Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 11/1 pp. 8-13
  • Akwai Dalilin Da Zai Sa Ka Yi Begen Aljanna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwai Dalilin Da Zai Sa Ka Yi Begen Aljanna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wahayi na Aljanna
  • Mutanen da Aka Maido Aka Inganta
  • Ka Ƙarfafa Ra’ayinka na Aljanna
  • “Sai Mun Haɗu a Aljanna!”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Kada Ka Daina Bauta wa Jehobah Tare da Mutanensa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Yi Aiki don Kyautata Yanayin Salama da Muke Mora
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • A Ina Aljannar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Take?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 11/1 pp. 8-13

Akwai Dalilin Da Zai Sa Ka Yi Begen Aljanna?

“Na san wani mutum wanda . . . bisa ga ikon Almasihu . . . an ɗauke shi zuwa Firdausi [Aljanna].”—2 KORANTIYAWA 12:2-4.

1. Waɗanne alkawura na Littafi Mai Tsarki ne ke ba mutane da yawa sha’awa?

ALJANNA. Ka tuna yadda ka ji sa’ad da ka fara jin alkawarin da Allah ya yi na aljanna a nan duniya? Ka tuna sa’ad da ka koyi cewa ‘makaho zai iya gani, kurma zai ji magana, kuma rafufukan ruwa za su yi gudu cikin hamada’ da gwanin sha’awa. Annabcin kyarkeci da tumaki da kuma damisa fa? Ba abin sha’awa ba ne sa’ad da ka karanta cewa ƙaunatattu da suka mutu za a ta da su zuwa aljanna a duniya da za a maido?—Ishaya 11:6; 35:5, 6; Yahaya 5:28, 29.

2, 3. (a) Me ya sa za a iya cewa begenka da ke bisa Littafi Mai Tsarki ba marar tushe ba ne? (b) Wane ƙarin dalili na bege muke da shi?

2 Begenka yana da makama. Kana da dalili na kasancewa da tabbaci game da alkawuran da Littafi Mai Tsarki ya yi game da Aljanna. Alal misali, kana da tabbaci a kalmomin Yesu ga mugu da aka rataye: “Za ka kasance tare da ni a Firdausi [Aljanna].” (Luka 23:43) Ka gaskata alkawarin nan: “Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin sammai da sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zamansa.” Kuma ka gaskata da alkawarin da Allah ya yi na share dukan hawayen mu, ba kuma sauran mutuwa, baƙin ciki, kuka, da kuma azaba, duk za su wuce. Wannan yana nufin cewa aljanna za ta sake kasancewa!—2 Bitrus 3:13; Wahayin Yahaya 21:4.

3 Amma wani dalilin kuma na wannan begen Aljanna shi ne wani abu da duka Kiristoci a duk duniya suke ciki a yanzu. Menene wannan? Allah ya kafa aljanna ta ruhaniya kuma ya shigar da mutanensa ciki. Furcin nan “aljanna ta ruhaniya” zai kasance baɗani ko kuma mai wuyan fahimta, amma an annabta wannan aljanna, kuma ta wanzu.

Wahayi na Aljanna

4. Wane wahayi ne 2 Korantiyawa 12:2-4 ya ambata, waye wataƙila ya gan shi?

4 Game da wannan, ka lura da abin da manzo Bulus ya rubuta: ‘Na san wani mutum wanda . . . aka ɗauke shi zuwa sama ta uku bisa ga ikon Almasihu—ko yana cikin jiki ne, ko ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani. Na kuma san mutumin nan, an ɗauke shi zuwa Firdausi [Aljanna]—ko yana cikin jiki ne, ko ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani—ya kuma ji waɗansu maganganu, waɗanda ba dama a faɗa, irin ma waɗanda ɗan adam ba shi da iznin faɗa.’ (2 Korantiyawa 12:2-4) Wannan ayar ta bi bayan ayoyin da Bulus ya kāre manzancinsa a ciki ne. Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki bai ambata wani mutum da aka ɗauke zuwa sama ba, Bulus ne ya gaya mana. Yana yiwuwa cewa Bulus ne ya ga wannan wahayin. Sa’ad da Jehovah ya nuna masa wannan wahayin, wane “firdausi” [aljanna] ne ya shiga?—2 Korantiyawa 11:5, 23-31.

