Za A Iya Yin Nasara A Aure A Duniya Ta Yau
“Ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala ke ƙulluwa a cikinta.”—Kolosiyawa 3:14.
1, 2. (a) Menene game da ikilisiyar Kirista yake da ban ƙarfafa? (b) Menene ake bukata don a yi nasara a aure?
IDAN muka duba waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista, ba abu mai daɗaɗa rai ba ne mu ga ma’aurata da yawa da suke da aminci ga abokan aurensu na shekara 10, 20, 30, ko kuma fiye da haka? Sun manne wa abokan aurensu har a lokaci mai wuya ma.—Farawa 2:24; Karin Magana 18:24.
2 Yawancin mutane za su yarda cewa sun sami ɗan matsala a aurensu. Wata mai lura da ayyukan mutane ta rubuta: “Waɗanda suke farin ciki a aurensu su ma suna da damuwa. Da lokacin farin ciki da kuma na baƙin ciki . . . Amma . . . waɗannan mutane sun ci gaba cikin aurensu duk da wahala na rayuwar zamani.” Ma’aurata da suka yi nasara sun koyi yadda ake bi da matsaloli da kuma wahala da matsi da rayuwa ke kawowa, musamman idan suna da yara. Abin da suka fuskanta a rayuwa ya koya wa irin waɗannan ma’aurata cewa ƙauna ta gaske “ba ta ƙarewa har abada.”—1 Korantiyawa 13:8
3. Adadin aure da kashe aure ya nuna menene, waɗanne tambayoyi wannan ya kawo?
3 Akasarin haka, ma’aurata da yawa sun rabu. Wani rahoto ya ce: “Za a kashe rabin dukan aure-aure da aka yi a Amirka a yau. Kuma rabin waɗannan kashe aure za su faru ne cikin shekara 7 da watanni takwas bayan auren . . . Cikin mutane kashi 75 da suka sake aure, kashi 60 bisa ɗari za su sake kashe auren.” Har a ƙasashe da dā ba sa yawan kashe aure a yanzu adadin ya ƙaru. Alal misali, a Japan, adadin kashe aure ya ƙaru ninki biyu a shekarun baya bayan nan. Menene ke jawo wannan yanayin da wani lokaci yake shafan waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista? Menene ake bukata don a yi nasara a aure ko da Shaiɗan yana ƙoƙari ya yi wa wannan tsarin zagon ƙasa?
Tarko da Za a Kauce Wa
4. Waɗanne abubuwa ne za su iya kawo matsala cikin aure?
4 Kalmar Allah ta taimake mu mu fahimci abubuwa da ke kawo matsala cikin aure. Alal misali, ka yi la’akari da kalmomin manzo Bulus game da yanayi da zai kasance a wannan kwanaki na ƙarshe: “A zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai. Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zage-zage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka, da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta, da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah, suna riƙe da siffofin ibada, amma suna saɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.”—2 Timoti 3:1-5.
5. Me ya sa ‘mai sonkai’ zai sa farin ciki na aurensa cikin haɗari, wane gargaɗi Littafi Mai Tsarki ya ba da game da wannan?
5 Idan mun bincika kalmomin Bulus, za mu ga cewa da yawa cikin abubuwa da ya tsara za su iya ɓata dangantaka ta aure. Alal misali, “masu sonkai” ba sa damuwa da wasu. Maza ko mata da suke son kansu kawai na ƙudura aniya su samu abin da suke so. Ba sa so su bar abin da suke so domin wani. Shin irin wannan hali zai kawo farin ciki a aure? Ko kaɗan. Manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci, har da ma’aurata: “Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali’u, kowa na mai da ɗan’uwansa ya fi shi. Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula, har da ta ɗan’uwansa ma.”—Filibiyawa 2:3, 4.
6. Ta yaya son kuɗi zai lalata nasaba na aure?
6 Son kuɗi zai iya kawo matsala tsakanin mata da miji. Bulus ya yi kashedi: “Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su faɗa tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda ke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da halaka. Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukan rai.” (1 Timoti 6:9, 10) Sakamako na baƙin ciki da Bulus ya yi kashedi a kai yana faruwa cikin aurace-aurace da yawa a yau. Ma’aurata da yawa suna ƙyaliya da bukatun abokan aurensu, har da biyan bukatar motsin rai da abokantaka mai daɗaɗa rai a kai a kai, don neman kuɗi.
7. A wasu yanayi, wane hali ne ke kawo rashin aminci cikin aure?
7 Bulus ya kuma ce a wannan zamanin ƙarshe wasu za su zama “marasa tsarkaka, da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci.” Wa’adi na aure ya kamata ya kawo gami na dindindin, ba cin amana ba. (Malakai 2:14-16) Amma wasu sun mai da soyayyarsu ga waɗanda ba abokiyar aurensu ba ce. Wata mata a shekarunta na 30 da mijinta ya bar ta, ta yi bayani cewa kafin ya bar gida, ya soma nuna so ga wasu mata. Ya ƙi ya yarda cewa wannan halin bai dace da mai aure ba. Ta yi baƙin ciki sosai da ta fahimci abin da yake faruwa kuma ta yi ƙoƙari ta yi masa gargaɗi cewa yana bin mummunar tafarki. Duk da haka ya yi zina. Ko da an yi masa gargaɗi, ba ya son ya saurara. Sai ya faɗa cikin wannan tarko.—Karin Magana 6:27-29.
8. Menene zai sa mutum ya yi zina?
8 Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi sarai game da zina! “Mazinaci marar hankali ne, gama hallaka kansa yake yi.” (Karin Magana 6:32) Ba a yin zina nan da nan bisa motsin rai. Yadda Yakubu marubucin Littafi Mai Tsarki ya nuna, ana zina bayan an yi sha’awarta ƙwarai. (Yakubu 1:14, 15) Sannu-sannu mazinacin zai daina kasancewa da aminci ga abokiyar aurensa da ya ko ta yi wa’adi za su yi rayuwa tare. Yesu ya ce: “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita.”—Matiyu 5:27, 28.
9. Menene darasin da ke cikin gargaɗi na Karin Magana 5:18-20?
9 Saboda haka, littafin Ƙarin Magana ya faɗi tafarki mai kyau da za a bi cewa: “Saboda haka ka yi farin ciki tare da matarka, ka yi murna da budurwa da ka auro, kyakkyawa mai kyan gani kamar barewa, bari kyanta ya ɗau hankalinka. Bari ƙaunarta ta kewaye ka. Ɗana, don me za ka fi son matar wani? Don me za ka bar matar wani ta lallame ka da daɗin bakinta?”—Karin Magana 5:18-20.
Kada Ka Yi Hanzarin Aure
10. Me ya sa yake da kyau mu mai da hankali mu san wadda za mu aura?
10 Za a samu matsala cikin aure sa’ad da ma’aurata suka yi aure cikin hanzari. Mai yiwuwa ba su kai yin aure ba kuma ba su da wayo. Wataƙila ba su mai da hankali su san juna da kyau ba. Wato su san abin da suke so da abin da ba sa so, makasudinsu a rayuwa, da yadda iyalansu suke. Ya fi kyau a mai da hankali a san wadda za ta zama abokiyar aure. Ka tuna da Yakubu, ɗan Ishaku. Ya yi wa wanda zai zama surukinsa aiki na shekara bakwai kafin a yarda ya auri Rahila. Yana shirye ya yi hakan domin yana sonta da gaske, ba kyaun siffarta ba.—Farawa 29:20-30.
11. (a) Waɗanne abubuwa ne aure ya ƙunsa? (b) Me ya sa yin magana da ya dace yake da muhimmanci cikin aure?
11 Aure ba soyayya ba ne kawai. Gami na aure na haɗa mutane biyu daga wurare, da kuma masu halaye dabam dabam. Sosuwar zuciyarsu ya bambanta, kuma sau da yawa iliminsu ya sha bambam. Wani lokaci ya ƙunshi haɗa al’adu da harsuna biyu. Ban da wannan ma, yana gama mutane biyu masu ra’ayi dabam dabam a kan dukan iri-irin al’amura. Waɗannan ra’ayoyi su ne sashe na musamman na aure. Za a iya kushe wa ko kuma a riƙa gunaguni a kai a kai sa’ad da ake furta waɗannan ra’ayoyi, zai iya zama da ban ƙarfafa kuma. Hakika, ta kalmominmu za mu iya sa abokin aurenmu baƙin ciki ko kuma mu ƙarfafa shi. Magana da garaje zai iya kawo damuwa cikin aure.—Karin Magana 12:18; 15:1, 2; 16:24; 21:9; 31:26.
12, 13. Me ya sa mutum zai bukaci abin da zai yiwu a aure?
12 Saboda haka, yana da kyau mu ba da lokaci sosai mu san wadda za mu aura. Wata ’yar’uwa Kirista da ta ƙware ta ce: “Idan kana bincika wadda za ka aura, ka yi tunanin halaye goma masu muhimmanci da kake so ta kasance tana da su. Idan tana da bakwai, ka tambayi kanka, “Ina shirye na ƙyale sauran ukun da ba ta da su? Zan iya jimrewa da waɗannan kasawar kowace rana?’ Idan kana shakkar kanka, ka dakata ka sake tunani.” Amma, mu nemi abubuwa masu yiwuwa. Idan kana son ka yi aure, ka san cewa ba za ka taɓa samun kamiltacciyar mace ba. Kuma wadda za ka aura ita ma ba za ta samu kamiltaccen namiji ba!—Luka 6:41.
13 Aure ya ƙunshi sadaukarwa. Bulus ya nuna wannan sa’ad da ya ce: “Ina so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure yakan tsananta kula da sha’anin Ubangiji, yadda zai faranta wa Ubangiji rai. Mutum mai aure kuwa yakan tsananta kula da sha’anin duniya ne, yadda zai faranta wa mata tasa rai. Hankalinsa ya rabu biyu ke nan. Mace marar aure, ko budurwa, takan tsananta kula da sha’anin Ubangiji, yadda za ta kasance tsattsarka a jiki, da kuma rai. Mace mai aure kuwa takan tsananta kula da sha’anin duniya, yadda za ta faranta wa mijinta rai.”—1 Korantiyawa 7:32-34.
Abin da Ya Sa Ake Kashe Wasu Aure
14, 15. Waɗanne abubuwa ne ke raunana gami na aure?
14 Wata mata Kirista ba da daɗewa ba ta fuskanci baƙin cikin kashe aure sa’ad da mijinta ya bar ta bayan shekaru 12 na zaman aure kuma ya soma dangantaka da wata mace. Shin ta lura da wasu abubuwa kafin su rabu? Ta ba da bayani: “Ya kai lokacin da ba ya yin addu’a kuma. Ba ya zuwa taro na Kirista da wa’azi don dalilai da ba su da muhimmanci. Sai ya ce ya taƙura ko kuma ya gaji ainun ya zauna tare da ni. Ba zai yi mini magana ba. Ba ya tattauna abubuwa na ruhaniya da ni kuma. Abin baƙin ciki ne da ya zama wani dabam. Ba mutumin da na aura ba.”
15 Wasu ma sun faɗi abubuwa makamancin wannan: ana gane mutum da ke son barin abokiyar aurensa ta rashin ruhaniyarsa, ba ya nazarin Littafi Mai Tsarki, ba ya addu’a, ba ya halartar taron Kirista kuma. A wata sassa, mutane da yawa da suka bar abokiyar aurensu sun daina dangantakarsu da Jehobah. Domin haka ba sa mai da hankali kuma ga batutuwa na ruhaniya. Ba sa ɗaukan cewa Jehobah, Allah ne rayayye. Alkawarin sabuwar duniya ta adalci ba zai ƙara kasancewa da gaske ba. A wasu yanayi, wannan rashin ruhaniya na somawa kafin abokin auren marar aminci ya soma dangantaka a waje.—Ibraniyawa 10:38, 39; 11:6; 2 Bitrus 3:13, 14.
16. Menene ke ƙarfafa aure?
16 Akasarin haka, wasu ma’aurata masu farin ciki sun ce sun yi nasara cikin aurensu ne domin ruhaniyarsu. Suna addu’a tare kuma suna yin nazari tare. Mijin ya ce: “Muna karanta Littafi Mai Tsarki tare. Muna zuwa wa’azi tare. Muna jin daɗin yin abubuwa tare.” Darasin a bayane yake: Kafa dangantaka mai kyau da Jehobah na ƙarfafa aure.
Ku Kasance Masu Gaskiya Kuna Sadawa
17. (a) Waɗanne abubuwa biyu ainihi ke sa a yi nasara cikin aure? (b) Ta yaya Bulus ya kwatanta ƙauna ta Kirista?
17 Da abubuwa biyu kuma da ke sa a yi nasara cikin aure: zama masu gaskiya da kuma magana da juna. Idan mutane biyu suna son juna, ba za su mai da hankali ga kasawar juna ba. Ma’aurata na iya shigan aure da tunanin abubuwa da yawa, wataƙila domin abin da suka karanta a littafin soyayya ko kuma suka kalla a fim. Amma bayan haka sai ma’auratan su fuskanci ainihin aure. Sa’an nan ɗan kasawa ko kuma halaye masu ban haushi za su iya zama babbar matsala. Idan ya kasance hakan, Kiristoci na bukatar su nuna albarkar ruhu, da ƙauna ke cikinta. (Galatiyawa 5:22, 23) Ƙauna tana da iko sosai. Bulus ya kwatanta irin wannan ƙauna ta Kirista yana cewa: “Ƙauna tana sa haƙuri da kirki. . . . Ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo. . . . tana sa daurewa cikin kowane hali, da bangaskiya cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya cikin kowane hali, da jimiri cikin kowane hali.” (1 Korantiyawa 13:4-7) Hakika, ƙauna ta gaskiya tana jimre wa kasawar mutane. Ba ta bukatar kamilta.—Karin Magana 10:12.
18. Ta yaya sadawa za ta ƙarfafa dangantaka?
18 Sadarwa tana da muhimmanci. Ya kamata mata da miji suna magana kuma suna sauraron juna ko shekaru nawa ne suka yi cikin aure. Wani miji ya ce: “Muna faɗan yadda muke ji amma da halin abokantaka.” Ya kamata mata da miji su saurari juna kuma su fahimci abin da ɗayan ba ya son ya faɗa. Da shigewar lokaci, ma’aurata da suke farin ciki suna fahimtar ra’ayin da ba a faɗa ba da kuma sosuwar zuciya da ba a nuna ba. Wasu mata sun ce mazansu ba sa sauraronsu. Wasu maza sun ce matansu suna son a yi taɗi lokacin da bai dace ba. Sadarwa ta ƙunshi juyayi da fahimi. Yana da kyau mata da miji suna sadawa sosai.—Yakubu 1:1.
19. (a) Me ya sa neman gafara zai iya kasancewa da wuya? (b) Menene zai motsa mu mu nemi gafara?
19 Wani lokaci sadarwa ta ƙunshi neman gafara. Ba koyaushe wannan yake da sauƙi ba. Mutum mai tawali’u ne zai yarda da kuskurensa. Amma yana taimako wajen ƙarfafa aure! Neman gafara daga zuciyarmu zai kawar da matsala na nan gaba kuma zai sa a riƙa yafewa kuma a magance matsaloli. Bulus ya ce: “Kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma ku yafe. Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala ke ƙulluwa a cikinta.”—Kolosiyawa 3:13, 14.
20 Tallafa wa juna yana da muhimmanci cikin aure. Ya kamata mata da miji Kirista su amince da juna, su kuma dogara ga juna. Kada su rena juna ko kuma a wasu hanyoyi su rage darajar juna. Ya kamata muna yaba wa abokan aurenmu; kada mu zarge su. (Karin Magana 31:28b) Ba za mu rage darajarsu ba ta wajen mai da su kamar wawaye da kuma ta wajen zancen banza. (Kolosiyawa 4:6) Suna iya ƙarfafa juna ta wajen furta kalmomin soyayya a kai a kai. Faɗa kalmomin soyayya irinsu: “Har ila ina son ki. Ina farin ciki kina tare da ni.” Irin waɗannan abubuwa ne za su ƙarfafa dangantaka kuma su sa a yi nasara cikin aure a duniya ta yau. Da wasu har ila, talifi na gaba zai ba da ƙarin ja-gora ta Nassi a yadda za a yi nasara cikin aure.a
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani, ka dubi littafin nan Asirin Farinciki na Iyali, da Shaidun Jehobah suka wallafa.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Waɗanne abubuwa suke halaka aure?
• Me ya sa yin aure cikin hanzari ba shi da kyau?
• Ta yaya ruhaniya ke shafan aure?
• Waɗanne abubuwa ne ke ƙarfafa aure?
20. Ta yaya Kirista zai yi sha’ani da abokiyar aurensa a ɓoye da kuma a gaban mutane?
[Hoto a shafi na 18]
Aure ba dangantaka na soyayya ba ne kawai
[Hotuna a shafi na 20]
Dangantaka na ruhaniya da Jehobah na taimakon ma’aurata su yi nasara cikin aure