Jehovah ‘Mai Kiyaye Mu A Lokatan Wahala’
“Ubangiji yakan ceci adalai, ya kiyaye su a lokatan wahala.”—Zabura 37:39.
1, 2. (a) Menene Yesu ya yi addu’arsa domin almajiransa? (b) Menene nufin Allah game da mutanensa?
JEHOVAH shi ne maɗaukaki duka. Yana da ikon da zai iya kāre masu bauta masa da aminci a dukan fasalolin da ya so. Yana iya ware mutanensa a zahiri ma daga duniya kuma ya ajiye su a wurin da babu damuwa. Amma, Yesu ya roƙi Ubansa na samaniya game da almajiransa: “Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan.”—Yahaya 17:15.
2 Jehovah bai so ya ɗauke mu “daga duniya” ba. Maimako, nufinsa ne mu ci gaba da rayuwa tare da sauran mutane a wannan duniya domin mu sanar da saƙonsa na bege da ta’aziyya ga mutane. (Romawa 10:13-15) Amma kamar yadda Yesu ya nuna cikin addu’arsa, rayuwar da muke yi cikin duniyar nan tana sa “mugun” ya same mu. Mutane masu rashin biyayya da miyagun iskoki suna jawo azaba da baƙin ciki, kuma Kiristoci ma suna shaida wahalar nan.—1 Bitrus 5:9.
3. Dole masu bauta wa Jehovah da aminci su fuskanci me, amma wace ta’aziyya muka samu cikin Kalmar Allah?
3 A lokacin irin gwajin nan mutum yakan iya yin sanyin gwiwa. (Karin Magana 24:10) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran masu aminci da yawa da suka sha wahala. Mai Zabura ya ce: “Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.” (Zabura 34:19) Hakika, miyagun abubuwa suna faruwa wa “mutumin kirki.” A wasu lokatai kamar mai Zabura Dauda, zai zama kamar ‘an ragargaza mu sarai an ci nasara a kanmu’ ne. (Zabura 38:8) Duk da haka, abin ban ta’aziyya ce mu san cewa “Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.”—Zabura 34:18; 94:19.
4, 5. (a) Me za mu yi bisa ga Karin Magana 18:10 domin mu samu kāriyar Allah? (b) Waɗanne matakai za mu iya amfani da su don mu sami taimakon Allah?
4 Daidai da addu’ar da Yesu ya yi, Jehovah yana kāre mu da gaske. Shi ‘yake kiyaye mu a lokatan wahala.’ (Zabura 37:39) Littafin Karin Magana ya yi amfani da irin furcin nan da ya ce: “Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.” (Karin Magana 18:10) Wannan nassi ya bayyana wata muhimmiyar gaskiya game da yadda Jehovah yake damuwa sosai da halittunsa. Allah yana kāre adalai musamman waɗanda suke biɗansa da gaskiya, a ce kamar muna gudu ne zuwa cikin hasumiya ta kāriya.
5 Sa’ad da muke fuskantar matsaloli masu tsanani, ta yaya za mu iya gudu zuwa wajen Jehovah don mu sami kāriya? Bari mu bincika muhimman matakai uku da za mu iya amfani da su don mu sami taimakon Jehovah. Na ɗaya, dole mu je wajen Ubanmu na samaniya cikin addu’a. Na biyu, dole mu aikata daidai da ruhunsa mai tsarki. Na uku kuma, dole mu ba da kai ga tsarin Jehovah ta wurin yin tarayya da ’yan’uwa Kiristoci da suke sauƙaƙa wahalarmu.
Ikon Addu’a
6. Yaya Kiristoci na gaskiya suke ɗaukan addu’a?
6 Wasu masana kiwon lafiyar jiki sun ce yin addu’a zai sa a sami sauƙin baƙin ciki da wahala. Ko da yake lokacin bimbini kamar na yin addu’a yana iya sauƙaƙa wahala, haka yake ma idan mutum ya ji amon wani abu ko kuma an dafa masa hannu a kafaɗa. Kiristoci na gaskiya ba sa ɗaukan cewa addu’a wata aba ce ta wartsakewa kawai ba. Muna ɗaukan addu’a cewa sadarwa ce ta ibada da Mahalicci. Addu’a ta ƙunshi ibadarmu da gaba gaɗinmu ga Allah. Hakika, bautarmu ta ƙunshi yin addu’a.
7. Menene yake nufi a yi addu’a da gaba gaɗi, kuma ta yaya irin addu’o’in nan suke taimakonmu a jimre da wahala?
7 Dole mu yi addu’a da gaba gaɗi ko dogara ga Jehovah. Manzo Yahaya ya rubuta: “Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato in mun roƙi kome bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu.” (1 Yahaya 5:14) Jehovah Mafifici, Allah maɗaukaki na gaskiya kaɗai yana mai da hankali sosai ga addu’o’in masu bauta masa. Abar ta’aziyya ce sanin cewa Allahnmu mai ƙauna yana saurarar mu sa’ad da muke gaya masa alhininmu da kuma matsalolinmu.—Filibiyawa 4:6.
8. Me ya sa Kiristoci masu aminci bai kamata su tsorata ko su ji ba su cancanta ba sa’ad da suke zuwa gaban Jehovah cikin addu’a?
8 Kada Kiristoci masu aminci su tsorata, ko su ji ba su cancanta ba, ko kuma su yi rashin gaba gaɗi a zuwa wurin Jehovah ta wurin addu’a. Gaskiya kam, idan kamar wasu sun ba mu kunya ko kuma kamar matsaloli sun sha kanmu, ba ya mana sauƙi mu je gaban Jehovah cikin addu’a. A irin lokatan nan, yana da kyau mu tuna cewa Jehovah yana “juyayin mutanensa da ke shan wahala” kuma yana “ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya.” (Ishaya 49:13; 2 Korantiyawa 7:6) Muna bukata mu je wajen Ubanmu na samaniya da gaba gaɗi musamman a lokatan azaba da wahala don ya kiyaye mu.
9. Wane matsayi bangaskiya take da shi a yadda muke zuwa wurin Allah cikin addu’a?
9 Don mu amfana sosai daga gatar addu’a, dole mu kasance da bangaskiya ta gaske. Littafi Mai Tsarki ya ce “wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa.” (Ibraniyawa 11:6) Bangaskiya ya wuci kawai a gaskata Allah ya wanzu. Bangaskiya ta gaske ta ƙunshi ƙarƙƙarfan imani game da iyawar Allah da kuma sha’awarsa ya albarkace mu don mun yi biyayya gare shi. “Ubangiji yana lura da masu aikata adalci, yana kuma sauraron roƙonsu.” (1 Bitrus 3:12) Sanin cewa Jehovah yana kula da mu da kyau yana daɗa wa addu’o’inmu ma’ana.
10. Idan Jehovah za ya kiyaye mu a ruhaniya, yaya ya kamata addu’o’inmu su zama?
10 Jehovah yana sauraron addu’o’inmu domin muna yinsu da zuciya ɗaya. Mai Zabura ya rubuta: “Ina kira gare ka da zuciya ɗaya, ka amsa mini, ya Ubangiji.” (Zabura 119:145) Addu’o’inmu ba kamar na waɗanda suke bin al’adun addini ba ne, addu’o’inmu suna da dalili kuma ba rabi da rabi muke yinsu ba. Sa’ad da muka yi addu’a ga Jehovah da “zuciya ɗaya” abin da muke faɗa yana cike da ma’ana da kuma manufa. Bayan irin sahihan addu’o’in nan, mukan shaida sauƙi da ake iya samu daga tura ‘wahalarmu wa Jehovah.’ Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari, “zai taimake” mu.—Zabura 55:22; 1 Bitrus 5:6, 7.
Ruhun Allah Shi Ne Mataimakinmu
11. Wace hanya ɗaya ce Jehovah yake amsa mana sa’ad da muka ‘yi ta roƙon’ taimakonsa?
11 Jehovah ba Mai Jin addu’a kawai ba ne, amma kuma Mai Amsawa ne. (Zabura 65:2) Dauda ya rubuta: “Nakan kira gare ka a lokacin wahala, saboda kakan amsa addu’ata.” (Zabura 86:7) Daidai da haka, Yesu ya ƙarfafa almajiransa su ‘yi ta roƙon’ taimakon Jehovah domin ‘Uba na samaniya’ za ya “ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.” (Luka 11:9-13) Hakika, ikon aiki na Allah mai taimako ne ko kuma mai ta’azantar da mutanensa.—Yahaya 14:16.
12. Ta yaya ruhun Allah zai taimake mu sa’ad da kamar matsaloli za su sha kanmu?
12 Ko sa’ad da muke cikin gwaji ma, ruhun Allah yana iya ba mu “mafificin ikon nan.” (2 Korantiyawa 4:7) Manzo Bulus ya jimre wa yanayi da yawa na wahala, da gaba gaɗi ya ce: “Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafata.” (Filibiyawa 4:13) A yau ma, Kiristoci da yawa sun sabonta a ƙarfi na ruhaniya da kuma na jiye-jiye domin sun sami amsar roƙe-roƙensu. Sau da yawa kamar matsaloli ba sa shan kanmu ba bayan mun sami taimako daga ruhun Allah. Domin wannan ƙarfi da Allah yake bayarwa, za mu iya faɗi kamar manzon: “Ana wahalshe mu ta kowace hanya, duk da haka ba a ci ɗunguminmu ba. Ana ruɗa mu, duk da haka ba mu karai ba. Ana tsananta mana, duk da haka ba mu zama yasassu ba. Ana ta fyaɗa mu ƙasa, duk da haka ba a hallaka mu ba.”—2 Korantiyawa 4:8, 9.
13, 14. (a) Ta yaya Jehovah yake kiyaye mu ta wurin rubutacciyar Kalmarsa? (b) Yaya yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya taimake ka?
13 Ruhu mai tsarki ya hure kuma ya kiyaye rubutacciyar Kalmar Allah domin amfaninmu. Ta yaya Jehovah ya zama mai kiyaye mu a lokatan wahala ta wurin Kalmarsa? Hanya ɗaya ita ce ta yi mana tanadin hikima da kuma tunanin kirki. (Karin Magana 3:21-24) Littafi Mai Tsarki yana koyar da hankulanmu kuma yana gyara tunaninmu. (Romawa 12:1) Ta wurin karatu da kuma nazarin Kalmar Allah a kai a kai, tare da yin amfani da ita, ta haka ‘hankalinmu ya horu yau da kullum su rarrabe nagarta da mugunta.’ (Ibraniyawa 5:14) Wataƙila ka shaida yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suka taimake ka ka tsai da shawara mai kyau sa’ad da kake fuskantar wahala. Littafi Mai Tsarki yana ba mu hikima da za ta taimake mu mu sami maganin matsaloli masu wuya.—Karin Magana 1:4.
14 Kalmar Allah tana mana tanadin wani tushen ƙarfi—wato, begen ceto. (Romawa 15:4) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa miyagun abubuwa ba za su ci gaba har abada ba. Duk ƙunci da muke shan wahalarsa na ɗan lokaci ne. (2 Korantiyawa 4:16-18) Muna da “sa zuciyan nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta gare shi.” (Titus 1:2) Idan muka yi murna game da sa ran nan, kowane lokaci za mu tuna da alkawuran Jehovah game da nan gaba mai kyau, da zai sa mu iya jimre da ƙunci.—Romawa 12:12; 1 Tasalonikawa 1:3.
Allah Yana Nuna Ƙaunarsa Gare Mu ta Wurin Ikilisiya
15. Ta yaya Kiristoci za su iya zama albarka ga juna?
15 Wani tanadi daga wurin Jehovah da zai iya taimakonmu a lokatan wahala shi ne abokantaka da muke mora cikin ikilisiyar Kirista. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” (Karin Magana 17:17) Kalmar Allah ta ƙarfafa duka a cikin ikilisiya su daraja kuma ƙaunaci juna. (Romawa 12:10) “Kada kowa shi biɗa ma kansa, amma abin da za ya amfana maƙwabcinsa,” in ji manzo Bulus. (1 Korantiyawa 10:24) Idan muna irin tunanin nan zai sa mu mai da hankali ga bukatun mutane maimakon namu gwaji. Yayin da muka ba da kanmu mu taimaki mutane, ba taimakonsu kawai muke yi ba amma kuma muna samun farin ciki da gamsuwa da ke rage nauyin da muke ɗauke da shi.—Ayyukan Manzanni 20:35.
16. Ta yaya kowane Kirista zai iya kasance mai ba da ƙarfafa?
16 Ƙwararrun maza da mata suna da muhimmin mataki na ƙarfafa juna. Domin su iya yin haka, sun sa ya zama da sauƙi a zo wajensu kuma suna ba da kansu. (2 Korantiyawa 6:11-13) Ikilisiya tana samun albarka sosai sa’ad da duka suna yaba wa matasa, suna ƙarfafa sababbi masu bi, kuma suna ƙarfafa masu baƙin ciki. (Romawa 15:7) Ƙaunar ’yan’uwanci ma na taimakonmu mu kauce wa halin tuhumar juna. Kada mu yi saurin kammala cewa wani rigima da muka yi da juna rashin ruhaniya ne ya jawo haka ba. Daidai ne Bulus ya aririci Kiristoci su “ƙarfafa masu rarraunar zuciyar.” (1 Tasalonikawa 5:14) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Kiristoci masu aminci ma suna shan wahala.—Ayyukan Manzanni 14:15.
17. Wane zarafi muke da shi da za mu ƙarfafa gamin ’yan’uwanci na Kirista?
17 Taron Kirista yana ba mu zarafin da za mu ta’azantar kuma mu ƙarfafa juna. (Ibraniyawa 10:24, 25) Irin wannan taɗi mai kyau ba a taron ikilisiya kawai ake yin sa ba. Maimako, mutanen Allah suna neman zarafi su yi tarayya ko da a lokacin shaƙatawa ne. Idan aka yi wani yanayi na wahala, za mu kasance a shirye mu taimaka wa juna domin ƙarfafa gami na abokantaka da muke da shi. Manzo Bulus ya rubuta: “Kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai . . . gaɓoɓin su kula da juna . . .. Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.”—1 Korantiyawa 12:25, 26.
18. Wane hali za mu kauce wa sa’ad da muka rarrauna?
18 A wasu lokatai, yakan mana wuya mu mori tarayya da ’yan’uwa Kiristoci. Ya kamata mu yaƙi irin wannan domin kada mu cuci kanmu daga samun ta’aziyya da kuma taimakon ’yan’uwa masu bi. Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Mutumin da ya kula da kansa kaɗai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya faɗi maganar da ke daidai ba zai yarda ba.” (Karin Magana 18:1) ’Yan’uwanmu maza da mata kulawa ce ta Allah a gare mu. Idan muka amince da wannan tanadi mai kyau, za mu iya samun sauƙi a lokacin wahala.
Ka Kasance da Hali Mai Kyau
19, 20. Ta yaya Nassosi suka taimake mu mu ƙi da mugun tunani?
19 Lokacin da muke sanyin gwiwa da kuma baƙin ciki, yana da sauƙi mutum ya yi mugun tunani. Alal misali, sa’ad da wasu suke wahala, suna tuhumar kansu da cewa ba su da ruhaniya suna kammala da cewa wahalar da suke sha alamar rashin amincewar Allah ce. Amma ka tuna cewa Jehovah ba ya gwada kowa da “mugunta.” (Yakubu 1:13) “Ba da gangan ba ne [Allah] yakan wahalar da ’yan adam ko ya sa su baƙin ciki,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Makoki 3:33) Akasarin haka, Jehovah yana baƙin ciki sa’ad da bayinsa suke shan wahala.—Ishaya 63:8, 9; Zakariya 2:8.
20 Jehovah ne “Uba mai yawan jinƙai, Allah na dukan ta’aziyya.” (2 Korantiyawa 1:3) Yana kula da mu kuma zai ɗaukaka mu a lokacinsa. (1 Bitrus 5:6, 7) Idan muka fahimci ƙaunar Allah a gare mu, za ta taimake mu mu kasance da hali mai kyau har mu yi murna kuma. Yakubu ya rubuta: “Ya ku ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.” (Yakubu 1:2) Me ya sa? Ya amsa: “Domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.”—Yakubu 1:12.
21. Duk da wahalar da za mu sha, wane tabbaci Allah ya ba waɗanda suka kasance da aminci gare shi?
21 Kamar yadda Yesu ya yi mana gargaɗi, muna da wahala a duniya. (Yahaya 16:33) Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa ba ‘ƙunci ko masifa ko tsanani ko yunwa ko huntanci ko hatsari’ da zai raba mu da ƙaunar Jehovah da Ɗansa. (Romawa 8:35, 39) Abar ta’aziyya ce sanin cewa kowace wahala muka fuskanta ta ɗan lokaci ne! Kafin lokacin, cikin jirar da muke wa ƙarshen wahalar ’yan Adam, Ubanmu mai ƙauna, Jehovah yana kulawa da mu. Idan muka ruga wajensa don ya kāre mu, zai zama “mafaka ne ga waɗanda ake zalunta, wurin ɓuya a lokatan wahala.”—Zabura 9:9.
Me Muka Koya?
• Me ya kamata Kiristoci su sa rai a rayuwarsu cikin wannan muguwar duniya?
• Ta yaya addu’o’inmu za su kasance da ban ƙarfafa sa’ad da muke fuskantar gwaji?
• Yaya ruhun Allah yake mataimaki?
• Me za mu iya yi don mu taimaki juna?
[Hoto a shafi na 10]
Dole ne mu biɗi Jehovah kamar a ce muna gudu zuwa wata ƙarfafan mafaka
[Hotuna a shafi na 12]
Ƙwararru a ruhaniya suna amfani da kowane zarafi su yaba wa kuma su ƙarfafa juna