5. Menene Bulus ya gani, kuma wane irin “firdausi” [aljanna] ne?

5 Ba wai wannan matanin na nuna cewa “sama ta uku” na nufin sararin duniya, ko kuma wata duniya ba ce. Sau da yawa, Littafi Mai Tsarki na amfani da adadi uku domin ya nuna nanaci, ƙarfi, ko iko. (Mai Hadishi 4:12; Ishaya 6:3; Matiyu 26:34, 75; Wahayin Yahaya 4:8) Da haka, abin da Bulus ya gani a wahayin mafifici ne. Na ruhaniya ne.

6. Wane aukuwa na tarihi ne ya ba da fahimi a kan abin da Bulus ya gani?

6 Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki na farko sun ba mu fahimi. Bayan mutanensa na dā sun yi masa rashin aminci, Allah ya ƙudurta cewa zai bar ’yan Babila su zo su yaƙi Yahuda da kuma Urushalima. Hakan ya jawo halaka a shekara ta 607 K.Z., bisa ga tarihin Littafi Mai Tsarki. Annabcin ya faɗi cewa ƙasar za ta zama kango har tsawon shekara 70; bayan haka Allah zai ƙyale Yahudawa da suka tuba su dawo su maida sujada ta gaskiya. Hakan ya faru daga shekara ta 537K.Z., zuwa gaba. (Maimaitawar Shari’a 28:15, 62-68; 2 Sarakuna 21:10-15; 24:12-16; 25:1-4; Irmiya 29:10-14) Ƙasar kuma fa? Cikin shekaru 70, ta zama daji, ƙasar ta tsastsage, ta zama wajen zaman diloli. (Irmiya 4:26; 10:22) Duk da an yi wannan alkawarin: “Zan [Jehovah] ji juyayi a kan Sihiyona, da dukan masu zama a kufanta. Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu, kamar lambun da na dasa a Aidan [ko aljanna].”—Ishaya 51:3.

7. Menene zai faru bayan halaka ta shekaru 70?

7 Hakan ya faru bayan shekaru 70. Tare da albarkar Jehovah, yanayin sun yi kyau. Ka zana wannan a zuciyarka: “Hamada za ta yi farin ciki. Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani. Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna. . . . Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa, waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna. Rufuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada, yashi mai ƙuna kuma zai zama tafki, ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za ta cika da maɓuɓɓugai. Inda diloli suka yi zama, ciyawar fadama da iwa za su tsiro.”—Ishaya 35:1-7.

Mutanen da Aka Maido Aka Inganta

8. Ta yaya muka sani cewa Ishaya sura ta 35 tana magana ne game da mutane?

8 Hakika wannan canji ne! Daga halaka zuwa aljanna. Kamar ƙasar da ta zama kango a dā kuma ta zama mai ni’ima, haka wannan da sauran tabbataccen annabce-annabce suka nuna cewa za a samu canji a mutane. Me ya sa muka ce haka? Domin Ishaya ya mai da hankali ne ga waɗanda “Ubangiji ya fansa” da za su komo ƙasarsu da “murna” kuma za su yi “farin ciki.” (Ishaya 35:9, 10) Wannan ba ya nuni ga ƙasar, amma ga mutane. A wata sassa kuma Ishaya ya annabta game da mutanen da aka maido Sihiyona: “Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kamar yadda iri yakan tsiro ya yi girma. . . . Dukkan al’ummai kuwa za su yi yabonsa.” Ishaya ma ya ce game da mutanen Allah: “[Jehovah zai] bi da ku kullayaumin . . . , [ya] sa ƙasusuwanku su yi ƙarfi, ku zama kamar lambun da ake yi masa banruwa.” (Ishaya 58:11; 61:3, 11; Irmiya 31:10-12) Saboda haka, kamar yadda yanayin ƙasa za ta ƙara kyau, za a sami canji a mutanen Yahudawa da za a maido.

9. Wane “firdausi” [aljanna] ne Bulus ya gani, kuma yaushe wahayin ya cika?

9 Yanayin tarihin ya taimaka mana mu fahimci abin da Bulus ya gani a wahayinsa. Wannan ya haɗa da ikilisiyar Kirista wadda ya kira, “gona ce ta Allah” kuma wadda za ta ba da amfani. (1 Korantiyawa 3:9) Yaushe ne wannan wahayin zai cika? Bulus ya kira abin da ya gani ‘wahayi,’ wani abu da zai faru nan gaba. Ya san cewa bayan mutuwarsa, waɗanda suka fanɗare za su taso. (2 Korantiyawa 12:1; Ayyukan Manzanni 20:29, 30; 2 Tasalonikawa 2:3, 7) Ba za a iya kwatanta Kiristoci na gaskiya da lambun da ke da ni’ima ba sa’ad da ’yan fanɗarewa suka fi ƙarfinsu kuma suka ci nasara a kansu ba. Duk da haka, lokaci na zuwa da za a sake ɗaukaka ibada ta gaskiya. Za a maido da mutanen Allah saboda ‘masu adalci su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu.’ (Matiyu 13:24-30, 36-43) Hakan ya faru bayan ’yan shekaru sa’ad da aka kafa Mulkin Allah a sama. Kuma bayan shekaru da yawa, an ga cewa mutanen Allah sun mori aljanna ta ruhaniya wadda Bulus ya gani a wahayi.

10, 11. Duk da cewa mu ajizai ne, me ya sa za mu iya cewa muna cikin aljanna ta ruhaniya?

10 Hakika, mun san mu ajizai ne, saboda haka ba abin mamaki ba ne cewa wani lokaci matsaloli sukan taso a tsakaninmu, yadda ya faru a tsakanin Kiristoci a kwanakin Bulus. (1 Korantiyawa 1:10-13; Filibiyawa 4:2, 3; 2 Tasalonikawa 3:6-14) Amma dai, ka yi tunanin aljanna ta ruhaniya da muke mora yanzu. Idan aka gwada da yanayin rashin lafiya na ruhaniya da dā muke ciki, an warkar da mu a ruhaniya. Ka bambanta yanayinmu na yunwa a dā da kuma abinci na ruhaniya da muke mora yanzu. Maimakon fama kamar muna zaune a cikin busashiyar ƙasa ta ruhaniya, mutanen Allah sun sami yardarsa da kuma albarka. (Ishaya 35:1, 7) Maimakon kasancewa kamar cikin kurkuku marar haske na ruhaniya, mun sami hasken ’yanci da kuma tagomashin Allah. Waɗanda ba su taɓa jin annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki ba, sun zo domin su saurara kuma su fahimci abin da Nassosi suka ce. (Ishaya 35:5) Alal misali, miliyoyin Shaidun Jehovah a kewayen duniya sun yi nazarin littafin nan Daniel’s Prophecy (Annabcin Daniyel), aya aya. Bayan haka kuma sun yi nazarin kowace sura na littafin Ishaya na Littafi Mai Tsarki. Wannan abinci na ruhaniya mai wartsakewa ba tabbacin aljannarmu ta ruhaniya ce ba?

11 Ka yi tunanin canje-canje a halayen mutane na ƙabilai dabam dabam da suke ƙoƙarin fahimtar da yin amfani da Kalmar Allah. Waɗanda sun riga sun kawar da halaye irin na dabba da suke da shi a dā. Wataƙila kai ma ka yi hakan, kuma ka sami sakamako mai kyau, haka nan ma ’yan’uwanka maza da mata na ruhaniya suka yi. (Kolosiyawa 3:8-14) Saboda haka, sa’ad da kake cuɗanya da ikilisiyar Shaidun Jehovah, kana tare ne da mutane masu salama da suke da halaye masu kyau. Ko da yake ba kamiltattu ba ne, duk da haka, ba a kiransu zakuna ko mugayen namomin daji. (Ishaya 35:9) Menene wannan zumunci na ruhaniya mai ban al’ajabi ke nunawa? Hakika, muna morar yanayi ne da muke kira aljanna ta ruhaniya. Kuma aljannarmu ta ruhaniya alama ce ta aljanna ta duniya da za mu mora idan muka kasance da aminci ga Allah.

12, 13. Menene za mu yi idan muna so mu kasance a cikin aljannarmu ta ruhaniya?

12 Duk da haka, akwai wani abu da ya kamata mu tuna. Allah ya gaya wa ’yan Isra’ila: “Ku kiyaye dukan umarnan da na umarce ku da su yau domin ku sami ƙarfin da za ku haye, ku shiga, ku ci ƙasar.” (Maimaitawar Shari’a 11:8) A Littafin Firistoci 20:22, 24, an sake ambatar wannan ƙasar: “Ku kiyaye dokokina duka, da ka’idodina duka, ku kuma aikata su domin kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku. Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. ” Hakika, mallakar Ƙasar Alkawari ya dangana ne a kan dangantaka mai kyau da Jehovah Allah. Domin Isra’ilawa sun ƙi su yi wa Allah biyayya shi ya sa ya ƙyale Babiloniyawa suka ƙwace kuma cire su daga ƙasarsu.

13 Akwai abubuwa masu yawa da ke ba mu sha’awa game da aljannarmu ta ruhaniya. Mahallin yana da kyaun gani kuma yana kwantar da hankali. Akwai salama tsakaninmu da Kiristoci waɗanda sun riga sun kawar da halaye irin na dabba da suke da shi dā. Suna ƙoƙarin su zama masu kirki da ban taimako. Duk da haka, kasancewa a cikin aljannarmu ta ruhaniya na bukatar fiye da kasance da dangantaka mai kyau da mutanen nan. Tana bukatar kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehovah da kuma yin nufinsa. (Mika 6:8) Mun shiga wannan aljanna ta ruhaniya don son ranmu ne, amma muna iya sulluɓewa ko kuwa a cire mu idan ba mu kiyaye dangantakarmu da Allah ba.

14. Menene zai taimaka mana mu kasance a cikin aljanna ta ruhaniya?

14 Abu mafi muhimmanci da zai taimaka mana shi ne ci gaba da samun ƙarfafa daga Kalmar Allah. Ka lura da yaren alama da ke Zabura 1:1-3: “Albarka ta tabbata ga mutumin da ba ya karɓar shawarar mugaye . . . Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari’ar Allah, yana ta nazarinta dare da rana. Yana kama da itacen da ke a gefen ƙorama, yakan ba da ’ya’ya a kan kari, ganyayensa ba sa yin yaushi, yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.” Ƙari ga haka, littattafan Littafi Mai Tsarki na amintaccen bawan nan mai hikima suna ba da abinci na ruhaniya a aljanna ta ruhaniya.—Matiyu 24:45-47.

Ka Ƙarfafa Ra’ayinka na Aljanna

15. Me ya sa Musa bai iya ja-goran Isra’ilawa zuwa Ƙasar Alkawari ba, amma menene ya gani?

15 Yi la’akari da wani hoton Aljanna. Bayan da Isra’ila ta yi tafiya cikin jeji na shekara 40, Musa ya ja-goranci mutanensa zuwa Filin Mowab, gabashin Kogin Urdun. Domin kasawar Musa, Jehovah ya ce Musa ba zai ja-goranci Isra’ila zuwa ƙetaren Urdun ba. (Littafin Ƙidaya 20:7-12; 27:12, 13) Musa ya roƙi Allah: “Ka yarje mani, ina roƙonka in haye in ga wannan kyakkyawar ƙasa a hayin Urdun.” Ko da ba zai shiga ba, bayan ya hau Dutsen Fisga da ya ga yankuna dabam dabam na ƙasar, Musa ya san cewa “kyakkyawar ƙasa” ce. Yaya kake tunani ƙasar take?—Maimaitawar Shari’a 3:25-27.

16, 17. (a) Ta yaya ne Ƙasar Alkawari ta dā ta bambanta da ta yanzu? (b) Me ya sa za mu yarda cewa Ƙasar Alkawari ta dā ta yi kama da aljanna?

16 Idan ra’ayinka bisa yadda yankin yake ne a yanzu, za ka iya tunanin busashiyar ƙasa ta yashi, hamada mai duwatsu, kuma mai zafi. Amma, akwai dalilin da zai sa a kammala cewa dukan yankin dabam yake a lokacin Littafi Mai Tsarki. A jaridar Scientific American, Dokta Walter C. Lowdermilk, masani a batun ruwa da ƙasa ya bayyana cewa “an ɓata ƙasar na shekaru dubu.” Wannan masanin kimiyyar noma ya rubuta: “ ‘Hamada’ da ta sake ƙasa mai ni’ima ta dā ɗin nan aikin ’yan Adam ne, ba yadda yake ba.” Hakika, bincikensa ya nuna cewa “wannan ƙasar dā yankin aljanna ce.” Hakan ya nuna cewa ’yan Adam sun ɓata abin da dā “aljanna ce wurin kiwo.”a

17 Idan ka yi tunani a kan abubuwan da ka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki, za ka ga cewa wannan maganar daidai ne. Ka tuna tabbacin da Jehovah ya ba mutanen ta wurin Musa: “Ƙasar da za ku haye ku mallaka, ƙasa ce ta tuddai da kwarurruka wadda ruwan sama ke shayar da ita. Ƙasa ce kuma wadda Ubangiji Allahnku ke lura da ita.”—Maimaitawar Shari’a 11:11, 12.

18. Ta yaya ne wataƙila Ishaya 35:2 ya nuna wa Isra’ilawa da suka je bauta yadda kamanin Ƙasar Alkawari za ta kasance?

18 Idan aka ambata gwanin kyau da ni’ima na wasu wurare na Ƙasar Alkawari hakan na kawo yanayin aljanna a zuciya. Wannan ya bayyana sarai daga annabcin da ke Ishaya sura 35, wadda ta samu cikanta ta farko sa’ad da Isra’ilawa suka dawo daga Babila. Ishaya ya annabta: “Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna, za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon, da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon. Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah, ya ga girmansa da ikonsa.” (Ishaya 35:2) Yadda aka ambata Carmel, Lebanon, da kuma Sharon, babu shakka ya nuna wa Isra’ilawa kamanin ƙasar.

19, 20. (a) Ka kwatanta wuraren Sharon na dā. (b) Wace hanya ɗaya ce za mu iya ƙarfafa begenmu na Aljanna?

19 Yi la’akari da Sharon, iyakar filin da ke tsakanin tudun Samariya da kuma Bahar Rum. (Dubi hoto a shafi na 10.) Tana da gwanin kyau da kuma ni’ima. Wuri ne mai dausayi, da yin kiwo, amma tana da itatuwan oak a ɓangaren da ke arewacinta. (1 Tarihi 27:29; Waƙar Waƙoƙi 2:1; Ishaya 65:10) Da haka Ishaya 35:2 ta annabta maidowa da kuma ƙasa mai fure da daraja, mai kama da aljanna. Wannan annabcin kuma yana nuni ga aljanna ta ruhaniya mai ban sha’awa, da ke dangane da abin da Bulus ya gani a wahayi. A ƙarshe, wannan annabci tare da wasu sun ƙarfafa begenmu na aljanna na duniya domin ’yan Adam.

20 Sa’ad da muke zaune a cikin aljannarmu ta ruhaniya, muna iya ƙarfafa godiyarmu da kuma begenmu ga Aljanna a duniya. Ta yaya? Ta wajen ƙara fahimtar abubuwan da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Kwatancin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma annabce annabce sukan ambata wasu wurare. Za ka so ka fahimci inda wuraren nan suke sosai da kuma dangantakarsu da sauran wurare? A talifinmu na gaba, za mu tattauna yadda za ka iya yin hakan da fa’ida.

[Hasiya]

a Denis Baly a cikin littafin The Geography of the Bible ya ce: “Yanayin tsiron ƙasa sun fuskanci canje-canje masu yawa tun lokacin Littafi Mai Tsarki.” Me ya jawo hakan? “Domin ɗan Adam na bukatar itace don ya dafa abinci kuma ya yi gini, saboda haka . . . sai ya fara sare itatuwan, da haka sai ya bayyana ƙasar ga farmakin yanayi. Sakamakon wannan a mahalli shi ne, a hankali a hankali yanayi ya zama muhimmin abu wajen yin ɓarna.”

Ka Tuna?

• Wace ‘aljanna’ ce manzo Bulus ya gani a cikin wahayi?

• Game da Ishaya sura 35, menene cikarta ta farko, kuma wace dangantaka take da shi da wahayin da Bulus ya gani?

• Ta yaya za mu iya ƙarfafa godiyarmu ga aljannarmu ta ruhaniya da kuma begenmu na aljanna a duniya?

[Hoto a shafi na 10]

Filin Sharon, wuri mai ni’ima a Ƙasar Alkawari

[Inda aka Dauko]

Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.

[Hoto a shafi na 12]

Musa ya gane cewa “kyakkyawar ƙasa” ce

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba