Ta Yaya ‘Masu Tawali’u Za Su Gaji Duniya?’
“ƘILA kana sane da kalmomin Yesu masu daɗaɗa zuciya cewa “masu tawali’u . . . za su gaji duniya.” Amma domin dukan abin da mutane suke yi wa juna da kuma duniya, menene kake tsammani zai rage da masu tawali’u za su gāda?”—Matiyu 5:5; Zabura 37:11.
Myriam Mashaidiyar Jehovah ta yi amfani da wannan tambayar ta soma taɗi daga Littafi Mai Tsarki. Mutumin da take wa magana ya amsa cewa idan Yesu ya yi wannan alkawari, yana nufin duniya ta cancanci a gāje ta, kuma ba wurin da aka ragargaje ba ne ko kuma kango da ba a zama a ciki.
Wannan babu shakka amsa ce mai kyau. Amma muna da dalilin kasance da irin wannan ra’ayi mai kyau kuwa? Hakika, gama Littafi Mai Tsarki ya ba mu ƙarfafan dalilai mu gaskata cewa alkawarin zai cika. Cikar alkawarin yana da nasaba ta kusa da nufin Allah don ’yan Adam da kuma duniya. An tabbatar mana cewa Allah zai cika nufe-nufensa. (Ishaya 55:11) To, menene nufin Allah na asali game da ’yan Adam, kuma yaya zai cika?
Madawwamin Nufin Allah Game da Duniya
Jehovah Allah ya halicce duniya don takamaiman nufi. “Ubangiji ne ya halicci sammai, Shi ne wanda yake Allah! Shi ne ya shata duniya ya kuma yi ta, Ya kafa ta, ta kahu da ƙarfi, za ta yi ƙarƙo! Bai halicce ta hamada da ba kome a ciki ba, amma wurin zaman mutane. Shi ne wanda ya ce, ‘Ni ne Ubangiji, ba kuwa wani Allah, sai ni.” (Ishaya 45:18) Saboda haka an halicce duniya musamman don mutane su zauna a ciki. Ƙari ga haka, nufin Allah ne duniya ta zama madawwamin gidan ’yan Adam. Ya “sa duniya ta kahu sosai a bisa harsashin gininta, ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.”—Zabura 104:5; 119:90.
An ga nufin Allah game da duniya a aikin da ya ba mutane biyu na farko. Jehovah ya ce wa Adamu da Hauwa’u: “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da ke da rai da ke kai da kawowa cikin duniya.” (Farawa 1:28) Duniya da Allah ya danƙa wa Adamu da Hauwa’u za ta zama musu da ’ya’yansu gida madawwami. Mai Zabura ya sanar ƙarnuka da yawa bayan haka: “Samaniya ta Ubangiji ce kaɗai, amma ya ba mutane duniya.”—Zabura 115:16.
Don su kasance da irin wannan zato mai girma, Adamu da Hauwa’u da kuma ’ya’yansu dole kowannensu ya amince cewa Jehovah Allah, Mahalicci Mai Ba da Rai ne, Mamallakinsu ne kuma su yi masa biyayya. Jehovah ya yi bayani filla-filla game da wannan sa’ad da ya ba mutumin wannan umurni: “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace da ke gonar, amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.” (Farawa 2:16, 17) Domin Adamu da Hauwa’u su ci gaba da zama a gonar Aiden, dole ne su yi biyayya da wannan umurni mai sauƙi da ke a bayyane. Yin hakan zai nuna suna godiya ga dukan abin da Uba na samaniya ya yi musu.
Sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah rashin biyayya da gangan ta taka umurni da aka ba su, sun ƙi da wanda ya yi musu tanadin kome da suke da shi. (Farawa 3:6) Don haka suka yi hasarar kyakkyawan gidansu na Aljanna ba don kansu kawai ba amma don ’ya’yansu. (Romawa 5:12) Rashin biyayyar ma’aurata na farko ya canja nufin Allah ne game da duniya?
Allah da Ba Ya Sakewa
Ta wurin annabinsa Malakai, Allah ya sanar: “Ni ne Ubangiji, ba na sākewa.” (Malakai 3:6) Da yake magana game da wannan ayar, manazarcin Littafi Mai Tsarki na yaren Faransa, L. Fillion ya lura cewa wannan sanarwa tana da nasaba ta kusa da cikar alkawuran Allah. “Da Jehovah ya halaka mutanensa masu tawaye,” in ji Fillion, “amma da yake ba ya sakewa game da alkawuransa, ko da menene ya faru zai cika alkawura da ya yi dā.” Allah ba zai manta da alkawuransa ga mutane ɗaiɗai, al’umma, ko kuma dukan mutane ba, amma zai yi su a nasa lokaci. “Zai cika alkawarinsa har abada, alkawaransa kuma don dubban zamanai.”—Zabura 105:8.
