Tambayoyi Daga Masu Karatu
Me ya sa Shaidun Jehovah suke ɗaukan cewa adadin 144,000 da aka ambata a littafin Wahayin Yahaya na zahiri ne ba na alama ba?
Manzo Yahaya ya rubuta: “Na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba’in da huɗu ne.” (Wahayin Yahaya 7:4) A cikin Littafi Mai Tsarki furcin nan “waɗanda aka buga wa hatimin” na nuni ga rukunin mutane da aka zaɓa daga cikin ’yan Adam da za su yi sarauta da Kristi a sama bisa Aljanna mai zuwa a duniya. (2 Korantiyawa 1:21, 22; Wahayin Yahaya 5:9, 10; 20:6) An fahimci cewa adadinsu 144,000 na zahiri ne don dalilai masu yawa. An ga dalili ɗaya cikin mahallin Wahayin Yahaya 7:4.
Bayan an gaya wa manzo Yahaya game da wannan rukunin 144,000 a cikin wahayi, an nuna masa wani rukuni. Yahaya ya kwatanta wannan rukuni na biyu cewa su ‘ƙasaitaccen taro ne, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al’umma, da ƙabila, da jama’a, da harshe.’ Wannan ƙasaitaccen taron waɗanda za su tsira wa “matsananciyar wahala” ne mai zuwa da zai halaka wannan muguwar duniya.—Wahayin Yahaya 7:9, 14.
Amma, ka lura da bambancin da Yahaya ya nuna tsakanin ayoyi 4 da 9 na Wahayin Yahaya sura 7. Ya ce rukuni na farko “waɗanda aka buga wa hatimin” suna da takamaiman adadi. Amma, rukuni na biyu “ƙasaitaccen taro,” ba su da takamaiman adadi. Da wannan, yana da kyau a ɗauka cewa adadi 144,000 na zahiri ne. Da a ce adadin nan 144,000 na alama ne kuma yana nuni ga rukunin da ba shi da iyaka, da ba za a ga bambancin waɗannan ayoyi biyu ba. Da haka ayoyin sun nuna cewa adadi 144,000 na zahiri ne.
Manazarcin Littafi Mai Tsarki dabam dabam na dā da na yanzu, sun kammala hakan—cewa, adadin na zahiri ne. Alal misali, da yake magana game da Wahayin Yahaya 7:4, 9, wani mai tsara ƙamus ɗan Britaniya, Dokta Ethelbert W. Bullinger ya lura haka a shekara 100 da ta shige: “Furci ne mai sauƙi na gaskiya: takamaiman adadi ne da ya saɓa da adadi da babu iyaka a wannan sura.” (Littafin Apocalypse or “The Day of the Lord,” shafi na 282) Kwanan baya, Robert L. Thomas, Ƙarami, Farfesa na Sabon Alkawari a makarantar Master’s Seminary a Amirka ya rubuta: “Ɗaukan cewa adadin 144,000 na alama ne ba shi da tushe mai ƙarfi.” Ya daɗa cewa: “Takamaiman adadi ne da ke [7:4] da ya saɓa da adadin da babu iyaka na 7:9. Idan aka ɗauka cewa na alama ce, ba za a ɗauki kowane adadi cikin littafin Wahayin Yahaya a zahiri ba.”—Revelation: An Exegetical Commentary, Littafi na 1, shafi na 474.
Wasu sun yi musu cewa tun da yake littafin Wahayin Yahaya ya cika da yaren alama, dukan adadin da ke cikin wannan littafin, har da adadin 144,000 dole ya zama na alama. (Wahayin Yahaya 1:1, 4; 2:10) Wannan kammalawa ba daidai ba ne. Hakika, littafin Wahayin Yahaya yana cike da adadi na alama da yawa, amma ya haɗa da adadi na zahiri ma. Alal misali, Yahaya ya yi maganar “sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.” (Wahayin Yahaya 21:14) A bayyane yake cewa adadi 12 da aka ambata a cikin wannan ayar na zahiri ne, ba na alama ba. Ƙari ga haka, manzo Yahaya ya rubuta game da “shekarun nan dubu” na sarautar Kristi. Yadda bincike na Littafi Mai Tsaki ya nuna wannan adadin na zahiri ne.a (Wahayin Yahaya 20:3, 5-7) Saboda haka, ko za a ɗauki adadi cikin littafin Wahayin Yahaya a zahiri ko na alama ya dangana da abin da ya faru da abin da ake tattaunawa.
Kammalawar shi ne cewa adadi 144,000 na zahiri ne kuma yana nuni ga adadin mutane kaɗan, ƙaramin rukuni ne idan aka gwada da “ƙasaitaccen taro,” ya kuma yi daidai da wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, a wahayi na gaba da manzo Yahaya ya gani, an kwatanta 144,000 cewa waɗanda ‘aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari.’ (Wahayin Yahaya 14:1, 4) Furcin nan “nunan fari” na nuni ga wakilai kalilan da aka zaɓa. Yayin da Yesu yake duniya, ya yi maganar waɗanda za su yi sarauta da shi a Mulkinsa na samaniya, ya kira su ‘ɗan ƙaramin garke.’ (Luka 12:32; 22:29) Hakika, waɗanda aka fanso daga cikin mutane da za su yi sarauta a sama kaɗan ne idan aka gwada su da waɗanda za su zauna cikin Aljanna mai zuwa a duniya.
Saboda haka, mahalli na Wahayin Yahaya 7:4 da furci game da shi da ke cikin wani waje a Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa adadi 144,000 na zahiri ne. Yana nuni ga waɗanda za su yi sarauta da Kristi a sama bisa aljanna ta duniya, da za ta cika da mutane masu farin ciki babu iyaka da suke bauta wa Jehovah Allah.—Zabura 37:29.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani a kan Shekara Dubu na Sarautar Kristi, ka duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand! shafofi na 289-290, da Shaidun Jehovah suka buga.
[Blub on page 321]
Adadin magadan samaniya 144,000 ne kawai
[Hoto a shafi na 31]
“Ƙasaitaccen taro” ba su da iyaka
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 31]
Taurari: Hoton Anglo-Australian Observatory da Davin Malin ya ɗauka