah ta gina dangantaka mai kyau da wannan uwa da ba ta iya fita. Sun shaƙu da ita ta wurin taimaka mata, suka zama abokai, wannan ya sa suka ƙulla gami mai kyau. Nan da nan ta zama mai ƙwazo ƙwarai a addininsu kuma ba abin da zan iya yi in hana hakan faruwa.” Kamar yadda saƙon Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah suke koyarwa da kuma halayensu na Kirista ya motsa zuciyar wannan ’yar Katolika ta dā, haka zukatan miliyoyin mutane a gewayen duniya take motsawa a yau.
Irin wannan ilimantarwa—ilimantawa ta Mulki—da ke bisa Littafi Mai Tsarki, tana ɗaukaka darajarsa da kuma ƙa’idodinsa a kan ɗabi’a. Tana koyar da mutane su ƙaunaci kuma daraja juna ko daga ina ne suka fito. (Yahaya 13:34, 35) Tana kuma taimaka wa mutane su saurari wannan gargaɗin: “Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” (Romawa 12:2) Domin sun bar yayin rayuwarsu na dā kuma suna bin ƙa’idodi da dokoki na Mulkin, miliyoyi sun sami salama da farin ciki a yanzu da kuma zato mai kyau don nan gaba.—Kolosiyawa 3:9-11.
Wani abin taimako na musamman da ya taimaka aka sami wannan haɗin kan a dukan duniya shi ne wannan jarida, Hasumiyar Tsaro. Ta hanyar salon fassara da na’urar buga littattafai a harsuna masu yawa, ana buga talifofin nazari na Hasumiyar Tsaro a cikin harsuna 135 a lokaci ɗaya, kuma fiye da kashi 95 na masu karatunta a gewayen duniya za su iya nazarin wannan littafin a yarensu.
Wani marubucin Mormon ya tsara nasarar da masu wa’azi na ƙasashen waje waɗanda ba ’yan cocinsa ba suka samu. Ya lissafa Hasumiyar Tsaro da Awake!, da Shaidun Jehovah ne suka buga, a matsayin jaridu mafi kyau na yin wa’azi, kuma ya ce: “Babu wanda zai taɓa cewa Hasumiyar Tsaro da Awake! suna nuna son kai—akasin haka, suna ba da azancin tsaro wanda ban taɓa ganin irinsa a cikin littattafai na wani addini ba. Gaskiyar da ke cikin Hasumiyar Tsaro da Awake! suna wartsakarwa, da bincike na gaskiya kuma suna faɗin abubuwan da suke faruwa a duniya.”
Mun sami tabbaci masu yawa da suka nuna cewa Mulkin Allah ya kasance a yau. Cikin farin ciki da ƙwazo Shaidun Jehovah suna bayyana “bisharan nan ta Mulkin Sama” wa maƙwabtansu, kuma suna gayyatarsu su zama talakawansa. (Matiyu 24:14) Kana murna da wannan begen kuwa? Kana iya jin daɗin albarkar da ake samu daga yin tarayya da waɗanda aka ilimantar kuma suna yin ƙoƙarin su bi ƙa’idodin Mulkin. Mafi muhimmanci kuma, kana iya more begen rayuwa a cikin Mulkin da aka yi alkawarinsa a sabuwar duniya “inda adalci zai yi zamansa.”—2 Bitrus 3:13.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani, ka duba sura ta 10, “Mulkin Allah Yana Sarauta,” a cikin littafin nan Sani Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, Shaidun Jehovah ne suka buga, shafi na 90-97.