Ta yaya za mu tabbata cewa Jehovah bai canja nufinsa na asali ba game da duniya? Za mu tabbata da wannan domin a duk cikin hurarriyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, an ambata nufin Allah ya ba wa mutane masu biyayya duniya. (Zabura 25:13; 37:9, 22, 29, 34) Ƙari ga haka, Nassosi ya kwatanta waɗanda Jehovah ya albarkace su da zama cikin kwanciyar hankali, kowanne yana zaune a “gindin ɓaurensa, ba wanda zai tsoratar da shi.” (Mika 4:4; Ezekiyel 34:28) Waɗanda Jehovah ya zaɓa “za su gina gidaje su kuwa zauna a cikinsu, ba waɗansu dabam za su mori gidajen ba. Za su dasa gonakin inabi su kuwa ji daɗin ruwan inabi, ba waɗansu dabam za su sha shi ba.” Za su more salama har da dabbobin jeji.—Ishaya 11: 6-9; 65:21, 25.
Littafi Mai Tsarki ya ba da hoton alkawarin Allah a wata hanya. A lokacin sarautar Sarki Sulemanu, al’ummar Isra’ila ta more salama da kwanciyar hankali. A lokacin sarautarsa, “Mutanen Yahuza da na Isra’ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.” (1 Sarakuna 4:25) Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya “fi Sulemanu,” kuma da yake magana game da sarautarsa, mai Zabura cikin annabci ya sanar: “Adalci ya bunƙasa a zamaninsa, wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.” A lokacin, za a “sami hatsi mai yawa a ƙasar, da ma amfanin gona ya cika tuddan.”—Luka 11:31; Zabura 72:7, 16.
Don ya cika maganarsa, Jehovah Allah zai tabbata cewa ba kawai za a sami gadō da ya yi alkawarinsa ba amma za a maido da dukan ɗaukakarsa. A Wahayin Yahaya 21:4, Kalmar Allah ta gaya mana cewa a sabuwar duniya da aka yi alkawarinta, Allah ‘zai share dukkan hawayen [mutane]. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.’ Hakika abin da aka yi alkawarinsa zai zama Aljanna.—Luka 23:43.
Yadda Za a Sami Gadō da Aka Yi Alkawarinsa
Za a mai da duniya zuwa aljanna a mulkin da ke shugabanci daga sama, Mulkin da Yesu Kristi ne Sarkinsa. (Matiyu 6:9, 10) Na farko, wannan Mulkin zai “hallaka masu hallaka duniya.” (Wahayin Yahaya 11:18; Daniyel 2:44) Sa’an nan, da yake shi “Sarkin Salama” ne Yesu Kristi zai cika wannan kalmomin annabci: “Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin.” (Ishaya 9:6, 7) A wannan Mulkin, miliyoyin mutane har da waɗanda za a maido su zuwa rai ta wurin tashin matattu za su sami zarafin zama a duniya.—Yahaya 5:28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15.
Su wanene za su more wannan gadō na ban al’ajabi? Ka yi la’akari da kalmomin Yesu: “Albarka tā tabbata ga masu tawali’u, domin za su gaji duniya.” (Matiyu 5:5) Menene yake nufi kada a kasance da tsanani, ko a kasance da tawali’u? Ƙamus ya ba da ma’anar “tawali’u,” ko “rashin tsanani,” cewa ladabi da biyayya ne. Amma kalmar Helenanci na asali tana nufin fiye da haka. Littafin nan New Testament Wordbook na William Barclay ya ce: “Mai hankali yana da ikon ɗabi’a.” Yana nufin hankali da ke taimaka wa mutum ya jimre wa azaba ba tare da ƙiyayya ba ko ya yi ramako, domin dangantaka mai kyau da Allah, kuma wannan dangantaka ta zama masa tushen samun ƙarfi.—Ishaya 12:2; Filibiyawa 4:13.
Mai tawali’u yana amince da mizanan Allah a dukan fannonin rayuwarsa; ba ya nace wa ra’ayinsa ko kuma ya bi ra’ayin wasu mutane. Ana iya koyar da shi, yana shirye Jehovah ya koyar da shi. Mai zabura Dawuda ya rubuta: “[Jehovah] yana bi da masu tawali’u a tafarkin da ke daidai, yana koya musu nufinsa.”—Zabura 25:9; Karin Magana 3:5, 6.
Za ka kasance cikin “masu tawali’u” da za su zauna a duniya? Ta sanin Jehovah da nufinsa ta wurin nazarin Kalmarsa sosai da yin amfani da abin da ka koya, kai ma za ka yi sauraron zama a cikin aljanna ta duniya kuma ka zauna har abada a cikinta.—Yahaya 17:3.
[Hoto a shafi nas 4, 5]
Salama da kwanciyar rai na sarautar Sulemanu ya nuna hoton gadō da aka yi alkawarinsa
[Inda aka Daukos]
Tumaki da tudu na baya: Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.; Arabian oryx: Hai-Bar, Yotvata, Israel; manomi da ke huɗa: Garo Nalbandian
[Hoto a shafi na 5]
Sabuwar duniya ta adalci na nan gaba—za ka kasance a wurin?