Ka Kasance Da Daidaitaccen Ra’ayi Game Da Shan Giya
“Ruwan inabi da barasa sukan sa ka ka yi ta tā da murya, ka zama wawa. Wauta ce mutum ya bugu.”—KARIN MAGANA 20:1.
1. Ta yaya ne mai zabura ya nuna godiya wa kyauta masu kyau daga Jehovah?
ALMAJIRI Yakubu ya rubuta cewa: “Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki.” (Yakubu 1:17) Mai zabura ya motsa ya yi godiya domin kyauta masu kyau daga Allah, ya rera: “Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu, tsire-tsire kuma don amfanin mutum, saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona, don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki, ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara’a, da abincin da zai ba shi ƙarfi.” (Zabura 104:14, 15) Kamar ciyawa, abinci, da māi, ruwan inabi kyauta ce mai kyau daga Allah. Amma yaya ya kamata mu yi amfani da shi?
2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna game da yin amfani da giya?
2 Kyauta mai kyau na da daɗi sa’ad da aka yi amfani da ita a hanyar da ta dace. Alal misali, zuma na “da kyau” amma “shan zuma da yawa ba shi da kyau.” (Karin Magana 24:13; 25:27) Ko da yake an yarda a sha “ruwan inabi kaɗan,” yin maye matsala ne mai tsanani. (1 Timoti 5:23) Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Ruwan inabi da barasa sukan sa ka ka yi ta tā da murya, ka zama wawa. Wauta ce mutum ya bugu.” (Karin Magana 20:1) Menene ma’anar yin maye?a Me za a iya cewa shi ne yin maye? Menene daidaitaccen ra’ayi a wannan batu?
Ta Yaya Ake ‘Buguwa’ da Giya?
3, 4. (a) Menene ya nuna cewa Littafi Mai Tsarki ya hana shan giya a bugu? (b) Menene alamun buguwa?
3 A Isra’ila ta dā, ana jifan ɗa da gagararre ne, mashayi mai zarin ci. (Maimaitawar Shari’a 21:18-21) Manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci: “Kada ku [yi] cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan’uwa, mai bi, in yana fasiki, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.” Lallai kuwa, Nassosi sun haramta yin maye.—1 Korantiyawa 5:11; 6:9, 10.
4 Sa’ad da yake kwatanta alamu na yin maye, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, ko da ya ke ja wur yake, har kana iya ganin kanka a cikin ƙoƙon, yana kuwa da kyan gani sa’ad da kake motsa shi. Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka. Idanunka za su riƙa gane-gane, ba za ka iya tunani ko ka faɗi magana sosai ba.” (Karin Magana 23:31-33) Yin maye na kama ne da saran maciji mai dafi, yana jawo rashin lafiya, yana ɗimauce hankali, har da fita hayyaci. Mai yin maye yana iya “gane-gane.” Kuma hakan na iya sa shi ya yi ta furta maganganun da ba su dace ba, da kuma sha’awar da ba ta dace ba, da ba zai yi ba a cikin hankalinsa.
5. A wace hanya ce yawan shan giya ke da lahani?
5 Idan mutum ya saba da shan giya amma kuma yana mai da hankali domin kada wasu su fahimci cewa yana maye fa? Wasu sukan nuna alamar buguwa kaɗan bayan sun sha giya mai yawa. Amma fa, yin tunanin cewa hakan ba shi da lahani ruɗin kai ne. (Irmiya 17:9) A hankali a hankali, mutum yana iya dogara ga giya kuma ya zama mai “jarabar giya.” (Titus 2:3) Game da yadda mutum yake zama mashayi, mawallafiya Caroline Knapp ta ce: “Sannu a hankali ake zama mashayi.” Yin maye mugun tarko ne!
6. Me ya sa ya kamata mutum ya guje wa yawan shan giya da zarin ci?
6 Ka yi la’akari da gargaɗin Yesu: “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko. Don haka za ta aukar wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa.” (Luka 21:34, 35) Ba sai shan giya ya kai ga yin maye ba kafin ya mai da mutum rago ko mai gyangyaɗi a zahiri da kuma a ruhaniya. Idan ranar Jehovah ta kama mutum a cikin wannan yanayin fa?
Abin da Yin Maye Ke Iya Jawowa
7. Me ya sa yawan shan giya bai jitu da umurnin da ke 2 Korantiyawa 7:1 ba?
7 Yawan shan giya na jawo wa mutum haɗarurruka masu yawa—na ruhaniya da na jiki. Wasu cikin cututtukan da yin maye ke jawowa sune cututtukan hanta, da kuma taɓin hankali kamar sambatu. Kasancewa mashayi na dogon lokaci na iya jawo ciwon daji, ciwon sukari, da kuma cututtukan zuciya da na ciki. Yin maye bai jitu da ja-gorar Nassi ba: “Mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta cikin tsarki.”—2 Korantiyawa 7:1.
8. Menene sakamakon yawan shan giya in ji Karin Magana 23:20, 21?
8 Yin maye na jawo ɓad da kuɗi, har ma kora wajen aiki. Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā ya yi gargaɗi: “Kada ka zauna da mashayan ruwan inabi, ko masu haɗama.” Me ya sa? Ya yi bayani: “Gama bugaggu da ruwan inabi da masu zarin ci za su zama matalauta. Idan iyakar abin da kake yi daga ci sai barci ne, nan da nan za ka ga kana saye da tsummoki.”—Karin Magana 23:20, 21.
9. Me ya sa yake da muhimmanci kada ka sha giya idan za ka tuƙa mota?
9 Sa’ad da yake nuni ga wani haɗari, littafin nan The Encyclopedia of Alcoholism ya ce: “Bincike ya nuna cewa giya na rage iya tuƙi, mai da hankali, da gani.” Sakamakon yin tuƙi sa’ad da mutum ya yi maye na da haɗari. A ƙasar Amirka kaɗai, kowace shekara dubbai suna mutuwa kuma fiye da dubu ɗari suna samun rauni wajen haɗari domin maye. Matasa musamman sukan faɗa cikin wannan haɗari da sauƙi, domin ba su saba da tuƙi da shan giya ba. Wanda ya sha giya mai yawa kuma ya ce zai yi tuƙi, zai iya cewa yana daraja kyautar rai daga Jehovah Allah? (Zabura 36:9) Domin rai na da tsarki, zai fi dacewa kada mutum ya sha giya sa’ad da zai ko za ta yi tuƙi.
10. Ta yaya ne giya za ta iya shafan hankalinmu, kuma me ya sa hakan ke da haɗari?
10 Yawan shan giya yana jawo wa mutum ciwo na jiki da kuma na ruhaniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ruwan inabin da bai sa hauka ba [ya] kan kawar da hankali.” (Yusha’u 4:11) Giya na shafan hankalin mutum. “Sa’ad da mutum ya sha giya,” in ji mujallar nan National Institute on Drug Abuse ta Amirka, “giya na bin inda abinci ke narkewa zuwa cikin jijiyar jini, nan da nan sai ta shiga cikin ƙwaƙwalwa. Daga nan sai ta fara rage sashen yin tunani da jiye-jiye da ke cikin ƙwaƙwalwa. Daga bisani mutumin sai ya kasa kame kai.” A cikin irin wannan yanayi, muna iya “zama wawa,” muna iya yin abin da bai dace ba ga wani, kuma yana iya sa mu faɗā wa jaraba cikin sauƙi.—Karin Magana 20:1.
11, 12. Waɗanne haɗari na ruhaniya ne yawan shan giya ke iya jawowa?
11 Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya umurta: “Duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.” (1 Korantiyawa 10:31) Shan giya mai yawa yana sa a ɗaukaka Allah ne? Kirista ba zai so ya yi suna wajen shan giya mai yawa ba. Irin wannan suna zai jawo kunya ga ɗaukakar Jehovah da sunansa.
12 Idan rashin daidaita na shan giya na wani Kirista ya jawo tuntuɓe ga ɗan’uwa mai bi, wataƙila sabon almajiri ne fa? (Romawa 14:21) Yesu ya yi gargaɗi: “Duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi [tuntuɓe], zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyansa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.” (Matiyu 18:6) Yin maye na iya hana mutum wasu gata a cikin ikilisiya. (1 Timoti 3:1-3, 8) Kuma abin da ba za a manta ba shi ne matsalar da yin maye ke iya jawowa a cikin iyali.
Ta Yaya Za a Guje Wa Haɗarin?
13. Menene muhimmancin ƙin shan giya da yawan?
13 Abin da zai taimaka a guje wa haɗarin yin maye shi ne, ba wai sanin bambancin da ke tsakanin shan giya da yawa da buguwa ba, a’a, amma sanin bambanci da ke tsakanin daidaita da kuma sha da yawa. Waye ne ya kamata ya gaya maka yawan giyar da za ka sha, da za ta iya sa ka maye? Tun da yake hakan ya shafi abubuwa da yawa, babu doka mai tsanani game da iyakar giya da ke da yawa. Ya kamata kowa ya san cikinsa kuma kada ya wuce hakan. Menene zai taimaka maka ka san giyar da za ta yi maka yawa? Akwai ƙa’idar da za ta yi maka ja-gora?
14. Wace ƙa’ida ce za ta taimaka maka ka san bambancin buguwa da daidaita?
14 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka riƙe hikimarka da basirarka. . . . Za su tanada maka rai, rai mai daɗi da farin ciki.” (Karin Magana 3:21, 22) Ƙa’idar da ya kamata ka bi, ita ce: Duk yawan giyar da ka sha da ta dami hankalinka da tunaninka, ta wuce kima ke nan a gareka. Saboda haka, ya rage gareka ka san cikinka!
15. A waɗanne irin yanayi ne zai fi kyau kada mutum ya sha giya?
15 A wasu yanayi, zai fi kyau ma kada ka sha. Mace mai ciki tana iya cewa ba za ta sha giya ba domin illa da za ta iya yi wa ɗan tayin. Kuma ba zai fi dacewa ba idan muka ƙi shan giya a gaban wanda yin maye ya taɓa zama matsala ko kuma wanda ba ya son giya domin lamirinsa? Jehovah ya umurci waɗanda suke hidimar firist a haikalin zama: “Kada . . . ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa’ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu.” (Littafin Firistoci 10:8, 9) Saboda haka, kada ka sha giya kafin ka halarci tarurruka na Kirista ko kuma sa’ad da kake hidimar fage ko sa’ad da kake kula da wasu ayyuka na ruhaniya. Bugu da ƙari, a ƙasashen da aka hana ko aka ka’ide shekaru da mutum zai kai kafin ya sha giya, zai dace a bi dokokin waɗannan ƙasashe.—Romawa 13:1.
16. Ta yaya ne za ka yanke shawarar abin da za ka yi idan aka ajiye giya a gabanka?
16 Sa’ad da aka ajiye giya a gabanka, ka tambayi kanka: ‘Ya kamata in sha kuwa?’ Idan ka yanke shawarar za ka sha, ka san cikinka kuma kada ka wuce. Kada ka jarabtu domin alfarmar da aka yi maka. Kuma ka mai da hankali da giya da ake bayarwa wajen biki kamar wajen ɗaurin aure. A wasu wurare, an yarda yara su sha giya. Saboda haka, hakkin iyaye ne su faɗakar da yaransu game da yadda ake yin amfani da giya kuma su lura da yadda yaransu suke shan giya.—Karin Magana 22:6.
Kana Iya Magance Matsalar
17. Menene zai taimaka maka ka gane cewa ƙila kana da matsalar yawan shan giya?
17 Yin maye ya zame maka matsala ne? Babu shakka, idan shan giya ya zama zunubi na ɓoye, zai sha kanka wata rana. Saboda haka, ka binciki kanka sosai. Ka tambayi kanka: ‘Ina yawan shan giya fiye da dā ne? Giyar da nake sha ta fi ta dā ƙarfi ne ainu? Ina shan giya ne domin in guje wa damuwa, ko matsaloli? Wani cikin iyalina ko abokina ya nuna damuwa game da yadda nake shan giya? Shan giyar da nake yi ta jawo matsaloli a cikin iyalina? Yana yi mini wuya in bar giya na mako, wata, ko watanni? Ina ɓoye wa wasu yawan giyan da nake sha?’ Idan amsoshin tambayoyin nan e ne fa? Kada ka zama kamar mutumin da ya ‘dubi idonsa a madubi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa.’ (Yakubu 1:22-24) Ka ɗauki mataki domin ka magance matsalar. Menene za ka yi?
18, 19. Ta yaya za ka iya daina yawan shan giya?
18 Manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci: “Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha’a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu.” (Afisawa 5:18) Ka san iyakar giyan da za ta yi maka yawa, kuma ka dasa aya. Ka ƙudurta cewa ba za ka wuce hakan ba; kuma ka kame kanka. (Galatiyawa 5:22, 23) Kana da abokan da suke matsa maka ka tsoma kanka cikin maye? Ka tsare kanka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima, yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.”—Karin Magana 13:20.
19 Idan kana shan giya ne domin ka guje wa wasu matsaloli, ka mai da wa matsalar hankali sosai. Ana iya magance matsalar ta yin amfani da shawarar da ke cikin Kalmar Allah. (Zabura 119:105) Kada ka ɓata lokaci, ka nemi taimako wajen wani dattijo Kirista da ka amince da shi. Ka yi amfani da dukan tanadin da Jehovah ya yi don gina ruhaniyarka. Ka ƙarfafa dangantakarka da Allah. Ka yi addu’a a kai a kai, musamman ma game da kumamancinka. Ka roƙi Allah ya ‘gwada muradinka da tunaninka.’ (Zabura 26:2) Kamar yadda aka ambata a cikin talifi na baya, ka yi ƙoƙarin yin tafiya cikin aminci.
20. Waɗanne matakai za ka ɗauka domin ka magance matsalar yawan shan giya?
20 Idan kuma matsalar yawan shan giya ta ci gaba kuma fa, duk da ƙoƙarin da ka yi? Sai ka bi shawarar Yesu: “In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga rai dungu, da ka shiga [Jahannama] da hannu biyu.” (Markus 9:43) Amsar ita ce: Kada ka sha giya. Wannan shi ne abin da wata mata mai suna Irene ta tsai da shawarar yi. “Bayan na yi ƙoƙarin in daina shan giya har na tsawon shekara biyu da rabi,” in ji ta, “sai na fara yin tunani cewa wataƙila shan kwalba guda zai dace, domin in ga yadda zan magance matsalar. Amma duk lokacin da na ji haka, sai in yi addu’a ga Jehovah. Na ƙudurta cewa ba zan ƙara shan giya ba har sai sabuwar duniya, wataƙila har a can ma.” Daina shan giya zai fi dacewa maimakon ka rasa rai a sabuwar duniya ta Allah.—2 Bitrus 3:13.
“Ku yi ta Gudu Hakanan, don Ku Ci”
21, 22. Wace tangarɗa ce za ta iya hana mu kai wa ƙarshen tseren da muke yi na rai, kuma yaya za mu iya guje wa hakan?
21 Sa’ad da yake kamanta ran Kirista da gudu, ko gasa, manzo Bulus ya ce: “Ashe, ba ku sani ba, a wajen tsere dukan masu gudu suna ƙoƙarin tsere wa juna, amma ɗaya ne kaɗai ke samun kyautar cin? To, sai ku yi ta gudu hakanan, don ku ci. Duk masu wasan gasa sukan hori kansu ta kowane hali. Su kam, suna yin haka ne, don su sami lada mai lalacewa, mu kuwa marar lalacewa. To, ni ba gudu nake yi ba wurin zuwa ba, dambena kuwa ba naushin iska nake yi ba. Amma ina azabta jikina ne, don in bautar da shi, kada bayan na yi wa waɗansu, wa’azi, ni kaina a soke ni.”—1 Korantiyawa 9:24-27.
22 Waɗanda suka gama tsere ne za su sami lada. A tseren rai, yin maye na iya hana mu kai wa ƙarshen tseren. Dole ne mu kame kanmu. Yin gudu da tabbaci na bukatar kada mu ‘bugu.’ (1 Bitrus 4:3) Akasarin haka, muna bukatan mu kame kanmu a kowane abu. Idan ya zo batun shan giya, hikima ce mu “ƙi rashin bin Allah da mugayen sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi zamanmu . . . da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah.”—Titus 2:12.
[Hasiya]
a Kamar yadda yake a cikin wannan talifin, ruwan inabi na nufin giya.
Ka Tuna?
• Menene yin maye?
• Wane lahani ne ake samu ta yin maye?
• Ta yaya za ka kauce wa haɗarurruka na yin maye?
• Ta yaya mutum zai iya magance matsalar yin maye?
[Hoto a shafi na 29]
Ka shawarta da wuri iyaka yadda za ka sha
[Hoto a shafi na 30]
Ka riƙa yin addu’a ga Jehovah a kowane lokaci game da kumamancinka