Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 9/1 pp. 14-19
  • Dokar Ƙauna A Zukata

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dokar Ƙauna A Zukata
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dokar da Aka Rubuta a Cikin Zuciya
  • Dokokin da Aka Kafa Bisa Ƙauna
  • Nuna Ƙauna na Nufin Yin Biyayya
  • Nuna Ƙauna
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Abin Da Ake Nufi Da Mu Ƙaunaci Makwabcinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Kaunar Allah Ke Nan”
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 9/1 pp. 14-19

Dokar Ƙauna A Zukata

“Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu.”—IRMIYA 31:33.

1, 2. (a) Menene za mu tattauna yanzu? (b) Ta yaya ne Jehobah ya bayyana kansa a Dutsen Sinai?

A TALIFAI biyu na baya, mun koyi cewa sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai, fuskarsa na ta yin annuri wadda ke nuna ɗaukakar Jehobah. Mun kuma tattauna game da lulluɓin da Musa ya yi. Bari yanzu mu tattauna wani batu da ya jitu da wannan da ke da ma’ana ga Kiristoci a yau.

2 Sa’ad da Musa yake kan dutsen, Jehobah ya ba shi umurni. Isra’ilawan da suka taru a ƙarƙashin Dutsen Sinai, sun shaida bayyanar Allah mai ban mamaki. “Aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da ke cikin zango suka yi rawar jiki. . . . Hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sinai duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuke, ya yi sama kamar na wurin narka ma’adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.”—Fitowa 19:16-18.

3. Ta wace hanya ce Jehobah ya bai wa Isra’ila Dokoki Goma, kuma menene wannan al’ummar ta fahimta?

3 Jehobah ya yi wa mutanen magana ta mala’ika, kuma ya yi musu tanadin Dokoki Goma. (Fitowa 20:1-17) Babu shakka, waɗannan dokokin sun zo ne daga wajen Maɗaukaki Duka. Bayan haka, Jehobah ya rubuta waɗannan dokokin a kan allunan dutse, allunan da Musa ya fasa sa’ad da ya ga Isra’ilawa suna bauta wa gunkin ɗan maraƙi. Jehobah ya sake rubuta dokokin a kan dutse. A wannan lokacin, fuskar Musa tana annuri sa’ad da ya sauƙo daga kan dutsen dauke da allunan. Dukansu sun fahimci cewa waɗannan dokokin suna da muhimmanci sosai.—Fitowa 32:15-19; 34:1, 4, 29, 30.

4. Me ya sa Dokoki Goma suke da muhimmanci sosai?

4 An saka alluna biyun da aka rubuta Dokoki Goma a cikin akwatin alkawari da ke cikin wuri Mafi Tsarki na mazauni, daga baya kuma a cikin haikali. Dokokin da suke ɗauke da ita sun ambata ainihin mizanan Dokar alkawari ta Musa, kuma sun ambata hanyoyin da Allah zai mulki al’ummar Isra’ila. Sun ba da tabbacin cewa Jehobah yana hulɗa ne da ainihin zaɓaɓɓun mutane.

5. A waɗanne hanyoyi ne dokar Allah ga Isra’ilawa ta nuna ƙaunarsa?

5 Waɗannan dokokin sun bayyana abubuwa masu yawa game da Jehobah, musamman ma ƙaunarsa ga mutanensa. Wannan kyauta ce mai tamani ga waɗanda suka yi biyayya da su! Wani masani ya rubuta: “Babu wani tsari na ɗabi’a da mutane suka kafa, . . . da ya yi daidai ko kuma da ya kusanci waɗannan kalamai goma na Allah.” Game da Dokar Musa gabaki ɗaya, Jehobah ya ce: “In za ku yi biyayya da ni, ku kuma kiyaye maganata, za ku zama mutanena. Dukan duniya tawa ce, amma ku za ku zama zaɓaɓɓiyar jama’ata. Za ku zama daular firistoci da al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.”—Fitowa 19:5, 6.

Dokar da Aka Rubuta a Cikin Zuciya

6. Wace doka ce ta fi dokokin da aka rubuta a kan dutse tamani?

6 Hakika, waɗannan hurarrun dokokin suna da tamani sosai. Ka sani kuwa cewa shafaffun Kiristoci suna da wani abu da ya fi dokokin da aka rubuta a kan dutse tamani? Jehobah ya annabta kafa sabon alkawari wanda ya bambanta da Dokar alkawarin da ya yi da al’ummar Isra’ila. “Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu.” (Irmiya 31:31-34) Yesu, wanda shi ne Matsakanci na sabon alkawari, bai ba da rubutaccen tsarin doka ga mabiyansa ba. Ya saka dokar Jehobah cikin zukatan almajiransa ta wajen abin da ya yi da abin da ya ce.

7. Su wanene aka fara bai wa “shari’ar Almasihu,” kuma su wanene suka bi ta daga baya?

7 Ana kiran wannan dokar “shari’ar Almasihu.” An fara ba da wannan dokar ce ga al’umma ta ruhaniya, wato, “Isra’ilan gaske na Allah,” ba ga al’ummar Isra’ila zuriyar Yakubu ba. (Galatiyawa 6:2, 16; Romawa 2:28, 29) Isra’ilan Allah sune Kiristocin da aka shafa da ruhu. Bayan haka, “ƙasaitaccen taro” daga dukan al’ummai waɗanda suke son su bauta wa Jehobah, suka bi su. (Wahayin Yahaya 7:9, 10; Zakariya 8:23) A matsayinsu na “tumaki” guda ƙarƙashin “makiyayi . . . guda,” rukunonin biyu sun sumbaci “shari’ar Almasihu,” sun ƙyale ta ta shugabanci dukan abin da suke yi.—Yahaya 10:16.

8. Wane bambanci ne ke akwai tsakanin Dokar Musa da kuma dokar Kristi?

8 Ba kamar Isra’ilawa waɗanda suke bin Dokar Musa domin an haife su a cikin al’ummar Isra’ila ba, Kiristoci suna ƙarƙashin dokar Kristi domin sun zaɓi su yi haka. A nan ƙabila ko kuwa wurin haihuwa ba shi da amfani. Sun koyi game da Jehobah da hanyoyinsa kuma suna ɗokin yin nufinsa. Tun da yake suna da dokar Allah “a cikinsu,” rubuce a alamance “a zukatansu,” shafaffun Kiristoci ba wai suna yi wa Allah biyayya ba ne domin zai hori waɗanda suka yi masa rashin biyayya; kuma ba wai suna yi masa biyayya ba ne kawai domin an ce su yi. Biyayyarsu ta kafu ne a wani abu mai muhimmanci sosai da kuma iko, kuma waɗansu tumaki suna yin biyayya ne domin suna da dokar Allah a zukatansu.

Dokokin da Aka Kafa Bisa Ƙauna

9. Ta yaya ne Yesu ya nuna cewa ƙauna ce abu mafi muhimmanci a cikin dokokin Jehobah?

9 Za a iya taƙaita muhimmancin duka dokokin Jehobah da kuma mizanansa da kalma ɗaya: ƙauna. Wannan sashe ne kuma zai ci gaba da kasancewa sashen bauta ta gaskiya. Sa’ad da aka tambaye shi Dokar da ta fi girma, Yesu ya amsa: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.” Na biyun ita ce, “Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.” Sai ya ce: “A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.” (Matiyu 22:35-40) Yesu ya nuna cewa Dokoki Goma da kuma dukan Nassosin Ibrananci sun dangana ne a kan ƙauna.

10. Ta yaya muka sani cewa ƙauna ita ce cibiyar dokar Kristi?

10 Ƙaunar Allah da kuma maƙwabta suna cikin muhimman dokar da ke cikin zukatan Kiristoci? Hakika! Dokar Kristi ta ƙunshi ƙaunar Allah daga zuciya, kuma ta ƙunshi sabuwar doka, wato, Kiristoci su kasance da ƙauna na saɗaukar da kai ga juna. Ya kamata su ƙaunaci juna kamar yadda Yesu ya ƙaunaci almajiransa, kuma ya ba da ransa da son rai domin abokansa. Yesu ya koya wa almajiransa cewa su ƙaunaci Allah da kuma junansu, kamar yadda shi ya ƙaunace su. Ƙaunar da suke nuna wa juna, ita ce ainihin halin da zai sa a gane Kiristoci na gaskiya. (Yahaya 13:34, 35; 15:12, 13) Yesu ya umarce su su ƙaunaci maƙiyansu.—Matiyu 5:44.

11. Ta yaya ne Yesu ya nuna ƙauna ga Allah da kuma mutane?

11 Yesu ya kafa kamiltaccen misali ta nuna ƙauna. A matsayinsa na babban halittan ruhu a sama, ya karɓi damar faɗaɗa bukatun Ubansa a duniya. Ban da ransa da ya bayar domin mutane su sami rai madawwami, ya nuna wa mutane yadda za su yi rayuwa. Yana da tawali’u, alheri, taimako, ya taimaka wa gajiyayyu da waɗanda aka zalunta. Ya faɗi “maganar rai madawwami,” kuma ya taimaka wa mutane su san Jehobah.—Yahaya 6:68.

12. Me ya sa za mu iya cewa ƙaunar Allah da na maƙwabta ba su da bambanci?

12 Ba a iya bambance ƙaunar Allah da ta maƙwabta. Manzo Yahaya ya ce: “Ƙauna ta Allah ce. . . . Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da ya ke gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai ma taɓa gani ba.” (1 Yahaya 4:7, 20) Jehobah shi ne tushen ƙauna. Ƙauna ce ke rinjayar dukan abin da yake yi. Muna nuna ƙauna domin an halicce mu a siffarsa. (Farawa 1:27) Ta wajen nuna ƙauna ga maƙwabtanmu, muna nuna ƙaunarmu ga Allah.

Nuna Ƙauna na Nufin Yin Biyayya

13. Idan muna so mu ƙaunaci Allah, menene ya kamata mu yi da farko?

13 Ta yaya za mu ƙaunaci Allah, wanda ba ma gani? Mataki na musamman na farko, shi ne saninsa. Ba za mu iya ƙauna ko mu amince da baƙo ba. Da haka, Kalmar Allah ta ƙarfafamu mu san Allah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki, ta wajen addu’a, da kuma yin tarayya da waɗanda suka san shi kuma suke ƙaunarsa. (Zabura 1:1, 2; Filibiyawa 4:6; Ibraniyawa 10:25) Linjila huɗun suna da tamani sosai, domin sun bayyana halin Jehobah kamar yadda rayuwa da kuma hidimar Yesu Kristi suka nuna. Muradinmu na yin biyayya ga Allah da kuma yin koyi da halinsa na daɗa ƙarfi yayin da muka san shi kuma muka nuna godiya ga ƙaunar da ya nuna mana. Hakika, ƙaunar Allah ta ƙunshi yin biyayya.

14. Me ya sa za mu iya cewa dokokin Allah ba matsananta ba ne?

14 Idan muka ƙaunaci mutane, za mu san abin da suke so da abin da ba sa so, kuma za mu bi da su haka. Ba ma son mu ɓata wa waɗanda muke ƙauna rai. Manzo Yahaya ya rubuta: “Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne.” (1 Yahaya 5:3) Ba matsananta ba ne, kuma ba su da yawa. Ƙauna ce ke yi mana ja-gora. Ba ma bukatar mu haddace dokoki masu tsanani da za su yi mana ja-gora; ƙaunar Allah ce za ta yi mana ja-gora. Dokokin Allah ba matsananta ba ne, domin muna farin cikin yin hidima ga waɗanda muke ƙauna da gaske. Za mu so yin nufin Allah idan muna ƙaunarsa. Da haka, za mu sami amincewar Allah, za mu amfani kanmu, kuma ja-gorarsa za ta amfane mu sosai.—Ishaya 48:17.

15. Menene zai motsa mu mu yi koyi da Jehobah? Ka ba da bayani.

15 Ƙaunar Allah tana motsa mu mu yi koyi da halayensa. Idan muna ƙaunar mutum, mukan so halayensa da kuma zama kamarsa. Yi la’akari da dangantakar da ke tsakanin Jehobah da Yesu. Wataƙila suna tare a sama na biliyoyin shekaru. Suna ƙaunar juna sosai. Yesu ya yi kama da Ubansa na samaniya sosai har ya gaya wa almajiransa cewa: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.” (Yahaya 14:9) Yayin da muke ƙara sani da kuma nuna godiya ga Jehobah da Ɗansa, za mu motsa mu zama kamarsu. Ƙaunarmu ga Jehobah, tare da taimakon ruhunsa mai tsarki, zai sa mu ‘yar da halinmu na dā da ayyukansa, mu ɗau sabon halin nan da ake sabontawa.’—Kolosiyawa 3:9, 10; Galatiyawa 5:22, 23.

Nuna Ƙauna

16. Ta yaya ne muke nuna ƙauna ga Allah da kuma maƙwabta ta wajen wa’azi da aikinmu na koyarwa?

16 Mu Kiristoci muna ƙyale ƙaunar Allah da maƙwabta ta motsa mu mu saka hannu a wa’azin Mulki da kuma aikin almajirantarwa. Da haka, muna faranta wa Jehobah Allah zuciya, “wanda ke son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” (1 Timoti 2:3, 4) Ta haka, za mu sami farin cikin taimaka wa wasu su rubuta dokar Kristi a zukatansu. Kuma za mu yi farin cikin ganin yadda halayensu ke canjawa domin su nuna hurarrun halayen Jehobah. (2 Korantiyawa 3:18) Hakika, taimaka wa wasu su san Allah, shi ne kyauta mafi tamani da za mu iya ba su. Waɗanda suka yi abota da Jehobah za su sami farin ciki har abada.

17. Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙaunaci Allah da kuma maƙwabta fiye da abin duniya?

17 Muna raye ne a duniyar da ake son abin duniya ake kuma daraja shi. Duk da haka, abin duniya ba za su kasance har abada ba. Ana iya sace su ko kuwa su lalace. (Matiyu 6:19) Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi: “Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.” (1 Yahaya 2:16, 17) Hakika, Jehobah zai dawwama har abada da kuma waɗanda suke ƙaunarsa da kuma bauta masa. Saboda haka, bai fi muhimmanci ba mu ƙaunaci Allah da kuma mutane fiye da biɗan abin duniya, wanda abu ne na ɗan ƙanƙanin lokaci?

18. Ta yaya ne wata mai wa’azi na ƙasar waje ta nuna ƙauna na saɗaukar da kai?

18 Waɗanda suke biɗan ƙauna suna ɗaukaka Jehobah. Yi la’akari da Sonia, wadda mai wa’azi ce na ƙasan waje a Sinigal. Ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata mai suna Heidi, wadda ta kamu da cutar ƙanjamau daga mijinta wanda ba mai bi ba ne. Bayan mutuwar mijinta, Heidi ta yi baftisma, bayan haka, ta soma rashin lafiya, kuma an kwantar da ita a asibiti ɗauke da Cutar Kanjamau. Sonia ta ce: “Ma’aikatan asibitin sun yi iya ƙoƙarinsu, amma ba su da yawa. An kira waɗanda suke cikin ikilisiya domin su kula da bukatunta a asibitin. A dare na biyu, na zauna a kan tabarma kusa da gadonta kuma na kula da ita har sa’ad da ta cika. Likitan da ke wurin ya ce: ‘Babban matsalarmu ita ce, ’yan’uwa suna gudun ’yan’uwansu idan suka sani cewa suna ɗauke da Cutar Kanjamau. Me ya sa ke da ba ki da dangantaka da ita, ba ƙasar ku ɗaya ba, kuma ba launin ku ɗaya, ki ka yarda ki sa kanki cikin wannan haɗari?’ Na bayyana masa cewa a nawa ra’ayin, Heidi ’yar’uwata ce sosai kamar uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya. Domin dangantakata da Heidi, wadda kamar ’yar’uwa take a gare ni, na ɗauka abin farin ciki ne in kula da ita.” Kuma Sonia ba ta ɗauki cuta ba daga kula ta ƙauna da ta yi wa Heidi.

19. Tun da yake muna da dokar Allah a zukatanmu, wane zarafi ne muke da shi?

19 Za a iya samun yawancin misalan ƙauna na saɗaukar da kai a tsakanin bayin Jehobah. Babu wani rubutaccen tsarin doka da ke bayyana mutanen Allah a yau. Maimako, mun ga cikar abin da aka rubuta a Ibraniyawa 8:10: “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da jama’ar Isra’ila, bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, wato zan sa shari’una a birnin zuciyarsu, in kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan kasance Allahnsu, su kuma su kasance jama’ata.” Bari mu ci gaba da daraja doka ta ƙauna da Jehobah ya riga ya rubuta a zukatanmu, kuma mu yi amfani da kowane zarafi mu nuna ƙauna.

20. Me ya sa dokar Kristi dukiya ce marar kima?

20 Abin farin ciki ne mu bauta wa Allah tare da ’yan’uwanmu na dukan duniya da suke nuna irin wannan ƙaunar! Waɗanda suke da dokar Kristi a zukatansu suna more wata dukiya marar kima a wannan duniyar da babu ƙauna. Suna morar ƙaunar Jehobah kuma suna son gamin ƙauna mai ƙarfi na ’yan’uwantakarsu. “Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, ga jama’ar Allah su zauna tare kamar ’yan’uwa!” Ko da yake Shaidun Jehobah suna zaune ne a ƙasashe da yawa, suna yin yare dabam dabam, da kuma al’adu dabam dabam, suna morar haɗin kai na addini da ba shi da na biyu. Wannan haɗin kan na kawo alherin Jehobah. Mai zabura ya rubuta cewa: “A can ne [cikin mutane masu haɗin kai cikin ƙauna] Ubangiji ya alkawarta albarkarsa, rai na har abada.”—Zabura 133:1-3.

Za Ka Iya Amsawa?

• Menene muhimmancin Dokoki Goma?

• Mecece dokar da aka rubuta a zukata?

• Wane matsayi ne ƙauna ke da shi a “shari’ar Almasihu”?

• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ƙaunarmu ga Allah da maƙwabta?

[Hoto a shafi na 15]

Isra’ilawa suna da dokar da aka rubuta a kan allunan dutse

[Hotuna a shafi na 16]

Kiristoci suna da dokar Allah a zukatansu

[Hoto a shafi na 18]

Sonia da wata yarinya ’yar Sinigal a taron gunduma na shekara ta 2004

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba