Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 2/1 pp. 27-30
  • Darussa Daga Littafin Nehemiah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Nehemiah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “HAKANAN AKA GAMA GANUWA”
  • (Nehemiah 1:1–6:19)
  • “KA TUNA DA NI, YA ALLAHNA, TARE DA ALHERI”
  • (Nehemiah 7:1–13:31)
  • Samun Albarkar Jehobah na da Muhimmanci!
  • “Ku Rinjayi Mugunta Da Nagarta”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • “Ka Tuna da Ni, Ya Allahna, Tare da Alheri”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ganuwar Urushalima
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ganuwar Urushalima
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 2/1 pp. 27-30

Maganar Jehobah Rayayyiya Ce

Darussa Daga Littafin Nehemiah

SHEKARA goma sha biyu ta shige tun aukuwa na ƙarshe da aka rubuta cikin littafin Ezra na Littafi Mai Tsarki. Lokacin “fitowar doka a maida Urushalima, a gine ta kuma” ya yi kusa, aukuwar da ya nuna somawar makonni 70 na shekaru zuwa lokacin da Almasihu zai zo. (Daniel 9:24-27) Littafin Nehemiah tarihi ne na mutanen Allah game da sake gina garun Urushalima. Yana ɗauke da aukuwa na musamman na fiye da shekaru 12, daga shekara ta 456 K.Z., zuwa wani lokaci bayan shekara ta 443 K.Z.

Gwamna Nehemiya ne ya rubuta littafin, kuma labari ne mai daɗi game da yadda aka ɗaukaka bauta ta gaskiya ta wajen nuna ƙuduri da kuma dogara ƙwarai ga Jehobah Allah. Ya kuma nuna yadda Jehobah ya canja al’amura don ya cika nufinsa. Labari ne kuma game da shugaba mai ƙarfi mai gaba gaɗi. Saƙon littafin Nehemiya ya koyar da darussa masu kyau ga dukan masu bauta ta gaskiya a yau, “gama maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.”—Ibraniyawa 4:12.

“HAKANAN AKA GAMA GANUWA”

(Nehemiah 1:1–6:19)

Nehemiya yana fadar Shushan, yana wa Sarki Artaxerxes Longimanus hidima a matsayi na ɗaukaka. Sa’ad da ya ji labari cewa mutanensa “suna cikin wahala da shan zargi ainu: ganuwar Urushalima ta rushe, ƙofofinta kuma sun ci wuta,” Nehemiya ya damu ƙwarai. Ya yi wa Allah addu’a sosai don ya yi masa ja-gora. (Nehemiah 1:3, 4) Da shigewar lokaci, sarkin ya lura cewa Nehemiya yana baƙin ciki, sai aka ba shi zarafin zuwan Urushalima.

Bayan ya isa Urushalima, Nehemiya ya bincika garun daddare, sai ya gaya wa Yahudawan shirinsa na sake gina garun. Aka soma ginin. Aka kuma soma hamayya ga aikin. Amma don shugabancin Nehemiya da gaba gaɗi, “aka gama ganuwa.”—Nehemiah 6:15.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:1; 2:1—Ƙirgen “shekara ta ashirin” da aka ambata cikin waɗannan ayoyi biyu na nuni ga lokaci ɗaya ne? Hakika, shekara ta ashirin na sarautar sarki Artaxerxes ne. Amma yadda aka yi ƙirge a waɗannan ayoyin ya bambanta. Tarihi ya nuna cewa shekara ta 475 K.Z., ne shekara da Artexerxes ya hau gadon sarauta. Tun da yake marubutan Babila suna ƙirga shekarun sarauta na sarakunan Fasiya daga Nisan (Maris/Afrilu) zuwa Nisan, shekarar da Artaxerxes ya hau gadon sarauta ya soma a Nisan 474 K.Z. Saboda haka, shekara ta ashirin na sarauta da aka ambata a Nehemiah 2:1 ya soma a Nisan 455 K.Z. Watan Chislev (Nuwamba/Disamba) da aka ambata a Nehemiah 1:1, wanda ya gabata ne, wato shekara ta 456 K.Z. Nehemiah ya kuma nuna cewa wannan watan ya faɗa a shekara ta ashirin na sarautar Artaxerxes. Wataƙila a wannan yanayin yana ƙirga shekarun daga watan da sarkin ya hau gadon sarauta. Mai yiwuwa kuma cewa Nehemiah yana amfani da tsarin ƙirgen da Yahudawa a yau suke kira shekarar ’yanci da yake somawa a watan Tishri, da ya yi daidai da Satumba/Oktoba. Ko yaya dai, shekarar 455 K.Z, ne aka ba da umurni a sake gina Urushalima.

4:17, 18—Ta yaya mutum zai yi aikin gini da hannu ɗaya kawai? Wannan ba matsala ba ce ga masu ɗaukan kaya. Muddin aka ɗaura kayan a kansu ko kuma kafaɗarsu, za su iya daidaita kayan da hannu ɗaya “ɗayan hannu kuma yana riƙe da makaminsa.” Maginan da suke bukatar su yi aikinsu da hannu biyu “kowane yana da takobinsa a rataye gareshi, da hakanan ya yi gini.” A shirye suke su kāre kansu idan magabtan suka kai musu hari.

5:7—A wane azanci ne Nehemiya ya soma “faɗa kuma da hakimai da mahukumta”? Waɗannan mutanen suna taka Dokar Musa ta wajen karɓan ruwa daga ’yan’uwansu Yahudawa. (Leviticus 25:36; Kubawar Shari’a 23:19) Bugu da ƙari, ruwan da masu ba da bashin suke karɓa yana da yawa. Idan suka bukaci wannan kowane wata, “kashi ɗaya na ɗari” zai yi daidai da kashi 12 na ɗari a shekara. (Nehemiah 5:11) Zalunci ne a ɗora wa mutane da suke da nauyin biyan haraji da kuma ƙarancin abinci wannan. Nehemiya ya soma faɗa da mawadatan ta wajen yin amfani da Dokar Allah ya tsauta musu kuma ya fallasa laifinsu.

6:5—Tun da yake ana saka wasiƙu na asiri cikin jaka da ke rufe, me ya sa Sanballat ya aika wa Nehemiya “wasiƙa a buɗe”? Mai yiwuwa Sanballat yana da nufin ya bayyana tuhumar ƙaryar da ke cikin wasiƙar a fili ta wajen aika ta a buɗe. Wataƙila yana tsammanin wannan zai sa Nehemiya fushi sosai ya bar aikin gini kuma ya kāre kansa. Ko kuma Sanballat yana tunani cewa abubuwa da ke cikin wasiƙar za su kawo hargitsi tsakanin Yahudawa ya sa su daina aikinsu. Nehemiya ya ƙi ya tsorata kuma ya ci gaba da aikin da Allah ya ce ya yi.

Darussa Dominmu:

1:4; 2:4; 4:4, 5. Sa’ad da muka fuskanci yanayi mai wuya ko kuma tsai da shawara mai muhimmanci, ya kamata mu “lizima cikin addu’a” kuma mu aikata daidai da ja-gora ta tsarin Allah.—Romawa 12:12.

1:11–2:8; 4:4, 5, 15, 16; 6:16. Jehobah yana amsa addu’a da bayinsa suke yi daga zuciyarsu.—Zabura 86:6, 7.

1:4; 4:19, 20; 6:3, 15. Ko da yake Nehemiya mutumi ne mai juyayi, ya kafa misali mai kyau na mutum mai aikatawa da gaba gaɗi don adalci.

1:11–2:3. Ainihin abin da ke sa Nehemiah farin ciki ba matsayinsa mai girma na mai shayarwa ba. Amma yana son a faɗaɗa bauta ta gaskiya. Ainihin damuwarmu da kuma dalilin farin cikinmu ya kamata ya zama bautar Jehobah da kuma yin kome da zai gabatar da ita.

2:4-8. Jehobah ya sa Artaxerxes ya ba Nehemiah izini ya je ya sake gina garun Urushalima. “Zuciyar sarki tana hannun Ubangiji kamar magudanan ruwaye,” in ji Misalai 21:1. “Yan kan juya ta dukan inda ya ga dama.”

3:5, 27. Bai kamata mu ji ba za mu iya yin aikin da ake yi game da bauta ta gaskiya, kamar “hakiman” Tekoiyawa ba. Maimakon haka, za mu iya yin koyi da Tekoiyawa da suka ba da kansu da yardan rai.

3:10, 23, 28-30. Yayin da wasu suka ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu shelar Mulki sosai, yawancinmu na tallafa wa bauta ta gaskiya kusa da gidanmu. Muna iya yin haka ta wajen sa hannu a aikin gina Majami’ar Mulki da kuma tallafa wa kayan agaji amma musamman yin aikin wa’azin Mulki.

4:14. Sa’ad da muka fuskanci hamayya, mu ma za mu sha kan tsoro ta wajen tuna da “mai-girma, mai-ban razana.”

5:14-19. Gwamna Nehemiya misali ne mai kyau na tawali’u, rashin son kai, da kuma hikima ga dattawa Kirista. Ko da yana da himma wajen nanata Dokar Allah, bai sha kan wasu ba don son kai. Maimakon haka, ya nuna ya damu da waɗanda aka zalunta da kuma matalauta. Nehemiya ya kafa misali na musamman ga dukan bayin Allah a wajen nuna karimci.

“KA TUNA DA NI, YA ALLAHNA, TARE DA ALHERI”

(Nehemiah 7:1–13:31)

Jim kaɗan bayan an gama gina garun Urushalima, Nehemiya ya saka ƙofofi kuma ya yi shiri a kāre birnin. Sai ya rubuta tarihin asalin mutanen. Da dukan mutanen suka taru “a cikin filin nan mai-fādi wanda ya ke gaban ƙofar ruwa,” Ezra firist ya karanta littafin Dokar Musa, kuma Nehemiya da Lawiyawa suka bayyana wa mutanen Dokar. (Nehemiah 8:1) Da suka koya game da Idin Bukkoki sai suka yi bikin da farin ciki.

Da aka yi wani biki, a lokacin “zuriyan Isra’ila” suka yi ikirarin zunubansu, Lawiyawan suka sake maimaita sha’anin Allah da Isra’ila, sai mutanen suka yi rantsuwa za su “yi tafiya cikin shari’ar Allah.” (Nehemiah 9:1, 2; 10:29) Tun da yake har ila babu mutane da yawa a Urushalima, an jefa ƙuri’a don mutum ɗaya cikin kowane 10 da ke zama waje da birnin ya shigo ciki. Bayan haka aka keɓe garun da farin ciki har “aka ji motsin farinciki na Urushalima tun daga nesa.” (Nehemiah 12:43) Shekara goma sha biyu bayan isowarsa, Nehemiah ya bar Urushalima ya koma aikinsa wurin Artaxerxes. Ba da daɗewa ba, Yahudawan suka soma bin mummunar ɗabi’a. Da Nehemiya ya koma Urushalima, sai ya aikata don ya gyara yanayin. Ya yi roƙo don kansa: “Ka tuna da ni, ya Allahna, tare da alheri.”—Nehemiah 13:31.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

7:6-67—Me ya sa lissafin Nehemiah na raguwar mutane da suka dawo Urushalima tare da Zarubabel ya bambanta da ƙirgen Ezra na mutum ɗaɗɗaya a kowane iyali? (Ezra 2:1-65) Dalilin wannan bambancin mai yiwuwa domin Ezra da Nehemiya sun yi amfani da littafin asali da ya bambanta ne. Alal misali, adadin waɗanda suka yi rajista su koma ƙasarsu ƙila ya yi dabam da adadin waɗanda ba su koma ba. Mai yiwuwa littattafan sun bambanta domin wasu Yahudawa da suka kasa bayyana asalinsu sun yi haka daga baya. Amma dukan labaran sun jitu a kan abu ɗaya: Adadin waɗanda suka dawo da farko shi ne 42,360 ban da bayi da kuma mawaƙa.

10:34—Me ya sa aka ce mutanen su kawo itace? Dokar Musa ba ta bukaci a ba da hadayar itace ba. Wannan domin bukata ce da ta kama. Ana bukatar itace da yawa domin a ƙone hadayu a kan bagadi. Mai yiwuwa babu isashen ma’aikata da ba Isra’ilawa ba ne da suke hidima na bayi a haikali. Shi ya sa, aka jefa kuri’a don a tabbata an ci gaba da kawo itace.

13:6—Har tsawon wane lokaci ne Nehemiya ya bar Urushalima? Littafi Mai Tsarki ya ce “bayan waɗansu kwanaki,” Nehemiya ya roƙi arziki daga sarki domin ya koma Urushalima. Saboda haka, ba zai yiwu ba a san tsawon lokaci da ya yi tafiya ba. Da ya koma Urushalima, Nehemiya ya iske cewa ba a tallafa wa tsarin firistoci, kuma ba a kiyaye dokar Assabaci. Mutane da yawa sun auri mata daga wasu al’ummai, yaransu ma ba sa yaren Yahudawa. Da yake yanayi ya taɓarɓare sosai ya nuna cewa Nehemiya ya daɗe bai dawo ba.

13:25, 28—Ƙari ga yin “faɗa” da Yahudawa da suka juya wa Allah baya, waɗanne abubuwa ne Nehemiya ya yi don ya gyara yanayin? Nehemiya ya “zage su” ta wajen sanar da su hukuncin da ke cikin Dokar Allah. Ya “bubbuga waɗansu daga cikinsu” wataƙila ta wajen ba da umurni a yi musu hukunci. Don ya nuna ya yi fushi, ya “fizge musu gashinsu.” Ya kuma kori tattaɓa kunne na Babban Firist Eliyashib, wanda ya auri ’yar Sanballat Bahorone.

Darussa Dominmu:

8:8. Da yake mu malaman Kalmar Allah ne, muna ‘ba da fasararta’ ta wajen furta kalmomi sosai da kuma nanatawa da ba da bayanin Nassosi daidai, don a fahimta sarai.

8:10. Muna samun “farinciki na Ubangiji” ta wajen mai da hankali ga bukatunmu na ruhaniya da gamsar da shi da kuma bin ja-gora ta tsarin Allah. Yana da muhimmanci mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, mu riƙa halartan taron Kirista a kai a kai, kuma muna yin wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa da himma!

11:2. Mutum ya bar gadonsa kuma ya ƙaura zuwa Urushalima ya ƙunshi kashe kuɗi da wasu hasara. Waɗanda suka ba da kansu su yi wannan ya nuna halin saɗaukar da kai. Mu ma muna iya nuna irin wannan halin sa’ad da muke da zarafin ba da kanmu mu yi wa wasu hidima a taron gunduma da wasu lokaci.

12:31, 38, 40-42. Rera waƙa hanya ce mai kyau na yabon Jehobah da kuma furta godiyarmu a gare shi. Ya kamata mu rera waƙa da dukan zuciyarmu a taron Kirista.

13:4-31. Dole ne mu mai da hankali kada mu ƙyale abin duniya, ɓatanci, da kuma ridda su shafe mu.

13:22. Nehemiya ya san zai ba da lissafi ga Allah. Mu ma muna bukatar mu sani cewa za mu ba da lissafi ga Jehobah.

Samun Albarkar Jehobah na da Muhimmanci!

Mai Zabura ya rera: “Idan ba Ubangiji ya gina gidan ba, banza magina su ke aiki.” (Zabura 127:1) Littafin Nehemiya ya kwatanta gaskiyar waɗannan kalmomi da kyau!

Darassin a bayane yake a gare mu. Idan muna son mu yi nasara a kowane abu da muke yi, dole ne mu sami albarkar Jehobah. Za mu yi tsammani Jehobah zai albarkace mu ne idan ba mu saka bauta ta gaskiya farko a rayuwarmu ba? Kamar Nehemiya bari mu sa bautar Jehobah da ci gabanta damuwarmu ta musamman.

[Hoto a shafi na 27]

“Zuciyar sarki tana hannun Ubangiji kamar magudanan ruwaye”

[Hoto a shafi na 28]

Nehemiya mutumi mai aikatawa mai juyayi, ya zo Urushalima

[Hotuna a shafuffuka na 29, 30]

Ka san yadda ake ‘fasara’ Kalmar Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba